Gangar jikinsa na aura13
Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 13
A zaure Malam Habu ya shinfida tabarmar kaba da wani yagulallen filo da zanin gado irin na da dinnan shekara aru-aru da suka shude. Nan ne shinfidarsa da yake kwana nan ne dakinsa dan duk sanyi da damuna a nan yake saboda Iya Abu ta mamaye dakunan gidan. Dakinsa din ya barwa Hannah data girma ya dawo zaure don da da tana yarinya tare suke kwana a dakin. Ko yaushe Hannah zaka ganta a zaune a gefen Babanta tana lallabashi tana wayar masa da kai game da makarantarsu. Tana nuna masa muhimmanacin karatu da kuma irin bacin ran da Haisam zaiji idan bata koma ba. Ta kwashe labarun abubuwan da suka faru tun tana aji daya har tazo aji shida yadda Haisam yake kula da ita da irin tataburzar da aka sha yi akanta da dalibai da Malamai har ya kwatar mata *yancinta babu mai dukanta ko zaginta yanzu, kuma yayi alkawarin zai iya kashe ko waye yake son ya takura mata. Malam Habu ya gamsu sosai da bayanan Hannah ya kuma san Haisam ba zai yadda a cuce ta ba.
Hutu ya rage sati guda sai ga Uwar biyu ta dira a garin su Hannah ta iske Hannah da Mahaifinta a zaure a zaune zance daya dai suke ta nanatawa kullum shine zancen ya barta ta koma makaranta. Bayan sun gaisa da Uwar biyu ta fadi abunda ke tafe da ita cewar tazo ne ta tafi da Hannah hutu ya kare sai Malam Habu ya kekashe idanuwansa ya ce shifa babu inda Hannah zata je. Hannah tayi mamaki da taji ya fadi haka yanzu bayan ya yarda da tayi masa bayani sai kawai Hannah ta rushe da kuka, magiyar duniyar nan Uwar biyu ta dinga yiwa Malam Habu amma yaki yarda daga karshe Uwar biyu tayi musu sallama ta tafi. Tana isa Kazaure ta wuce gidan su Safiyanu abokin Haisam bata same shi ba ance yana Kano sai ta koma gida ta zuba ido ko Allah zai jeho mata Haisam ko Safiyanu idan zasu kawo sayayyar Hannah ta makaranta tunda sunsan hutu ya kare zasu kawo. Har gobe a koma makaranta Uwar biyu bata ga Safiyanu ba balle Haisam. A can kuwa Hannah hankalinta ya gama tashi taji shiru Yaya Haisam baizo ya taya ta rokar Babanta ba, sai ta dauka shima yayi fushi ne ya ce to abar masa *yarsa kar tayi karatun mana. Da la’asar likis Hannah da Mahaifinta suna zaune akan lintsimemiyar tabarmar kaba a zauren kasa da rufin ciyawa Hannah kuka take yau tun da safe. Malam Habu yayi lallashin duniyar nan tayi shiru ta hakura tama cire ranta a makarantar don shi ya gama magana bazata koma makaranta ba. Ta ki ci ta ki sha sai kuka take rafsawa. Kwatsam suka ji sallama daga idon nan da Hannah ta yi sai tayi ido hudu da Yaya Haisam, Safiyanu da Uwar biyu suka yi sallama suka shigo. Da sauri Hannah ta dauko musu tabarma ta shinfida musu suka zazzauna ta koma ta dauko musu ruwa a randa cikin kwanan sha. Ta kawo ta durkusa kasa ta gaishe su ta koma gefe ta zauna. Murna ce ta rufe Malam Habu yama rasa inda zaisa wadannan manyan baki, *yan gayu, ya lalubo kudi a aljihunsa ya ce Hannah tayi maza taje bakin kasuwa ta suyo musu fura da nono, su Haisam suka ce kai haba ai su a koshe suke ya barshi kawai. Bayan sun gaggaisa Malam Habu ya gama yi musu sannu da zuwa da taki ta kare, sai Safiyanu ya nisa ya ce “Baba munzo ne mu ba da hakuri akan dalilin da yasa ka hana Hannah zuwa makaranta, shine muka zo da kanmu mu roke ka Baba duka-duka saura wata nawa ne yanzu Hannah zata gama karatunta ta dawo gida.
Nan da nan Malam Habu ya canja fuskar fara’ar da yake ta gushe ya ce “Wai me yasa kuke sani ina muku kin kyautawa ne? Bana so ku tambaye ni abinda zan kasa baku na gama magana don Allah don Annabi ku bar zancen karatun *yar Baba, na yanke shawara ba zata koma ba. Haisam kokarin da yake Allah Ya saka maka, hakan ma ya isa ba sai ta kara yin wasu watannin ba. Na ce da Uwar biyu ta yi maka godiya ka cika min alkawarin da ka dauka wallahi ko bata karasa ba ai ka cika alkawari ba laifinka bane. Alkawari da amana ai ba karamin aiki bane cika su, amma cikin yardar Allah ka cika kai dai, Ubangiji Ya saka maka da gidan aljannah. Amma Hannah ba zan bari ta koma ba. Haisam yayi dan murmushi gami da gyaran murya ya ce “Amin Baba, amma idan baka manta ba a ranar dana karbi amanar Hannah nayi alkawarin Hannah zata yi karatu to kai ma a lokacin kayi min alkawari, kaga alkawari girma ne da shi baka cika ba, kayi min alkawari zaka bar Hannah tayi karatu don sai dama nasa kayi alkawari zaka dinga turo Hannah makaranta baza ka hana ta ba wataran sannan nayi maka alkawarina. Malam Habu yayi shiru zuwa dan wani lokaci can ya nisa ya ce “Anyi haka yaro haka akayi nayi maka alkawari to amma ai abinda yarinyar nan ta ce gargadi fa tayi min akan kada in kara tura *yata makarantar nan kaga ai kome tayi mata bata da laifi nine ban ji ba kenan. Haisam ya katseshi ya ce “Kare lafiyar Hannah da duk wani abunda zai cuce ta yana daga cikin manar dana dauka in Allah Ya so babu mai yiwa Hannah wani abu. Ramlah kuwa ta fada ne kawai a cikin bacin rai amma babu abinda zata yiwa Hannah, a ina ma zata ganta balle tayi mata wani abu? Ta dai fadi son ranta donta tsorataka,kawai kaga Baba kuma abinda ta fada ba haka bane Hannah karatu take haikan a makaranta, kanwa ce Hannah a wajena ni ne mai tsawatar mata ma misali da ace tana soyayya da samari a makarantar. Baba mufa canfa akwai doka babu yadda za’ayi wata ta shigo cikin makarantar dauke da wata guba taje ta cuci dalibai don haka Baba ka kwantar da hankalinka ni da kai duk mu cika alkawuran da muka daukarwa Allah. Malam Habu ya ce “To shikenan Allah Ya taya mu cikawa. Hannah dauko kayanki ku tafi Allah Ya kiyaye hanya. Su duka suka ce “Amin, sai murna ta dira a zukatansu. Cikin farin ciki da jin dadi Hannah ta shiga ta fara hado kayanta, Iya Abu tayi caraf ta fito daga bayan kyauren da take labe ta hau Malam Habu da fada “Au yarda kayi da wannan dadin bakin da suka yi maka. Duk wannan gaskiyar data baiyana yarinya iskanci suke a makarantar don yana aiko maka dana goro shine kaki fadar Allah saboda abin duniya? Kallo daya Haisam yayi mata yaga irin wadannan mutanen ne masu abun haushi masu kama da aljanu munana masu bakin hali yaji ya tsani Iya Abu har baya so ya kara kallon fuskar shegiya.
Hannah ta rataya jakarta ta fito ko kallon Iya Abu bata yi ba balle tayi mata sallama. Ta duka ta yiwa Babanta godiya tayi masa sallama ta wuce cikin mota. Haisam ya danko kudi mai yawa ya ajiye a gaban Malam Habu, Safiyanu ma haka ya debo kudi ya ajiye masa suka yi masa sallama dukkaninsu yana godiya suna godiya suka shiga mota suka tafi.
Ba Safiyanu ba har Haisam ya ji ya sake tausayawa rayuwar Hannah saboda ganin yadda gidansu yake. Gidan kasa ne anyi masa katanga da kara rufin azare abin dai abun tausayi talauci ne dai tsagwaronsa. Babu abinda zaka daga a gidan ka sayar dashi dari biyar komai raga-raga. Kaico! Hannah na komawa makaranta tasa littafinta a gaba tahau karatu. Sune yanzu masu shirin zana S.S.C.E don haka babu wasa sai karatu.
Kwance tashi su Hannah sun fara zana jarabawarsu ta karshen (S.S.C.E). Saboda daman tuni sun gama tsarge karatu. Sai suka ga cin tuwo yafi jarabawar wuya sai kawai suka fede ta. Geography course din Malam Haisam ita ce wacce suka yi ta karshe da misalin karfe hudu na yamma suka gama daman jakunkunansu suna bakin hall din da suke jarabawar suna fitowa sai kowacce ta dauki jakarta sai tafiya daman kowacce ta kagu taje gida taga *yan gidansu basu taba irin wannan dadewan a makaranta ba, har watanni bakwai a makaranta. Hatta Hannah da bata so a yi hutu itama yanzu so take taje gida taga Mahaifinta sai mafarkinsa take kullum ta kwanta barci. Hannah da kawayenta sun sha kukan rabuwa musamman ita da Nusaiba sun saba sosai gashi zasu rabu. Gashi kuma babu waya a garinsu Hannah balle su dinga gaisawa a waya. Rauda ma ta rungume Hannah tana kuka taji duk babu dadi yanzu da zasu rabu, kuka wiwi Juniors suke yi na rabuwa da Seniors dinsu zasu tafi su barsu musamman Hannah basu ji dadin rabuwa da ita ba saboda tayi musu mutunci, samun shugabar dalibai irin Hannah sai an bincika. Ta koya musu abubuwa na cikin kungiyoyinsu (club) na makarantar. A haka kowacce ta tafi gida kuka wiwi. Safiyanu ne yazo ya dauki Hannah ya kaita gidan Uwar biyu. Yau Haisam tun kafin su shiga Jarabawa yazo yayi musu sallama ya koma gidansa ya rufe kansa ko wajen da ake bankwana bai zo ba saboda tsananin bakin cikin rabuwa da *yan ajinsa da yake matukar so. Gidan Uwar biyu ma sai washe gari yaje ya samu Hannah acan. Bayan sun gaisa ya ce da Hannah. Yau zaki tafi gida ko sai kin sake hutawa kamar sati daya anan sannan ki tafi? Hannah tayi caraf ta ce “Yaya Haisam yau zan tafi na dade banga Baba ba. Haisam yayi dariya ya ce “Wato ke yanzu kin bar Kazaure kenan zaman Kazaure sai mu? Tayi dariya ta ce “Sai ku ai mu mun daku wannan hutun har na daina sha’awar garin Allah Yaya Haisam. Haisam ya mike ya ce “To ki shirya zanje nan makwabta Safiyanu yana ciki wajen abokansa ana wanke masa motar ana gamawa sai ku fito zan aiko yaro yayi kiranku sai mu kaiku tasha ku tafi. Da har can garin zamu kaiku in yiwa Baba godiya ince masa gaki na dawo masa dake lafiya na cika alkawari shima ya cika, to sai Safiyanu ya ce Kano zai tafi da Kakarsa in anjima. Hannah tayi dariya ta ce “Kai Yaya Haisam ai babu komai yana gani na ma yasan lafiya na dawo lallai kuwa ka cika alkawari. Ya juyo ya kalleta ya ce “Ko? Tayi murmushi ta ce “Eh. Sannan ya fita yana murmushi.
Bayan fitarsa da dadewa sosai yaro ya shigo ya ce “Wai Uwar biyu da Hannah su fito inji su Safiyanu suna kofar gidan Dallatu. Daman a shirye suke tsaf sai Hannah ta fara dorawa yaron jibgegiyar Jakar kayanta. Jakunkunan uku ne. Yakai ya dawo ya dauki biyu sannan yazo ya dauki ta karshe sannan suka fito Uwar biyu ma da buhunta a kanta, suka shiga motar sai tashar Kazaure. Hannah ta hado kayanta kakaf na gidan Uwar biyu, katifa da bokiti kuwa ta ba Uwar biyu kyauta. Kaya masu kyau atamfofi da shaddoji da yawa Hannah ta bawa Uwar biyu kyauta da *yarta Halima. Dake kaya tsadaddu leshina uku, shadda da atamfa bibbiyu Yaya Haisam ya yiwa Hannah na Candy. Bayan takalma da sarka da dan kunne harda ta gwal ya suyo mata. Suna isa tasha a bakin tasha Safiyanu ya tsaya da motar. Ma’aikatan nan *yan Union su biyu suka zo suka tambaye su ina zasu da suka fada sai suka ce babu motar Babban-mutum yanzu amma baza a dade ba zata zo Haisam ya ce su kwashe Jakunkunan su kai cikin tasha. Hannah da Uwar biyu suka shiga cikin tasha. Safiyanu da Haisam suna bakin mota a tsaye a bakin tasha. Can suna tsaye suna hira sai Safiyanu ya kalli agogo ya ce yanzu fa muka yi da Hajja Kakata zan dawo mu tafi Kano tana can tana jira na. Haisam ya ce “Ai ba komai jeka kawai nima idan naga tafiyarsu acaba zan hau in koma cikin makaranta. Suka yi sallama Safiyanu ya shiga mota ya tafi, Haisam kuma ya shiga cikin tasha.
A cikin wata *yar rumfa ya iske Hannaah a zaune akan Jakar kayanta Uwar biyu kuma akan wani benci suna *yar hira suna jiran zuwan mota. Ya karasa cikin *yar rumfar yana tambayarsu. Har yanzu motar bata zo ba ne? Uwar biyu ta ce “Sun dai ce yanzu zata zo munzo da wuri ne wai daman motar bata zuwa da wuri. Ta mike da sauri daga kan bencinta tace da Haisam ya zauna, ya ce “Lah babu komai yi zamanki mana. Uwar biyu ta ce “A’a ka tsaya a tsaye? Ga kawayena acan suna sayar da zogale bari inje wajensu mu gaisa daman dan kar in bar Hannah ita kadai shine yasa banje ba tun dazu. Uwar biyu ta tafi, Haisam ya zauna yana kallon Matafiya da masu mota ana ta hayaniya. Can ya juya ya kalli Hannah wacce ke zaune akan jakarta tayi jigum kamar tunanin wani abu take, ya kura mata ido kawai yana tunani a ransa. Babu abinda ya fara tunawa sai a ranar da aka fara kawo Hannah makaranta ta ci dammara ta hau ta zauna akan akwatinta tayi jigum tayi shiru a lokacin da Babanta ya tafi ya barta. Amma yanzu maimakon dammarar data ci sai tayi shar da wani tsadadden bakin leshi mai duwatsu kala-kala suna sheki a jikinta. Dinki ne filet riga da siket ta yafa dan yalolon gyale ta dana daurin dan kwali yayin da lallausan gashin nan nata mai santsi baki da tsawo ta tufke da bakin ribon a keyarta. Hannah na dago kai sai taga Yaya Haisam kallonta yake kawai a lokaci guda sai kowannensu ya sakarwa dayan murmushi. Abunda itama ta fara tunawa ranar da Babanta ya kawota makaranta ta hau kan akwati ta zauna tayi shiru Yaya Haisam yana zaune akan benci yana kallonta.
Mai tallar biredi ne ya zo ya ishe su da a sayi beridi ga gardi, zaki biredin tsaraba. Haisam ya kalli Hannah ya ce “Baza ki sayi abun tsaraba ba ne ki kaiwa yara? Hannah ta ce “Kyalesu Yaya. Ya ce “Ban gane kyalesu ba, haka zaki yi wata bakwai kije musu hannu Rabbana biscuit ko sweet za ki shiga Aishalle ki saya? Ungo kudin ki aiki wani yaron. Ya ciro kudi a aljihunsa, Hannah tayi dariya ta ce “Su fa sunfi ganewa ayi musu tsarabar biredi. Haisam ya ce “Su sha tea da safe dashi? Hannah ta ce “A’a su ringa gutsira a haka, su duka suka yi dariya. Haisam ya ce da mai biredi ya sauke ya je ya siyo jakar bacco ya dawo. Ba dadewa sai ga mai biredi dauke da jakar bacco. Haisam ya ce ya juye biredin duka a ciki. Hannah ta rike baki ta ce “Yaya Haisam wadannan manya-manyan biredi har wajen guda takwas ai suna da girma sunyi yawa biyu ma sun isa. Haisam ya ce “A’a basuyi yawa ba kowa yazo yayi miki sannu da zuwa sai ki yago masa gayan biredi ki bashi kice ga tsaraba. Su dukkansu suka kyalkyale da dariya harda mai sayar da biredi dadi ya kamashi ana masa ciniki. Mai lemon fata ne ya garzayo da sauri yaga an siye na abokinsa, shima ya bude muryarsa gaba daya yana “A sayi na tsaraba, shima Haisam ya ce ya siyo bacco ya zo ya juye duka farantin, yayi cololo kuwa don cika. Nan da nan ya garzaya da sauri ya siyo bacco yazo ya juye sai kudinsu tumus a hannu. Suka jerawa Hannah bakkuna a gaba suka tafi suna murna. Hannnah ta dago ta kalli Haisam fuskarta cike da murmushi gami da nuna jin dadin kulawar da yake yi mata ta ce “Yaya na gode fa kwarai da gaske Ya ce “Babu komai Hannah. Hannah ta dago ta kalleshi suka hada ido ta ce “Yaya Haisam baka bani abun busa naba da tsakiyoyin da ka ce in baka zaka boyemin kada Malamai su kwace min din nan tun randa aka kawoni aji daya. Haisam ya tuntsire da dariya Hannah ma haka ya ce “Bazan baki ba sai kinyi wannan danmarar da kika yi sannan zan baki sarkokinki. Suka sake tuntsirewa
da dariya ya ce “Busa nake yi da abun busarki fa, kusan kullum da daddare kafin in kwanta zaki yi mamaki idan aka ce yanzu na fiki iya busar da wakar. Nafa rike yadda kuke wakar, da Amratu kanwata zanje in kaiwa a gida ashe baki bani ba, bari inje in dauko miki. Hannah tayi sauri ta ce “Bansan kana so ba na bar maka har tsakiyoyin ma in so kake. Ya ce “Eh suma Amratu zan bawa ta dinga kwalliya dasu. Hannah tayi dariya ta ce “Amratu baza tayi kwalliya dasu ba, ko mu *yan kauye mun daina saka irinsu.
Motar da zata je Babban-mutum ce ta shigo, doguwar bus ce nan da nan Uwar biyu ta taso ta ce dasu, “Hannah ga mota nan tazo daga jakar su zuba a but. Kwandasta ya zo ya debi jakunkunan kayan Hannah da tsarabar ya zuzzuba a but, Hannah da Uwar biyu suka shiga kujerar baya su biyu kacal sauran wajen Haisam ne yake biya daman haka yake musu in dai ya kawo su tasha to mutane hudu basa zama a baya. Hannah da Uwar biyu ne kawai suke zama ya biya kudin kujerun. Matafiya suna shiga mota, Haisam yazo jikin wundon Uwar biyu ya mika mata kudaden motarsu da kuma wanda zata bawa Mahaifin Hannah kamar yadda ya saba aika masa, Uwar biyu tana ta godiya. Haisam ya zaga ta wundon Hannah wacce jikinta yayi sanyi tana daf da fashewa da kuka, ya mika mata wata ambulan fal da kudi, ya fara yi mata nasihohi masu tsuma zuciya kamar yadda ya saba yi mata amma wannan karon nasihohin sunsha bam-bam da na kullum hade da bankwana yake yi ya ce “Hannah Alhamdulillahi Allah Ya kawo mu ranar da kika gama makaranta kin zana jarabawar karshe Allah Ubangiji ya baki sa’a. Hannah ki kula da addininki sosai daman can ke mai addinice nasan da haka amma ki kara. Kada ki damu a duk halin da kika tsinci kanki, na wahala kona jin dadi duk Allah ne ke jaraba bawansa. Duk tsananin da kike ciki Allah Yana sane dake kuma Yana sonki ba wai Ya wareki bane don ya tsaneki yake hadaki da masifu iri-iri da bakin ciki.ba Allah (S.W.A) Yana jaraba bawansa ta duk inda Yaso kiyi kokari kici jarabawar, ki kuma dinga gode masa a duk rintsin da kike ciki. Idan kika gode maSa a duk yanayin da kika godewa Allah to Shi zai canja miki, ina so ki kula cewar babu wani mutum a duniya da zai zama shine gatanki, gatan kowa Allah ki rike wannan Allah Shi Ya halicce ki Shi Yake badawa kuma Shi Yake hanawa, babu me miki wani abu banda Allah, kici gaba dayin tawakkali Allah Yana sane da ke.
Tsananin kukan da Hannah take rusawa shine ya dabar-bartar da Haisam ya rasa abunda zai ce shima ji yayi kwalla ta cika masa ido taf sai kawai ya juya ya tafi ya ce “Allah Ya kiyaye hanya, sai anjima. Wani kululin bakin ciki ne ya zo ya tokarewa dukkansu a wuya tsananin bakin cikin rabuwa da juna. Gagarumin tashin hankali ya mamaye zukatansu kowanne na fidda ran sake ganin dan Uwansa kuma. Ta yaya Hannah zata zo Kano tace tazo ta gaishe da Malaminta bayan Ramlah na nan na nemanta zata hallaka ta idon ta idon ta tace sai taga bayanta. Shi kuma yaya za’ayi Haisam ya je garinsu Hannah bayan duk gari ya dauka sharrin da Ramlah tayi, Iya Abu na yadawa Hannah ba karatu take yi ba soyayya take yi da wani Malaminta.
Hannah tayi zugum a zaune a mota ji take duk duniyar babu dadi. Yanzu zaman din-din-din zata je suyi da Iya Abu tasan ba karamin bakin ciki zata hadu dashi ba a gidan. Ga tsananin bakin cikin rabuwa da Yaya Haisam saboda sun saba sosai don tafi jin bakin cikin rabuwa dashi akan Nusaiba wacce suke kwana tare su tashi, komai tare hatta bacci baya raba su. Uwar biyu ma sai duk jikinta yayi sanyi, shikenan idan ta kai Hannah gida baza ta dawo ta dauketa ba kuma. Suka isa gidan su Hannah, Hannah ta shiga gida da sauri tana murna zata ga Babanta. A shimfidarsa a zaure ta ganshi a kwance sharkab babu lafiya ashe watansa wajen hudu kenan a haka. Ciwo kullum gaba yake sake yi sai an kwantar an tayar.