Gangar jikinsa na aura14

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

 Chapter 14

Hannah ta gigice har tana neman rasa hankalinta
yayin
da taga Mahaifinta ya zama kashi kwance kurkut
dashi.
Qaninsa ne Uwa daya Uba daya yazo yana zaman
jinyarsa, dan Iya Abu cewa tayi ya mutu mana tace
ta
gaji da zaman jinya tunda yaki warkewa tayi na
Allah
*yan Uwansa kuma suzo suci gaba da kula dashi
ita ta
huta. Hannah tasa kuka taje ta tsuguna a gabansa
ta
ce
Sannu Baba. Ya ce “Yauwa sannu *yar Baba ashe
da
rabon kizo muyi magana dake ban mutu ba nace
aje a
kirawo min ke a makaranta kizo kiga gawar
Mahaifinki
basu je ba. Cikin shesshekar kuka Hannah ta ce
“Ba zaka mutu ba Baba daina fada ma. Uwar biyu
ma
ta matso kusa dashi ta ce “Sannu Malam Habu ya
jiki?
Ya ce “Jiki dai gashinan Uwar biyu sai dai kuyi min
addu’a idan na mutu, Allah Ya saka miki da alheri
ke da
Haisam da gidan Aljannah abunda kuka yiwa
Hanne na
gode. Uwar biyu ma hawaye take yi. Hannah kuka
kamar ranta zai fita. Anan Uwar biyu ta yini sai da
la’asar tace zata tafi suka yi sallama da Malam
Habu
dake radau yana magana tashi tsaye ne baya iya
yi.
Hannah ta rakata har tasha. A hanya Uwar biyu
take
bawa Hannah shawara ta ce “Tun da ke mai ilimi
ce kiyi
amfani da iliminki, ki kai Mahaifinki asibitin Babura
tunda kudin da Haisam ya bawa Mahaifinki da
wanda
ya baki mai tsokane zai isheku. Da abarshi a gida
ana
masa jike-jike duk wata cuta ake kara masa.
Mutum a
kwance har wata hudu ya kare sai kashi da fata. A
tashar Uwar biyu ta sami mai mota aka yi tsada
zata je
gida a dauko marar lafiya a kaishi asibiti. Hannah
da
Uwar biyu suka shiga mota, dake itama Uwar biyu
daman motar Babura zata shiga daga Babura zata
hau
ta Gumel. Sai kawai su duk su tafi tare. Motar taje
har
kofar gidan, direban da kwandasta da kanin Malam
Habu suka ciccibeshi suka sashi a mota suka
shiga
suma da *yan kayayyakinsu suka nufi asibitin
Babura.
Iya Abu nata yiwa Hannah surutu tana cewa gata
nan
Uwar iya yi wai har tayi kudin din da zata dauki
Mahaifinta ta kai asibiti wai har asibitin Babura ta
zama *yar boko. Sai da Uwar biyu tayi wata guda
cur a
Gumel sannan ta dawo Kazaure tana zuwa tana
niyyar
ta shaidawa Haisam halin da Mahaifin Hannah ke
ciki
sai aka ce mata ai bayan tafiyar su Hannah da sati
biyu
shima ya bar koyarwar ya kwashe kayansa ya
koma
Kano. Ta nemi Safiyanu shima aka ce mata ai shi
tunda
yayi aure a Kaduna ya tare da sabuwar amaryarsa
a
can ya sami aiki, sai Uwar biyu ta hakura da
sanarwa
Haisam don ita bata taba zuwa Kano bama balle
ta tafi
nemansa. Su Hannah kuwa sai da suka shafe wata
guda da kwana shida sannan aka sallamesu daga
asibiti. Kanin Mahaifinta ne a wajensa amma itama
takan je tayi kwana biyu uku acan har dai suka
dawo
gida gaba daya. Jiki da sauki tunda yana zama da
kansa ba sai an tallafo shi ba. Sai dai kudaden
hannun
Hannah sun kare kakaf saboda siyan magungunan
asibiti.
Nan fa balokokon Iya Abu ya tashi akan taga
Hannah
bata da kudin da zata sayi dan biskit da madarar
da
take sha idan tazo hutu da, dole ta ci tuwan gidan.
Hannah ce shara, wanke-wanke da dafa abinci
tuka
tuwan bakar dawa da miyar kuka a murhun kasa.
Kwanci tashi su Hannah sunyi wata biyar da gama
makaranta. Hannah har ta fara zuwa makarantar
bokon
garinsu tana koyarwa. Duk da dai ba’a dauketa a
matsayin Malama ba don Jarabawarta bata fito
ba.
Amma a karshen wata ana bata dan na batarwa.
Ranar
asabar babu makaranta. Da sassafe bayan Hannah
ta
gama wanke-wanke tana kokarin daura tukunyar
tuwon burabuskon gero miyar kuka na rana sai
kawai
Iya Abu tazo ta kashe wutar da ruwan tuwon. Ta
ce ta
canja ra’ayi yau an fasa yin abincin ranar saboda
unguwa zata ita da jikokinta don haka meye
amfanin
tuwon. Ta dauke garin tuwon da kukar kadin tasa
a
daki ta datse ta yafa mayafinta zata fice. Ran
Hannah
ya baci ta ce “To Baba fa, me zai ci shi da bashi
da
lafiya? Yau jikin nasa a rikice yake tunda sassafe
amai
yake. Iya Abu ta ce “Sai yaci hakuri ko ki kwashe
aman
da yayi ki dumama masa. Cikin fushi Hannah ta ce
“Ina
raye a duniya Mahaifina ba zaici amai ba insha
Allah
“Mari tas Iya Abu ta sakar ma Hannah akan
lallausan
kuncin nan nata ta ce “Ke kin isa ina fada kina
fada
lalle wuyanki ya isa yanka. Malam Habu da yake
kwance sai jikinsa ya dau kakkarwa tashin hankali
ya
dira a zuciyarsa yaji marin da aka sakarwa Hanne
sai
ya hau hawaye yana kira “Yar Baba yi hakuri zo
nan
wajena ki zauna. Hannah tana hawaye ta je gefen
shinfidarsa ta zauna Iya Abu tana tsaye akansu
tana ta
balokokonta tayi har ta gaji ta kama hannun
jikokinta
suka fice, da taji ba’a kulata ba. Zuwa can wani
lokaci
mai dan tsawo Hannah da Mahaifinta sunyi zugum
suna tunani sai ta jiyo mai tallar fura da nono ta
zo
tazo wucewa, da sauran *yan canji a jakarta ta
tashi
ta leka ta kirawota, ta dauko kwanon sha ta saya.
Ta
dama ta tashi Mahaifinta zaune ta bashi yasha ya
koshi
sannan ta gyara masa kwanciyar ya kwanta ta
koma
gefensa ta zauna tayi lamo zuciyarta cike da
takaici ga
yunwa tana addabar cikinta. Can Malam Habu ya
ce
“Yar Baba, ta ce “Na’am Baba. Ya ce “Allah Yayi
miki
albarka ya baki miji na gari mai sonki kamar
Haisam,
sai Hannah tayi shiru tana tunani da mamaki ya
akayi
Mahaifinta yake hada mijinta da Haisam.
Malam Habu ya ce “Ya ba ki amsa ba? Ta ce
“Baba
kamar Haisam kuma? Ya ce “Eh kamar yadda yake
kula
dake yake nuna miki kauna. Tayi murmushi ta ce
“Mutunci ne dashi da tausayi amma ba soyayya
bace.
Malam Habu yayi dan tari ya ce “*yar Baba matso
kusa
dani kiji. Hannah ta matso kusa dashi. Ya ce “Yar
Baba
babu mai sonki a duniyar nan kamar Haisam, babu
mai
rikeki tsakani da Allah irin Haisam, babu mai rikeki
amana ko bayan raina wanda ko dar bana yi sai
shi
*yar Baba. Haisam yana matukar sonki. Hannah ta
ce
“Meka gani kake cewa haka? Ba sona yake ba ko
kadan
mutunci ne ai bai taba gaya mun ba. Malam Habu
ya
nisa ya ce “Yanzu tashi kije ki nemi gidansu a
Kano
kice na amince masa ya zo zan bashi ke ya aureki.
Hannah ta zabura ta ce “A’a Baba ya za’ayi inje
kawai
ince masa ka yarda yazo ya aure ni bayan bai ce
zai
aureni ba. Malam Habu ya ce bakya yimun musu,
karki
fara daga yau bazan ce kiyi abunda zaki cutu ba
jeki
kawai ki fada masa. Haisam ne zai rike mun ke
amana
*yar Baba duk duniyar nan shine kadai na yadda
ya
aureki. Jeki ki shiryo ki tafi yi sauri *yar Baba.
Hannah
ta tashi a sanyaye zuciyarta cike da zulumin
wannan
al’amari.
Ta shiga cikin gida ta sake salla wanka ta saka
wani
dandatsetsen sabon leshinta kalar brown ta yafa
gyalenta a kusa da Babanta ta ce “Na shirya zan
tafi,
ya laluba karkashin tabarmarsa ya dauko wasu
kudi ya
bata, ya ce tayi kudin mota. Ta ce ya barshi tana
da
kudin mota, ya ce ta karba shi mai zaiyi da kudin
in
bata karba bama kwashe su za’ayi, kudin da ya
tattarane na *yan dubiya. Har Hannah takai bakin
kofa
zata fita sai ta tuno ai bata san kwatancen gidan
su
Haisam ba gashi bata taba zuwa Kano ba sai can
ta
tuna akwai inda ya rubuta mata kwatancen
gidansu a
jikin littafinta (slum book) da ta bashi ya cike
mata. Ta
koma daki da sauri ta binciko cikin littattafanta ta
dauko sai kawai ta jefa littafin a jaka ta fito.
Malam
Habu na kwance bacci ya fara daukarsa yaji
motsin
mutum sai ya bude ido ya ce “Waye? Hannah ta
ce “Ni
ce Baba, ya ce “Baki tafi ba ne, *yar Baba ko
bakyason
zuwa ne? Ta durkusa a gabansa ta ce “Baba ba
haka
bane mantuwa nayi na dawo amma yanzu zan tafi
zan
bi ta gidan Iya Salma(tsohuwar matarsa ta fari) ko
ita
tazo ta taya ka zama kafin in dawo baza a barka
kai
kadai ba. Malam Habu ya ce “To Allah Yayi miki
albarka. Hannah ta ce “Amin Baba Allah Ya baka
lafiya
ya ce “Amin *yar Baba, kuma ko bayan raina a
daura
aurenki da Haisam ina fatan kema kina sonsa?
Hannah
tayi dariya ta rufe ido, alamar kunya Malam Habu
yayi
dariya shima ya ce “Yar Baba fada min gaskiya
mana.
Ta ce “Baba saboda tsananin kyautatawa da kula
da
yake mun sune suka sa nake ganin girman Yaya
Haisam har naji babu wani mutum da nake so da
tsananin kauna bayan kai Mahaifina sai kuma shi.
Baba
ina son Yaya Haisam sosai har nakan kasa bacci
yanzu
saboda tunaninsa da kewar sa musamman yanzu
da
muka rabu. To amma Baba babu yadda zanyi sai
naga
kamar shi ba haka yake nufi a zuciyarsa ba.
Malam
Habu ya ce “Tashi kije shima yana sonki fiye da
yadda
kike ji. Amma muyi addu’a kafin ki tafi mu karanta
Salati goma ga Annabi (S.A.W). Suka karanta
Malam
Habu ya dinga kwarara addu’oi sannan daga
karshe
suka shafa. Hannah ta sake yi masa sallama ta
fita.
Tana fita gidan Iya Salmai ta nufa ta shaida mata
abunda ke tafe da ita. Nan da nan Iya Salmai ta
zari
gyalenta ta nufi wajen tsohon mijinta dan uwanta
abun
kaunarta wacce dole ce ta raba su don ta kula
dashi
kafin Hannah ta dawo. Hannah na isa tasha ta
tarar da
mota fijo zata je Kano ta cika saura wajen mutum
daya
tayi sauri ta fada sai tafiya.
Babu abinda Hannah take ji a ranta yau sai
tsananin
farin ciki, ji take kamar anyi mata albishir da gidan
aljannah. Tana san Yaya Haisam har a ranta, to
shima
kuma a yadda ta lura yana sonta sosai kuwa
wadannan
dara-daran idanuwan nan nasa ne take hangowa a
zuciyarta idan yana kallonta. Da wasu fararen
hakoransa tas idan yana mata nasiha wai waya
ganni a
Kano yau a kusa da Yayana Haisam kuma wai
yazo
muyi aure an bashi ni. Hannah ke fada a zuciyarta,
dadi
marar misaltuwa ya disu a zuciyarta kowa ya ga
Hannah yasan tana cikin farin ciki a yau. Sun isa
Kano
lafiya a tashar *yan kura aka sassauke su. Hannah
ta
fito daga mota ta kalli gabas da yamma kudu da
arewa,
taga bil’adama ne burjik a gaba da bayanta. Ta ce
a
ranta “Ikon Allah KANO MAI MATA DA MAZA DA
MOTA
DA KUDI DA ILIMI DA WAYEWA, TA DABO TUMBIN
GIWA
KO DAME KAZO AN FIKA, MAI DALA DA GWAURON
DUTSE. Yanzu ina zan fara dosa gabas ko
yamma?
Abum ya bata mamaki ganin yadda ake kallanta
har
wasu mazan waiwayenta suke. Da farko ta dauka
kowa
ya ganta yasan bakauyiya ce bata taba zuwa Kano
ba,
ta fita daban da *yan garin sai da ta ji wasu
samari su
biyu sunzo wucewa sunce mata “Ke kyakkyawa
dan
rufe fuskar nan taki kada kisa wasu mazan suyi
hatsari
a garin kallonki. Sannan ta yarda tsabagen farin da
suka gani da kyakkyawar fuskar da kirarta suke
kallo
sai tayi sauri ta dora gyalenta aka ta rufe fuskarta
idanuwanta kawai ta bude, ta ce a ranta duk
kyawawan
matan garin nan daman har wani kyau na zasu
gani??
Kwalelensu Yaya Haisam ya riga su.
Ta bude jakarta ta dauko littafin da adireshin
gidansu
Haisam ke rubuce ta karanta sunan unguwar
Sulemanu cresent, sai ta sami kwandasta mota. Ta
ce
“Malam don Allah ina motar Sulemanu cresent? Ya
ce
“A’a gaskiya babu takamaimai motar da take zuwa
irin
wadannan manyan unguwanni, amma shawarar da
zan
baki ki sami mai tasi ki dau shata ya kaiki har
kofar
gida. Ga masu tasi nan a tsattsaye babu kowa a
ciki. Ya
nuna mata su, tayi godiya ta karasa wajensu.
Babu
abinda ta fara hangowa sai wajen waya an rubuta
“Make your call here” ta karasa wajen masu wayar
ta
ce “Anan ake yin waya? Mai waya ya ce “Eh nan
ne, ta
dauko littafin nan ta dubo lambar Nusaiba ta mika
masa. Bugu daya wayar ta shiga ta fara ringin,
wata
mata ce ta dauka sannan ya mikawa Hannah kan
wayar Hannah ta karba tana kallon wayar don ita
bata
san yaya zata yi ba. Mai waya ya ce “Kudinki yana
tafiya an dauka fa kisa a kunnenki kiyi magana.
Sannan Hannah ta tuno yadda taga ana yi. Bayan
ta
gaishe da matar sai ta ce “Hannah kawar Nusaiba
ce,
Nusaiba nake nema. Matar tayi dariya ta ce “Oh
Hannah ce? Nice Mami Mahaifiyar Nusaiba, ai
Nusaiba
tana London har ma an samar mata admission
tana
jiran sakamakon jarabawarta ne ta fara
karatu. Hannah tayi bakin cikin rashin samun
Nusaiba
a waya sai suka yi sallama ta mikawa mai waya
kan
wayar, ya duba ya ce “Minti uku kika yi, ta ce
“Nawa
ne? Ya fada ta dauko ta bashi, sannan ta juya ta
tafi.
Murna take kawai a zuciyarta yau gata a Kano
tana
wadaka da komai irin na *yar birni har kan waya
yau
ta rike lallai.
Wani mai tasi Inyamuri baya jin Hausa ta samu sai
suka fara yarawa da turanci. Ta ce Sulaimanu
cresent
zai kaita ya fadi kudi ko ragi bata nema ba ita a
tunaninta komai a birni a ka’ide yake ba’a neman
ragi
kuma ita burinta kawai ya kai ta taga Haisam.
Suna
shiga unguwar sai ta dauko littafinta ta duba
lambar
gidan ta gayawa direban, a shema a kofar gidan
suke
sai ya ce to ai ga gidan ta zaro kudinsa ta bashi
ta fito
daga motar ya ja motarsa ya tafi. Tsantsari, wani
tsalelen gida ne gidan su Haisam yafi duka gidajen
layin tsaruwa Hannah tayi matukar mamakin ganin
gidan su Haisam saboda bata taba zaton Haisam
dan
gidan gawurtaccen mai kudi bane irin wannan.
Wasu
tsala-tsalan motoci ta gani a wajen get din gidan
sun
doshi guda goma. Ta tafi kofar gidan
makwabtansu ta
zauna akan wata kwalbati tana tunanin yadda
za’ayi
yau taga Haisam. Don ita wannan tafkeken get
dogo
baza ma ta iya bude shiba balle ta shiga. Wani
buzu
mai gadi ne ya leko ta jikin get ya hango Hannah
a
kofar gidan da yake gadi sai yayi wuf ya fito ya ce
“Kai
me kana yi anan? Ta ce “Wani nake nema, ya ce
“Waye
wani, ba zaka tambaya ba zaka zo ka zauna
anan?
Hannah ta ce “Haisam na can gidan. Ya ce “Ka ce
na
can gidan me yasa kazo nan ka zauna kuma.
Kaima
bakauye ne ko? Don ka yi kama da *yan garinmu
masu
yalalo-yalalo gashi. Sai duka suka yi dariya shi da
Hannah. Mai gadin ya leka kofar gidan su Haisam
da
yaji hayaniyar mutane. Sai ya ce mata “Yauwa ga
Haisam din can sun fito ita da abokanayenta.
Hannah
ta ce “Dan Allah dan garinmu kirawo min shi akwai
maza bazan iya zuwa ba. Buzu ya karasa wajen
Haisam
ya shaida masa wata na kiransa, Haisam cike da
mamaki ya tunkaro wajen da Hannah ke tsaye sai
tasa
gyale ta rufe fuskarta. Ya karaso inda take a tsaye
yayi
mata sallama ta make murya ta amsa. Ya ce
“Wace ce?
Hannah ta sake make murya ta ce “Bakuwa ce.
Haisam
ya hada girar sama data kasa ya ce “Wai wacece
in ba
zaki fada ba zan koma ina da abunyi. Hannah ta
yaye
mayafin a hankali ta bude fuskarta. Wai, kamar
wani
hasken walkiyane ya haskewa Haisam ido da yaga
fuskar Hannah, cikin fara’a da mamaki Haisam ya
ce
Hannah! Hannah kece!! Tayi lallausan murmushi ta
ce
“Yaya Haisam ni ce, ta duka ta gaishe shi. Taga
Haisam
ya caba ado da wata babbar riga mai aiki a wata
tsadaddiyar shadda fara sol yasa bakin takalmi da
bakar hula yayi matukar kyau. Tayi dariya ta ce
“Yaya
Haisam yau kaine da babbar riga? Har kafi kyau
haka.
Ya ce “Haba? Ta ce “Allah. Ya ce “Yaya su Baba,
da
sauran *yan gidanku? Ta ce sunanan lafiya sunce
na
gaisheku, ya ce “Muna amsawa, to zo ki shiga
cikin
gida ku gaisa da Hajiya. Hannah ta dan yatsune
fuska
ta ce “Kai sai dai watarana ni kunya nake ji kuma
sauri
nake sai dai idan na dawo, ya ce “Au dama ba nan
kika
zo ba ne? Hannah ta ce “Ni kuwa wa gareni a
Kano idan
ba kai ba? Gurinka nazo, Baba ya aikoni. Haisam
ya ce
“To gani fada min aiken. Zumudin yaji abunda aka
aiko
ta ya kama Haisam. Tayi shiru ta hau rufe fuska.
Cikin
zumudi Haisam ya ce “Haba Hannah ki fada mun
mana
kunyar me kike ji ne? Ta ce “Baba ne ya ce inzo in
fada
maka cewar kazo ka nemi aurena ya baka ni. Tun
kafin
ta karasa sai taga Haisam ya fara dariya da alama
farin
ciki ya cika zuciyarsa. Ya kurawa Hannah ido na
wani
dan lokaci ya ce “Shi ne abunda kika kasa fada
daman?
Ya sake yin dariya ya tsaya yana kallan Hannah
wacce
take rufe idanuwanta saboda kunya ga tsananin
farin
ciki.
Ya nisa sannan ya ce “Yanzu Baba da kansa ya ce
ki zo
ki cemin ya bani ke? Hannah ta amsa da “Eh, ya
ce
“Yanzu ya bani ke kacokan a matsayin matata?
Yanzu
Baba ya yarda ki zama uwar *ya*yana mun zama
daya
dangina sun zama danginki, Iyayena sun zama
Iyayenki? Yanzu Baba ya yarda na zama abokin
rayuwarki na dindindin har abada? Yanzu Hannah
kin
amince zaki zama abokiyar zamana har abada?
Hannah
cike da fara’a da murmushi take amsawa Haisam
tambayoyinsa da “Eh’ Haisam yayi murmushi ya
sunkuyar da kai na dan wani lokaci can ya dago
ya
kurawa Hannah ido yayin da kowannensu ya
sakarwa
dan uwansa murmushi da wasu masun kauna da
suke
firfitowa daga idanuwan kowannensu, tare da yiwa
junansu wani kallo mai kunshe da so, kauna
muradin
ganin juna. Haisam yayi ajiyar zuciya ya nisa ya
ce
“Alhamdulillahi Hannah na daukarwa Allah alkawari
na
cika, sannan na cika burina dana kudira akanki na
inga
kin kammala karatunki. Kuma yanzu na dawo gida
zan
cika wani tsohon alkawari dana dauka. Nan da nan
Hannah ta kurawa Haisam ido ta daina murmushin
da
take alamar bata gane abunda Haisam yake cewa
ba.
Haisam ya ce “Hannah na gode madalla, ki yi mun
godiya a wajen Mahaifinki. Good bye, Good bye
Hannah. Ya fara ja da baya, yana daga mata
hannu
yana yi mata murmushi. Bakinta ya dau rawa tana
so
tayi magana ta kasa. Gaba daya jikinta ya hau
karkarwa inda jakar dake rataye a kafadarta ta
sulmiyo. Wasu maroka ne suka wayar mata dakai
akan
abunda Haisam yake nufi suna cewa. Ango Haisam
kasha kamshi fari mai farar aniya kaga angon
Ramlah,
*yan boko bayin nasara an daura aure lafiya ankai
maka
amarya gidanta lafiya. Wani abokinsa ne ya taho
da
sauri ya ce da Haisam “Ana tayin waya daga
wajen
daurin aure waje ya cika kai ango kawai ake jira
muje
ka shiga mota mu tafi mana. Haisam da abokansa
suka
shiga tsala-tsalan motocinsu suka zo suka wuce
Hannah anan a tsaye tana karkarwa ido da ido
suke
hadawa da Haisam har suka wuce suka tafi. Ta
juya
tabi motar da kallo har suka hau titi suka kure. Sai
Hannah ta tsuguna a wajen ta rushe da wani
azababban kuka mai radadin fita. Dakyar buzu mai
gadin nan ya dinga bata hakuri ta dauki jakarta
dankwalinta a hannu sai gyalenta ta yafa akai ta
tafi.
Acaba ta hau har tashar *yan kura wannan karon
ma
taci sa’a tana shiga mota ta cika. Kallo daya zaka
yiwa
Hannah kasan hankalinta a tashe yake matuka don
kwandasta sai da yayi magana uku yana cewa ta
bada
kudin motarya bata jiba, hankalinta yana can tana
tunanin daman Haisam ba sonta yake ba, Ramlah
yake
so shine ita da Mahaifinta suke yaudarar kansu.
Yaya
Haisam me yasa kayi min haka me yasa baka
fahimci
son da nake yi maka ba? Ta nisa ta ce “Ko da
yake
bashi da laifi bai yaudare ni ba, ya taimakamin ne
saboda Allah ni na dorawa raina sonsa. Bai san
ina yi
ba kuma, amma na rabu da farin cikin rayuwa na na
rasa
mutum na farko dana taba ji inaso a rayuwata,
gashi
tun bayan gama makarantarmu ko bacci ma
neman
gagarata yake na kwallafa raina da tunaninsa da
tsananin son sa. Sai da wata mata ta kusa da ita
ta
tattabata sannan hannah ta farfado daga tunanin
da
take yi. Kwandasta ya ce “Kudin mota nake
tambayarki
kinyi shiru kina tunani. Sannan Hannah ta zabura
ta
dauko kudin mota ta mika. Mota ta bar cikin Kano
ta
kama hanya  sai Babban-mutum.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE