Gangar jikinsa na aura15

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 15

Suna isa Babban-mutum, tun
daga tasha Hannah ta dinga jin
faduwar gaba kafarta kamar
baza ta iya
daukar taba dakyar take jefa
kafar burinta kawai ta isa gida
taje ta fada jikin Mahaifinta ta
sharbi
kukanta son ranta tunda yanzu
duk duniya shine kadai ya rage
mata gaba da baya. Kamar
yadda data shiga Kano taga
mutanen garin suna kallonta har
da waiwaye yanzu ma a garinsu
haka ta gani
sai kallonta ake tana tafiya har
da masu nunata kamar basu
santa da ba, Hannah tayi
mamakin irin
wannan kallo da ake yi mata ta
ce a ranta “To ko sun san son
maso wani nake? Wanda nake
so yayi
aurensa da wacce yake so.
Kallon nan dai da ake yi mata ya
daure mata kai. Haka dai
Hannah ta ci gaba da tafiya tana
sauri don ta karasa wajen Mahaifinta
shine kadai mai lallashinta, mai
gaya mata kalaman
da zata ji dan sanyi a ranta. Ta
kusa kofar gidansu, kwatsam
taga wata kungiyar maza dauke
da gawa
sun yi gabas ana Hailala. Taji
gabanta ya fadi ta dubi kofar
gidansu sai taga taron wadansu
mazan da yara a zazzaune ana
jan carbi ta ce a ranta “Ba dai
gawar Babana bace waccan? Sai
ta zubar da takalmanta da
jakarta ta shiga gida da gudu
don ta duba zaure ko shimfidar
Babanta yana nan kuwa.
Tana shiga taga shimfidarsa
wayam baya nan ga silifas dinsa
da butarsa a gefe to ko ban daki ya
zaga. Ga kwanon furarsa a gefe
awurin wacce ta dama masa
yasha ya rage.
Nan da nan taga su Iya Abu dasu
Iya Salmai sun fito daga cikin
gida suna rusa kuka idonsu yayi
jawur suka riketa suna cewa.
Sannu Hannah, wannan ke aka
yiwa mutuwa Allah Ya jikan
Mahaifinki da sunanki a bakinsa
har
ya mutu.
Sai wani jiri ya kwashi Hannah
ta fada kan shimfidarsa ta
rirrike filonsa ta kudindine ta
runtse ido ji take dama kasa ta
bude ta fada  itama bakin cikin
rayuwa ya isheta. Ta kwalla ihu
tana kara tana cewa “Inalillahi
wa inna ilaihi raji’un. Allah kana
sane da ni, Allah ka san halin da
nake ciki. Allah
baka tsane ni ba, baka kuma
manta da ni ba. Bani da kowa a
duniya, babu wanda ya ragemin
kuma. Allah kai ne gata na, kai
ka halicceni, ka halicci Mahaifina
kuma ka halicci Haisam, ka
hadani da su
muka saba kuma kai ka raba ni
dasu Allah. Allah kai ne abin
godiya. Allah na gode maka,
Allah kai
ne jagorana, Allah kar ka barni
na dauwama a cikin bakin ciki.
Allahu akbar, sai kowacce ta
rushe da kuka, hatta Iya Abu
data tsani Hannah yau Hannah
ta bata tausayi matuka. Sai ta
rushe da kuka ta dinga rike
Hannah tana lallashi.
Da kyar matan nan suka iya
banbare Hannah daga kan
shinfidar Mahaifinta suka shiga
da ita cikin gida. Hannah tana
rusa kuka kamar ranta zai fita
amma ta nemi hawaye ta rasa.
Sai tayi shiru ta shiga dakinta ta
kwanta ita da Mahaliccinta ne
kadai sukasan
san me take ji a ranta, wani abu
ne ya tokare mata a
zuciya kamar dutse abun yafi
karfin kuka. Hannah ta kalli
gabas da yamma kudu da arewa
taga babu wani mai fitar da ita
daga tsananin bakin cikin nan
da take ciki sai Allah. Ta tuno
nasihohin da Haisam yayi mata a
ranar karshen da ya raka su
tasha tasa
hannu a jakarta ta lalubo carbi
ta fara ja. Addu’oi iri-iri Hannah
ko magana ta daina yi, *yan
gaisuwa a
jere a jere suna ta shigowa
dakinta suna yi mata gaisuwa
sai dai kawai ta bisu da kallo har
sha’awa take yi idan taga masu
kuka da hawaye. Don ita kukan
ma take nema ido rufe tayi ko
taji dan sanyi
a ranta ta kasa. Sallah ce kawai
ta ke fito da Hannah tsakar gida
sai kuma da asuba take shiga
ban daki
tayi wanka.
Banda wannan babu abinda
Hannah take yi sai lazumi. Babu
ci ba sha sai da akai kwana da
kwanaki Hannah ta ki cin abinci
sannan su Iya Salmai suke dama
dan farau-farau suka tsaya
tsayin daka akanta suka ce sai ta
sha. Kurba kawai take ba don
dadi ba ji take sha kamar madaci
suka
dura mata don rashin jin dadin
bakinta da take ji. Anyi sadakar
bakwai kowa ya watse gida ya
zama daga Hannah sai Iya Abu,
*ya*yanta ma duk sunyi aure
kowacce ta koma gidan mijinta,
sai mutuwa ta sake dawowa
Hannah sabuwal fil sai a yanzu
ne ta fara samun zubar da
hawaye. Kullum Hannah kuka
take rusawa ita kadai a daki babu
mai lallashinta kaico Hannah.
Sati daya sati biyu Iya Abu ta gaji
da ciyar da Hannah, a yau da
sassafe shida da rabi Iya Abu
tazo ta fara bugawa Hannah
kofa kamar zata karya kyauren
Hannah na kishingide akan
abun sallah
tun asuba bayan tayi sallah ta
zauna tana jan carbi gyangyadi
ya dauketa kamar a mafarki take
jin bugun kofar tayi firgigit ta
bude ido taga ba mafarki take yi
ba ta zabura da sauri taje ta
bude
kofar. Iya Abu ta gani a tsaye ta
kama tsantsan tayi kalar rashin
mutunci. Hannah taji gabanta ya
yanke ya fadi tasan rashin
mutunci ya motsa yau kuma sai
yadda Allah Yayi da ita. Ta ce
“Hannah an gama Hada-Hadar
mutuwa nayi
na Allah nayi na Annabi na ciyar
da ke a aljihuna har sati biyu. Ga
goro can na aika an suyomin
zan
dafa in fara zuwa kasuwa ina
siyarwa don nima dan kudin
cefanen hannuna ya kare
Ubanki bakar dawa kadai ya bar
mana a rumbu don haka ke
kinci kashinki sauran ta zama
kashin *ya*yana zan ringa siyar
da goro ina samun na cefane
ina tuka dawata, daga yau ki
fara ciyar da kanki kafin a raba
gado dama sunce sai na fita
daga takaba kar kice daman ban
gaya miki ba dan kar in ajiye
tuwon
dumame kizo ki gutsirar mun
tuwo, in kuwa kika sake kika
gutsirarmin sai na shake ki kin
amayo shi. Hannah ta sunkuyar
da kai kasa hawaye ya zubo
shar ta ce “To, naji “Iya Abu ta
tafi ta barta
anan a tsaye kamar an kafata ta
rasa mafita kuma. Hannah ta
kasance tana kwana da yunwa
sai ruwa da take ta dirka wai ko
Iya Abu taji tausayinta ta dinga
bata dan tuwo amma taga
makatau, sai ta shirya ta nufi
gidan Malam Uba kanin
Mahaifinta ta shaida masa
cewar yanzu bata da abunda
zata ci
ko zai ajiye mata kwano a
gidanasa ta dinga zuwa tana
daukar abinci ko da sau daya ne
a rana. Yana budar bakinsa sai
ya ce mata daman ta girma ta
rika wai ita *yar boko ga irinta
nan abincin da zata ci ya
gagareta shi dai shawara daya
da yaga ta dace
tunda duk samarin garin suna
tsoron zuwa wajenta suce suna
sonta ganin ita *yar boko ce to
ta yarda yayi wa Alhaji Bilya mai
kudin garin nan magana ya zo
ya aureta, zata fi karfin abinci
don har tuwon shinkafa dafawa
akeyi a gidansa da daddare.
Wani daci ya disu a zuciyar
Hannah da taji
bayanin kanin Mahaifinta. Alh
Bilyan da yake magana wani
shirgegen tsohon mutum ne
matan
sa uku *ya*ya kuwa sun doshi
talatin da yawa Iyayensu basa
gidan kuma jikokinsa ma
sa’anninta ne, manomi ne ba
laifi yana samu a dai garin shi
mai
kudi ne amma ai tana zuwa
gidan ada wajen kawayenta
tasan yadda yanayin gidan yake. Wata
katuwar tukunya ake dorawa a
gidan kamar ta *yan makaranta
girki ma kadai ya ishi matan
baya
ga dukan mata da yake yi yana
da ciwon kuturta kuma harma
ta fara fitowa. Hannayensa da
bakinsa
zaka kalla kasan kuturu ne
yatsun ne kawai basu gama
guntulewa ba amma sun fara
Ruwa. Hannah
ta tabbatar lallai Baba Uba ba
sonta yake yi ba tunda zai
hadata da Alh Bilya aure. Tayi
shiru a
durkushe a gaban Malam Uba
tana jin bayanan da yake yi mata
ya ce “Kin amince inje in sanar
masa
ko kuma kina da magana kiyi.
Hannah ta nisa ta sunkuyar da
kai kasa ta ce “Baba ba na ki jin
maganarka bane ko naki yardaba
Alh
Bilya fa kasan halinda yake ciki
yana da lalurar kuturta, Baba
yanzu zaka yarda in aure shi a
haka? Malam Uba ya fusata ya
zaburo Hannah da fada “Ke kinfi
sauran matan zani ne? Asirinsu
a rufe ko goya shi zaki yi kina
yawo dashi? Kuma shi da kansa
ya
same ni ya ce yana son ki zai
aure ki. Nake jira daman a gama
zaman makokin nan in shaida
miki.
Tunda kinki sai ki tafi ki nemo
abinda zaki dinga ci gardiya
dake kinki aure babu mai ciyar
dake, tashi ki tafi bani waje
mutumiyar banza. Hannah ta
tashi sumi-sumi ta fice tana
sharbe hawaye. Tana fita ta nufi
makarantar boko, ta kuwa ci
sa’a ta sami Alhajiji wani
ma’aikacin da yake zuwa daga
local
government ta rubuta takardar
neman aiki (application) tuntuni
zai nemar mata aikin koyarwa
a primaryn garin.
Hannah cike da fara’a da murna
ta zo ta durkusa
har kasa ta gaishe da Alhajiji ya
amsa, tun kafin ta ce masa
komai ya ce “Hannah na kai
takardar
neman aikinki wajen manyana
Alhamdulillahi kansilan garin
nan ya gani ya sa hannu an kai
ofishin secretary. Murna ta rufe
Hannah ya ci gaba da
cewa “To amma abunda
sakatare ya ce shine baza
su iya daukarki aiki ba saboda
akwai wadatattun Malamai a
wannan makarantar akwai
makarantun da aka rurrubuta
za’a kara ma’aikata amma
daman banda garin nan don
haka sai dai kiyi hakuri.
Hannah taji ba dadi hankalinta
Ya tashi ta ce “Yanzu
Malam Alhajiji ko share-share
baza a dauke ni ba ko can local
government din? Ya ce kai
share-share ai kinfi karfin yin
shara Hannah ki je dai kici gaba
da addu’a, na manta ma ban
fada miki ba na tambaya ance
resul dinku na jarabawa (s.s.c.e)
ya
fito amma an rike na F.G.G.C
Kazaure saboda kunyi
matukar ci sosai wai har da
masu nine distinction kinga dole
aki sakin sakamakon sai anyi
kyakkyawan bincike ko an baku
amsa ne. Hannah ta ce “Binciken
zai dade ne? Ya ce “Gaskiya irin
wannan yana daukar kusan
shekara ma ba’a saki ba. Amma
daman da da result dinki a
hannu da tuni na samar miki
aiki ko ba’a nan garin ba.
Hannah ta
dade a tsugune a gaban Alhajiji
tayi shiru ta rasa yadda zata yi,
can ta yunkura zata mike da
kyar
saboda jikinta yayi sanyi sai
Alhajiji ya miko mata *yan kudi
ya ce “Gashi kya dan kashe. Dadi
ya
lullubeta ta sami nacin abinci
don yunwa take ji. Ta yi masa
godiya ta nufi gidan Iya Salmai,
ta isketa a
zaure ta kasa zogale tana zaune
tana jiran masu saya. Hannah
tayi sallama ta shiga, bayan sun
gaisa
Iya Salmai ta ce “Hannah lafiyar
ki kalau kuwa kin birkice gaba
daya kamar ba ke ba? Hannah
tayi
murmushin karfin hali ta ce “Iya
yunwa nake ji ko da sauran
dumame? Ta ce “Wada na
ajiyewa ya tafi kwallo, rabonki
ne zuba ki ci. Da sauri Hannah ta
mike ta nufi kicin don ta zubo
tuwan. Iya Salmai ta bita da kallo
cike da tausayinta. Sharkab tana
kuka Hannah ta fito ta sami Iya
Salmai tana cewa “Allah
Sarki Habu ka mutu kabar
yarinya marainiya a duniya
kaine daman gatanta. Hannah ta
zauna a
sanyaye tana cin tuwon su duka
hawaye suke yi. Iya Salmai na
tausayinta itama Hannah na
tausayin kanta. Bayan ta ci ta
koshi tasha ruwa taje ta ajiye
kwanon a cikin gida ta wanke
hannunta sannan tazo ta zauna
ta shaidawa Iya Salmai halin da
take
ciki ta ce kuma tana neman
alfarmar idan da hali Iya Salmai
ta ajiye mata kwanon tuwo a
gidanta
tana aika mata. Iya Salmai taji
dadi kwarai da Hannah bata yi
kauron baki ba tazo ta sanar
mata da wuri ta ce insha Allah
kome taci da kashin Hannah to
amma itama ba kullum suke
dora tukunya sau uku a rana ba.
Itama ba da ko *ya
gareta ba bishiyoyin zogale ne
burjik a shuke a gidanta. Ta
tsinka ta dafa ta sayar ko azo a
tsinka
danye a biyata. Daga ita sai
Wada wani dan kanwarta data
rasu ta barshi tun ranar da aka
haife
shi ta dauke shi. Shima yana
kokari ya samo kudi,
to da haka suke cin abincin,
ranar da ba’a samu ba
su sayi na siyarwa ko su hakura
idan babu kudin sayan na
sayarwar. Iya Salmai ta ce “Ai
idan naga *ya*yan Habu raina
dadi yake yi, ba don Habu yana
dan Uwana bama, soyayyar da
nake masa ce
Hannah har yau ina jin
dandanonta a raina. Hannah tayi
shiru tana tunani a ranta tana
kuma tausayawa kanta cewar.
In har Iya Salmai bata daina jin
dandanon soyayyar da take
yiwa Mahaifinta ba har yanzu
shekararsu tafi ashirin da biyar
da rabuwa gashi kuma ma har
ya mutu tana zancen sonsa,
ashe har abada Iya Salmai baza
ta daina jin dandanon son nan
ba. To itama tana kyautata zaton
haka zata kasance da son
Haisam tunda
gashi dai yanzu bata ganinsa
yayi aurensa ma amma sai kara
jin kara sonsa take ashe itama a
haka zata dauwama kenan har
karshen rayuwarta.
“Soyayyar gaskiya ce. Hannah ta
fada a baiyane. Iya Salmai ta ce
“Soyayyar gaskiya ce Hanne.
Haka dai suka yini suna hira
Hannah ce ta dafa musu
abincin dare suka ci sannan
suka yi sallama Hannah ta tafi
gida. Sun rabu akan Iya Salmai
zata ringa tura Wada yana kawo
mata abinci duk sanda suka
sami damar dafawa.
Haka Hannah ta kasance duk
sanda Iya Salmai ta
dafa abinci ta aiko mata taci
ranar da itama bata dafa ba
haka Hannah take zama da
yunwa. Ta rame kurkut da ita sai
ido da dogon hanci ta yi duhu
kuma saboda tsabar wahala da
tsananin tunani.
Ranar da Iya Abu ta fita daga
takaba sai mai gari ya hado
Manyan Malaman garin da masu
fada aji na garin da *yan Uwan
Malam Habu don a raba
gadonsa ga Iyalansa.
A zauren gidan aka zazzauna ga
Iya Abu ga *ya*yanta kakaf
mata da maza ga Hannah a gefe,
itama da Iya Salmai. Mai gari ya
ce “A karantawa Mamacin
kulhuwallahu kafa uku-uku, da
Inna a’adaina kalkausar uku-
uku aka shafa Allah Ya kai
kabarinsa. Sai mai gari ya fara
da cewa “Malam Habu ya rasu
yabar mace daya da
*ya*ya takwas. Dukiyarsa kuwa
wannan gidan ne da kuma
katuwar gona, amma tun ranar
daya mutu aka biya masa
basussukan da ake binsa da dan
kudin daya bari. Ga manyan
Malamai nan zasu raba gado. Ga
sunayen *ya*yan nan a wajensu
zasu shiga cikin gidan su
tsattsaga su bawa kowa nasa
bangaren. Iya Abu ta nisa ta ce
“Ina da magana ni dai nice
matarsa Uwar *ya*yansa kuma
bare daya ce Hanne don haka a
tabbata an bata bangarenta
daban kar a saka min ita a cikin
kason *ya*yana azo ana rigima.
Mai gari ya ce “Ai Abu
rabon gado ba’a cewa ga bare
Allah ne Ya raba da kansa don
haka duk yadda ta kama haka
za’ayi. Malamai sun yi iya
kokarinsu sun kacaccala dan
mitsitsin gidan nan da gona.
Allah cikin ikonsa Hannah bata
tashi da komai ba sai runbun
ajiyar abinci wani dan mitsitsine
kasa ce turmus a kasan da
gidan tururuwa sai dan wani
bangare karami a tsakar gida
shine kashin Hannah a gona
kuwa bata ciki. Murna ta lullube
Iya Abu gona da gaba daya
dakunan gidan nata ne da
*ya*yanta sai ta ce
“Wannan rabo yayi dai-dai to
yanzu sai mai gari kasa Hanne ta
hada kayanta ta koma runbunta
ta
tashi daga dakin nan. Mai gari
ya ce “Haba Abu har yanzu
tsangwamar da kike yiwa Hanne
baki bari ba har Mahaifinta ya
mutu ma bakya rangwanta mata
ba. Iya Abu ta ce “A’a babu wani
rangwami *yan haya zansa a
sauran dakunan ina karbar kudi
wannan abu ne fa na gado. Nan
fa duk suka hadu suna ta bawa
Iya Abu Hakuri ta bar Hannah ta
ci
gaba da zama a dakin da take
har Allah Ya yanke mata wannan
zama tunda komai dadewa aure
zata
yi. Iya Abu ta kekashe
idanuwanta ta ce in anga Hannah yau ta sake
kwana a cikin dakin nan
nata to ta bata kudin haya ne a
matsayin tana haya.
A cikin mutanen dake wajen
harda Alh Bilya ya ce to tunda
Abu ta ce haka shi yayi alkawari
zai dinga biyawa Hanne kudin
haya daga yau ya tambayi Abu
ko nawa ne kudin hayar dakin
da Hanne ke
ciki ta kai-kai ce ta zambada
kudi ya zaro ya biya ba tare da
ya nemi ragi ba, ya biya na
shekara ya san
Iya Abu kora da hali take yiwa
Hannah ta zambada kudi dan a
ce yayi tsada a kama mata a
wani gida cikin ikon Allah sai
taga ya biya.
Mai gari da sauran mutanen
dake wajen suka dinga shiwa
Alh. Bilya albarka. Hannah ita da
Baba Uba ne
kadai suka san manufar Alh
Bilya shi a nufinsa auren Hannah
zaiyi shi yasa ya fara yi mata
hidima,
wani gululun bakin ciki ne ya
dira a zuciyar Hannah
musamman da ya biya mata
kudin haya ta san lallai
da gaske yake auren nata yake
so yayi ita ko gara a kasheta da
a daura mata aure da wannan
mutumin kamar ta ce bata son
kudin hayar baza ta zauna a
gidan ba karya ya biya sai tayi
tunani in ba gidan uban nata ba
a ina zata zauna saita hakura
kawai tayi shiru idan ta ce zata
koma gidan Iya
Salmai to ai daki daya ne kacal a
gidan dan karami ita da Wada
suke kwana a dakin, ba zai
yuwu ita ta
hadu da Wada a daki daya ba
saboda yanzu Wada shekararsa
goma sha takwas yama girme ta
da
shekara daya don haka ya
haramta su cusu a daki daya.
Bayan nan babu kuma gidan
wanda zata iya
zuwa ta zauna duk danginta.
Da daddare bayan kowa ya
shiga bacci ya kwanta Hannah
na juyi akan *yar katifarta ta
kasa bacci
tsananin bakin ciki ne ya
dameta a ranta babu abinda
take nanatawa a ranta sai
zancen hayar nan, ita da gidan
Ubanta yau ta zama *yar haya
sai ta rushe da kuka harta gaji.
Ta ce “Allah kana ji,
kuma kana ganina, kana kuma
sane da irin abubuwan bakin
cikin da nake gani tun ranar da
Mahaifiyata ta sako ni a duniya
Allah ka fitar dani,
kai ne gatana Ya Sarkin
Sarakuna. A haka Hannah ta
kasance har shekara guda da
rasuwar Mahaifinta yau ta ci
abinci gobe ta rasa wannan bai
dameta ba
sosai irin zirga-zirgar da Alh
Bilya yake yi a danginta yana
cewa shifa yana so ya aureta.
Dan har yaje ya sanarwa da mai
gari, mai gari yasa aka kira
Hannah fada ya shaida mata
abun da Alh Bilya yake nema a
wajenta shin ta amince zata
aure shi, ta yarda tana so a
daura auren? Hannah ta fito gar
da gar ta fadi gaskiya ta ce
“Ranka ya dade banki jin
shawarar da ka bani ba amma
dan Allah ina so a
barni haka bana so in auri
kowa. Gaba daya aka dau salati
aka fara yiwa Hannah cari “To
ba’a garin nan ba, duk garin
nan wacece ta taba kaiwa
shekara goma sha takwas ba a
yi mata auren fari
ba? Hannah ta ce “Ba zan Iya
auren Alh Bilya ba a matsayinsa
na Mahaifina dan ni tamkar
Mahaifina
yake a wajena. To haka aka yi da
Hannah a fada.
Alh Bilya yaji haushin Hannah
data ki yarda amma yasan
tuggun da zai tafka mata ya
rama.
Bayan anyi haka da Hanna a
fadar mai gari da kwana uku,
Alh Bilya yazo har cikin gidan su
Hannah da rana tsaka. Hannah
na daki a kwance tana jin
yunwa tana jiran a kawo mata
abinci daga
gidan Iya Salmai tana fargabar
ko suma basu yi abinci ba ne sai
ta jiyo muryar Alh Bilya yana
rafsa
sallama Iya Abu ta fito. Bayan
sun gaisa Iya Abu ta ce “Yau
Alhaji da kanka a gidan namu?
Ya ce “Eh
wallahi zauwa nayi mu gaisa inji
ko yaushe kudin hayar dana
biya yake karewa? Iya Abu tayi
dariya
ta sosa kwarkwata a kai ta ce
“Ai saura wata uku ina jin, ya ce
“To ki raba kudin hayar gida
hudu ki
dauki kashi uku naki ki bani
kashi daya na ragowar
watannin uku ki kori Hanne
daga dakin da take haya in bata
biya ki ba babu ruwana.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE