Gangar jikinsa na aura16

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

 Chapter16

Iya Abu ta bata rai ta ce “To ni
yanzu na kashe kudi
yaya kake so nayi a ina zan
samo kudinka da zan dawo
maka dashi? Hanne fakara’u ko
sisi bata dashi ina zata samo
wani kudin haya ta biyani?
Gaskiya Alh Bilya kai ya dace kaci
gaba da biyan kudin haya don
haka kace a gaban maigari, ya
ce “Kash ni baki fahimce ni ba
Abu
ba don in takura miki ba nace ki
bani sauran kudin ki rike sauran
kudin ina nufin a yanzu ki koro
Hanne daga dakin da take haya
donni bada yawu na take zaune
a dakin ba kuma ba’a kudina ba.
Iya Abu tayi dariya ta ce
“Oh na gane wato yanzu dai na
rike ragowar kudin watanni
ukun da suka rage kenan
sannan in koro Hanne waje idan
bata biyani kudin haya ba ko, ko
ba haka kake nufi ba? Alh Bilya
yayi dariya ya ce
“Haka nake nufi mana. Iya Abu
ta ce “An gama ai a gabanka zan
koro shegiyar. Gaban Hannah ya
yanke ya fadi tayi zunbur ta
tashi zaune ta dafe kirji tana ta
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.
Iya Abu ta wangale labulen
dakin ta shiga ta sami
Hannah a kan katifa a
zaune ta mikawa Hannah hannu
ta ce “Bani kudi, Hannah ta ce
“Bani da kudi. Iya Abu ta
wawuri jakar Hannah zata
wurgar waje Hannah ta rike
tana mata magiya tayi
hakuri dan Allah ta rufa mata
asiri. Amma kamar zuga Iya Abu
take. Hannah ta fito da gudu
daga dakin ta zo ta durkusa a
gaban Alh Bilya tana rokonsa
dan Allah yayi hakuri
ya bar mata kudin hayar wata
uku kafin nan zata san yadda
zata yi ta sake biya. Amma yayi
kunnen uwar shegu da ita yana
cewa “Yauwa Abu ki tattaro
kakaf kayanta ki watso. Ana
cikin wannan hali sai ga
Wada nan dauke da kwanon
abinci ya kawo mata abincin
rana ya sami Hannah kace-kace
tana kuka a durkushe a gaban
Alh. Bilya tana rokonsa Iya Abu
kuwa tana
ta faman watsi da kayanta. Cikin
kuka Hannah ta ce “Wada kaga
halin da nake ciki jeka ka kira
Iya
Salmai tazo ta tayani rokarsu.
Nan da nan Wada ya garzaya
dan ya shaidawa Iya Salmai
halin da yazo ya tarar da
Hannah. Bayan tafiyar Wada ba
dadewa sai ga Iya
Salmai da mai gari da tawagarsa
sun shigo gidan suka iske su
Hannah a cikin wannan hali. Mai
gari ya ce “Subhanallahi Alh Bilya
da girmanka, meye haka?
Alh Bilya ya ce “Ranka ya dade
babu yadda za’ayi taci gaba da
zama a cikin kudina bayan bata
sona shi yasa nazo na ce to in
Abu taga zata bar Hanne taci
gaba da
zama a kyauta to, amma in dai
nine ke biyan kudin nan
dole Hanne ta fita don bazan
barta taci gaba da zama a
kudina ba tunda bata sona. Nan
dai aka hau bama Alh Bilya da
Iya Abu baki ana musu wa’azi
da nasihohi akan rayuwa ce
kuma suma suna da *ya*ya zasu
iya mutuwa su bar *ya*yansu
suma ayi musu haka.
Hannah tasa gefen zaninta ta
goge hawaye ta mike daga
durkusan da take yi ta juya ta
kalli su mai
gari ta ce “Ku kyale su, ni na
hakura da zama a dakin zan
koma rumbun in zauna. Hannah
ta fara dibar
jakunkunan ta tana shigarwa
cikin rumbun nan mai gidan
tururuwa da cinnaku ga
buhunhunan dawa
dana kaikayi. Hannan abun
tausayi Iya Salmai ta ce “Haba sai
kace ba raina ai bazan barki ki
zauna a nan
dakin mai tururuwa ba, ko
Wada ya dinga fitowa yana
kwanciya a waje ni da ke mu
dinga kwana a daki. Hannah
tana hawaye ta ce “Iya Salmai
kyale ni gara in mutu in huta da
irin wannan rayuwar.
Ana cikin wannan badaqalar ne Musa
dan makwabcinsu ya shigo
ya ce “Wasu maza ne guda biyu
gasu nan a waje wasu farare ne
kamar larabawa sunce suna
neman
Hanne *yar gidan Malam Habu.
Mai gari ya ce “Larabawa daga
ina? Musa ya ce “Sun ce wai
daga Niger suke, maigari ya ce
to muma ai tafiya zamu yi mu
tafi kawai. Har Hannah suka yiyo
waje wasu samari farare sol-sol
ne guda biyu a tsaye a kofar
gidan.
Daya daga gani ko tambaya
babu jinin Hannah ne don
kamar su daya kamar an tsaga
kara, mai gari ya
ce “Kune bakin daga Niger?
Suka amsa da “Eh, sannan suka
duka suka gaishe da su maigari.
Hannah ta tsaya a gefe tana
kallon wadannan baki nata, bata
san su ba
amma daya daga cikin samarin
kamar su daya futik daga gani
babu tambaya daga tsatso daya
suka fito. Mai gari ya ce “To ga
Hannen, yaya kamar baku
san juna ba. Mai kama da
Hannah ya ce “Ni sunana Ahmad
wannan abokina ne sunansa
Bello Madu. Ni kanin Mahaifiyar
Hanne ne Uwa daya Uba daya,
Hanne bata taba ganina ba ban
taba ganinta ba shine nazo na
nemota dan muga juna. Hannah
na jin haka sai ta
daka tsalle ta rungume Ahmad
sai ita dashi suka rushe da kuka.
Mai gari da sauran mutane sai
suka hau
girgiza kai suna masu
tausayinsu.
Mai gari ya ce “Alhamdulillahi
gara da Allah Ya kawo ku sai mu
koma daga ciki a tattauna.
Bayan kowa ya sami waje ya
zauna, Hannah ta tashi ta dauki
kwano ta kwalfo musu ruwa a
randa ta kawo musu. Bayan
sunsha mai
gari ya fara bayani ya shaida
musu duk halin da Hannah take
ciki yanzu ma ga jakunkunanta
nan a watse a
waje, dakin da zata zauna ma
yanzu ya zama garari.
Ahmad ya matse hawaye ya ce
“Hakika tuntuni munji halin da
Mahaifiyarki ta shiga har ta rasu
mun san kuma halin
*yarta Hanne zata shiga amma
da yake ni ina yaro bani da ikon
inzo in dauketa shi yasa na
hakura. A
kwanakin nan kuma na dinga
mafarkai iri-iri na *yar uwata
marigayiya Uwar Hanne, kullum
na kwanta bacci sai inga Yayata
Habi tazo tana cewa Ahmad dan
Uwana yanzu ba zaka je ka
nemo *yata ba Hanne kaga
halinda
take ciki a duniya ba, ko daren
jiya ma nayi mafarkinta abu
daya kuma take maimaitawa,
don haka yanzu daman nazo da
niyyar mu tafi da ita ko da
Mahaifinta yana nan zan rokeshi
ya bani ita idan bata yi aure ba
in tafi da ita, balle kuma yanzu
da ya rasu dole in
tafi da ita. Iya Abu ta tabe baki
ta ce “Malam tunda ransa ya
hana akai Hanne wannan garin.
Mai gari da jama’arsa suka yiwa
Iya Abu caa suka rufeta da fada
suna cewa “Ba yanzu kika gama
mata watsi da kaya ba? Bayan
bakar wahalar da take sha tun
tana karama ta zamo tamkar
baiwa a gidan nan.
Ahmad ya ce “Ba saikun bata
bakinku bama wajen
bata amsa mu dai zamu tafi da
ita. Sai yanzu daya mutumin yayi
magana wato Bello Madu, ya ce
“Ai
anan kusa muke a garin Dashi
muke, Dashi da Babban mutum
ai border ce ta raba.
Ni costom ne ina aiki a border
lokaci lokaci zan dinga kawo
muku Hanne kuna gaisawa.
Ahmad ya katse shi ya ce “Bello
Madu duk
zancen ka lallashi matar nan bai
taso ba kaga kankat din garin
wato Maigari da jama’arsa sun
bamu
izinin mu tafi da ita, to ita
wacece kuma da zata ce sai
Hanne ta zauna yunwa ta kashe
ta. Iya Abu taji wani dacin bakin
ciki ya rufeta ganin Hannah ta
sami wajen
da zata je ta huta, ta so ace da ta
yiwa Hannah watsi da
kaya duk garin ta rasa inda zata
zauna. Ahaka dai aka rabu
Ahmad da abokinsa Bello Madu
suka yiwa
mai gari da jama’arsa sallama
suka daukarwa Hannah
Jakunkunanta, Hannah ta yafa
gyalanta ta
rungume Iya Salmai suna kukan
rabuwa Hannah da Kawunnanta
suka tafi.
Sun isa garin Dashi da daddare
gidan Ahmad suka sauka,
Ahmad yana da mata daya da
*ya*ya biyu.
Sunan matarsa Hajir itama irinsu
ce buzuwa. Hajir ta tari Hannah
cikin fara’a da murna ta kaita
daki ta kawo mata ruwa tasha
sannan ta zauna suka gaggaisa
sannan ta je ta shirgowa
Hannah tuwo. Hannah ta ci
tuwon nan kamar tunda Allah Ya
halicceta bata
taba cin tuwo mai dadin haka
ba, saboda tsabar yunwar da
take ji, ta ci tayi nat sannan ta ce
a nuna mata ban daki
zata yi alwalla. Hajir ta nuna
mata. Hannah ta shiga ta dauro
alwalla ta zo ta yi salla tana
idarwa taje ta
watsa ruwa tayi wanka tazo ta
kwanta. Hajir taji tana son
Hannah, tana sonta da kawa
daga gani ma sa’anni ne.
Hajir ta zauna a gefen shimfidar,
Hannah na kwance suna ta hira
kala-kala, Hajir bata bar dakin ba
sai da taga Hannah ta fara bacci
sannan ta hure mata fitila ta
rufo mata kofa ta fita ta nufi
dakin kwanciyarsu.
Da asuba Hannah ta farka taji
ana kiran assalatu ta mike ta
nufi ban daki tayi alwala tazo
tayi sallah ta
zauna tana ta lazumi. Gyangyadi
ne ya dinga daukar Hannah ta
mike ta koma kan katifa ta koma
bacci tayi tayk barci har sha dayan
rana babu wanda ya tashi
Hannah
sai da tayi barcinta ta gaji ta
farka da kanta. Tana tashi tayi
ido hudu da soye-soyen abinci
kala-kala Hajir tazo ta jera mata.
Ba Hajir kawai ba *yan Uwan
Uwar
Hannah da yawa labari ya kai
musu cewar Hannah ta zo don
haka suka aiko mata da abincin
karin kumallo iri-iri sunka ce
kafin suzo su ganta. Hannah ta
fada wanka tayi brush sannan
ta saka kayanta tazo ta zauna a
gaban abincin burjik a jere a
tsakar dakinta duk nata
ne sai taji wani farin ciki ya
lullubeta ba’a sabanba.
Yau Hannah ce da barcin safe ta
farka taga abinci burjiki an
jere mata, haka Allah Ya ke,
duniya juyi-juyi. Tun kafin
Hannah ta gama karin kumallo
taji tsofaffi da
mata suna sallama a tsakar gida,
*yan Uwan Mahaifiyar
Hannah ne suka fara cici rindon
zuwa ganin Hannah. Sai koke
koke daga su har Hannah taga
dangin
Uwarta cunkus amma suka ce
mata wadannan ma kadan
ta gani dan tushen zuriyarsu
abzinawa ne (buzaye) suna
Agadas state. Sai dai wani abu
guda da Hannah ta lura duk
danginta talakawa ne sosai
suna cikin rashi,
wasu nono suke sayarwa a
rugage, wasu kuma manoma
ne. Kawu Ahmad ne kawai dan
boko wayayye mai dan hali akan
sauran koyarwa yake a
makarantar firamaren garin har
ya sami matsayin mataimakin
headmaster.
Shima dai rufin asiri ne kawai
ba wani arziki gare shi ba.
Gidansa ginin kasa ne dakuna
uku ne, bandaki da zana aka
zagaye, kicin kuwa a tsakar gida
aka
dasa murhuna. Haka dai Hannah
taji ta shiga wata sabuwar
rayuwa mai dadi fiye da
rayuwarta ta da a
gidansu.
A koda yaushe tana godewa
Allah da Yayi mata canji daga
ukuba da bakin ciki hantara Ya
kawo ta inda
ake tarairayarta. Hannah da Hajir
sun shaku sosai a koda yaushe
suna tare suna wasa da dariya.
Tun Hannah na boyewa Hajir
wasu abubuwan na dangane da
rayuwarta har ta yaba da
hankalinta ta fara gaya mata
wasu abubuwan da suka faru
da ita ada na dangane da
tsananin son
Haisam da ranar rabuwarsu. Ta
ce har yau kullum da daddare
sai tayi kuka idan taje kwanciya
bacci
saboda tunaninsa. Hajir ta
tausayawa Hannah sosai har
hawaye tayi mata, daga karshe
tayiwa Hannah nasihohi akan
tayi hakuri kaddara ce daga
Allah
haka Allah Ya rubuto musu.
Bayan zuwan Hannah da kamar
wata guda Kawu Ahmad da
sauran manyan danginsu suka
kira
Hannah babban zauren dake
gidan. Bayan ta gaishe da
kowannensu ta koma gefe ta
takure. Baba Sha’aibu ya ce
“Hannah kinsan dalilin da yasa
muka kiraki nan?
Hannah cikin ladabi ta amsa
musu da “A’a, ya ce
“To a matsayinmu na Iyayenki
da Kakkaninki munyi nazari mun
kuma tsayar da shawara, abinda
da nake nufi da munyi nazari
shine bai kamata ba mu zuba
miki
idanu haka nan babu aure ba. Don
haka ya kamata kiyi aure a
watannan. Gabanta ya
yanke ya fadi ras dajin kalmar
aure cikin rudani ta ce …….
“Wa zan aura ai ni bani da kowa
a garinmu anan garin ma babu
wanda ya ce yana sona. Su duka
suka kyalkyale da dariya.
Ahmad ya ce “Hannah kwantar
da hankalinki dole mu aurar
dake ga mai sonki kece dai baki
sani ba
amma zuwanki garin nan maza
sun doshi goma suka sameni
suka ce suna sonki. Shawarar da
muka yanke ita ce muduba a
cikin su waye yafi hankali,
addini, sana’a, asali wanda zai
rikeki tsakani da Allah mu aura
miki shi tunda ke bakuwa ce ba
sanin halayensu kika yi ba babu
kuma ishasshen lokaci da za’a
barki kina soyayya
dasu har ki zabi miji mu baza
mu zaba miki wanda zai cuceki
ba. Hawaye ne ya fara zubowa
shar daga idanuwan Hannah
babu wanda ya fado mata a rai
sai Haisam, soyayyar da take
yiwa Haisam sai kara yabanya
take a cikin ranta, Hannah ta cire
sha’awar
auren wani a rayuwarta tunda
ta rasa Haisam shine ma hawaye
yake zuba daga idanuwanta
don tasan ta rasa wanda take so
duk duniyar nan ta rasa farin
ciki kuma.
Wannan hawaye na Hannah da
yake zubowa daga idanuwanta
yasa jikin su Ahmed yayi sanyi
kuma mamaki ya rufe su yaya
za’ayi Hannah ta fara
kuka tun kafin taji waye aka
zabar mata ta aura. Ko akwai
wanda
ta kudira zata aura ne basu sani
ba? Inna Rabi ce ta ce “Hannah
kukan me kike bafa cewa muka
yi dole sai kin auri wannan
wanda muka zabar miki ba idan
kina da
wanda kike so fadi mu aura
miki. Daman ganin babu kowa
ne shi yasa muke tunanin
hadaki da wani.
Hannah ta share hawaye ta
girgiza kai ta ce “Babu wanda
nake so zan aura duk wanda
kuka zabar min
zanyi biyayya in aure shi ko
waye, kuma nasan baza ku
zabar min wanda zai cutar da ni
ba. Gaba daya
suka fara shiwa
Hannah Albarka suna jinjina
mata bisa tsananin biyayya da
take yi musu, Allah Ya yi mata
albarka. Kawu Ahmad yayi
gyaran murya ya gyara zama ya
ce “Hannah tun farkon zuwanki
abokina
koma in ce ya zama dan uwana
saboda tun muna yara muke
tare nasan halinshi ciki da bai
fiye da Uwar da ta haifeshi bata
sanshi ba fiye da yadda nasan
yadda yake, yana da mutunci da
sanin ya kamata ya ce yana
sonki tsakani da Allah zai aureki
wannan aboki
nawa shine Bello Madu abokina
din nan da muka je Nigeria
garinku dashi muka dauko ki,
yana da sana’arsa kuma yana da
ilimi gaba daya boko da arabiya
yanzu ma babba ne ba laifi a
aikinsa aikin custom yake sune
suke tsaye a bodar Nigeria zuwa
niger. Ni dai a ganina Bello
Madu ne kawai ya cancanci ya
aure ki ko ya kika
gani?
Iya Ma’ida ta ce “Wanne irin yaya
ta gani bayan ta gama magana
ta ce ko waye muka zabar mata
tana so. Cancanta ma ai ba sai
an fada ba sun dace ai.
Hannah ta sunkuyar da kai sai
hawaye shar ya sake keto mata.
Bello Madu kam ya cancanci a
soshi bashi da makusa kyau
kuwa kamar shi yayi kansa dan
buzayen
asali kamar balarabe, hankali da
tausayi kuwa ba’a magana don
da yaji labarin Hannah hawaye
ya dinga yi don tausayinta bashi
da makusa ko kadan amma ita
abun da ya kara sata kuka shine
tana matukar ganin mutuncinsa
don haka bata so aka ce shine
zai aure ta ba don duk wanda
ya aureta sai yayi hakuri
saboda bazai sami soyayyarta
ba GANGAR JIKINTA zai aura
zuciyarta na wajen Haisam har
abada. Hankalin Hannah ya sake
tashi sosai da taji sunan wanda
zata aura. Kawu Ahmad ya ce “Ni
wannan kukan naki ne yake
tsoratani Hannah kiyi magana
idan akwai wani abun da yake
damunki. Hannah ta yi dan
murmushi ta
girgiza kai ta ce “Babu komai
zabin da kuka yi min yayi.
Inna Goshi ta dau buda kowa ya
hau cewa “Allah Ya sanya alheri
ya baku zaman lafiya. Hannah ta
mike
ta shiga cikin gida bata tsaya a
ko’ina ba sai cikin dakinta ta
rufe kofa ta fada kan katifa sai
ta bude
shafin kuka mai tsanani taji a
ranta kamar wata sabuwar
soyayyar Haisam aka kara zuba
mata taji
sonsa ya sake sarketa kamar
zata yi hauka. Bayan anyi haka
da kwana uku Hannah na zaune
tsakar gida tana tankaden gari
da yamma tana taya Hajir aiki,
Hajir kuma na wajen murhu
tana kada
miyar kuka, suna taba hira. Hajir
ta ce “Hannah ina ganin kinfi
sauran mata yin sa’ar samun
kintsattsan miji a duk *yan
matan garin nan saboda duk
yawanci
*yan matan garin babu wacce
bata kaiwa Bello Madu hari ba
farin jini gareshi sosai.
Kyawunsa ne, ko kuwa iliminsa,
ko kuma jan ajinsa ne yake
rudarsu oho? Amma ke
gashi kwatsam ya damu da
sanki kinsan tun ba yauba
Kawunki Ahmad ya fadamin
cewar Bello Madu yana sonki
amma ya gargadeni da nayi
shiru kai in
sanar miki har sai ya sanarwa
da magabatansa shima.
Hannah ta cije tayi dan
murmushi ta ce “Hajir kenan
wato nayi sa’a sosai ashe dana
sami Bello ta sama, ba tare da
nasha wahala ba? Amma ni a
wajena sai dai ma
ince shine yayi sa’a sosai ma
kuwa. Alhamdulillahi amma
akwai matsala tabbas.
Hajir ta juyo gaba dayanta tana
kallon Hannah can ta ce “Ban
gane akwai matsala ba, wacce
irin matsala kuma Hannah? Ko
bakya sonsa ne? Hannah ta
girgiza kai ta ce “A’a naki shi
bayan shine zabin Iyayena ina
sonsa mana. Muryar Bello Madu
ce ta ce
“Assalamu Alaikum. Kai tsaye ya
shigo cikin gidan kamar yadda
ya saba shigowa daman. Kai
tsaye wajen Hannah ya dosa,
Hajir ta amsa masa sallamarsa
gami da yi masa tsiya
ta ce “Oh dan halak kaki ambato
yanzu zancenka fa muke yi ango
kasha kamshi daga zuwanka ka
doshi wajen Hannah, da idan
kazo wajen wa kake dosa?
Bello Madu ya kyalkyale da
dariya ya ce “Kai Hajir kin fiye
tsokana kinsan da sai inyi sati
biyu a boda ban damu da zuwa
garin nan in kwana ba amma
yanzu
kusan kullum sai nazo garin nan
ko banzo gidan nan ba ina jin
dadin garin saboda matar da
nake so tana cikin garin. To
yanzu an bani izini inzo wajenta
kina nufin sai
in doshi wajenki duhu, bayan
daga shigowata hasken fuskar
Hannah ne ya bugi idanuwana.
Kinsan ko a kabari haske ake
nema ana neman tsari da duhu.
Hajir ta rike baki ta ce “Ah Bello
Madu daina hadani da duhun
kabari Allah Ya baka hakuri.
Wannan hira tasu ta bawa
Hannah dariya bata san sanda ta
tuntsire da dariya ba duk da
wani kululun bakin cikin daya
dira
a ranta yanzun nan da Bello ya
shigo. Haisam kawai zuciyarta
take haska mata, inama- inama
ace da Haisam za’ayi musu
auren nan wata guda ya rage
ayi bikinta. Bello Madu ya ce
“Hajir yi hakuri
bada duhun kabari nake hadaki
ba ni na isa? Ai nasan kokarin
da kike min wajen turani fadar
zuciyar
Hannah tun dazu ina zaure a
tsaye ina jin hirar da kuke yi,
kuyi hakuri ba labe nake yi
muku ba ina doso kaina Bello
Madu naji ana ambato shiyasa
na dakata sai da na gama jin
komai.
Hajir ta yi dariya ta ce “A’a Baba
Bello ka fara labe a gidan
mutane dai kawai zaka ce min.
Ya karasa wajen Hannah ya
jawo wata kujera a gefenta ya
zauna a hankali yayin daya
kafawa Hannah ido yana
kallonta, ji yake tamkar ya
hadiyeta saboda son da yake yi
mata, fargabarsa daya yana
tsoron kada Hannah taki
amincewa da soyayyar da yake
yi mata haka nan
ko bayan abokinsa Ahmad ya
shaida masa an bashi Hannah
yayi farin ciki amma farin cikin
ragagge ne yana gudun kada a
takurawa Hannah ta aure shi
yazo ya rasa soyayyarta amma
yau sai gashi da kunnensa yaji
Hannah ta ce “Ni na kishi bayan
shine zabin Iyayena ina son sa.
Don haka yau yafi kowa farin
ciki. Hannah ta dago a kunyace
ta gaishe shi ya amsa cike da
fara’a ya mika hannu ya karbi
rariyar dake hannunta ya fara
tankade Hannah na zuba masa
gari yana tankadewa. Hajir
kuma tana yi masa tsiya tana
cewa “Wai
Bello wannan bamu san wanne
irin abu za’ayiwa Hannah ba
bayan anyi auren, tuwan ma nasan kai
zaka dinga tuka mata.

Hmm wai ya abin yake ne!!?

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE