Gangar jikinsa na aura18

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter18

Cikin shesshekar kuka Hannah ta ce “Kawu na
zalunci
kaina, na kuma zalunceka da ban fada maka
gaskiyar
abunda yake damuna ba. Kawu na kasance ina
cikin
wani hali na tsananin damuwa wanda har nake
tunanin
bazan iya auren kowa ba. To amma dole nasan
za’ayi
min aure shi yasa na hakura na amince na aureka
a
tunanina zan iya daurewa in zauna amma yanzu
bayan
da akayi auren ciwon da yake damuna ya dawo
min
danye bana jin zan iya zaman aure har in samu
aljarnar da kowacce mace take nema a karkashin
tafin
kafar mijinta ta hanyar biyayyar aure. Kawu kayi
hakuri
ka yafe ni dan Allah ka rufamin asiri. Ka
sauwakemin
mu zauna a haka ba tare da kowa ya sani ba,
saboda
sai in halaka idan muka zauna a haka da igiyar
aurenka. Bello ya bude baki yana kallon Hannah
can ya
taso yazo gabanta ya durkusa ya rike hannunta
cikin
siririyar murya mai dauke da tsananin dimaucewa
ya
ce “Hannah, fadamin ni Kawunki ne mai shirin
taimakonki ta kowacce hanya kada kiji tsoron
fadamin
ko mene ne. Ta janye hannunta a hankali ta
share
hawayenta ta ce “Idan baka manta ba a labarin
dana
baku a garinmu nace nayi makarantar sakandire
da
taimakon Allah da taimakon Yaya Haisam, son
Yaya
Haisam ne ya zame mun dafi a zuciyata wanda
dafin
nan zai iya zamar min ajalina. Kawu Bello ina son
Haisam harni kaina ina mamakin yadda akayi
zauciyata ta kamu da sonsa haka nayi addu’ar
don
Allah Ya goge mun, nayi azumin nayi kukan
kullum
akan Allah Ya yayemun amma kamar karamin
ake.
Daga karshe sai nake addu’ar Allah Ya dauki
raina da in
dauwama a haka amma ka ganni har yanzu a
haka na
rasa yadda zanyi. Ta rushe da kuka. Bello yayi
shiru
yana kallonta can ya nisa ya ce “Hannah me
yasa baza
kiyi addu’ar Allah Ya hadaki da Haisam ba kuyi
aure
kike addu’ar Allah Ya yaye miki sonsa ko kuma
Allah Ya
dauki ranki? Hannah ta goge hawaye ta ce
“Haisam
yayi aure a ranar da Mahaifina ya rasu “Bello ya
gyara
ya zauna a gaban Hannah ya lankwashe kafa don
jin
labarin wannan rikirkitaccen ala’amari na
Hannah.
Hannah bata boye masa ba ta bashi labarinta da
Haisam tun daga ranar da Babanta ya kaita
makaranta
har ranar da taje gidansu ta iske shi zai tafi
daurin
aurensa, daga karshe ta ce “Ashe Yaya Haisam
ba sona
yake ba taimako kawai yayi min ni kuma zuciyata
ta
kamu da tsantsar kaunarsa. Don haka ne a koda
yaushe nake addu’ar Allah Ya yayemun sonsa
bana
addu’ar Haisam yazo ya aureni. Bello Madu yayi
murmushin karfin hali ya ce “Haisam yana sonki
yana
kaunarki sosai fiye dani kaina da duk wani mai
sonki a
duniya. Akwai wata matsalar da tasa bai aureki
ba
Hannah.
Hannah cike da mamaki ta kurawa Bello ido ta ce
“Me
yasa kace haka, me ka gani da ka fadi haka?
Bello ya ce
“Saboda ke yarinya ce shi yasa baza ki fahimci
hakan
ba, kuma nasan irin yadda kike ji Hannah bawai
haka
ta taba faruwa akai na ba a’a ina kwatanto nima
rayuwata zata iya shiga irin wannan halin da kika
shiga
idan na rasa kine, saboda kece wacce na taba ji ina
so a
duniya. Ni na yadda na amince zan ci gaba da
zama
dake a haka a matsayinki na matata amma babu
zancen saki a tsakanina dake in Allah Ya yarda
sai dai
mutuwa ta raba mu saboda son da nake miki,
Hannah
da ace Haisam nacan yana jiranki baiyi aure ba
da zan
daukeki in kaiki wajensa in aura miki shi don kiyi
rayuwa cikin fari ciki, ni in dawo gida in zauna
ciwon
son da nake yi miki ya kashe ni na yadda in dai
na ceto
rayuwarki. Amma yanzu da yake Haisam yayi
aure kiyi
hakuri, a cikin kashi dari bisa dari na soyayyar da
kike
yiwa Haisam, ki daure ki bani kashi daya a cikin
dari
har karshen rayuwarmu ta aure na gode. Hannah
ki
daure ki ci gaba da zama dani a haka kada ki
barni ni
dake muyi biyu babu, kin rasa Haisam ni kuma in
rasa
ki. Yasa hannu ya jawota jikinsa zai rungumeta
tayi
sauri ta mike ta juya masa baya. Ya tashi a
sanyaye
yaje ya rufe kofa ya datse da mukulli. Yayin da
Hannah
taji wannan rana tamkar ranar da Mahaifinta ya
rasu ta
kuma rasa Haisam yau gata a daki daya zata
kwanta
gado daya da wani a matsayin mijinta ba Haisam
ba.
Hawaye yaci gaba da tsiyayo mata daga
idanuwanta.
Bello yazo ya rungumeta ta bayanta yana mai
sunbatar
kunnuwanta da gefen kumatunta cikin
sanyayyiyar
murya Hannah ta ce “A matsayinka na mijina
akan
babu yadda zanyi ka sami GANGAR JIKINA amma
ruhi,
zuciyata tana wajen Haisam. Bai iya bata wannan
amsar ba cik ya dauketa ya dorata a tsakiyar
gado.
Hannah ta shide tama fita haiyacinta saboda
tsananin
bakin ciki yau ga wani daban zai fara saninta *ya
mace
kafin Haisam, wannan bakin cikin ne yayi mata
yawa
yasa ta fita hayyacinta tama iya cewa suma tayi
amma
gogan naka baima lura ba ji yake yau tamkar an
masa
albishir da gidan aljannah gashi ya auri Hannah
harma
ta mallaka masa GANGAR JIKINTA.
A ranar da Hannah ta cika sati guda ta fara sanin
halin
Uwar mijinta ashe da kara take yi mata. Da
sassafe ko
tashi daga bacci basu yi ba Inna Haule tayi dirar
mikiya
a bakin kofar dakinsu tana bugun kofar da karfi
tana
fadin a tashi haka baccin ya isa duk inda sati
guda yayi
angama cin amarci bakunta ta kare kin zama
*yar gida
fito ki dora dumame. Indo zata je rafi debo ruwa.
Furgirgit Hannah ta mike ta diro daga kan gado,
ta bude
kofa ta fito. Ta durkusa har kasa ta gaishe da
Inna
Haule. A yatsune ta amsa ta ce “To a tafi wajen
murhu
a dora dumame ga dawa da gero can idan kuka
karya
kumallo ke da Indo ku surfa. Bello wanda yaji
tamkar
yayi ihu saboda takaici yasan Hannah kuma ta
shiga
uku ta lalace kamar yadda amaryar Babansa Indo
take
dandana wahala kullum kamar baiwa. Ya tashi
zaune
ya rike kai tausayin Hannah yana ratsa zuciyarsa
da
tunano ina zai samo mata mafita kafin ta zama
baiwa.
To amma babu wata mafita tunda har yau har
wayewar
gobe Inna Haule ta ki amince masa ya koma
gidansa
shi da matarsa. Da ya isheta ma da maganar sai
ta ce
duk ranar daya sake rokonta wannan bukata tasa
Allah
Ya isa kuma zata tsine masa, don haka Bello yaja
bakinsa yayi gum.
Haka Hannah ta kasance tana yin iya kokarinta
na
ganin ta farantawa Uwar mijinta tana binta sau
da kafa
kafin ta saka ta aiki tuni ma tayi mata, amma a
banza
Inna Haule bata gani. A ko da yaushe zagin
Hannah
take tana cewa auren da ba gara ma ai bai cika
aure
ba. Wai Hannah ta mallake mata da don da sai
yayi sati
biyu, uku bai zo garin ba daga wajen aikinsa
amma
yanzu baya sati guda. Zantuttuka barkatai
marasa
ma’ana dai na nuna tsana tsagwaronta. To
wannan
al’amari yasa Hannah ta sake fitar da rai daga
samun
zaman lafiya a rayuwarta. Inna Haule halinta
daya da
Iya Abu koma tafi Iya Abu, ko Uwarka ka yanka
musu
ka dafa ka basu baza su gode maka ba. Sai dai
kawai
idan abun ya isheta ta shiga daki tayi kuka ta
gaji. Idan
Bello Madu ya dawo ya ganta a wannan hali sai
ya
shiga lallashinta yana bata hakurin nan nasa,
babu
abinda yake karawa Hannah banda takaici. Abu
daya
ya gano logarta in har yana so tayi dariya a duk
Bakin
bacin ran da take, shine ya ce mata Haisam.
Haka yake
sakata a gaba ya tilasta mata ya ce dole sai ta
bashi
labarin Haisam tun tana jin kunya da nauyinsa
har ta
saki jiki tayi ta bashi labarin Haisam na dariya
suyi
dariya na tausayi ya tausaya mata, na tambaya
ya
tambayeta. Da haka Bello ya fara samun shiga a
wajen
Hannah. A koda yaushe Hannah na kirga
kwanakin
yaushe Bello zai dawo daga wajen aiki saboda
dashi ne
kawai take hira mai dadi har tayi dariya hirar ita
ce
hirar Haisam.
Hannah da Indo ne suke surfe a yau, Inna Haule
ta fita
unguwa shine ma suka samu suna *yar hira. Duk
da
Indo ta girmewa Hannah amma duk da haka bata
fi
shekara ashirin da shida ba a matsayin suruka
take a
wajen Hannah tunda matar Baban mijinta ce.
Amma
dole tasa suka zama kawaye. Hannah na bakace
dusar.
Indo tana tikar dawa a turmi, Indo ta tsagaita da
dakan
ta ce “Hannah sai dai hakuri ni harna saba da
wannan
bauta haka Allah Ya rubuto mana rayuwarmu.
Hannah
tayi ajiyar zuciya ta ce “Allah Yana barin
bawansa a
halinda Ya so Ya ganshi. Amma duk abubuwan
da Inna
ke yi mun baya damuna irin duk abunda muke yi
mata
batagani, dubi fa irin aikin da muke yi kamar
zamu
mutu yanzu idan tazo cewa zata yi munyi ha’inci
bata
surfu ba. Ga zagin da take yimin akan gara ni na
rasa
yadda zanyi da rayuwata wallahi. Indo ta ajiye
tabarya
ta ce “Ai wai ke kina nufin duk abinda ake baki
sani ba
a gidan nan yau? Hannah ta ajiye faifan dake
hannunta
ta tattara hankalinta gaba daya a wajen Indo
tana jiran
taji me yake faruwa. Indo ta ce “Ko da yake kin
tafi
debo ruwa dazu da sassafe Inna Haule tasa na
shiga
dakinki na miko mata akwatinan aurenki guda
biyu
wadanda baki dinka kayan ciki ba tasa almajiri ya
daukar mata wai zata kai wani gida ajiya tunda
ba’ayi
miki gara ba suma baza ki daura lefansu ba.
Daman wata uku ta daukar miki a kawo gara
gashi
yanzu kin shiga wata na hudu da aure. Don haka
da
zarar Bello ya dawo zata sa ya sake ki, lefan
kuma ta
kaiwa wata yarinyar a daura masa aure da wacce
zata
kawo mata gara. Kuma kinsan Bello babu yadda
zaiyi
idan tasa shi a gaba ta ce ya sake ki. Hawaye ne
sharrr
yake zuba daga idanuwan Hannah ta mike da
gudu ta
shiga daki ta tarar wayam an kwashe akwatina
sai
kwaya daya *yar karamar kaya kala uku ne ta
dunka a
lefen, su suka rage sai sauran tsofaffin kayanta
nada
ga sunan a zube a kasa an watsar mata. Sai ta
kwanta
a kan gado ta fara rusar kuka, Hannah ta kware
wajen
iya kuka dan ko gasar masu iya kuka aka je ta
duniya
ina ganin ita zata zo ta daya. Can ba dadewa
Inna
Haule ta dawo ta tarar da Indo ce kadai take
aikin
abincin rana ta ce “Ina Hannah? Indo ta ce
“Ciwon ciki
take tana daki. Ta leka ta tarar da Hannah
sharkaf cikin
kuka sai ta ce “Babu wani ciwan ciki ba ciwan
ciki ba ko
ciwan nakuda kike sai kin bar gidan nan bazan
iya ba
harkar talauci anyi biki ko gara babu lefen dana
dauke
ne shine yasaki bakin ciki ya kwantar dake. Haka
Hannah
ta yini shiru a kwance babu ci babu sha sai kuka,
Allah
cikin ikonsa sai ya jeho mata Bello da yamma
kwanakinsa biyu jal da tafiya ba zato ba
tsammani
Hannah taji sallamarsa ya shigo, furgigit tayi ta
tashi
zaune kallo daya yayi mata yasan akwai abunda
aka yi
mata har ta sha kuka. Yaje da sauri ya zauna a
kusa da
ita ya jawota jikinsa ya tambayeta meke damunta
take
kuka. Ta amsa masa da ba komai, ya ce yasan
dole da
wani abu karta boye masa ta fada masa gaskiya.
Sai ta
ce cikinta ne yake ciwo, yayi shiru shi dai ya jita
ne
kawai amma bai gamsu ba. Sai can da aka jima
hankalinsa yakai wajen akwatina yaga basa nan
ya ce
“Hannah ina akwatinanki suke? Tayi shiru can ta
ce
“Inna ta kwashe ta kai ajiya wai tunda ba’ayimin
gara
ba wata zata kaiwa ta aura maka ita, ni ka sake
ni. Sai
ta rushe da kuka. Bello ya cije baki don tsananin
bakin
ciki yayi shiru ya kasa magana sai yasa hannu
yana
goge mata hawaye ya nisa ya ce “Daina kuka
kece baki
sani ba na bawa Ahmad kudin da zai saya miki
gara
kakaf, yanzu ma cikon kudin da zai karasa
sayayyar na
kawo masa. Daman zan koma wajen aiki tunda
ina da
aikin dare. Daman Inna bata ganni ba ance tana
makwabta bari inyi sauri in tafi baza ta san nazo
garin
bama balle tayi min maganar sai in cewa Ahmed
suyi
kokari su kawo garar gobe kinga an kashe
bakinta kafin
in dawo. Ya rungume Hannah ya sumbaci
kumatunta
ya ce “Bazan sake ki ba Hannah ina sonki da yawa ki
kwantar da hankalinki kinji ko? Sannan ya fice
yana
sauri ya tafi. Hannah ta bishi da kallo yayin da
zuciyarta ke ce mata “Ba Haisam kadai ba Bello
Madu
ma mai sonki ne Hannah ki kaunace shi.
Haka kuwa akayi washe gari da misalin karfe uku
na
yamma sai Hannah taji buda an doso cikin gidan
kamar a mafarki taga kartan maza suna ta ajiye
buhunhuna a kofar dakin Innah Haule. Mata suna
ta
shigowa da fantekun alkaki, nakiya dibulan da dai
sauransu. Wannan al’amari ya bawa Inna Haule
mamaki, nauyi da kunya saboda sunyi mata bazata
duk tabi gari tana fadin ba’ayiwa Hannah gara ba
kuma
ba zasu iya yi ba kwatsam sai taga gara wacce
ko
*ya*yan attajiran garin ba’a taba yi musu gara
mai
yawan buhunhuna haka ba.
Hmm bello madu dai ya bude wuta wato shida hanne mutu ka raba me zai faru? Ku biyoni!!!!!

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE