Gangar jikinsa na aura19

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter19

Nan dai Inna Haule ta hau borin kunya tana cewa “Ashe kuna tafe ku ka ki sanar min nima in gayyato *yan uwana suzo su tayani karbar irin wannan abun alhairi sannunku da zuwa ku shigo daki mana ya zaku zauna a waje. Hannah debo tabarmarki dana Indo a shimfidawa baki. Ai da kun sanarmin zaku zo da nasa anyi muku girke-girke da soye-soye irin wannan abun arziki haka. *Yan uwan Hannah suka ce “Babu komai ai ba zama muka zo yi ba mun kawo gara gata nan, zamu koma don *yar mu ta sami salama a zamanta na aure da mijinta. Suka yaba mata ba dadi.
Washe gari da sassafe Inna Haule taje ta debowa Hannah akwatinanta ta kawo mata amma an kwashee wasu kayan da yawa babu. Ta kuma gargadi Hannah kada ta sake ta fadawa danginta ko mijinta tayi shiru da bakinta. Da Bello Madu ya dawo faran-faran Inna Haule ta kira shi ta nuna masa gara har tana cewa “Allah Sarki ashe ba karamin shiri suke yi ba shi yasa basu kawo da wuri ba irin wannan yawan gara sai ka ce *yar Sarkin noma ka auro. Bello yayi dariya ya ce “Allah Ya sanya alheri ya bamu zaman lafiya. Ya nufi dakin Hannah, bayan tayi masa sannu da zuwa ta kawo masa abinci da ruwa ya sha, sai ya janyo akwatinan ya bude kamar yadda ya zarga tabbas Mahaifiyarsa zata kwashe wasu kayan, haka kuwa ya gani ta kwashe kaya da yawa. Ya waiga ya Kalli Hannah sai ta sunkuyar da kanta kasa bata ce masa komai ba. Ya ce Hannah an kwashe miki lefenki ko? Kiyi hakuri zan suyo miki wasu insha Allah idan muka yi albashi wani watan. Hannah ta dago cikin ladabi da tattausar murya ta ce “Ni na yafe duniya da lahira ba sai ka biyani ba, wahalar zata yi maka yawa. Kawu Bello babu abinda zance maka sai godiya da wannan garar da ka yimin Allah Ya saka da alheri domin ka kwatar min *yanci na tun daga ranar da aka kawo Inna bata sake yimin gori ba. Yanzu zanyi zaman farin ciki a gidan aurena. Yayi murmushi ya ce “Farin cikinki shi ne nawa Hannah, Allah Ya kara sanya ki a farin ciki fiye dana yanzu. Ta ce “Amin na gode.
Karshen wata nayi Bello ya dau albashi sai da ya sissiyawa Hannah kayayyakinta da Mahaifiyarsa ta kwashe, cikin dare ya kawowa Hannah a boye ya ce ai hakkinta ne dole ya biya ta. Hannah tayi godiya ta karba. Haka Hannah da Bello suka kasance yana kyautata mata a boye komai ya gani na sakawa kona marmari sai ya suyo mata da daddare ya shigo mata da shi ya bata a boye ba tare da ya bari Mahaifiyarsa ta gani ba. Bello yana kara son Hannah saboda ladabinta hankali da nutsuwa da Uwa Uba tsananin hakurinta da tawakkali. Ita kuwa Hannah har yau har wayewar gobe ta kasa masanya gurbin Haisam ta mayar da Bello amma mafarkin Haisam take, idan tunani take Haisam kawai take hangowa a zuciyarta. Tana kokarin mayar da soyayyar da take yiwa Haisam kan Bello saboda ita ma ta saka masa soyayyar, saboda irin kyautata mata da yake amma abu ya faskara haka dai take dagewa tana nunawa Bello tana sonsa wanda a zuciyarta ba haka ba ne. Wasu lokuta da yawa idan suka tashi da safe, Bello yakan ce mata yaya Haisam? Don naji jiya kina kiransa a mafarki. Hakika Hannah duk sanda ta kwanta mafarkin Haisam take yi ashe har ambatonsa take a fili. Saboda tsananin son da Bello yake yi mata ya yarda ya amince kuma zai zauna da ita a haka. Bai taba nuna mata bacin ransa ba, ita kuwa Hannah sai taji tausayinsa ya kamata nauyi da kunyarsa ta lullubeta. Amma yaya zata yi tunda
GANGAR JIKINTA YA AURA zuciyarta na wajen Haisam.
Matsalar gara ta wuce tsakaninta da surukarta sai kuma matsalar da Inna Haule ta dauko ta dorawa Hannah ita ce har yanzu Hannah ko batan wata bata yi ba balle ta samu ciki. Fada da gori a wajen Inna Haule babu dare babu rana. Bello yayi kokarin ya wayar mata da kai akan cewa ba laifin Hannah bane ciki Allah ne ke badawa amma abu ya ci tura Inna Haule taki saurarawa Hannah cewa take ga sa’annin aurenta nan dukka ciki garesu wata bakwai-bakwai tunda yanzu watan Hannah bakwai da aure.
Yau Hannah tun karfe biyun dare take kai kawo a tsakar gida bacci ya gagari idanuwanta. Duk bude idon da Bello zaiyi sai yaga Hannah tana fita ko tana shigowa cikin dakin kamar a mafarki yake ganinta. Can yaji ana kiraye-kirayen sallar asuba tayi. Yasa hannu ya laluba gefensa yaji Hannah bata nan. Yayi firgigit ya tashi ya fito tsakar gida ya hango Hannah a gaban murhu tana hura wuta. Ya karasa inda take ya ce “Hannah yau lafiyarki kalau kuwa tun dare kike shige da fice kinki ki kwanta, yanzu da asubar nan wutar me kike hurawa? Hannah ta danyi murmushi ta ce “Kawu ka manta yau da duku-duku oganka ya ce zai aiko da mota za kuje Agadas shine nake dora maka ruwan wanka naji yau garin da sanyi-sanyi. Yayi murmushi ya ce “Ai jinsa nayi kawai, meye abun turo mota da duku-duku sai ka ce zamu bar kasar, Hannah ta ce “Agadas ai da nisa shi yasa, kuma watakila ba kwana za kuyi ba ko? Ya ce “Gaskiya Agadas da nisa ba kuma cikin garin zamu shiga ba Local Government din Agadas din zamu Aderbisanat local government zamu je ina ganin wajen 540km ne kuma bana jin zamu kwana ziyarar aiki zai kai can mu kuma yan rakiya ne. Hannah ta ce “Allah Ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya. Ina jin kiran sallah assalatu kafin ruwan yayi zafi ga buta ka fara yin sallah. Ta mika masa buta ta durkusa har kasa, Bello ya tsaya yana kallonta kawai saboda wata tsantsar soyayyarta ce take kara sarke masa zuciya. Musamman wannan kulawa da ladabi da Hannah take yi masa, ya karbi butar ya shiga ban daki, kafin ya idar da sallar Hannah ta hada masa ruwan wanka takai masa ban daki ta zo ta durkusa a gabansa har sai da ya idar ta ce masa ta kai masa ruwan wanka. Ya tashi ya shiga wanka, kafin ya fito ta debo masa wankakkun kayansa data wanke ta goge masa ta dora a kan gado ta goge masa takalmin da zaisa kamar yadda ta saba yi masa kullum.
Bayan ya kammala yana goge-gogensa da *yan shafe-shafe sai ya dauko kayan da Hannah ta fitar masa ya saka. Ta zo tana balle masa maballin wuyan rigarsa, yayi murmushi ya ce “Hannah na gode da irin wannan hidima da kulawa da kike nunamin wannan yasa nake kara sonki dari bisa dari, idan akwai soyayyar da tafi dari bisa dari ina miki Hannah sai dai anya kuwa na sami kwaya dayan nan kacal da nake so a sammin a cikin darin da ake yiwa Haisam? Cikin kunya Hannah ta ce “Haba daya kacal ai kafi guda daya. Ya ce “A’a Hannah zancen gaskiya muke, nawa aka karamin? Tayi dariya ta ce “Kawu ka wuce goma ma zaka kai sha biyar. Su duka suka tuntsire da dariya. Ya ce “To tunda a wata bakwai na sami goma sha biyar nan da shekara bakwai zan iya tadda Haisam. Suka sake tuntsirewa da dariya. Muryar Innah Haule ce ta katse musu dariyar da suke yi tana bakin kofar dakinsu tana cewa “Tun dazu magana nake muku baku jini ba kun shige daki kuna tuntsira dariya da duku-dukun safiyar nan to motar ofishinku ce ta zo suna ta kwankwasa gida. Daman Hannah abunda kika sani kenan ki shiga daki da miji kina dariya aikin kenan ciki fal kashi, babu gurbin kwanciyar da sai gurbin tarin kashi. Hannah tayi kasake jikinta yayi sanyi fara’ar da take ta koma ciki ranta ya baci domin da ana siyar da ciki da ta suyo, haka kuma da a wani waje ake nemoshi da taje ta nemo duk wahala koda kuwa zata mutu ne. Ko ta huta da wannan zagi da gorin da ake yi mata. Bello yayi ajiyar zuciya ya ce “Inna gani nan zuwa shiryawa nake. Ta wuce ta tafi tana tsaki tana cewa “Kaje ka dawo dai daga tafiyar kazo mu zauna muyi maganar
saboda bazai yu ba, in zuba muku ido haka kawai aure yau wata bakwai kenan babu ciki ba alamarsa kaina da kafata turawa yarinya abinci nake sai dai ta ci tayi kashi kawai. Ai ba dan tazo ta cika mana shadda muka aurota ba muma muna so muga dan jariri a gidanmu. Tunda ta shanye ka ta asurce ka baka ganin laifinta to ni bata asurce ni ba dole ma ka sake ta ka auro mai haihuwa don daki daya garemu a gidan nan. Har Inna Haule tayi nisa ta juyo ta dawo ta tsaya a kofar dakin su Hannah ta ce “Hannah kiyi ki fito daga dakin nan yau duk ke zaki yi aikin gidan nan shara wanke-wanke surfe da girki ki fara debo ruwa tukunna idan kin cika randunan gidan nan kakaf sai ki fara aikin gida da yamma kuma kije gona ki tsinko wake da gyada dan sun nuna. Yau wacce kuke aikin tare Indo aikenta zanyi garin magarya wajen kawata. Tunda ba ciki gareki ba ba goyo ba ai wannan aikin bazai gagareki ba, sai dai idan kinji kashi kiyi a gonar, tunda cikinki sai kashi babu haihuwa, kinga kuwa kashin naki ya zamar mana taki a gonar kinga kin taimaka kema. Bello Madu ya fusata baisan sanda ya ce “Haba Inna ki daina yiwa Hannah gorin haihuwa ba laifinta ba ne, rashin haihuwa Allah ne Yake bayarwa. Innah har yanzu daman Hannah ce take dauko ruwa a rafi ina almajiran dana dauko aiki nace zan dinga biyansu. Ita taji da aikin gidan su kuma almajiran suje gonar. Hannah tasa hannu ta toshe masa baki ta ce “Yi shiru karka sa taji haushina, Mahaifiyarka ce babu komai duk zanyi aikin.
Inna Haule ta rike baki ta ce “Inye dannan ka fara fada in fada dani akan matarka lallai abun babba ne, jeka ka dawo ka sameni don wallahi ina ganin zamanka ya kare da wannan yarinyar mai kama da tumatur ina ganin rabaka take so tayi da kowa a duniya har dani dana haifeka. Ba’a haiyacinka kake ba na sani bayinka bane. Ta tafi tana surutanta dai barkatai. Hawaye yana zuba shar daga idon Hannah, Bello yasa hannu ya goge mata zuciyarsa cike da tsananin tausayinta amma yafi jin tausayi kansa da kansa, saboda zaifi Hannah shiga wani hali idan Mahaifiyarsa tasa ya saketa don shine yafi sonta fiye da yadda take sonsa idan ya rabu da Hannah ya rabu da farin cikin rayuwarsa.
Kalma daya ce yasan idan ya fadawa Hannah duk irin bacin ran da take zata yi dariya idan ya ambaci sunan Haisam, yayi dan murmushi ya kalleta ya ce “Hannah dama a ce a yanzu haka kina da ciki ki haifamun da namiji in saka masa suna Haisam. Hannah ta dago ta dubeshi idanuwanta a cike suke da hawaye sunyi jawur don kuka amma saida murmushi ya subuce mata a take taji zuciyarta ta fara dan hucewa daga tsananin tafasar da take yi saboda kunar maganganun da Inna Haule ta fada mata. Hannah ta ji wani dan sanyi a ranta wani abu ya dazu a zuciyarta da Bello ya ce dama a ce tana da ciki ta haifi da namiji ya saka masa suna Haisam taji dama ace hakan ta faru . Amma data tuna yanzu ma haka al’ada take don haka zancen ciki ma babu shi, sai ta sake rushewa da kuka. Bello ya jawota ya rungumeta a kirjinsa yana shafa lallausan gashinta ya ce “Hannan lallai yau ranki ya baci sosai har in kira miki Haisam amma kici gaba da kuka kiyi hakuri ki yafewa Innata muci gaba da yi mata addu’a Allah Yasa ta gane gaskiya Allah Ya cusa mata soyayyarki a ranta. Hannah tayi ajiyar zuciya ta ce “Amin, amma ka tayani addu’a Allah Ya bani ciki kafin karshen watan nan ina ganin haka shi zai saka soyayyata a zuciyar Inna. Bello ya ce “Amin ya Allah, zan dukufa da addu’a kema kiyi Allah Ya amsa mana. Ya goge mata hawayen idanuwanta ya sumbaci kumatunta ya ce “Haisam sunan danmu fa. Hannah ta kyalkyale da dariya ta rufe ido sai taji wani farin ciki ya lullubeta. Ta tsuguna ta jawo takalminsa ta fara saka masa a kafa tana sake goge masa da tsumma. Ta feshe masa jikinsa da turare ta ce “Kawu Allah Ya kiyaye hanya ku je lafiya ku dawo lafiya. Ya ce “Amin Hannah Allah Yasa na zo na sameki lafiya cikin farin ciki. Yana tafiya yana waiwayan Hannah, itama ta fito har bakin kofar dakin ta tsaya tana daga masa hannu har ya shiga dakin Mahaifiyarsa sannan Hannah ta koma daki.
A zaune a kofar gado Bello ya iske Mahaifiyarsa tana tunani tana gyada kai ya durkusa ya gaisheta ta amsa a fusace ta fara masa fada ta ce “To dan nan abunda nake so da kai shine kada ka sake ka yimin musu akan duk hukuncin da na yanke akanka ina nemar maka aure a gidan dagacin garin nan *yar Sarauta ka dace ka aura tunda ka makalewa Hannah baza ka iya sakinta ba to ta zauna anan gidan tare dani ita kuwa waccan idan anyi auren sai a kaita gidan ka. Bello ya daga kai ya kalleta zauciyarsa cike da bakin ciki. Gidan da yasha magiya ta yarda akai Hannah taki yau gata da bakinta tana cewa yayi aure ya kai matarsa can amma bada Hannah ba. To ashe Hannah din ta tsana kawai. Ya nisa ya ce “Inna me zai hana mu tare mu duka da amaryar da Hannah duk in hadasu acan din. Ta girgiza kai ta ce “Na ce maka karka yimin musu ko? Haka naga dama, tashi kaje ka dawo din mu karasa maganar amma idan ka matsa akan sai ka mayar da Hannah gidanka zaka sa ince sai ka sake ta don wallah Hannah baza ta tare a wancan gidan ba sai dai idan bani na haifeka ba. Ko bayan raina ka kaita can Allah Ya isa. Bello ya rike kai don takaici can ya ce “Naji Inna na gode, dan Allah ki yafe min duk abin da nayi miki, idan na bata miki rai a rayuwata gaba daya. Ta yi dariya ta ce “Babu abinda ka taba yimin wallahi ko musun ma daka tarka kake mun bayin kanka bane ta shanye ka ne, na yafe maka Allah Yayi maka albarka. Bello ya mike ya fita hawaye ne shar yake fita daga idanuwansa. Yana fitowa yaga Hannah tana jika gero. Tayi sharkaf da hawaye daga gani ta gama jin duk maganganun da suke yi. Kallo daya yayi mata yaji hawaye ya sake kece masa. Ya zo ya wuce ta gabanta ya ce “Hannah kiyi hakuri, ki sake yin hakuri, Allah Yana tare da mai hakuri. Ta bishi da kallo tana hawaye yana waiwayenta yana hawaye har ya fice. Tayi shiru tana sauraren karar tafiyar motarsu har suka yi nisa ta daina jin karar motar. Ta rushe da kuka tana cewa a ranta. A bakin ciki ashe zan dauwama? Yanzu aure Inna zata sa Kawu Bello zaiyo ya tare da amaryarsa a gidansa ni abarni anan, me yasa Inna ta tsaneni? Me nayi mata ta tsane ni? Me yasa kowa ya tsane ni a duniyar nan? Ubangijina yana sane dani, Allah Ka san halin da nake ciki, Allah Ka fitar dani, Allah Kai ne abin godiya.
Bayan fitar Bello Madu da kamar awa guda. A lokacin Hannah tana surfa gero, Inna Haule tana tsakar gida tana cin dumamen tuwo, Indo kuwa daga wanka ta fito zata shirya ta tafi Magarya inda Inna Haule zata aiketa. Suka ji mota turus ta tsaya a kofar gidansu. Wani ma’aikaci ne mai sanye da kayan *yan sanda yayi sallama ya shigo ba tare da ya gaishe da su ba. Ya ce “Nan ne gidan su custom Bello Madu ko? Inna Haule ta tsaya da cin tuwonta ta ce “Nan ne amma baya nan waye yake nemansa? Ya ce “Ina zuwa. Ya fice, gaban Hannah ya dau faduwa daf-daf daman tun daren jiya ta kasa bacci sai faduwar gaba take. Ta jingine tabaryar da take surfe ta tsaya. Kawai ji suka yi ana cewa “Ku kama da karfi wajen kafadar zaku rike. Inna Haule ta zabura ta mike da gudu ta leko, Hannah ma ta biyota da sauri idanuwansu suka gane musu wannan gagarumin tashin hankali. Gawar Bello Madu ce ake shigowa da ita. Allah Yayi masa rasuwa a sanadiyyar hatsarin motar daya ritsa da su yanzu-yanzun nan suna hawa hanyarsu ta tafiya Agadas wata babbar mota ce ta gwara musu suka kutsa ta tsakiyar motar cikin ikon Allah Bello ne kawai ya rasu, sauran sun sami munanan raunika suna asibiti. Take Hannah ta fadi ta suma, yayin da Inna Haule take neman tube kayan jikinta don gigicewa, sai da aka rirriketa. Kafin ka ce kwabo gidan ya cika yayi makil da *yan Uwa da makwabta maza da mata.
An yi masa wanka, an suturtashi an kaishi an binne kamar yadda Shari’ar Musulunci ta tanada. Bello ya tafi ya bar rikicin gidansa kuma shi tasa ta kare a duniya, domin rikicin duniya da mai rai ake yi duk wani rai sai ya dandana mutuwa, Allah Ya sa mu cika da imani. Hannah ta yiwa Bello addu’a har yawun bakinta ya kame idan ta gaji da addu’a ta rushe da kuka tayi ta huta haka dai har akayi sadakar bakwai *yan zaman makoki suka watse aka bar *yan gida. Yayin da barci yake gagarar idanuwansu, kamar yadda Inna Haule take kuka cikin dare haka Hannah ma sai ta laluba kusa da ita taji ita kadai babu Bello sai ta tashi tayi ta kuka har ta godewa Allah. Kaico Hannah ta rasa kowa a duniya.
Hannah bata shiga wata matsala ba ta bangaren ci ko sha ko aikin gida ba har ta fita daga takabarta. Sai bayan ta fita daga takaba an fara zancen rabon gado sannan Inna Haule ta daka tsalle ta dire ta ce babu abunda za’a bawa Hannah na gadon danta tunda Hannah ba haihuwa tayi ba da Bello sai dai ta hada *yan komatsanta ta bar musu gida. Kawu Ahmad yaji haushi sosai ya kuma lashi takobin ko sama da kasa zata hade sai ya kwatarwa *yarsa Hannah hakkinta na tumulin takaba shari’a shi da Inna Haule har kotin koli idan bata bari an raba gadon nan da Hannah ba. Ya ce kuma babu inda Hannah zata je gidan zata zauna saboda Bello yana da gado a gidan Ubansa. Inna Haule kuma ta ce ita kuwa baza ta bayar da dukiyar Bello ba sai dai su zuba.
Makudan kudi kuwa aka kawo daga wajen aikin su Bello, gashi da filaye da wannan tafkeken gidan nan daya sha sumunti da bulo. Inna Haule kuwa ta ce duk nata ne banda Hannah ko sisi baza ta bata ba tunda ko kwai bata saka a gidan ba. Tashin hankali ya tabbata a zuciyar Hannah ta rasa yadda zata yi da rayuwarta da Kawunta zai hakura ya bar Inna Haule ta rike dukiyar Bello dukka ba sai an raba da ita ba. Saboda duniyar nawa take wanda ya tara ma ya tafi ya barta kowa ma mutuwa zai yi. Duk wani hango jin dadin rayuwar duniya ya goge a zuciyar Hannah babu abunda take bege sai mutuwa tazo ta dauketa ta tafi ta huta itama. Daga gidan Kawu Ahamad ake aiko mata da abincin dare da rana. Tafi tafiya suma wata rana basa aiko mata don yau da gobe sai Allah. Hannah ta fara fitar da zannuwan daurawarta da kwanukanta tana siyarwa sannan ta ci abinci.
Hmm hanne na ganin jarabawa
Mai zai faru!!!? Ku biyoni

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE