Gangar jikinsa na aura2
Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA
AURA
Chapter 2
Irin tsananin azabar da
suke gallaza mata da
bautar da ita din da ake
tamkar baiwa alokacin
cinikin bayi. Ta ce a ranta
“Da ina murna zanzo makaranta nabar gidan da
bana hutawa kuma ban
taba hutawa ba sai yanzu.
Gashi yanzu makarantar
ma sun koro mu dole mu
koma gida. Taci gaba da tuna irin tataburzar da aka
sha da Mahaifinta kafin Iya
Abu tabar su suka fito
daga gida zuwa
makarantar nan. Wai ita
idan Hanne ta tafi babu mai yi mata aikace-aikace su
shara wanke-wanke,
debo ruwa a rafi ko tuka-
tuka. Saboda haka nema
taki fur wai baza a kawo
Hanne makaranta ba. Yaranta kuma garda-
gardane maza da mata suna
zaune ko tsinke basa
daukewa sai Hanne wacce
bata da uwa a gidan. Allah
Sarki hawaye ne ya kecewa Hanne yayi ta
zuba daga idanuwanta.
Maganar da daya daga
cikin masu gadin keyi ita ta
katse ta daga tunanin data
dulmiya tana yi. Taji kamar daga sama yana cewa “Kai
kauyawa ma da rashin
tunani suke dan kawai
ance yarka taci
makaranta sai ka taho ka
zabi makarantar data yi maka kawai ka sako kai,
dubi yarinyar daya kawo
sai kace mai zuwa tallar
kalwa riga a cukurkude,
zanin daga kasa ya nade
kamar an nade tabarma. Takalmin kafarta harda
leda ta daure waye zai ce
daliba ce. Daya ya ce
“Danmarar data ci kai kace
dandali zata, ta daure
kugu tamau. Ina jin ma basu san ana dinka kayan
makaranta ba (Uniform)
balle takalmi kambas da
safa. Hanne tayi ajiyar
zuciya ta hadiye yawun da
ya cika mata bakinta tayi shiru, kanta a sunkuye a
kasa. Tace a ranta “Lallai
ko nafi maye kwakwa
dole na hakura da
makarantar nan harda
kayan makaranta ake dinkawa. Waye zai dinka
min? Ta sake kallon kayan
jikinta tace a ranta “Kayan
sallar tawa shine suke
cewa duk a cukurkude? Ni
ina ganin nayi ado kowa a garinmu da muka zo
wucewa yana cewa Hanne
yau kuma ina zaki kika ci
ado haka? Su anan kazan-
kazan suke ganina ashe,
dole mu koma gida ashe ban rabu da wahalar Iya
Abu ba. Kuka ya sake
kece mata har da
shessheka. Malam Habu ya
kalleta fuskarsa cike da
damuwa ya ce “Yi shiru yar Baba bari zamu san
yadda zamu yi mu koma
gida. Ni yanzu ke nake ji
gashi kudin da ya rage
mun a aljihuna saura Naira
ashirin kacal. Da niyyata innakai ki makarantar in
zan koma gida sai in hau
mota daga nan zuwa
tashar Kazaure daga can
kuma sai in kama hanya da
kafa har Babban-mutum (garinsu) idan dare yayi
mun in sami waje in
kwanta washe gari na
tashi naci gaba. Har dai in
karasa ko kwana nawa
zanyi a hanya. To yanzu ba zai yuwu ba tunda gaki, sai
dai kawai mu shiga mota
muje tashar Kazauren, ko
a bakin tashar sai in siyar
da akwatin nan ko katifar
koma duka mu samu muyi kudin motar komawa
gida. Hanne ta zabura ta ce
“Ka siyar da akwati da
katifa fa kace? Kansila ai
sai yasa a kamaka, cewa
yayi fa gwamnati ce ta siya ta bani. Malam Habu yayi
kasake yana tunani na
wani lokaci mai tsawo can
ya ce “To laifin waye? Shi
kansila da maigari basu
san da kudi za’a zo makarantar ba, babu
wanda ya bamu ko sisinsa,
kansila kullum yana min
alkawarin zai je ya karbo
kudin da za ayi miki
siyayya da kayan makaranta da komai da
komai, har cewa yayi
motar gwamnati ce zata zo
ta kawoki. Daga karshe ya
zo ya fara hanya hanya tun daga
gwangwarmar akwatin nan da katifa da bokiti
babu abunda ya kara
kawowa. Bansan wacce
shawara suka yi da
maigari ba kuma daga
karshe suka ce inzo in kawoki haka za’a aiko
miki kayayyakin daga
baya. To yanzu gashi
takardar makarantar ce
babu aka yi mana korar
kare ina ga idan muka shiga ciki aka ce mu kawo
kudi, muka ce babu ai sai a
rakomu da duka.
Cikin sauri Hanne ta ce
“Lah Baba na tuna jiya
maigari ya aiko da wata takarda da yamma ya ce ta
makaranta tace, baka nan.
Na karba nasa a akwatina
ko itace suke tambaya?
Malam Habu cike da
mamaki da zumudin dauko takardar ya ce “Haba yar
Baba kina yar karamarki
kike mantuwa, tun dazu fa
ake maganar takardar
duk baki tuna ba. Yi maza
ki dauko takardar in nuna musu ko itace takardar.
Hanne ta daga akwatin da
sauri ta bude, babu komai
a ciki sai kayan sawarta
kala biyu a cukurkude
suke kamar anyi sukuwar doki a kansu. Ta binciko
can kasan akwatin ta
dauko wata doguwar
takarda fara ta mikawa
Babanta. Malam Habu ya
karba da sauri ya doshi wajen masu gadin nan
yana cewa “Ga dai wata
takarda a cikin akwatinta
sai yanzu ta tuna ashe mai
gari ya aiko da ita jiya ku
dai ku duba ku gani ko ita ce. A yatsune daya daga
cikinsu ya karba ya duba
yana dubawa kuwa yaga
takardar shaidar an dauki
Hanne Habu Imamu a
F.G.G.C Kazaure ce wato (Admission letter)
Sun sha mamaki kwarai da
ganin nan makarantar
kuwa taci ba batan kai
suka yi ba. Cikin sakin
fuska suka yi musu izinin su kwaso kayansu suzo su
wuce. Cikin murna Hanne
da Mahaifinta suka kwashi
kayansu suka wuce izuwa
cikin makarantan. Basu
tsaya a ko’ina ba sai a bakin wani babban gini
wanda ya kunshi
doguwar baranda da
ofishin Malamai.
Babu kowa a wajen hatta
leburori masu share-share da goge-goge duk basa
nan, wajen tsit kamar
babu bil’adama. Suka sami
gindin wata bishiya suka
sauke kayansu. Hanne ta
hau kan akwatinta ta zauna Malam Habu ya ce
“To fa wannan shine ko in
kula, yanzu kuma ina zamu
dosa ko kuma wa zamu
tambaya? Ni wallahi abun
nan na makarantar bokon nan ya ishe ni daga nan sai
can ana tsattsare ka da
tambaya kamar a lahira
mun gama da masu gadi
yanzu kuma Allah ne kadai
Ya san wa zamu hadu dashi, kai Allah Ya kyauta,
wannan shine ake cewa ba
shiga ba fita wai an bawa
mahaukaci gadin kofa.
Shigowar wata dalleliyar
mota ce Jeep launin koriya (dark green) wacce ta
tunkaro inda suke, ita ta
katsewa Malam Habu
surutun da yake yi. Ta zo
daf da su ta tsaya babu
abinda yake tashi a cikinta sai sautin kida da sanyin
A.C maza ne samari guda
biyu suka fito daga gani
wa ne da kaninsa, kanin
yana sanye da kayan
bautar kasa a jikinsa wato (N.Y.S.C) Yayan kuwa wata
tsadaddiyar shadda ce fara
sol a jikinsa sai kamshin
wani tsadadden turare ne
yake tashi. Abunka da
kauyawa sai kallo suke dukka uba da yar,
kanin ya bude but din baya ya
dauko wata Jakar kaya,
ya mayar ya rufe ya ce da
wansa “Yaya Habib, na
gode sai dai nace maka Allah Ya kiyaye hanya.
Yaya Habib yayi murmushi
ya ce “To madalla. Allah Ya
bada sa’a sai yaushe kuma
zaka zo mana weekend?
Ina fatan dai wannan karan zaka yi kamar wata
baka zo ba ko? Su duka
biyun suka tuntsire da
dariya, kanin ya ce “Ai
Yaya ranar juma’ar nan
zaka ganni a gida ko ba’azo daukana ba ma
zanzo Kano, haba ai sai jini
na ya hau zama a kauye in
ba dole ba wa zai iya?
Yayan yana dariya ya
mikawa kanin hannu suka gaisa ya ce “To Allah Ya
taimaka, ina ganin ranar
juma’ar da zaka zo may be
baza mu hadu ba saboda
da sassafe zan tashi zuwa
america kai kuma nasan sai da yamma zaka taho sai
an tashi yan makaranta
ko? Kanin ya ce “Eh kuwa
ba zamu hadu ba Allah Ya
kiyaye hanya Ya dawo
mana da kai lafiya, Yaya akwatinan auren da nawa
da naka ya zamo iri daya.
Yaya Habib ya ce “Insha
Allahu, Yaya Habib ya
shiga mota har zai ja kofar
motar ya rufe sai ya juyo ya kalli Hanne da Babanta
ya ce “Salamu alaikum”
Malam Habu ya amsa gami
da daga hannu, Yaya Habib
yaja motarsa ya juya ya
nufi kofar fita kanin na tsaye yana daga masa
hannu.
Bayan da motar Yaya
Habib ta kure, idanuwansu
duka na kanta sannan
hankalin kowa ya dawo jikinsa. Tunanin Hanne ya
koma ga kallon
kyakkyawan ginin
makarantar ginin bulo da
bulo, yaune rana ta farko
da take tunanin take sa ran zata kwanta a dakin
ginin bulo ba gidan kasa
ba rufin azara. Ta ce a
ranta “Cafdijan yau kuwa
zan iya bacci? Anya bazan
ringa jin sanyi ba a wannan dogayen
gininnikan. Bata san sanda
tayi murmushi ba har
hakoranta suka fito, sai ta
wayence ta kifa kanta
akan cinyarta kada Babanta ya gane
murmushin dadi take.
Kyakkyawan saurayin
nan ya tunkaro inda suke
yana rataye da jakarsa a
kafadarsa, ya yiwa Malam Habu sallama gami da dan
dukawa kadan, kana ya
wuce su yaje gindin wata
bishiyar dake kusa da tasu
ya daga wani benci ya
zauna ya ajiye jakar kayansa a kusa dashi yaci
gaba da kallon Hanne da
Mahaifinta. Can Malam Habu
yaje ya same shi a inda
yake zaune ya ce “Dan
Allah *yan samari kai maka’aikaci ne anan ko
kaima bako ne? Yayi
murmushi ya ce “Yaya aka
yi Baba? Malam Habu ya ce
“Yarinya na kawo
makaranta tun dazu banga kowa ba balle in
tambayeshi hannun wa ya
kamata in dankata?
Saurayin nan ya gyara
zama gami da cire hular
dake kansa ya ce “Daliba, daliba ce wannan? Malam
Habu ya ce “Eh nan aka ce
na kawota kuma gama
takardar can bari ta miko
Dama korarmu akayi dazu
da babu takardar, ya kwalla kira ya ce “Hanne
kawo takardar nan ta
dazu.
Cikin sauri Hanne tasa
hannu a cikin bokiti dake
gabanta ta dauko takarda tazo ta mikawa Babanta da
hannu biyu ta duka har
kasa. Babu abinda wannan
saurayi yake sai kallon
Hanne sama da kasa kayan
jikinta yake kallo da takalmin dake kafarta
wanda ta daure da leda
saboda ya tsinke kudin
nanin ma aiki ne, tasha wata
uwar danmara kai kace
damben tsiya za’a kwasa, wuyan, hannu da kafa
tsakiyoyi. Saurayin nan ya
kula da lallai Hanne ita
kanta tana jin kunyar
shigar nan tata ganin
kallon da yake yi mata, sai yayi sauri ya fara duba
takardar da Malam Habu
ya mika masa. Ya karance
tsaf, sannan ya dago ya ce
“Hanne Habu Imamu ko?
Tace “Eh, ya ce “To Baba sai kun dan jira don nima
nan Malamin nake jira
gashi takamaimai ma ni
bansani ba ko yana
makarantar ko bayanan
don nima shigowata kenan. Malam Habu yayi
Hamma gami da yin dan
siririn tsaki ya ce “Yaro
yanzu ba yadda za’ayi ka
karbi yarinyar nan, dole
sai waccan din ya zo? Saurayin ya ce “Ni Malami
ne amma kuma ba
permanent teacher ba
bautar kasa (service) nazo
yi, a ka’idar wannan
makarantar kuma senior master ne ya kamata ya
karbeta musamman ma
kasancewarta sabuwar
daliba ce. Gashi yau lahadi,
dama litinin ce ko sauran
ranakun aiki lokacin principal tana nan, da
sauran pamanent teachers
duk sai su karbeta koda
senior master baya nan,
amma yanzu ku jira kadan
idan nan da minti talatin bai dawo ba, zan tashi
nima na shiga staff quaters
din na gani ko yana ma
cikin makarantar dan nima
shi nake so na gani zan
karbi mukullan gidana. Malam Habu ya ce “To Allah
Ya kawoshi lafiya bari nayi
sallar la’asar, nasan biyar
tayi ko sallar la’asar bamu
yi ba. Yaro ina buta? Ya
nuna masa wani fanfo can kusa dashi kuma da
zagayeyyen waje nan ne
Masallaci. Malam Habu ya ce
“To madalla. Ya kalli Hanne
wacce ke tsaye a gefe har
yanzu ya ce “Yar Baba koma kan akwatinki ki
zauna zanje nayi sallah
kinji. Cikin sanyin murya ta
ce “To, ta juya ta doshi
wajen akwatin. Malam
Habu ya bita da kallo zuciyarsa cike da
tausayinta ganin yininsu
guda babu abun da suka ci
tun dan kokon safe da
suka dan kukkurba a
tsattsaye bala’in Iya Abu ya hanasu su zauna su sha
sosai. Malam Habu ya
girgiza kai alamar
tausayawa kansu da
kansu ya ce “Allah Sarki
yar Baba hakuri dai za ki yi, ki kuma ci gaba dayi.
Sannan ya juya ya nufi
wajen fanfo. Kyakkyawan
saurayin nan na zaune
yana kallonsu zuciyarsa
cike da alamomin tambaya da tsananin tausayi. Can ya
nisa yayi ajiyar zuciya ya
zaro gilashin dake
aljihunsa ya saka a idonsa
gami da cusa hular dake
hannunsa a cikin aljihunsa na wando yasa hannunsa
ya dafe habarsa yaci gaba
da kallon Hanne dake
zaune kan akwatinta tayi
lamo tana tunani ba tare
da tasan wani na nan gefenta ta cikin gilas yana
kallonta ba. Ya ce a ransa
“Wadannan daga wanne
kauye suke? Sun kuwa
karanta takardar dake
hannunsu sunsan me ya kamata su tanada suzo
dashi? Kai basu san dokar
da aka rubuta ba a jikin
joining instruction din nan
ba. Lallai kuwa da sun san
me aka rubuta da baza taci uwar danmarar nan ba ta
shigo makarantar nan
haka ba.
Bayan kamar tafiyar
Malam Habu da minti
ashirin sai gashi ya dawo. Ya zo ya wuce ta gaban
saurayin ya ce “Sannun ka
da hutawa, ya katse
tunanin da yake ya ce
“Yauwa Baba. Malam Habu
ya kara da cewa “Har yanzu dai kaga shiru baizo
ba ga rana nan na shirin
faduwa yau kuwa anya
mai karbar yaran nan zai
dawo? Yayi murmushi ya
ce “Ina ganin ka kawo duk abubuwan da aka ce
ta siya da kudin
makaranta zan yi kasada
na karbeta yanzu in yaso
ranar litinin wato gobe
idan mutum yazo ya rubuta risitai yanzu sai
nayi magana da masu
gadin get din Hostel su
kirawo prefect din….
Malam Habu ya matso kusa
dashi ya ce “Yaro fadamin da Hausa sosai na gane me
kake cewa? Har da wani
abu da zan kawo nan
gaba? Ya ce “Eh Baba, ai a
rubuce a jikin takardar
aka rubuta za’a dinka mata kayan makaranta
har kala hudu, wanda zata
sa idan zasu aji da wanda
zata saka a dakunansu,
dana wasanni (sport) duk
an rubuta kuma lallai-lallai sai da kayan makaranta
za’a karbeta ba zata ta
saka kayan gida ba,
sannan daga karshe aka
rubuta zata zo da kudin
makaranta (school fees) shi kuma da yake sabuwar
zuwace sai kun biya sama
da dubu….. Malam Habu ya
katse shi da sauri ya ce
“Tsaya yaro karma ka
kirawomin wadannan dubunnai. Ta faru ta kare
wai anyiwa mai dami daya
sata, yaro na gode
madallah, sai anjima. Malam
Habu ya juya ba tare da ya
jira amsa daga bakin saurayin nan ba ya doshi
inda Hanne ke zaune da
saurinsa kamar zai kifa
cikin gaggawa, ya ce “Yar
Baba tashi maza mu tafi ga
magariba ta kawo kai. Cikin sauri ta mike ya
ciccibi akwati ya dora mata
akai ya sungumi bokiti da
katifa suka kama hanyar
get din fita. Sunyi taku
daya biyu sai sai suka ji magana kamar daga sama
ance “A’a Baba ina zaku
kuma? Su duka suka juya
dan ganin mai maganar sai
suka ga wannan
kyakkyawan saurayin ne ya taso yazo wajensu.
Malam Habu ya ce “To yaro
me zamu yi in ba tafiya ba,
dubunnan kudi fa naji
kana kira, kumama ka tsaya
cak ka kalleni dani da dubu daya a yanzu waye ya
ajiye wani? Daman
kansilan garinmu ne da
maigari suka sani dole na
kawo yar nan
makaranta, suka ce za’a aiko da kudin, na tabbata
har ga Allah basu san
kudin yakai dubunnai ba
da suma basu tanka ba.
Kuma kudin gwamnati
ba’a bashi babu yadda za’ayi nazo na ajiye
yarinya a makaranta babu
kudin makaranta babu
kayan makaranta na ce a
bimu bashi zamu kawo.
“Wannan ba zai yiwuba, inji saurayin. Malam Habu
ya ce “To ka gani cewa
suka yi na zo na kawo ta
za’a aiko da kudin kuma
yadda naji kalamansa shi
kansilan a tunaninsa kudin makarantar bai wuce dari
uku ba, bai san dubunnai
bane kuma koda shine
yazo ya kawota aka kira
dubunnan nan cewa zaiyi
ta fasa karatun. Don ko karamar hukuma baza ta
biya wadannan makudan
kudaden ba.