Gangar jikinsa na aura21

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

 Chapter 21

Ramlah ta sharbe hawayen da suka cika mata ido
ta ce “Hannah, Haisam yana sonki, Haisam ne mai
sonki, babu wani mai sonki a duniya irin Haisam.
Haisam ya fi kowa kaunarki a cikin duk masu sonki
a duniya. Hannah ta ce “Ramlah me yasa kika ce
haka? Ramlah ta ce “Abun da yasa nace haka
shine Haisam bai taba yin soyayya ba sai a kanki,
bai taba ganin wata *ya mace ba a duniya da yaji
yana sonta kamarki Hannah. Hannah ta dago ta
kalli Ramlah ta ce “Amma Haisam ke ya fara so
kafin ma mu hadu dashi har yayi miki alkawarin
zai aureki. Ramlah ta girgiza kai ta ce Haisam ya
sanni tuntuni amma ba sona yake ba. Allah Ya
jarabeni da tsananin son Haisam tun muna
America idan sunje hutu gidanmu. Nasha sanarwa
Mahaifiyata sai ta ce kada ma in fara bazai yiwu
ba, saboda Mahaifiyar Haisam Kawarta ce tasha
gaya mata cewa Haisam bashi da ra’ayin soyayya
ya ce shi bai taba jin yana son wata ba kuma yana
ganin bazai taba ji ba. Har muka dawo kasar nan.
Amma naki hakura naci gaba da cusa soyayyar
Haisam a zuciyata, na dinga kokarin nunawa
Haisam irin soyayyar da nake yi masa amma sai
yake nuna min baisan abunda nake nufi ba. Da
naga haka sai na dinga bin ta hanyar Iyayenmu
don na sami Haisam. Da farko Mahaifina na samu
nasa masa kuka cewar in ba’a bani Haisam ba zan
kashe kaina. Mahaifina ya lallashe ni ya ce “Duk
mai sauki ne zai sami Mahaifin Haisam. Haka
kuwa akayi Mahaifina yaje ya sami abokinsa
Mahaifin Haisam ya shaida masa bukatata.
Saboda sanin ra’ayin Haisam akan soyayya bai
amsa masa kai tsaye ba sai dai ya ce zai tuntubi
Haisam zai kuma yi shawara da Mahaifiyar
Haisam. Kusan shekara guda bamu ji wata
cikakkiyar amsa ba daga gidansu Haisam, to sai
nasan Haisam yaki amincewa ne yasa babu wata
cikakkiyar amsa da naji game da bukatata akan
nifa har yanzu ina son Haisam. Babu irin kalmar
da Mahaifina bai furta min ba wajen wayar min da
kai akan na cire son Haisam, in so masu sona ga
sunan barkatai suna zuwa, naki na ce Lallai-lallai
sai Haisam.
Nazo nayi yajin cin abinci naki ci naki sha na
kaura daki sai kuka. Iyayena suna ta lallashina
naki canja ra’ayina. Shi kuwa Haisam bai san ma
abunda nake yi ba, yana can Jami’a yana
karatunsa. Kawarki Rauda Kanwata nake aike da
wasika in shaidawa Haisam halin da nake ciki
amma bai taba bani amsar wasikata ba. Ko da
naje gidansu baya cemin komai koda zamu yini
tare ko uffan bazai ce min ba. Haka idan yazo
gidanmu wajen Auwal Yayana abokinsa idan muka
gaisa babu abunda zai sake cemin ko hira nake
musu bai cika sa baki ba. Da Mahaifina yaga na
damu sosai da son Haisam shi ne ya sake samun
Mahaifin Haisam suka zauna suka yi magana
sosai Mahaifina ya nuna bacin ransa ya ce ba
yadda za’ayi suce Haisam yaki amincewa tunda
bashi ya haifesu ba, su suka haifeshi in har suna
so zasu san yadda zasu sashi ya amince dole.
Gudun kada abokantakarsu ta baci Mahaifin
Haisam ya kira Haisam ya ce “Ko yaki ko yaso sai
ya aureni. Da farko Mahaifiyarsa taki ta ce baya
yiwuwa a yiwa namiji auren dole a barshi tunda ya
ce bashi da ra’ayin soyayya gashi yanzu karatu
yake a lokacin yana shekara ta karshe a jami’a.
Mahaifiyar Haisam taga dai abun zai koma tashin
hankali tsakaninta da Mahaifana da kuma mijinta
sai ta amince ta ce ayi auren, ta ci gaba da lallaba
Haisam akan ya yarda ayi bikin. Da aka zo sa
ranar auren Yaya Habib sai aka hada damu. Aka
saka ranar auren mu shekara daya dai-dai lokacin
da Haisam zai gama bautar kasa ni kuma na
gama sakandire sai ayi bikin. Har lokacin da aka
saka rana Haisam bai taba zuwa gidanmu ba da
sunan yazo zance. Ni ce kullum nake yi masa
waya musamman da tsakar dare. Yana amsa mun
wayar amma wani lokaci sai yayi barcinsa abinsa
ma ya barni a layin wayar ina ta magama ni kadai.
Haka a cikin hirarrakin da muke akwai wasu
tambayiyi da nake yi masa bai taba amsa mun ba
sai dai yayi shiru. Tambayoyin kuwa sune Haisam
yanzu kuwa kana jin sona a zuciyarka? Me yasa
baka zuwa gidanmu zance? Idan ban ganka ba ko
naji muryarka bana iya barci kaifa? Baya amsamun
duk wata tambaya da ta jibanci soyayya. Na sani
kuma na gane Haisam ba sona yake ba kiri-kiri
amma idona ya rufe tunda ni ina sonsa zan iya
zama dashi a haka.
Haisam yana bautar kasa a F.G.G.C Kazaure ina
gida ina jiransa ya gama sai ranar daurin aure a
bada da sadaki in zama matarsa kawai ya tage.
Kwatsam da Haisam ya kammala bautar kasa sai
ya ce shifa ba yanzu za’ayi bikin ba a yi na Yaya
Habib tunda shine babba ayi namu daga baya. Aka
yarda da bukatar Haisam tunda lallabashi ake yi
akayi bikin Yaya Habib. Sai kawai muka ji Haisam
ya koma F.G.G.C Kazaure a matsayin cikakken
Malami wai shi koyarwa yake so yayi shi yasa ya
nemo aikin acan. Na ce na yarda ayi bikin zan iya
binsa Kazaure mu zauna. Haka dai Haisam yayi ta
yi mana hanya-hanya yaki yarda ayi bikin. Da
yaga an takura masa ance ya baro Kazaure ya
dawo Kano ga kamfanin Babansa anan zaiyi aiki
ayi bikinmu kuma sai ya ce shi ya amince idan na
sami wani in aura don shi kuma sai nan da
shekara biyar. Na ce na yarda zan jira shi in shiga
Jami’a kafin nan nima na kare sai muyi auren
kawai. Ran Mahaifina ya baci Mahaifiyata ta
zazzageni ta ce bazan jira shi ba sai kace bani da
zuciya wanne irin so ne wannan. A lokacin akwai
wani saurayina mai suna Dalhatu dan jarida ne
yana sona sosai, yana so ya aureni nace bana
sonsa bazan aureshi ba dai-dai lokacin nan an
tura shi B.B.C London ya ce idan anyi bikinmu sai
ya tafi dani can London nayi karatun jami’ata, naki
fur. Babu irin nasihar da Iyayena basu yimin ba da
lallashi naki ji nifa idan ba Haisam ba sai dai in
fasa aure. Iyayen Haisam ma sun yi iya kokarinsu
wajen tilastawa Haisam ya dawo yazo ayi bikin
nan namu sai ya daina zuwa week end dinma da
yake zuwa kwata-kwata. To kowa ya rasa yadda
zaiyi da mu suka zuba mana ido sai addu’a.
Na shiga Jami’a a nan Kano B.U.K ina karantar
bangaren labaran *yan Jarida (mass
communication). Ina karatuna ina jirar Haisam na
sami samari kala-kala akwai kyawawan da suka fi
Haisam kyau nesa ba kusa ba akwai masu arzikin
da suka fi Haisam, masu sona fiye da Haisam
amma naki su ni sai Haisam don bazan manta ba
har Mahaifiyata take cemun zaki auri Haisam in an
takura masa amma ba zaki sami soyayyar da kike
nema ba. Na ce idan anyi auren zai so ni ai. Nasa
Kanwata Rauda ta binciko mun wanne irin buri ne
Haisam ya kudira a F.G.G.C Kazaure yake so ya
cika kamar yadda kullum yake cewa, Rauda ta ce
ai wata yarinya ce *yar ajinsu mai suna Hannah ya
ce kanwarsa ce tana jin saboda ita ya ki barin
makarantar. Na sa Rauda ta ci gaba da lura da
abinda yake gudana tsakanin Haisam da Hannah.
Kuna aji hudu (S.S 1) Rauda ta zo min da
cikakken bayani game da binciken da nasa tayi
mun. Ta ce abu ya tabbata Haisam son Hannah
yake yi, duk makarantar an sani zance ya fito fili.
Ta bani labarin irin gwagwarmayar da aka yi
tsakanin Haisam da Malamai masu takurawa
Hannah da Dalibai masu takura miki, Yaya Habib
ma ya fada mana yadda suka yi da Haisam har
Haisam ya wawuri adda kamar zai daba masa,
Yaya Habib ya ce Haisam sai addu’a saboda
kamar ya zautu a son wata yarinya don haka nema
yaki dawowa gida.
Raina ya baci sosai da naji ance Haisam yana son
wata, na lashi takobin ko wacece wannan Hannah
sai naga karshenta ko ani ko a ita, shine nabi
direban mu da zai dauko Rauda ranar hutu don in
ga wacece wannan Hannah? Kuma *yar waye?
Dame ta fini da Haisam yafi sonta da ni? In kuma
ja mata kunne akan ta rabu da mijina, don a
lokacin yadda nake ji zan iya hallaka duk wanda
yake kokarin ya rabani da Haisam. Na je
makarantar na tarar bakya nan ance su Haisam
sun tafi dake sai muka biki garin ku muka tarar
bakya nan, sai Mahaifinki. Na fadi maganganu iri-
iri a cikin bacin rai saboda Mahaifinki ya rabaki da
makarantar don ki rabu da Haisam. Haisam bai
bar Kazaure ba sai da kika gama makaranta da
sati biyu sannan ya dawo gida da kayansa.
Mahaifinsa na ganinsa cewa yayi Haisam har ka
cika burin daka kudira ka dawo? Haisam yayi
murmushi ya ce “Eh Baba, Mahaifiyarsa ta ce idan
baka gama cikawa ba ka koma ka gama ka dawo
Ramlah na jiranka ayi bikin ku. Haisam ya ce ya
gama sai dai kuma ya zo wajensu neman alfarma
guda daya don Allah su taimaka masa, suka
bukaci Haisam ya fadi abunda yake so ya fada
insha Allahu idan bata fi karfinsu ba zasu yi masa
sai ya zauna ya basu labarinki tas tun daga ranar
da aka kawo ki makaranta har halinda kike ciki a
gidanku, ya kuma bayyana musu tsananin son da
yake miki ya ce su taimakeshi su bashi izini ya
hadamu mu biyu ya aura saboda kece rayuwarsa
zai iya shiga wani hali idan suka ki amince masa.
Bai rufe bakinsa ba Mahaifinsa ya daka masa
tsawa ya ce bazai yuba karma ya sake yi musu
wata magiya. Mahaifiyarsa ma ta ce in har ita ta
dauki cikinsa wata tara ta haifeshi yasha nononta
har ya girma to bata amince masa ya auri Hannah
ba.
Kwana biyu Haisam ya fara ramewa kullum ka
ganshi yana tunani, kallo daya zaka yi masa kasan
yana cikin wani hali na tsananin damuwa, ya daina
ci ya daina sha balle yayi hira da mutane
Mahaifinsa da yaga haka sai ya kira shi ya ce yaje
ya same ni yayi mun bayani akan ko zan yadda ya
auremu mu biyu, idan na amince to zaije ya sami
matarsa Mahaifiyar Haisam ya lallasheta ta yarje
masa. Haisam ya sameni a lambun gidanmu da
yamma yake cewa in taimakeshi in ceto rayuwarsa
ya auremu mu biyu ni da ke. Na kekashe kasa
nace ban yarda ba, Haisam ya durkusa
gwiwowinsa biyu a kasa yana rokona in duba
girman Allah da tsananin son da nake yi masa da
zumuncin da yake tsakanin Iyayensa da Iyayena
tun suna yara in barshi ya aureki yayi min alkawari
zaiyi adalci a tsakaninmu kawai don ya ciro
Hannah daga cikin wahala ta dawo wajensa ba
don yafi sonta ba a kaina. Mahaifansa sunce in har
na amince suma sun yarda ya aure mu mu biyu.
Na ce har abada bazan taba amincewa ba.
Hawaye ne yake zubowa daga idanuwan Haisam
yana rokona amma naki fur.
Ramlah ta sharbe hawaye taci gaba da cewa.
Bayan anyi haka Haisam ya hakura akayi bikinmu
ranar daurin aure ma Haisam kuka yake ko a
bidiyo kaset an nuna babu abinda zaka gani a
idanuwan Haisam sai hawaye. Anyi biki an kaini
gidana kowa ya watse aka barni da Haisam. Babu
abinda Haisam yake sai dai ya zauna a falo yayi
shiru yana tunani sai inyi magana sau goma
Haisam baya sanin abinda nake cewa yana tunani.
Hira wannan ba mayi da Haisam balle zancen
wata soyayya, ina alkunya ina sharewa a matsayin
na sabuwar amarya bai kamata in dinga binsa shi
namiji bai bini ba. To in har zanyi sati ban shiga
bangarensa ba ba zaizo inda nake ba, gaisuwa ce
kawai take hada ni da Haisam. Bayan mun gaisa
sai kallo da ido kawai ko abinci na kai masa baya
ci sai da ruwan shayi kawai yake sha. Tun yana
lekawa ofis wajen aikinsa kamfanin Babansa anan
yake aiki harma ya daina zuwa kwata-kwata.
Yayansa Habib yayi fadan har ya gaji ya kyale shi,
abokansa gaba daya magana suke meke damun
Haisam ya canja gaba daya baya zuwa wajensa
babu walwala baya son yin magana ko sunje
wajensa. Nima har wannan abu na Haisam ya fara
damuna. Inyi wanka in caba ado amma Haisam bai
san ina yi ba. Sai mu yini a zaune Haisam bai
dago kai ya kalli fuskata ba balle yaga jan baki da
hodar dana shafa balle yaga fari da idon da nake
yi masa da kallon soyayyar da nake yi masa. In
takaice miki munyi wata hudu cur da Haisam a
haka ko hannu na bai taba rikewa ba balle ya
shiga dakina. Sai da abun ya isheni nayi yaji na
tafi gidansu naje na sami Mahaifiyarsa na shaida
mata halin da muke ciki da Haisam, ina kuka
kamar zan mutu. Ta lallasheni ta ce in daina kuka
muka tafi gidan ni da ita muka sami Haisam a
zaune a falonsa akan kujerar da ya saba zama
yayi tagumi yana tunani kamar yadda ya saba.
Hajiyarsa tayi masa fada sosai ta shaida masa
gara ya saki jikinsa ya dawo da walwalarsa
zamansa da ni daram kuma har abada baza ta
yarje masa yaje ya auro wata Hannah ba. Bayan
nan ne Haisam ya yarda ya shiga daki na da
daddare wani babban takaici ma muna kwance
yana kirana da sunan Hannah. Nayi fadan nayi
fushin sai dai ya bani hakuri ya ce mantawa yayi
gobe ma haka jikina ya fara sanyi na fara sarewa
na fara fitar da rai akan samun soyayyar Haisam,
yayi nisa sosai a fagen son Hannah.
Kullum sai sake dulmiya yake a tunanin Hannah,
baya cin abincin kirki ba a hira dashi shi dai gashi
nan ne kawai yana Kano amma zuciyarsa tana
Babban-mutum garinku. Wasu lokutan da yamma
yakan shiga lambu yana busa wani dan karfe dogo
kamar na azurfa da nayi bincike aka ce mun abun
busarki ne akwai wasu tsakiyoyi a akwatinsa suma
wasu lokutan yana dauko su ya baza a gado da
wani hoto tun kuna J.S.S one ke da Rauda
kanwata da Nusaiba Haisam a tsakiyarku shima ya
kura ido yana kallo in takaice miki soyayya ta fara
zautar da Haisam ni kuma ina gefe ina son maso
wani, ni da dutse duk daya nake a cikin gidan. A
haka muka shekara da Haisam sai muyi wata uku
sannan nake samu ya shiga dakina, to koda ya
shigo ma ba faranta min zaiyi ba daga karshe
sunan Hannah zai dinga kirana da shi. Nayi fada,
nayi yaji har na gaji Haisam baya tankamin balle
ya bini biko idan nayi yaji. Da kaina nake zuwa in
dawo. Ban sami kulawar Haisam ba, babu
soyayyarsa. Akwai abinci, ga kudi, galla-gallan
motoci duk wacce nake so ita zan shiga.
Mahaifiyar Haisam ce take yimin sutura, ba’a yin
wata guda sai ta aiko min da dinkuna haka
Mahaifinsa ya budemin account a banki yana
turomin da kudi. Yaya Habib duk wata yake
siyomin kayan abinci komai da komai. Mahaifana
kansu da kafarsu kudi suke bani suka kara rokona
inci gaba da hakurin zama da mijina tunda ni nace
naji na gani ina sonsa haka. Amma kuma dukka
gatan da surukaina suke yimin da Iyayena duk na
banza ne ba dadin rayuwata nake ji ba tunda na
rasa soyayyar mijina. Kowa ya rasa kan Haisam an
rasa yadda za’a kamo bakin zaren bare a warware
mana matsalarmu. Wani lokaci Mahaifiyata ta
kirani take shawarta ta ko zan hakura da wannan
aure in zo in auri mai sona shima yaje ya auro
wacce yake so nace ai ni ko da zan mutu gara naci
gaba da zama da Haisam a haka saboda tsananin
son da nake yi masa.
Haka naci gaba da zama da Haisam, kullum a cikin
tunani yake har zuciyarsa ta samu matsala ya
kwanta ciwo likitoci suka ce lallai-lallai Haisam
yana cikin matsananciyar damuwa da tunani da
kunci dole ne a dinga kwantar masa da hankali
don har zuciyarsa ta ta kamu da ciwo saboda
damuwa. Bamu da maganin wannan matsalar ta
Haisam saboda kece maganin, tsananin sonki shi
yake damunsa. Don haka ciwon Haisam ya ci gaba
da yaduwa kusan kullum a asibiti Haisam yake
daga ya dawo gida sai ciwo ya tashi a mayar
dashi asibiti Haisam ya rame yayi duhu abin
tausayi. Wani abin mamaki a karkashin filonsa na
asibiti abun busarki ne da tsakiyoyinki yake yawo
dasu. Likitoci sunyi-sunyi da Haisam ya rage
damuwa saboda samun lafiyar zuciyarsa abu ya
faskara. Akwai lokacin da Haisam yayi wata biyu a
kwance a premier clinic jikin babu sauki saida aka
mayar dashi Aminu Kano Teachin hospital amma in
yanzu kaga Haisam zaka dauka kafin ka fita bakin
kofar dakin zai mutu saboda tsananin jin jiki da
yake. Numfashinsa sama-sama dakyar abun
tausayi.
Hannah ta rushe da kuka gaba daya wajen sai aka
fara hawaye. Ramlah ma hawayen da take ya kara
karuwa. Ta ci gaba da cewa “Nafi kowa sanin
takamaimai meye ke damun Haisam ina ta zargin
kaina nice silar wannan ciwon na Haisam tunda
nice na raba shi da abar kaunarsa. Da naga haka
sai na yankewa kaina shawarar kawai in shiga gari
duk inda Hannah take inje in nemo wa Haisam
saboda ita ce kadai soyayyar da zan nunawa
Haisam a matsayina na mai tsananin sonsa bana
son in rasa shi gaba daya, gara na nemo masa
maganin wannan ciwo da yaki warkewa fiye da
shekara guda yana fama. Ban bari kowa ya sani
ba, ban shawarci kowa ba na shirya tsaf da kayana
da guzirina da direba na na shirya fita neman
Hannah. Na yiwa surukaina da Iyayena sallama
akan zanje Kaduna gidan wata kawata da mijinta
ya rasu inyi mata ta’aziyya kwana biyu kawai
zanyi. Mahaifiyata ta nemi ta hana ni tafiya
saboda ga jikin Haisam yayi tsanani yana kwance
a asibiti yaya za’ayi ince zanyi balaguro duk da
ma dai bani bace nake zaman jinyarsa kaninsa ne
Izziddin da Mahaifiyarsa ai sai suga ban damu
dashi ba harkata ma na tafi. Nasan hakan da ta
fada gaskiya ne bai kamata in tafin ba amma na ce
ni dai zanje ba dadewa zanyi ba. Tayi min fatan
Allah Ya kiyaye hanya sai na dawo, na tafi.
Hmm soyayyah!!!!!!!

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE