Gangar jikinsa na aura26

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter26

Mai girma Uwar gidan gwamna ce ta sako kafarta cikin katafaren dakin taron gefenta matar mataimakin gwamna ce daya gefen ta kuma wasu daga cikin matan kwamishinonin gwamna suma sun doshi goma bayansu kuma wasu mata ne guda biyu inyamurai suna tsaye da riga da suit da dan gajeren siket iyakar gwiwowinsu sune body guards dinta (S.S.). Dogon tebur guda aka ware mata da tawagarta. Suka zazzauna ita ce a tsakiya.
 Kayan jikinta irin na Hannah sai kalarce ta ban-banta, na Hannah green ne na matar gwamna kuma komai nata pink ne. Hannah ta kalli matar mai girma gwamna ta sake kallonta sosai itama matar gwamna ta juyo ta kalli Hannah suka hada ido tayi mata murmushi. Hannah ta juya ta kalli Haisam taga shima kallonta yake sai tayi murmushi ta ce “Yaya amma matar gwamna nan tayi kama da wata kawata. Haisam ya ce “Kawarki Nusaiba ko? Ta ce “Ashe kaima ka gani wallahi sak Nusaiba Idris. Yayi murmushi ya ce “Ai ba kama bace Nusaiba ce cewa tayi kar in gaya miki sai dai kawai ki ganta. Hannah ta dafe kirji don mamaki tana cewa “Wayyo Allah yanzu wannan Nusaiba Idris ce ashe zan sake ganin Nusaiba a rayuwata?
Hall ya cika ya tumbatsa da hamshakan matan masu kudi a hankali Hannah ta dinga hango wasu daga cikin kawayensu *yan makarantarsu ta hango Rauda ma a zaune a gefen Nusaiba. Ta ce ashe Rauda zata girma tayi tsawo da kiba? Mai waqane yake cashewa, kannen Ramlah da Haisam suna cashewa su Amratu. Sai Jibril mai jawabi a lasafika ya ce a bawa amarya da ango fili su fito su cashe. Kowacce ta koma ta zauna. Hannah ta kalli Haisam shima yana kallonta taji wani nauyi yaya za’ayi ta fito tayi rawa ita da Yaya Haisam a matsayinsa na Malaminta wanda take matukar jin kunyar. Sai taji ya kamo hannunta suka mike gaba daya suka fara saukowa daga kan stage. Ramlah ta aika wani kaninta wajen masu kida ta ce police band ne zasu kadawa ango da amarya wakar sarmadan kauna in tayi dadewa mutuwa ce ke rabawa. Haka kuwa akayi police band suka saki kida da waka. Ango da amarya ne kadai a tsakiyar fili. Ango ya tsaya cak yana kallon Amarya, itama amarya a tsaye take ta daga kai tana kallon Haisam. Sai hawaye yake zubowa daga idanuwanta, yasa hannu yana goge mata. Sai shima hawaye ya fara diso masa. Sai Ramlah ta taso tazo tana zuba musu kudi abunka da mata sarakan bidi’a nan fa kowacce tana ji da kudi ta bude bakin jaka ta nufo fili don ta yiwa ango da amarya liki. Jiddah (Hidaya) aka fi kiranta dashi matar Yaya Habib ta fara tasowa filin ta dinga yiwa Ramlah liki da *yan dubu dai-dai dake aminiyar Ramlah ce sosai. Sai sauran kawayensu suka shigo fili suna likawa Ramlah kudi daga *yan dari biyar-biyar sai *yan dubu-dubu ita kuma Ramlah tana likawa mijinta da amaryarsa kudi. Matar gwamna Haj. Nusaiba ta dinga liki ai kuwa police band da suka ga ruwan kudi sai suka saka himma suna sake dukan ganga. Lallai biki yayi biki Hannah ta rungume Nusaiba da Raudah sai hawayen farin ciki suke yi. Ba’a tashi daga taro ba sai karfe daya da rabi na dare. Bayan anci ansha an cashe.
Kwanan dangin Hannah biyu a gidan amarya kawai suna shakwatawa sai da Kawu Ahmed ya aiko ya ce maza-maza su hado su dawo su dukkansu kar a rage kowa sannan suka tarkato suka tafi ba’a son ran su ba. Hannah kuka suma kuka suka shiga motoci suka tafi. A hanya ne dangin Hannah suke yiwa Iya Haule habaici ganin duk jikinta yayi sanyi ganin Allah Ya sakawa Hannah da gidan tangaran ma bana suminti ba. Wata Kakar Hannah ce ta fara cewa “Allah Ya bawa Hannah gida, gida kamar ba’a duniya ba. Wata ta sake cewa “Oh harda ake tada jijiyar wuya wai baza akai Hannah gidan sumunti ba ashe gidan tangaran ma Allah zai bata. Sauran suka tsoma baki suna yabawa Inna Haule magana. Innah Haule tayi tsuru-tsuru a zaune a mota tasan da ita ake tasan tayi kuma ba sharri akayi mata ba.
Suna tafiya masu aiki mata suka shigo bangaren Hannah suka hau kalkalewa suka wanke ban dakuna suka shisshinfida sababbin zannuwan gado suka feshe gidan da turarurrukan kamshi. Wani kuku ne a kicin yana ta shirya mata abinci kala-kala. Hannah tayi kuri a zaune a katafaren dakinta dake sama ita kadai sai talabijin ta rasa meke damunta murna take ko bakin ciki. Taji ana kiran sallar magariba sai ta tashi ta shiga ban daki ta dauro alwala tazo ta shimfida abin sallah tayi sallar magariba da nafilfilin data saba. Ta zauna tana lazumi har sai da taji ana kiran sallar isha’i sannan ta tashi ta kawo sallar isha’i. Ta idar tana linke abin sallar ne taji wayar dake ajiye a gefen gadonta tana kara ta dauka a hankali gami da cewa Hello, sai taji muryar wani bagware ne turanci yake yi ya ce, “Madam nine kukunki daga kicin nake yi miki waya na gama abinci na jere miki a kan darning table zan iya tafiya babu wani abu da za’a dafa miki? Hannah taji wani abu banbarakwai wai namiji da suna Zainabu. Abu na farko daya bata mamaki wai yau ita ce Madam ake shaida mata an gama abinci tazo ta ci kawai in harma akwai wani abunda take so a dafa mata ta fada. Mamaki na biyu kuma shine yaya za’ayi a bar garjejen Namiji bama Bahaushe bane ya shiga gidan matar aure yana dafa mata abinci daga ita sai shi wannan ba tsarin Musulunci bane. Hannah ta ce zai iya tafiya babu wani abu da zaiyi mata. Taji motsin bude kofarsa ya fita. Ta zauna a gefen gado tayi shiru tana tunani. Can ta tuna ashefa yanzu ita amarya ce, kuma tunda babu kowa watakila Haisam ya shigo bari taje tayi wanka ta sake tsala kwalliya irin ta matan da suka san darajar mazansu. Tayi sauri ta fada ban daki ta dinga salla wanka ga sabulai nan kala-kala har dana ruwa. Tana fitowa ta zauna akan mudubin dake shake da kayan shafe-shafe ta fara rangada kwalliya da fesa turarurruka duk jikinta. Tasha hoda da jan baki da gazal ta zubo gashin kanta har baya bata tufke ba ta barshi bazar. Ta saka wani dogon siket na jeans da wata *yar yaloluwar riga bulawus mai dogon hannu da dan budadden kirji. Tasa wani takalmi marar nauyi mai kama da sosan katifa ta fara saukowa daga kan benen.
Tana isowa babban falon da ke kasa sai taji wayar da ke ajiye a falon tana kara. Hannan ta karasa kan teburin da wayar take a ajiye tasa hannu ta dauka sai taji muryar Ramlah ce take fara’a ta ce “Hello amarya yaya kadaici ke kadai yau kowa ya watse an barki ko? Aiya don’t worry haka rayuwar aure take sai a hankali zaki saba. Amma yau bazan barki ki kwana ke kadai ba zan kawo miki mai taya ki kwana gamu nan zuwa. Hannah tayi murmushi ta ce “Aunty Ramlah ina yini. Ramalah ta ce “Lafiya kalau kanwata gamu nan ma zuwa sai mu gaisa sosai. Suka ajiye kan waya. Hannah tayi jigum a tsaye tana mamakin yadda Ramlah take fara’a da nuna mata so da kauna ta ce a ranta “Allah kenan, ya hadani da duk abinda zanji sanyi a rayuwata. To wa Aunty Ramlah zata kawo mun ta taya ni kwana ina jin Amratu ce kai ko dai Haimsa ne? Hannah ta dubi matsattsun kayan dake jikinta taga gaskiya baza ta iya sakewa ba a gaban Haisam. Sai ta koma sama ta dora doguwar riga baka mai dan kwala kafin ta sauka sai taji muryar Ramlah tana sallama a falon kasa. Hannah ta sauka tana rangwada ta karaso wajen da Ramlah da Haisam suke tsaye tayi dariya ta ce “Sannunku da zuwa kuzo ku zauna. Suka zazzauna dukkan su fuskarsu cike da fara’a. Hannah ma ta zauna a kunyace ta gaishe suka amsa. Ramlah ta ce “Munzo muci abincin don yau anan zamu ci abinci in tayaku hira in tafi in barku, ko baki yi abincin damu bane? Sai a lokacin Hannah ta dubi dinning table taga katan teburi cike yake da manyan food flask din abinci tayi murmushi ta ce “Aunty na isa in ki yin abinci daku, da ku aka yi. Suka mimmike suka nufi dinnin area. Haisam ne a tsakiya Ramlah a gefensa na hagu, Hannah na daya gefen, suka fara zuzzubawa a filet suna ci suna hira. Ba sosai Hannah da Haisam suka cika magana ba, Ramlah ce take ta zuba surutu suna jinta suna satar kallon junansu. Bayan sun kammala suka dawo kan kujerun falo suka zazzauna suna kallon wani fim da ake yi a sonny. Haisam ne a tsakiyar kan doguwar kujera Hannah na gefensa Ramlah na daya gefen nasa duk a doguwar kujerar suke.
Haisam ya nisa yayi gayaran murya ya ce “Uwar gida Ramlah tare da amarya Hannah babu abinda zance daku sai godiya. Ina fatan alheri a rayuwarmu gaba daya ina fatan Allah Ubangiji Ya bamu zaman lafiya. Ramlah ke ce babba kuma alhamdulillahi kin nuna halin manya kinyi mana halacci babu abunda zance miki sai Allah Ya saka miki da alheri da gidan Aljannah. Ramlah kin kasance mai tsananin hankali da tunani dan haka don Allah ina rokarki da kici gaba da yadda kika fara kici gaba da nunawa kanwarki kuma abokiyar zamanki Hannah kaunar da kike nuna mata kada ki saurari mazuga masu zuwa suyi zuga don su hargitsa ma’aurata. Ramlah tayi murmushi ta ce “Haba Haisam ya kamata ka fahimceni idan nasa raina nace zanyi abu gaskiya babu mai zugani in fasa. Ina sonka da yawa naga ya dace in so duk abunda kake so don haka naji har raina ina son Hannah musamman na lura Hannah nada ladabi da son zaman lafiya, insha Allahu zamu zauna lafiya. Haisam ya juya ya kalli Hannah wacce kanta yake a sunkuye a kasa tana wasa da dan yatsanta yayi murmushi ya ce “Amarya ke baki ce komai ba. Hannah ta dago kai tayi murmushi ta ce “Insha Allahu zamu zauna lafiya zan zama mai yin biyayya a gareku kuma ni tsakanina daku sai godiya Allah Ya saka da alheri. Ramlah da Haisam suka amsa da “Amin. Ramlah ta yunkura ta mike tsaye fuskarta cike da fara’a ta kalli Haisam ta juya ta kalli Hannah ta ce “To amarya da ango zan tafi in barku sai da safe. Haisam ya ce “Uwar gida tafiya zaki yi bari mu raka ki har gidanki ko? Hannah ta mike suka dunguma suka fita suka nufi bangaren Ramlah. Haisam na tsakiya suna tafe suna hira har kofar shiga bangarenta suka raka Ramlah, Ramlah tayi murmushi ta ce “Rakiyar ta isa haka ku koma ni dai gudunmawata da zan baku anan ita ce na bawa kanwata kwana goma da angonta ku huta sosai. Hannah tayi murmushi ta sunkuyar da kai ta ce “A’a Aunty Ramlah kwana biyu ya isa. Haisam ya harari Hannah ya ce “Maimakon ki yi godiya shine kike ki har guduna kike? Su duka suka tuntsire da dariya. Ramlah ta juya ta shiga gida ta ce “Ni dai na barku lafiya sai da safenku. Tana shiga ta turo ta rufe tasa mukulli ta bame sai ta sulale ta zube a kasa yayin da wani zazzafan hawaye ya dinga zubo mata tsananin kishi ya kamata saboda tana son Haisam matukar so babu yadda ta iya dole taso abunda yake so. Hmmmm Kishi kumallon Mata, uhm.
Haisam da Hannah suka juya suka nufi bangaren Hannah, suna tafiya a hankali suna hira. Haisam ya kai hannu zai rike mata hannu sai yaga ta goce tayi gefe. Haisam yayi murmushi ya ce “Allah Ya baki hakuri  Hannata na fasa rike miki hannu tunda rowa kike min. Suka shigo cikin gida Haisam ya jawo kofar falon ya datse. Haisam ya ce da Hannah “Zo muje sama muyi sallah. Hannah ta langwabar da kai cikin siririyar murya ta ce “Yaya nayi sallar isha’i tun dazu. Haisam yayi murmushi ya ce “Ai nafila zamu yi. Ta mike kanta a sunkuye a kasa ta wuce gaba Haisam na biye da ita suka hau sama. Daki Hannah ta wuce kai tsaye ta shiga ban daki. Haisam kuma sai ya shiga daya dakin yana shiga sai ya cire kayansa ya daura tawul ya shiga ban daki don ya sake watsa ruwa a jikinsa bayan yayi wankan ne ya dauro alwala yana fitowa ya wuce wajen katuwar waduruf din dake dakin ya bude wani bangare kayan sawarsa ne da kayan bacci. Ya zabi wasu kayan bacci masu kyau da laushi tubus auduga ne zalla riga ce gajeriya iya cinya mai dogon hannu da dogon wando farare ne sol anyi musu fulawa da kalar shudi sababbine gar a ledarsu ya ciro ya saka a jikinsa ya juya ya nufi wajen mudubi wanda aka dankareshi da mayukan shafawa da mayukan nan masu kamshi kana ya feshe duk ilahirin jikinsa da tufafinsa da tsadaddun turarurruka masu masifar kamshi wannan na cewa wane wannan suka hadu suka bada wani daddadan kamshi. Haisam ya dauko comp ya taje gashinsa ya mulke da man gashi sai kamshi, hakika ko shi da kansa yasan yayi kyau a daren nan balle wacce yayi dominta. Ya fito ya nufi dakin da Hannah take zaune gefen gado ya ganta tayi shiru tana jiransa. Yayi sallama ya shigo ta dago ta dube shi suka sakarwa juna murmushi ta amsa masa cikin sanyayyiyar murya. Ya ce “Oh sorry my love na barki kina jirana ko? Tayi murmushi ta ce ba komai ai baka dadeba. Ya bude wadruf ya dauko wata katuwar sallaya ya shimfida ya juya ya kalli Hannah to Bismillah zo bayana ki tsaya zamu yi sallah raka’a biyu ta godiya ga Allah da Ya nuna mana wannan ranar da muka zama miji da mata da kuma yin addu’ar Allah Ya kade mana duk wata fitina Ya bamu zaman lafiya da zuri’a ta gari ko ba haka bane? Hannah tasa hannu ta rufe ido saboda murna da farin cikin daya rufeta da kunya ta ce “Haka ne Yaya.
Bayan sun idar Haisam ya daga hannu sama yana kwararo addu’oi Hannah na amsa masa da amin daga karshe suka shafa. Haisam ya juyo yana kallon Hannah kallo mai kunshe da tsananin soyayya da sha’awa ji yake tamkar ya hadiyeta a daren yau. Ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi mai hade da kunya. Ya nisa ya ce “Zo nan kusa dani Hannah. Ta matso kusa dashi ta zauna, ya ce “Nan kusa dani zaki matso sosai. Ta sake matsowa daf dashi ta zauna yasa hannu ya shafa gefen fuskarta a hankali har zuwa gefen wuyanta yayin da dankwalinta ya sulale zai
fadi kasa tayi sauri taja dankwalin ta daura ta dan ja da baya. Yayi murmushi ya ce “Ja da baya ma kike? Naga dole ki cire wannan bakar doguwar rigar da dankwalin ki saka rigar barci ko dasu zaki kwana? Hannah ta gyada kai ta ce “Da su zan kwana. Haisam yayi dariya ya mike yaje ya bude wadruf ya zabowa Hannah wata tsaleliyar rigar bacci. Rigar *yar karama ce iya gwiwa yaloluwa marar nauyi mai shara-shara, kalar pink ce anyi mata kwalliya da wani gashi mai laushi a kasan rigar da wuya, hannun rigar dan siriri ne wanda za’a iya daureshi ko a kwance. Ya ciro ta daga leda ya mikawa Hannah ya ce “Ina ganin gara kisa wannan zaki fi jin dadin bacci tunda bata da nauyi. Hannah ta karba ta daga rigar don taga yaya girman rigar take, sai taji gabanta ya yanke ya fadi saboda ita a gaskiya tana jin nauyi da kunyar Yaya Haisam yaya za’ayi ta iya sa wannan *yar riga a gabansa. Tana son Haisam matuka amma bata jin zata iya kwana a gado daya dashi zuciyarta ta tuno mata yadda Haisam yake da girma da kima a idanuwanta tamkar wani Kawunta take ganinsa saboda dawainiyar da yasha da ita tun tana yarinya. Haisam ya ce “Tashi ki saka ko inzo in taya ki balle maballin. Hannah ta ce “A’a, ta tashi ta mike ta tafi can lungun gado ta cire dankwalin rigar ta cire doguwar rigar sai matsattsen siket da rigar da suke jikinta (boody hook). Haisam ya koma kan kujerar da take gaban madubi ya zauna yayin da idanuwansa suke tsaye cak a kan Hannah, ta juyo ta dube shi taga ita yake kallo sai ta dauki rigar baccin ta nufi bandaki. Haisam ya ce “Ina za ki kuma? Cikin kunya kanta a sunkuye a kasa ta ce “Ban daki zanje in canja. Haisam ya bude baki zaiyi magana sai wayarsa ta fara kara. Hannah ta fada bandaki ta rufe kofa tasa makulli ta bame. Ya duba yaga mai yi masa waya sai yaga Safiyanu ne abokinsa daga Kaduna. Ya danna ya ce “Safiyanu yaya kake? Safiyanu ya kyalkyale da dariya ya ce “Daman na bugo ne don inyi tsokana in dami ango da amarya. Haisam yayi dariya ya ce “Babu kyau fa zaka dauki alhaki. Safiyanu ya ce “Tunda baka yi barci ba yanzu taimaka ka dubo min lambar Shafi’u na Dubai da kace saika zauna, yi hakuri ka bani yanzu saboda gobe fa zan tafi Dubai ina so in neme shi idan naje can. Haisam yayi ajiyar zuciya ya ce “Safiyanu ban da kaine wallahi da bazan fita ba a yanzu sai na je mota fa sannan zan dubo maka a diaryna. Safiyanu ya ce “Na sani abokina taimaka min nasan abun is not easy ango danye sharab kamar ka, ka fita kabar amarya at this late hours sorry dan Allah, ka mika min gaisuwata zuwa ga kanwata Hannah. Suna hira a waya Haisam ya bude kofar dakin ya fita ya sauko kasa ya bude kofa ya nufi wajen da motoci suke.
Bayan Hannah ta shiga ban daki sai ta fada wanka ta fito, ta saka rigar ta dubi kanta a madubi ta ganta tamkar wata baturiya rigar tayi matukar yi mata kyau har da wani ribon na daure gashi a sakale a jikin rigar. Hannah ta daure gashinta dashi. Ta sake kallon kanta a jikin mudubi sai taga duk ilahirin jikinta tana gani a cikin rigar sai ta girgiza kai ta ce a ranta gaskiya bazan yarda Yaya Haisam ya ganni a haka ba. Ta tsaya tayi shiru a bandaki tana tunanin yadda za’ayi ta fito a haka. Ta bude wata lokar gilas dake makale a jikin bangon ban dakin sai taga abubuwa ne kala-kala na gyaran baki, masu sa baki yayi kamshi, huci yayi wasai. Ta fara karanta  jikinsu daya bayan daya don ta sanin amfaninsu da yadda za’ayi amfani dasu. Bayan tayi brush sai ta shiga daukar kowannesu tana amfani dashi. Na kuskure baki ta kurba ta kuskure na fesawa ta fesa. Sai da ta dauki tsawon minti goma sha biyar tana abu daya. Da ta gama sai tazo ta bude kofar a hankali ta leko sai taga Haisam baya nan, ta fito daga ban dakin ta sake duba ko ina Haisam baya nan taji dan sanyi a ranta don da fargaba da kunya sun isheta. Ta nufi gaban madubi, nan fa ta zauna tana rangwada kwalliya shafe-shafe da feshe-feshen turare. Hannah ta kalli kanta da kanta tasan dole ne ma yau Haisam ya rikice saboda tayi kyau sosai.

Hmm su Hanna sarakan iyayi

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE