Gangar jikinsa na aura28
Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter28
Haisam yayi shiru can yayi murmushi ya dago ya kalli Hannah ya juya ya kalli Ramlah ya ce “Tun ranar dana fara ganin Hannah naji ta kwanta mun a raina a matsayin *yar yarinyar daya kamata in taimakawa a hankali kuma sai naga tana da hali nagari kamar ladabi da biyayya, kunya, tawakkali, hakuri sanin ya kamata, tsafta, tausayi da dai sauransu sai naji tana sake shiga raina amma bazan ce a lokacin soyayya nake yi mata ba saboda yarinya ce.
A hankali kuma naji Hannah ta hau wani matsayi a zuciyata wanda ya wuce sabo ya zama idan tunani nake tunaninta zanyi haka kuma idan ina hangoni da matata ta aure sai in hango Hannah,
daga nan kwakwalwata ta tantance mun son Hannah nake saina danne shi a zuciyata na kasa
furtawa, saboda wasu dalilai nawa masu karfi.
Haisam da Hannah suka hada ido suka yiwa juna murmushi. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta ce “Na gode
sai tambayata ta biyu. Kana tuna Hannah a zuciyarka kamar sau nawa a rana?
Haisam ya ce”Ko ina ganin Hannah ko bana tare da ita koda yaushe ina tunaninta. Ramlah ta ce “Ita tsohuwar abokiyar zamanka meye matsayinta a zuciyarka tsakaninka da Allah. Su duka ukun suka tuntsire da dariya. Haisam ya ce “Ita Aunty Ramlah da farko
bana ra’ayin soyayya don ni har kunya nake ji idan aka ce ina da budurwa daga baya naga lallai-lallai
Aunty Ramlah na sona da gaske sai naga ya kamata in aureta. To akasin da aka samu har ta bani haushi shine da naje na durkusa har kasa ina rokarta tayi min izini in auri Hannah taki. To shine nima na toshe mata hanyar walwala kamar yadda ta hanani nima. Su duka suka tuntsire da dariya.
Ramlah ta ce “Da fatan yanzu an bude mata hanyar walwala tunda ta bude maka ita ma. Yayi dariya ya ce “Ai tuntuni ma zancen da ake yi yanzu babu matsala ina sonta sosai. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta
ce “Allah Yasa haka ne amin. Ta fara rubuce-rubuce a jikin takardar dake hannunta. Can ta dago ta dubi
Hannah ta ce “Kanwata gare ki na dawo, shin yaushe kika fara jin son mijinki Haisam? Haisam ya zura mata ido kem yana kallonta. Hannah ta gyara zama tayi murmushi ta ce “Yaya Haisam dai wani muhimmin mutum ne a rayuwata. Tamkar dan jariri ne wanda ya budi ido daman wacce ya kamata ya fara sani a duniya ita ce Mahaifiyarsa. To haka ya kasance ina bude idona sanda na fara sanin meye rayuwa Yaya Haisam na fara sani don haka shine
wanda na saba dashi, dana fara sanin meye so sai tsuntsun son ya fada kansa, na kasance koda
yaushe shine a raina. Murmushi kawai Haisam yake yi Ramlah ta ce “Haka ne na gode kanwata. Ta sake yin rubuce-rubuce, daga karshe ta rufe littafin ta ajiye a gefe ta dago ta dube su ta ce “Abin da yasa nayi wannan tambayoyi shine akwai wani shiri da nake yi a zuciyata in har mijina ya bani izini ina so in fadakar da matasa samari da *yan mata game da soyayya saboda na koyi darussa da dama akan wannan lamari naku. Haisam ya ce “Ki fadakar a ina? Ramlah ta nisa ta ce “A matsayina na wacce ta karanci harkar yada labari ko ince *yar jarida a gidan radio mana. Haisam ya girgiza kai ya ce
“Bazan yarda wani kato ya dinga jiye min wannan zazzakar muryar taki ba. Hannah ta ce “Ai bashi da
aibu don mace tayi aiki a gidan radio. Ramlah ta ce “Yauwa kanwata fada masa, ni bama aiki nace zanyi ba kawai a sati sau daya zanyi shirin kuma ni zan dauki nauyin shirin. Haisam ya ce “Meye shirin?
Sai cewa kike shiri, fadamin me zaki ce acan kuma yaya sunan shirin? Ramlah tayi dariya ta ce “Ni dai zan fadakar akan soyayya mecece soyayya kuma yaya ake yinta, kuma dawa ya kamata ayi? Haisam ya ce “Haka sunan shirin kenan dawa ya kamata ayi soyayya? Ramlah ta ce “Sai nayi tunani dai in san sunan shirin da zansa. Kanwata ko zaki zabar
min sunan daya dace in sawa shirin. Ta tambayi Hannah. Hannah tayi dariya ta ce “Aunty kisawa shirin suna SOYAYYA GASKIYA CE. Haisam da Ramlah suka hada baki suka ce “Soyayya gaskiya ce. Ramlah ta ce “Gaskiya sunan yayi, haka zansa masa kanwata kince wani abu kema ina fatan zaki
tallafamin shirin yayi farin jin wajen bugomin waya da bada shawarwari a FREEDOM Radio zanyi shirin insha Allah in yallabai ya barni. Kaga itama kanwata Hannah sai ta rubuta Jamb wannan shekarar ta karbo result dinta tazo ta shiga B.U.K ni kuma ina *yan shirye-shirye na a gidan radio ni ina bala’in sha’awar yin aiki a gidan Radio ko telebijin tun ina
yarinya don haka nema na karanci Mass Communication. Kefa Hannah me kike sha’awar karanta. Hannah tayi murmushi ta ce “Ni da yake science’s nayi a secondry ina sha’awar in karanci medicine ko Biochemistry. Haisam ya dube su su
dukkansu ya tura hula keya ya ce “Ku gama shawarar ku ina jinku ba saina barku ba.
Ramlah ta ce “Haba yallabai ya zaka yi mana haka sai ka ce wani mutumin can kauye, kamar wani tsoho kake kokarin hana matanka karatu da aikin da zai anfani jama’a. Kaga yanzu kamata
yayi karshen watannan kai da amaryarka ku fita honey moon zuwa kasashe kuyi kamar wata guda a can. Ni kuma kafin ku dawo na fara shirina a FREEDOM. Haisam ya ce “To Uwar tsari tsara mana tafiyar wacce kasa zamu je. Ramlah ta ce “Kaga da farko ku fara zuwa Dubai daga can sai London ku huta sosai, ku wuce America da Germany daga can sai ku wuce saudia kuyi aikin Hajji tunda lokacin aikin Hajjin ya kusa ina ganin dai a wata biyu zaku je ku zagayo ku dawo.
Haisam ya dubi Hannah ya ce “Hannah haka yayi miki. Hannah tayi murmushi ta ce “Yayi mun tunda haka yayiwa Auntyna ai bani da zabi. Ramlah ta ce “Haka za’ayi yallabai ni kuma sai ka barni in fara
shirina a gidan radio duk sati. Haisam yayi dariya ya ce “Naga kin damu da wannan shirin naki to na
barki kije kiyi Allah Ya taimaka miki. Idan kinji an fara saida form din Jamb sai ki sayawa Hannah
idan a lokacin bama nan. Kafin mu tafi zan je Kazaure in karbo mata sakamakon jarabawarta, sai
ki cike mata form din tazo ta zana jarabawarta sai ta shiga B.U.K. Shikenan ku sakar mun marata in huta zance ya wuce ko? Suka hada baki dukkansu suka ce “Mun gode.
Murna ce ta lullubesu dukkan su musamman Hannah sai take ta nanata sunayen kasashen nan a
zuciyarta. Dubai, London, America da Makka. Lallai waya ga Hannah a turai, har aikin Hajji zan yi. Yadda
Hannah ta ke so taje Makka sai gashi ko sati bata yi ba a gidan miji an biya mata Makka. Sai Hamdala
take yiwa Allah a zuciyarta. La’asar tayi sai dukkaninsu suka tashi suka yi alwala suka yi jam’i suka yi sallar la’asar suka ci gaba da hirar da kallon talabijin sallah ce kawai take tashin su. Bayan sunyi sallar isha’i ne suka wuce teburin cin abinci suka ci abincin dare Ramlah ta raka su har bangaren Hannah tayi musu sai da safe ta dawo nata bangaren. Hannah tana mamakin irin wannan kirki irin na kishiyarta Ramlah ashe yanzu akwai kishiyoyi irin Ramlah da zuciyarta daya abinta wasa da dariya. “Hakika nayi dace da miji da kishiya ta gari. Hannah ta fada a zuciyarta. Babu bacin rai a zuciyar Hannah a yanzu sai farin ciki ko ina ta waiga. Haka Allah Yake ikonSa, Allah Mai Girma.
Kwanan Haisam goma a dakin Hannah kamar yadda Ramlah ta amince masa yayi. Haisam da
amaryarsa Hannah sun cancare da amarci a cikin kwana gomar nan. Sun farantawa juna an aiya ce
irin son da suke yiwa juna.
Bayan sun idar da sallar isha’i suka wuce kan teburin cin abinci suka ci suka koshi kamar yadda
suke yi kullum a bangaren Ramlah. Sai Haisam ya ce su taso suje
gidansu su gaishe da Hajiyarsa. Haisam ne yake tukawa Ramlah ce ta zauna a gidan gaba tunda ita ce zata karbi kwanan a daren yau.
Hannah ta zauna a kujerar baya. Suna ta hira wasa da dariya a hanya har suka isa Sulaimanu Cresent gidansu Haisam. Hajiyar Haisam tayi matukar yin farin ciki da taga danta da matansa suna zaune lafiya cikin farin ciki. Hankalin Haisam a kwance ita ma sai farin ciki ya kamata. Hannah da Ramlah suka durkusa gaba dayansu a gaban surukarsu suka gaisheta cikin ladabi da biyayya. Ta amsa musu cikin fara’ gami da yi musu nasihohi akan suci gaba
da zaman lafiya kamar yadda suka fara kada su saurari *yan zuga. Su toshe kunnuwansu saboda wasu mutane suna da bakin ciki basa so suga ana zaman lafiya. Ta ci gaba da cewa zaman lafiyarsu shine farin cikin danta Haisam, farin cikin Haisam kuma shine kwanciyar hankalinta daga karshe tayi musu godiya da fatan alheri.
Lemuna da snacks kala-kala tasa masu aiki suka kawo musu. Bayan sun sha hira sai Haisam ya ce su taso su tafi. Har bakin kofa Hajiyar Haisam ta rako su tayi musu sai da safe sannan ta koma gida suka shiga mota suka tafi. Gidan Yaya Habib suka nufa da yake Hotoro G.R.A suka daki gurbi don Yaya Habib baya gida amma matarsa Hidaya tana nan. Ta tare su da fara’a ta rungume aminiyarta Ramlah suka shiga cikin daki. Hannah da Haisam suka zauna a falo suna kallo talabijin din dake kunne. *ya*yan Yaya Habib guda biyu Zakar da Nana suka zo wajen Hannah da Haisam suna taya su hira. Ramlah da Hidaya suna cikin daki a zazzaune a gefen gado. Hidaya ta ce “Kinsan me yasa na jawo ki daki muka kebe? To ba wani abu bane illa ince ni da su Aisha Sule da Hauwa Muhammad muka ga mun dace muyi miki nasiha, wallahi Ramlah kin bamu mamaki duk wannan zafin naki ashe na banza ne iya bakin naki na masifa har kika yarda kika zama baiwa *yar kallo saboda wata yarinya *yar kauye. Gata zata kwace miki miji.
Ramlaha tayi ajiyar zuciya ta ce “Au har meeting ku ka shiga a akaina ke dasu Hauwa Muhammad?
Hidaya ta ce “Eh mana daman jibi muka yi zamu hadu a gidansu Aisha sule muje gidanki dan dole mu fada miki gaskiya akan abunda zai cuce ki meye kawancen idan bamu gaya miki ba wa zai fada miki. Wallahi wannan *yar buzuwar da kike gani kina wani kara wayar mata da kai sai ta waye ta ci ta koshi sai ta mamaye gidan ki zama *yar kallo. Ramlah ta ce “Haba Hidaya yanzu ke da kanki kike cemin haka? Bayan kinga duk tashin hankalin
da Haisam ya shiga da Iyayensa da danginsa gaba daya a sanadiyyar rabashi da Hannah. A gaban idona da bayan idona babu surutun da ba’ayi ba na ana cewa Haisam na hana shi ya auri wacce yake so gashi nan nima ban sami soyayyarsa ba.
Yanzu Allah Ya amsa addu’ata ya kuma yaye mun tsananin kishi ya cusa mun kaunar Hannah muna
zaune kalau da mijina kamar kowacce mace yanzu Hidaya ba sai ku tayani da addu’a ba da fatan alheri Allah Ya kara mun juriya da ci gaba da samun zaman lafiya ni da abokan zamana ba. Ramlah na rufe bakinta sai suka ji muryar Haisam ya leko yana cewa “To kus-kus din ya isa haka ku fito falo a hadu ayi hira har Hannah. Hidaya haka ake karbar baki? Hannah ce bakuwa sai kija *yar gida daki ki bar bakuwa a waje bayan kawo ta nayi itama ta saba da dangi. Hidaya da Ramlah suka yo waje Ramlah tayi dariya ta ce “Kuyi hakuri ina kallon kayan jariran data suyo su ne kasan ta kusa haihuwa. Hidaya ta tabe baki ta ce “Wa yaga bakuwa ai ni nan daka ganni bana marhaban da zuwan amarya ko ba tawa bace balle abunda yayi Ramlah shi yayi ni. Haisam ya dan harareta ya ce
“Ban gane ba? Hidaya ta ce “Haka zaka ce mana wannan bakuwar da kake cewa nayi nace bana marhaban da zuwan ta saboda ni Allah bai samin son amare ba me za’ayi da su, su shiga gida su tarar
da mace da *ya*yanta suyi kane-kane su kwace mata miji idan ba’ayi sa’a bama sai sun fitar da ita. Ni Ramlah na sani sai kai duk wata bakuwa ban santaba. Ramlah taji wani yarr jikinta nauyi da kunya suka rufeta tayi sauri ta katse Hidaya ta ce “Hannah ai kawarmu ce, bari in dauko mata lemo ma a kicin. Ta yunkura zata tashi Haisam yasa hannu ya dakatar da Ramlah ya ce “Ramlah barshi ba komai, ba sai kin dauko mata lemo ba tunda matar gidan bata dauko mata ba kema baza ki dauko ba, tunda ma ta ce Hannah ba bakuwarta bace sai mu tashi mu tafi inda ake nemanta ake sonta. Hannah ta sunkuyar da kai kasa jikinta yayi sanyi kalau. Hidaya ta sake yatsine fuska ta ce “Lallai Ramlah sannu da kokari irin wannan rawar kan mijinki yake yi akan amaryarsa *yar gwal ce kenan ba’a tabata. Hannah ta mike tayi wuf ta fice da sauri ta nufi wajen mota ta tsaya yayin da gabanta ya hau faduwa tana fargabar kada fa Hidaya ta zuga Ramlah ta canja musu yananyin zamansu in har Ramlah ta canja hali lallai Hannah zata shiga halin kunci muddin suka shiga yin tsiya- tsiya da Ramlah. Hawaye ya zubo sharr daga idanuwan Hannah ta jingina kanta a jikin mota tana hawaye. Haisam ya tsaya kawai yana kallon Hidaya haushinta ya hanashi tunano kalmar da zai fada mata ya girgiza kai ya juya ya dubi Ramlah wacce itama tayi tagumi a zaune ranta ya gama baci saboda abunda kawarta ta yiwa kishiyarta. Yayi
ajiyar zuciya ya ce “Ramlah ai kinji abunda Hajiyata ta fada muku dazu ko don haka ki kula, ki kiyaye sai kin toshe kunnuwanki saboda *yan zuga, *yan neman kar a zauna lafiya kiyi amfani da hankali da
tunani sai kinyi yaki da zuciyarki kinyi watsi da wasuwasun da ake cusawa a zuciyarki na munanan shawarwarin da ake baki.
Gaskiya Hidaya ba Hannah kika wulakanta ba ni kika wulakanta don Hannah bata san hanyar gidanki ba ni na kawota kuma Hannah bata auro kanta ba sai da na aurota na zo na hada ta da Ramlah, banji dadin abunda kika yimin ba Hidaya ko Yayana Habib ne yayi wa Hannah haka irin wannan wulakancin zan fada masa gaskiya kuma bazan sake takowa gidansa ba har abada balle Hannah
tazo.
To amma yanzu tunda ba shi bane yayi mun haka ba!! Ba zance na daina zuwa gidan ba kwata-kwata tunda donshi nake zuwa, na gode sai anjima. Ya mike ya fita a fusace. Ramlah ta da karfi cikin fushi ta ce “Hidaya ya zaki mun haka, me yasa kika mun haka Hidaya? Ya kike so nayi da rayuwata? Hidaya ta tabe baki ta ce “Dalla banza kema bacin rai kike don nayiwa kishiyarki wulakanci, ni Ramlah kina bani mamaki wallahi duk yadda akayi wannan amaryar taki ta shanyeki.
Tasa hannu zata riko Ramlah don taga Ramlah tayi matukar damuwa Ramlah ta kauce ta ce “Banji dadi ba gaskiya yau kin bata mun rai. Ramlah ta mike ta
fita. Hidaya ta bita da kallo har ta fice. Tayi murmushi ta rike baki ta ce “Banza wai fushi take akan na batawa kishiyarta, ki mutu mana ai har gida sai munzo mun yiwa Hannah tas sai dai a tsiremu.
Yarinyar data rikita miki miji har ya kusa mutuwa sabida ita kiri-kiri kina ganinta a cikin gidanki kin kasa yi mata komai, kema sai ta halaka ki tukunna.
Da Haisam ya fita ya nufi inda Hannah take a jingine a jikin mota tana kuka, yasa hannu ya dafa bayanta ta juyo da sauri sai taga Haisam tayi murmushi tasa hannu zata goge hawayen idonta da sauri don kar yaga kuka take sai Haisam ya rike hannun ya ce “Kuka kike yi? Ta sake zubo da hawaye sharr ya ce “Hannah daina kuka kinji kiyi hakuri, meye na kukan kuma me Hidaya ta isa ta sa ko kuma me zata hana karki damu mutane daban-daban masu halaye daban-daban dole daman a sami *yan zuga marasa son suga ana zaman lafiya. Ya rungumeta yana goge mata hawaye. Sallamar Ramlah ce tasa su duka suka dago. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta ce
“Kuka take yi? Haisam ya ce “Lallashinta nake yi don bata ji dadin abunda Hidaya tayi mata ba.
Ramlah ta matso ta dafata ta ce “Hannah yi shiru daina kuka kada ki damu kinji ko, ina da hankali
kuma nasan duk mai hankali mai kaunata bazai bani shawarar kar in zauna da kishiyata lafiya ba.
Kamar yadda Hajiya ta fada mana dazu sai na toshe kunne na kema haka zaki sami kawaye ko *yan
uwanki masu zuga akan zamana dake sai mun toshe kunnuwanmu mu duka. Hidaya kuma bata fahimci wacece kishiya ba kuma meye kishi bane amma insha Allahu komai zai dai-daita tsakaninki da ita.
Hannah ta gyada kai tasa hannu ta goge idonta ta ce “Naji Aunty Ramlah na gode. Haisam ya ce “To yi murmushi sai mu san kin huce. Sai su duka ukun suka tuntsire da dariya Hannah ya budewa Ramlah
kofar mota, ta shiga ta zauna sannan ta rufe itama ya bude kofar baya ta shiga ta zauna. Haisam ya
shiga ya kunna ya ja suka tafi. Basu tsaya a ko ina ba sai a kofar gidansu mai gadi ne ya taso a guje ya bude musu get. Ya duka har kasa ya mika gaisuwa.
Haisam ya wuce kai tsaye cikin gidan yaje ya tsaya a wajen da ake ajiye motoci su duka suka bude kofofin motar suka firfito. Haisam ya ce “To sai muje mu raka Hannah bangarenta. Suka dunguma suka nufi bangaren Hannah suna tafe suna hira har suka shiga. A babban falo suka zauna, Hannah ta shiga
kicin ta dauko lemon gwangwani guda uku wanda aka yishi da kwakwa ta dora akan dan faranti ta zo ta dora akan centre tebur ta dauki daya ta bude ta durkusa har kasa ta mikawa Haisam ta dauko wani ta bude ta durkusa ta mikawa Ramlah sannan ta
dauko na karshen ta bude ta koma kan doguwar kujera (three seater) kusa da Haisam ta zauna.
Ramlah ma na daya gefen na sa. Suna shan lemo suna kallon settlite tashar African magic wani Nigera film suke mai suna THE LAST UPPER fim din yayi musu kyau matuka saboda tsantsar soyayya ce ake yi a ciki. Basu iya tashi daga kallon nan ba sai da fim din ya kare, karfe daya da rabi na dare.
Haisam ya dubi agogo sai yayi sauri ya mike ya dubi Ramlah ya ce “Aunty ya kamata mu tafi haka
kada mu takurawa Hannah ko tana so taje ta kwanta tayi bacci nasan yau da bana nan sai tafi sakewa tayi ta juyi ita kadai a gado. Hannah ta kalleshi sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai.
Ramlah ta tuntsire da dariya ta ce “Kai Yallabai ka cika tsokana kana so dai ka cewa kanwata yau ta zama gauruwa da kyar in zata iya bacci. Hannah ba ta ce musu komai ba murmushi kawai take yi, ta mike ta je ta kashe talabijin ta kwashe gwangwanayen lemon da suka sha ta kai kicin.
Ta fito ta iske Haisam a tsaye a tsakiyar falon Ramlah na zaune har yanzu. Hannah ta ce “Muje to in raka ku. Ramlah ta ce “Ai ke muka rako ko za’ayi rakiyar kara ne? Barshi kanwata mu biyu ne fa.
Haisam yayi murmushi cikin tsokana ya ce “Nasan tsoro kike ji muje in rakaki sama ki kwanta. Hannah ta dan harareshi ta ce “Tsoron me?, ni ba tsoro nake ji ba, ni yanzu ma kallo zanyi gaba daya.
Haisam ya ce “Ai sama ma da kallo muje sama sai kiyi kallon. Ya juya ya kalli Ramlah ya ce “Ki jira ni
dan Allah minti biyu zan raka wannan gwauruwar. Ramlah tayi dariya ta ce “Ka cika tsokana, waccce irin gwauruwa bayan gata da miji a kusa da ita. In kuma kana ganin ba zata iya kwanciya ita kadai ba tazo muje mu kwana a bangarena. Haisam ya ce “Hannah kinji in baza ki iya kwana ba zo muje mu baki daki daya ki kwana. Hannah tayi dariya ta ce “Aunty Ramlah sai da safe babu komai zan iya kwana, ba tsoro nake ji ba. Ta wuce ta fara hawa sama Haisam na biye da ita suna shiga daki Haisam ya jawota ya rungume ta ya kalleta ya ce “Fada min gaskiya yau zaki iya barci da bana nan ko baza ki iya ba? Hannah ta sulale daga jikinsa ta nufi kofar bandaki ta juyo tayi masa fari da ido ta ce “Me yasa ka damu da sanin halin da zan shiga kai dai ba kana tare da Uwargidanka ba. Haisam ya rike baki ya ce “Ah tambayata kike me yasa na damu da halinda zaki shiga, Hannah kin manta Haisam da
Hannah? Hannah tayi murmushi ta ce “To yi hakuri tunda tambaya ka yi zan fada maka. Ta murda kofar bandaki ta shiga ta juyo ta dubi Haisam ta kashe ido ta ce “Daren yau zai zame min marayan dare kwana dayan da baka nan zai zame min tamkar shekara guda zan kagu gari ya waye wani daren yayi domin ka kusanto gareni. Guzurin da zan baka shine zuciyata tana gareka, amma kai ba zan so ka barmin zuciyarka gaba daya ba sai dai ka dan gutsuro min rabi, saboda idan ka bani gaba daya zan shiga hakkin abokiyar zamana, tunda yanzu Yaya Haisam bana Hanna bane ita kadai.
Haisam yayi murmsuhi ya gyada kai ya ce “Nagode Hannah kinyi gaskiya kuma nayi farin ciki da kike
sakani a hanyar adalci a tsakaninku. Kin iya magana kin iya tsara zance mai dadi kanwata zan
tafi da zuciyarki gaba daya amma gaskiya nima sai nayi da gaske zan iya bar miki rabin zuciyata saboda gaba dayanta tana gareki. Yana nufo inda Hannah take a hankali ya karaso bakin kofar inda take tsaye suka zubawa juna ido me cike da soyayya tamkar kada su rabu da juna suke ji, can Haisam ya nisa ya ce “Allah Ya jarabbeni da wani ciwo mai tsanani, wanda na rasa maganinsa, sai daga baya Allah Ya saukar min da maganin ciwon saboda daman kowacce cuta sai da aka saukar da maganinta kafin a saukar da ita. Hannah ta kalle shi cikin mamaki ta ce “Cuta! Wacce irin cuta Yayana?
Yayi murmushi ya juya yana tafiya a hankali ya nufi kofar fita. Hannah ta fito daga ban daki ta tsaya tana kallonsa zuciyarta cike da zulumin kada ya tafi bai faiya ce mata abunda yake nufi da wannan kalamai nasa ba. Yasa hannu ya bude kofar dakin sannan ya juyo ya dubeta yayi murmushi ya ce “Cutar ita ce tsananin sonki, maganin kuma dana sami wacce nake so Hannah na soki, ina sonki kuma, bazan daina sonki ba har abada, sai da safe kiyi bacci lafiya. Ya fita ya jawo mata kofa ya rufe.
Da bandaki zata shiga tayi wanka ta tsinci kanta ta nufi kan gado ta jawo filo ta kifa kanta tayi ruf da
ciki tana murmushi zuciyarta cike da farin ciki da shaukin so. Ta sami soyayyar wanda take tsananin so. Wata dankararriyar soyayyar da take yiwa Haisam ta dinga narkewa tana sake hawa kanta. Ta
lumshe ido sai ta hango kyakkyawar fuskarsa sai taji kamar muryarsa na yi mata rada a kunnuwanta.
Hmm kaiiiii ana zuba soyayyah anan