Gangar jikinsa na aura3

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 3

Saurayin nan yayi murmushi ya
girgiza kai ya ce
“Amma Baba bai kamata daga
kiran dubunnan
nan ka kwasheta haka da sauri
kace zaku tafi ba.
Malam Habu ya fara jin haushin
saurayin nan, ya
ce a ransa “Wai shin wannan
duk zancen nan da ake bai gane
ba ne? Makaranta sai da kudi
kuma
babu kudin jiran me zanyi, ko
shi bai san babu ba
ne? Saurayin nan yaci gaba da
cewa “Baba kuzo
ku ajiye kayan nan bai kamata
ka juya da yarinyar
nan ba, ai bai kamata ba. Ta ci
makaranta har
kun shigo cikin makarantar
sannan ku kwasa ku tafi
ka
ce ka fasa, babu fa abin da Uba
zai yiwa yarsa a
duniya in ba ya bata ilimi ba,
yarinya kamar
wannan ai kamata yayi tana
makaranta tunda
bata isa aure ba, me zata yi a
gidan? Malam Habu
ya sake jin haushin saurayin nan
kamar ya doke
bakin da yake masa wadannan
kalamai ya ajiye
bokitin dake hannunsa ya ce
“Yaro, wai shin a
harshen Hausa idan akace babu
me ake nufi? Yayi
murmushi ya ce “Baba kenan, na
gane duk dalilan da kake nuna
min yanzu, ni kuma abin da
nake so na rokeka shine ka fasa
tafiya da ita
tunda
ka kawota har cikin makarantar
ka kyaleta tayi
karatu. Abun da ya kamata ka
tambayeni shine
tayaya zata yi karatu tunda babu
kayan makaranta babu kudin
makaranta? Malam Habu
ya ce “To yanzu nasan ka gane
babu, ta yaya
zata
yi karatu babu kudin makaranta
babu kayan
makaranta? Kyakkyawan
saurayin nan ya ce
“Yauwa Baba kayi tambaya mai
kyau, amsar tambayar ita ce in
Allah Yaso Ya yarda Hanne
zata
yi karatu in har ka amince ka
yarda zaka ringa
turo ta makaranta da zarar hutu
ya kare ba sai ta
fara ba kace baza ta dawo ba ka
cire ta. Idan
kayimin alkawarin haka kuzo ku
ajiye kayan nan ka
tafi ka barta. Malam Habu yayi
jigum yana tunani,
a ransa ya ce “Wannan yaron me
yake nufi?
Hanya
zaiyi mana a dauki Hanne babu
kudin makaranta
babu kayan makaranta ko kuma
yaya za’ayi? Bana
tunanin dai shi zai biya mata
kudin makarantar
harda dubunnan da ko karamar
hukumar mu baza
ta iya biya mata ba yadda
zamanin nan ya canja
masu kudi basa taimako, babu
yadda za’ayi yaron
nan ya zare makudan kudi ya
baiwa yarinyar da bai santa ba
bai taba ganin ta ba bazan bar
yar
Baba a makarantar nan ba in
tafi ta wulakanta ba,
wacce bata san hanyar da zata
bi ta koma gida
ba
idan an korota. Yanzu akan
Naira goma masu
mota suke kokarin su danneni
su dauka ina ga dubunnan
kudade ga kayan makaranta har
kala
hudu waye zai dinko mata?
Saurayin nan ya katse Malam
Habu daga tunanin
da yake yi ya ce “Baba tunanin
me kake yi ne?
Karka yi kokonto ba zaka yi
dana sanin barin
Hanne a makarantar nan ba in
Allah Ya yarda babu abin da zai
sami Hanne sai alheri da
kwanciyar hankali ka tsarkake
zuciyarka ka danka
Hanne ga Allah wanda a koda
yaushe Yana kallon
halin da bayinsa suke ciki na
kunci kona farin ciki,
sannan ka danka Hanne amana
ce a wajena. Ni
kuma na maka alkawarin zan
karbi amana na rike.
Cikin
sanyin zuciya da gamsuwa da
kalaman
saurayin nan Malam Habu ya
juya ya kalle shi ya
ce “Allah Sarki duniya wani ya
munana maka wani
kuma ya dadada maka. Yaro
tunda ka ce Allah na
yadda ka kuma ambaci amana,
amana kalmace
mai girma mai wuyar rikewa
kace zaka rike tsakaninka da
Allah, na gode yaro, Allah Yayi
maka
albarka Ya biya maka
bukatunka. Abin da kayi
min
Ubangiji Allah Yayi maka fiye da
haka, yar Baba
muje mu ajiye kayan. Suka juya
harda saurayin wajen bencin da
yake, Malam Habu ya kama
akwatin dake kan Hanne ya
sauke mata ya juyo
ya
kalli saurayin nan dake zaune
akan benci ya ce
“Yaro bazan gaji da yi maka
godiya ba. Madalla
Allah Ya yi maka albarka zan tafi
na barku lafiya, af
kaga ko sunanka ban tambaya
ba. Saurayin nan
yayi murmushi ya ce “Sunana
Haisam, Baba.
Malam Habu ya ce “To madalla.
Ya juya ya kalli
Hanne wacce ke tsaye idonta ya
ciko da kwalla ya
ce “Yar Baba zan tafi na barki
ga Allah na barki ga
wannan bawan Allah. Sai ta
rushe da kuka ta
koma kan akwatinta ta zauna ta
kifa kai a gwiwa
tana kuka. Hawaye ya kecewa
Malam Habu ya ce
“Nima ba’a san raina zan tafi na
barki ba Allah Ya
kaddara saduwarmu. Ya juya ya
kalli Haisam ya ce
“Yaro mai wuyar suna har na
manta sunan na tafi,
sai wata rana. Haisam ya ce “To
Baba Allah Ya
kiyaye. Malam Habu ya juya ya
fara tafiya yana
face majina yana goge hawaye
da gefen babbar
rigarsa, sai yaji muryar Hanne ta
ce “Baba ya juyo ya ce “Yar
Baba. Ta taso da gudu ta karaso
inda
yake ta kama gefen zaninta ta
kwance sai ta
dauko wasu cukurkudaddun
yan Naira ashirin
guda hudu ta ce “Baba karka
tafi da kafa gashi ka
hau mota. Haisam dake zaune
har yanzu akan
benci yana kallonsu sai da yaji
kwalla ta cika masa
ido don tausayin Uba da yarsa.
Malam Habu ya
ce
“Allahu Akbar, yar Baba Allah
Yayi miki albarka.
Allah Ya baki ilimi mai amfani,
kinji? Waye ya baki
har murtala hudu? Hanne ta ce
“Dana shiga makwabta nayi
musu sallama suka babbani
wasu,
sauran kuma kudina ne da nake
tarawa tun na
yawon salla. Malam Habu ya ce
“Kya bani duka
ingo murtala biyu ni na dauki
murtala biyu, kema
ki rika siyan yar gyada kya
zauna haka kina
ganin yara suna siye-siye ke
bakya siyan komai? Hanne
ta ce “A’a Baba murtala biyu
baza ta kai ka gida
ba, bana so ka shiga mota
kudinka bai cika ba,
kana rokon ayi maka ragi irin na
dazu. Malam
Habu ya sake kecewa da kuka ya
ce “To yar
Baba na gode na tafi na barki ga
Allah baki da kowa,
baki da komai, ba ki san kowa
ba, Ya juya ya tafi.
Hanne na tsaye hawaye yana
zuba daga
idanuwanta tana kallon
Mahaifinta yana tafiya
yana waiwayenta. Taji wani
kululun bakin ciki
marar misali a kirjinta da
mummunan tashin hankalin
rabuwa da Mahaifinta, yaune
ranar da ta
taba rabuwa da Mahaifinta
daidai da rana daya
basu taba rabuwa ba. Gashi a
yau ya kawota inda
bata san kowa ba ya juya ya tafi
ya barta.
Hawaye
ne mai radadi yake zubo mata
har sai da ta daina hango
fararen kayansa ya kure, sannan
ta yi
ajiyar
zuciya tasa gefen mayafinta ta
goge idanuwanta
ta juya ta dawo kan akwatinta
ta zauna. Haisam
na zaune akan benci yana
kallonsu zuciyarsa cike
da tsananin tausayi ji yake wani
abu yana yawo a cikin kansa,
saboda wani abu guda daya
daya
bashi mamaki ya bashi al’ajabi,
shine ganin yadda
Hanne take da Mahaifinta suna
cikin tsananin
talauci amma suna da wadatar
zuci. Haisam yaci
gaba da kallon Hanne wacce
take zaune akan
akwati a gabansa ta sunkuyar
da kanta kasa tayi shiru kamar
mai tunani, amma hawaye na
digowa
daga ganinta hankalinta a tashe
yake tana cikin
damuwa. Ya gyara zama gami
da zare farin
gilashin da yake fuskarsa. Ya ce
“Hanne, kukan
mai kike yi ne? Bakya so ki
zauna a makaranta
kiyi karatu kamar sauran yara,ne?
kin fi so ki koma gida
ki
zauna da Baba? Hanne ta girgiza
kai alamar a’a,
ya
ce “To meye kikema kuka? In
kinsan bakya son
makarantar nan yanzu nayi
sauri na tsayar da Babanki kafin
yayi nisa sai ku koma gida.
Hanne
tayi sauri ta ce “A’a bana so na
koma gida, ya ce
“To ai kuka kike meyasa kike
kukan tunda kina
son
makarantar? Bakya son ki koma
gida inda zaki yi
wasa kuyi wake-wake da
kawayenki a dandali? Hanne tayi
dan murmushi ta sunkuyar da
kai.
Haisam ya ci gaba da cewa “Ni
kuwa na dauka
danmarar nan da kika ci ta
zuwa wake dandali ce.
Hanne tayi narai-narai da ido
kamar zata yi kuka
ta
ce “Ni ba’a barina naje dandali
wasa. Kullum aiki nake yi sai dai
inzo in wuce su in zani debo
ruwa.
Haisam ya sake gyara zama ya
ce “Ban gane ba
sai dai ki zo ki wuce su in zaki
debo ruwa? Ke
kullum a debo ruwa kike bakya
zuwa wasa?
Hanne
ta ce “Eh, sai dai su Saude
Yayyena da kanne na ne suke
fita wasa. Haisam ya ce “Ina
Mahaifiyarki
take? Hanne ta sake saka gefen
gyalenta ta share
hawaye ta ce “Tun ina shekara
biyu ta rasu. Yaji
gabansa ya yanke ya fadi ras,
saboda yanzu ya
gane Hanne a gidansu tana cikin
halin wahala
kasancewar Mahaifiyarta ta rasu
da alama kishiyar
Uwa tana wahalar da ita. Allah
Sarki Hanne ya
fada
a ransa yayin daya kura mata
ido. Hanne ta bashi
tausayi da, a yanzu kuma ta sake
kara bashi
tausayi akan tausayi wanda
badan ya daure ba da zai iya
rushewa da kuka. Can bayan
sun dauki
wani lokaci mai dan tsawo babu
wanda ya sake
cewa komai. Dukkaninsu kansu
a sunkuye a kasa
suna tunani, Haisam ya rike kai
da hannuwansa
guda biyu can ya dago ya kalli
Hanne ya ce
“Yanzu dai a gidanku ke kadai
Babarki ta haifa kenan baki da
Yayye ko? Hanne ta ce “Eh. Ya ce
“Shine kuma ake saki debo
ruwa kullum. Hanne ta
ce “Ba debo ruwa kawai ba
kullum ni nake wanke-wanke,
shara, wankinsu, da kai dabbobi
kiwo
daga
can nayo musu ciyawa. Haisam
ya buga kafa a kasa ya ce “Kai
wannan wanne rashin imani ne
haka? To ya akai kike zuwa
makaranta? Hanne ta
ce “Sai wajen sha dayan rana
koma wataran bana
zuwa, tun ana min dukan
makaranta har suka
daina su Malamai. Shine wani
Malami ya je ya
sami mai gari ya ce a yiwa
Babana magana a dinga
turoni makaranta da wuri tunda
ina da kokari,
Haisam ya ce “Sai da maigari ya
kira Babanki ya
fada masa sannan ake turaki
makarantar da wuri?
Hanne ta ce “Cafdijan shima
Baban ya isa? Ya ce
“Kamar yaya bai isa ba. Ta ce
“Shima tsoron Iya Abu yake,
matar tasa zaginsa take,
*ya*yanta
suyi
masa, sai dai in ana dukana ina
kuka shima ya
dinga yi. Hawaye ya sake kece
mata, shima ya ji
kwalla ta cika masa ido, ya
dauko wani hankici
fari kal a aljihunsa ya goge
idanunsa ya mika mata,
yace “Yi shiru Hanne daina kuka
goge hawayenki. Ta
karba ta goge.
Haisam ya ce “Bari na danyi miki
tambayoyi naji
kina kokari? What is your name?
Hanne ta ce “My name is Hanne
Habu. Ya ce “How old are you?
Ta
ce “I’m eleven years old. Wich
school are you? Ta
ce “I’m in Babban-mutum
special primary school.
Haisam yayi dariya ya ce “Hanne
Habu haka kike
da kokari? To ke da bakya zuwa
makarantar sosai
ya aka yi kika koyi duk wannan?
Hanne tayi murmushi ta ce “Ai
daga baya maigari yasa aka
kirawo ita iya Abu da kanta taje
fada ya saka
shaidu ya ce “Duk ranar data
hanani zuwa
makaranta ko na makara sai ya
kaita kara local
goverment. Sannan take barina
na tafi makaranta
da wuri sai dai idan na dawo
tayi ta dukana tana cewa ga
wanke-wankenta nan harya
bushe na
tsaya a hanya ina wasa. Haisam
yayi tsaki ya
girgiza kai alamar tausayawa.
Yayi gyaran murya
ya ce “Hanne ina so kiyi min
alkawarin zaki dage
kiyi karatu duk rintsi duk wuya.
Kar ki zo ki fara
ayi hutu ki koma gida kiga
kawayenki da yayyanki
suna gida basa zuwa makaranta
kema kiki
dawowa. Hanne ta ce
“Kwarankwatsa zan dawo.
Haisam ya kece da dariya ya ce
“Kwarankwatsa
ba
rantsuwa bace wallahi Allah za
ki ce. Hanne tayi dariya ta ce
“Mantawa nayi Malamin
makarantar
Islamiyya ya hana mu cewa
kwarankwatsa.
Haisam ya ce “Kina zuwa
Islamiyya kenan? Ta ce
“Eh, ada makarantar allo muke
zuwa daga baya
aka bude makarantar Islamiyya
da yamma da
kuma dare duka ina zuwa.
Haisam ya ce dakyau Hanne
yanzu idan anyi hutu kin koma
gida sai kici
gaba da zuwa ta Islamiyya karki
fasa zuwafa
kinji?
Hanne ta ce “To. Haisam ya ci
gaba da kallonta
har sai da Hanne ta fara jin
kunyar kallon da yake
mata sannan yayi murmushi ya
ce “Hanne duk wannan kwalliya
ce kika yi a fuskarki, ta zuwa
makaranta ce? Hanne tayi
murmushi ta sunkuyar
da kai kasa tana rurrufe fuska
da hannu ta ce “A’a
ba kwalliya bace. Ya ce “Gashi
nan kin rambada
kwalli kinja wata doguwar
jagira kinyi fashin goshi
da kwalli kinyi digo-digo duk
fuskarki kice ba kwalliya bace.
Ga wannan tsakiyoyi da kika
jifga a wuya da
hannu har kafarki ma kin daura,
Yana dubanta
yana dariya.
Hannan ta ce “Eh sarkar salla
tace Baba ya siya
mun. Ya ce “Kinga nan
makarantar an hana sawa idan
Malamai suka gani zasu kwace
su tsittsinka
miki, ciro su ki bani in ajiye miki
sai anyi hutu in
zaki tafi gida na baki. Cikin sauri
taji zancen
tsittsinkawa ta ciro ta bashi,
yadda take bala’in
kaunar sarkokin nan nata bata
son abun da zaisa
ta rasa su. Haisam ya karba yana
jujjuyasu yaga wasu irin tsohon
wuri ne aka jera su cikin lilo aka
daura ya ce a ransa “Yan kauye
suna gayu. Yayi
murmushi ya jawo jakar
kayansa ya bude wani
karamin zip ya zuba ya mayar ya
rufe. Ya juya ya
kalli Hanne ya ce “Kuma a cikin
akwatin naki bude
in gani ko kinzo da wani
abunda dokar makaranta ta
hana. Hanne ta tashi daga kan
akwatin ta bude
ya karkato ya leka akwatin babu
abunda ya hango
sai tsummokarai, cikin sauri ya
ce “Hanne meye
wancan nake hangowa kamar
miciji a cikin
akwatinki?
Hanne tasa hannu ta zaro wani
dan siririn gyale baki ya
kanannade ya kudindine ta ce
“Gyale ne
ba miciji bane. Haisam ya
kyalkyale da dariya ya
ce “Na dauka kofi kika yimin na
miciji. Hanne ma
tayi dariya ta ce “Gyale na ne
dan bansa ruwa ba
na kadeshi shiyasa ya
cukuykuye, ya sake leka
akwatin sai ya hango wani dan
dogon karfe mai huda huda a
jikinsa, jikinsa kamar farar
azurfa
yana kyalli ya ce “Hanne wannan
fa, karfen
menene? Dauko muga.
Hanne ta yi murmushi ta dauko
karfen ta mika
masa ya karba ya jujjuya bai san
ko meye ba ya
ce “Wannan kuma na maye.
Hanne ta ce “Idan naje
kiwo nake yiwa dabbobi busa
dashi, abun busa
ne.
Haisam ya ce abun busa kuma?
Hanne ta ce “Eh
kawo ka gani. Ta karbi karfen ta
mayar da
akwatin ta rufe ta koma kan
akwatinta ta zauna ta
kaikaice
ta fara busawa Haisam wannan
karfen kai kace
Sarkin busar Sarki ne yake yi,
karin busar mai
dadi
da alama dai waka ce, Haisam ya
buda kunnuwa yana sauraro ya
baza ido yana kallon yadda take
yi.
Can ta kyalkyale da dariya ta ce
“Haka nake yi.
Haisam yayi murmushi ya gyara
zama ya ce “To
ni
abunda ban gane ba, kamar
yaya sai kinje kiwo kike yi?
Daman a wajen kiwo ake yin
busa? Waye
ya koya miki kuma? Nan da nan
Hanne ta canja
daga yanayin farin cikin da
fara’a da sakin jikin da
take jikinta yayi sanyi ranta ya
baci.
Haisam ya ce “Ya kika canja nan
da nan daga
tambayarki? Hanne ta rushe da
kuka ta kifa kai da
gwiwa, Haisam yayi matukar
mamaki da ganin
wannan hali da Hanne ta fada
yanzu-yanzun nan
ya ce “Yaya kina dariya ki koma
kuka, Hanne
dago
kanki. Ta dago ya ce “Goge
hawayenki. Ta goge. Ya ce “Fada
min meye na kukan? Hanne ta
ce
“Wani abu na tuna shine ya sani
kuka. Haisam ya
ce “Meye abun da kika tuna?
Hanne ta sa hannu
ta sake goge hawayen da ke
idonta ta dauko abun
busar dake kan cinyarta ta rike a
hannunta tana jujjuya shi.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE