Gangar jikinsa na aura33
Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter33
Hannah ta gigice ta tsugunna a gaban yarinyar kafin ta tambayeta me ya same ta ta fara zubar da hawaye. Ta sa hannu a jakarta ta zaro wani hankici fari kal mai kamshi ta mikawa yarinyar ta ce “Goge hawayenki. Yarinyar ta karba tana gogewa kafin ta goge hawayen da ya zubo wani ya sake tsiyayowa. Hannah ta goge nata hawayen ta ce da yarinyar “Yaya sunan ki? Cikin shasshekar kuka yarinyar ta ce sunana Abida. Abida daina kuka goge hawayenki ki fada min dalla-dalla abin da yasa kike kuka zan taimake ki in Allah Ya yarda. Hannah ta tambayi Abida. Abida ta ce “Tallar wake da shinkafa nake yi, sai wani mutum ya kirani shagonsa ya ce in kawo masa zai siya na ajiye farantin abincin a kofar shagonsa sai ya ce in shigo ciki nace ai kofar karama ce farantin bazai iya wucewa ba sai ya ce to in dauko masa kwano daya in kawo masa. Na dauko kwanon abincin na shiga shagon sai ya ce mun zai saye abincin duka zai biya ni harma ya kara min kudin fiye da kudin abincina amma sai na yadda ya kwanta dani, na ce na ki ni ba *yar iska bace sai kawai ya rufe kofar ya kama ni da karfi na kwalla ihu da karfi shine ya doke min bakina har ya fashe ya bude
mun kofa yasa kafa ya maujeni na fado waje kan farantin abincin ya zube shine naje gida na fadawa Babarmu shine ta zane ni da bulala ta koroni ta ce duk inda zan nemo mata kudin abincinta inje in nemo. Yanzu bansan yadda zanyi ba. Abida ta rushe da kuka mai tsanani. Hawaye fal a idon Hannah tayi shiru can ta ce “Abida Babarki ita ta haifeki ko kuma kishiyar Babarki ce? Abida ta ce “Uwata ta mutu Ubana ya mutu wannan Yayar Mahaifiyata ce take rike ni. Hannah ta ce “Bata da *ya*aya sai ke kadai? Abida ta ce “Basa zuwa suna gida kullum wata rana kuma su tafi makaranta. Hannah ta ce “Kefa bakya makarantar? Ta ce “An cire ni da dai ina zuwa ajina ma iku yanzu na daina zuwa.
Hannah ta jawo Abida jikinta ta rungumeta ta fashe da kuka mai tsanani, tausayinta ya kamata ta tuno rayuwarta irin ta Abida ada maraici bashi da dadi. Can ta dago da kan Abida ta goge mata hawayen fuskarta ta ce “Abida dauko farantin ki zo muje kan tudun can mu zauna. Hannah na gaba Abida dauke da farantin abinci tana biye da ita. Ihun da Abida ta tsala ta kifar da farantin dake kanta shine ya razana Hannah taji gabanta ya yanke ya fadi ta juyo da sauri sai taga wata mata dauke da bulala da cakume rigar Abida ta baya tana kokarin taftafka mata murtikekiyar bulalar dake hannunta. Hannah ta taho da dauri ta fisge Abida daga hannun matar. Yayin da Abida ta taho a guje bayan Hannah ta labe fadi take “Hajiya ki taimake ni karki bari ta dake ni. Matar fada take harda kumfar baki danna ashar take tana cewa “Kyaleni da tsinanniyar yarinyar nan yau saina kusa kasheta idan ma ban kasheta ba, ta sani a Uku abincin naira na dukan naira har dari hudu da hamsin ta zubar min. Hannah hakuri take bawa matar kamar zata durkusa mata amma matar nan fadi take yau ta shiga uku asara ta sameta sai ta daki kudinta. Sai da taga magiyar da Hannah take yi tayi yawa har hawaye ne yake fitowa daga idanuwanta sannan matar ta tsagaita ta fara sauraron abinda Hannah ke cewa. Hannah ta goge hawayen fuskarta ta ce da matar “Kina Musulma Bahaushiya *yar Uwata ina rokarki ina hadaki da Ubangijinki ya baza ki saurareni ba? Haba Baiwar Allah wacce hasara ce ta sameki haka har zaki manta da Ubangijinki? Musulmin kwarai baya mantawa da Kalu innalillahi wa inna ilaihi raji’un, duk sanda masifa ta same shi. Kina ta dankara ashar kina fadin kin shiga uku kin lalace saboda Allah Ya dora miki asara ke kuwa baiwar Allah baza ki tattara al’amuranki gaba daya ba ki mika wajen Mahaliccinki mai bayarwa mai hanawa ba? Matar ta tsuke fuska yayin da haushin Hannah ya rufeta ta ce “Malama wa’azi kike mun ko kuma jaje kike mun? Don na kasa gane abin da kike nufi. Kin hanani in daki *yata kuma kina tutsuyeni akan nayi masifa dame zanji da asarar da nayo ko kuma da fadan da kike min? Hannah ta nisa ta ce “Yi hakuri ba fada nake yi miki ba shawara nake baki a matsayinki na *yar Uwata Musulma ki rike kalmar Kalu inna lillahi wa inna ilaihi raji’un a lokacin da masifa ta afka miki zaki ga yadda Allah Zai saka miki da alherinSa. Matar ta ce “Wannan kuma tasha nawa nake fada, yaya zanyi tunda Allah Ya hadani da shegiyar diya. Hannah ta ce “Karki ki shawarata nasan kina cikin bacin rai da damuwa amma ki ce Kalu inna lillahi wa inna ilaihi raji’un zaki ji sanyi a ranki. Matar ta ce “Bazan ki taki ba yarinya Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Hannah tayi murmushi ta ce “Yauwa sai ki jira kiga sakayyar da zaiyi miki. Ta ce da Abida ta tsince kwanikan da suka watse a kasa suzo su karasa kan wani dan dakalin siminti suka zauna. Abida kuma ta tsuguna a kasa cike da fargaba.
Hannah tasa hannu cikin jakarta ta zaro kudi naira dubu dubu guda goma ta mikawa matar, matar ta bude baki tana jujjuya kudin. Hannah ta ce “Naki ne wannan ki kara jari, amman dan Allah ki canja sana’a ki daina dorawa Abida talla kibar Abida ta koma makaranta tayi karatu ta daina talla. Ta zaro wata dubu goma ta mikawa matar ta ce “Wannan na Abida ne ki saya mata Uniform da takalmin makaranta da litattafai da jaka ta koma makaranta. Sai matar ta rushe da kuka ta durkusa a gaban Hannah tana godiya. Hannah ta kama hannun matar ta zaunar da ita ta ce “Babu komai Abida kanwata ce daga yau zan dinga taimakon ku insha Allah. Hannah tasa matar tayi mata kwatancen gidansu sannan Hannah ta rubuta lambar wayarta a wata *yar takarda ta mikawa matar ta ce idan suna da wata matsala ta buga mata waya ko nawa ne zata taimaka musu ita dai fatanta a daina dorawa Abida talla a daina tsangwamarta don Allah. Hannah ta dora da bawa matar labarinta tana nuna mata tasan irin halin da Abida take ciki kuma gallazawa maraya haramun ne. Matar tayi nadama tayi dana sani taji kunyar Hannah sosai. Kuka take kawai tana neman gafara wajen Abida ta yafe mata.
Haisam ne ya karkato da motarsa zai shiga get din makarantar ga mamakinsa sai ya hango Hannah zaune a gefe ita da wasu. Ya karkata motar ya nufi inda suke cikin rikicewa ya fito daga motar ya nufi inda suke saboda ya hango su suna magana suna koke-koke. Ba tare da sun ga zuwansa ba sai suka ga mutum a kansu ya tsaya kawai yana kallonsu cike da mamaki. Hannah tayi sauri ta goge hawayen dake idonta tayi murmushin dole ta ce “Yaya yaushe ka zo, Yaya ya akayi kasan ina nan? Ya ce “Zan shiga ciki na hango ku anan. Lafiya, wadannan fa, kukan me kuke yi? Matar ta rushe da kuka tana cewa tsakanina da ku sai godiya Allah Ya saka da alheri. Hawaye ne yake zubowa daga idon Hannah. Haisam ya zaro hankici a aljihunsa yana goge mata yaja hannunta suka shiga mota Abida da Babarta suna ta dagawa Hannah hannu suma suna ta kuka, Haisam ya ja mota suka tafi. Yayi shiru baice komai ba can ya nisa ya ce “Wannan yarinyar marainiya ce ko? Hannah ta kalleshi cikin mamaki ta ce “Yaya akayi ka sani. Haisam yayi murmushi ya ce “Haba *yar Baba nasan ki nasan halinki fiye da kowa ina ganin babbar matsalarki yanzu a rayuwarki bata wuce maraici ba, duk sanda naga kinyi kuka nasan kin tuna Mahaifanki wanda koda yaushe ina miki nasiha kiyi hakuri ki cirewa ranki tunanin mamaci duk wanda ya mutu ya mutu kenan bazai dawo ba har abada, naga yanzu kukan naki ya wuce maraicin da kike ciki ya koma kan duk marayun duniya kuka kike musu, kamar ma zuga ki nake nace bana son inga kina kuka hankalina yana bala’in tashi kinki ji. Hannah ta marairaice ido yayin da taci gaba da zubo da hawaye Haisam yasa hannu daya ya jawota jikinsa yana tuki da dayan ya ce “Yi hakuri to fada min yadda kika hadu da wadancan mutanen. Hannah ta gyara zama ta goge hawayen idonta ta fara bawa Haisam labarin abin da ya faru. Dai dai lokacin sun iso Tarauni ya karkata ya shiga wajen da ake sayar da kayan ciye-ciyen makulashe wato Oasis. Hannah ta ce “Zaka ci kek ne? Da ka bari naje gida sai inyi maka. Haisam ya ce “Haba ai sai wahalar tayi miki yawa tun shekaran jiya rabon da kiyi barcin kirki musamman jiya kusan a zaune kika kwana kina karatu. Tea din ma dana hada miki da safe ko kurba daya ba ki ba kika tafi kika barshi kuma yanzu na tabbata baki ci komai ba, naga duk kinyi wuri-wuri shine nake so in saya miki wani abu anan. Ya tsaya a bakin wajen ya ce da ita su shiga ciki, suka fito suka shiga. Hannah ta zazzabi abinda take so kamar meat pie da kek da shawarma sai juices na gwangwani da yogot. Bayan Haisam ya biya kudin suka zuzzuba musu a leda.
Suna fitowa bakin wajen Haisam ya kira almajiran da su ke bara a wajen ya mika musu ledojin duka ya ce su je su rarraba su ci. Hannah tayi kasake tana kallon ikon Allah, Haisam ya kalleta yayi murmushi ya ce “Kina mamaki ne? Yanzu na canja shawara baza ki ci kayan zakin nan ba gara mu wuce Tahir Guest Place ki huta sai da yamma ko ma da daddare mu koma gida. Hannah ta ce “Amma ai ya kamata mu koma gida Aunty Ramlah ta ganni tasan na dawo. Haisam ya ce “Zo mu tafi ke dai kin fi jin tausayin Aunty Ramlah a kaina komai ki ce Aunty Ramlah zanje in gani. Sun isa kayataccen katafaren Hotel din Tahir Guest Place dake unguwar Lamido Creasent. Kayataccen daki suka kama mai dauke da falo, darning area, ga daki mai dauke da katafaren gado da ban daki a ciki.
Abinci kala-kala ma’aikata suke shigo musu da shi suna jerawa akan darnin table. Hannah da Angonta sun ci sun sha sun gyatse har sun rage. Haisam ya ruko hannunta suka nufi cikin daki kai tsaye bandaki suka shiga dan su watsa ruwa su ji sanyi a jikinsu duk da ga sanyin split AC daya gauraye dakin daga can suka dauro alwala suka zo suka yi sallar azahar. Bayan sun idar ne suka kwanta akan katafaren gadon nan, yayin da Hannah taji gaba daya kashin bayanta ya hau qara saboda gajiyar da tayi saboda tsabar zama ga barci a idonta. Haisam yana mata tausa har barci mai dadi ya fara surarta. Kamar a mafarki taji Haisam na cewa “Gaskiya Nusaiba kawarki na sanki yanzun nan daga ofis din mai girma gwamna nake, na karbo miki takardun kwangila Nusaiba tasa a baki ta miliyan ashirin da biyar, bai fi ki kashe miliyan goma ba wajen gyaran jiki zaki gina mata da saloon da wajen kunshi. Rauda ma ta miliyan ashirin da biyar aka bata zata zuba kaya a sabon gidan da ta ginawa wan Babanta (interrior decoration). Bayan kwangilar titi da suka bani kwanakin baya ta miliyan dari biyu, yanzu ma sun sake bani kwangilar gina wani titin shima wasu miliyoyin ne gashi su biya akan lokaci ina gamawa. Hannah tayi zunbur ta tashi zaune tana sauraronsa. Yaci gaba da cewa “Na saya miki wannan katon filin na jikin katangar gidana anan za’a gina miki Masallaci da makarantar Islamiyya da ki kace kina son a gina miki. Hannah ta ce ina so a gina gidaje guda biyu a gefe don ina so in dauko Iya Salma da Uwar biyu su zauna a daya, Wada kuma ya zauna a daya yana kula da Super Market. Haisam ya ce “Filin babbane ai zai isa. Hannah ta rungume Haisam dan murna ta sumbaci bakinsa ta ce “Thank you my Dear, shima ya rungumeta daga nan suka shiga farantawa juna.
Bayan kwana biyu da sassafe Hannah ta tashi tafa shirya kayan tafiya a akwati guda kayanta dana Haisam sai akwatinan tsaraba da zata kai musu guda uku. Ta leko ta wundo ta kira shehu direba ya lufga a cikin but din motar da zasu tafi da ita mai kirar CRB. Wayar Hannah ce ta tashi Ramlah da Haisam daga barci Ramlah ta lalubi wayar ta dauka Hannah ta ce “Yayata yi hakuri naji muryarki kamar kina barci na tasheki gashi ba a son tashin mai ciki daga barci wallahi banji dadi ba yi hakuri, Ramlah tayi murmushi ta ce “Lah Kanwata babu komai wallahi. Kin tashi lafiya? Hannah ta ce “Lafiya kalau daman sallama zanyi miki saboda kar inzo in buga miki kofa da sassafe, sai dai ince sai Allah Ya dawo da mu. Ramlah ta ce “Haka tsai-tsaye sauri kike har ba za ki bari a gama break fast ba ku ci. Yallabai ne ya azazzale ki ya ce ki shirya da sassafe za ku fita ko? To ai kuwa ga shinan yana ta shirgar barcinsa ke ya hanaki kiyi barcinki. Haisam yayi zunbur ya mike ya fada ban daki da sauri. Ramlah tayi dariya ta ce “Yanzun nan kin ganshi muna magana ya mike ya fada wanka. Hannah tayi dariya ta ce “Cemin yayi in tashi da asuba in shirya tafiyar sassafe zamuyi, dan da asubama ya dinga waya na dauka ma ya shirya, to shikenan bari na jira shi. Ramlah ta ce “Ki fito kizo bangarensa ki same mu muci abinci, bari in yiwa su Zuwaira waya a bangarena ina ga sun gama abinci su shigo mana da shi. Hannah ta ce “To gani nan zuwa. Suka ajiye waya.
Suna cin abinci suna hira Hannah ta dubi Ramlah tayi murmushi ta ce
.. “Auntyna badan ina ganin kin kusa haihuwa ba da sai nayi wata guda a can amma yanzu sati daya zanyi kawai. Haisam ya harari Hannah ya ce “Wai ke me wayo kina so dai kice min komin abuna duk da rakiyar da zanyi dan karki dade kina so kice min sai kinyi sati acan, kin san dai bazan iya mikewa a garin surukai in ta kwana har sati daya ba. Hannah ta narairaice ido ta ce “Na dauka saukeni zaku yi ku juyo idan na gama kwanakin ku dauko ni. Haisam ya ce “In kin dauka ma to ki sauke ai kafarki kafata kwana daya jal za muyi. Ramlah ta ce “A’a bai kamata ba ai dole tayi dan kwanaki Yallabai. Haisam ya lura da Hannah ta kule tana daf da ta fashe da kuka sai ya hau lallashinta yana cewa “To shikenan ai amarya bata laifi za muyi shawara a hanya dai. Ramlah ta ce da Hannah “Ga atamfofi can a jaka nasa Shehu ya dauka ya saka a mota da kudi a ambulan ki rabawa *yan kungiyata. Hannah ta ce “Kai Aunty har yanzu dai wahala baza ta kare ba? Ramlah ta ce “Babu komai Hannah yiwa wani yiwa kai, Allah ne fa Ya bani ikon tashi daga nan na je Niger na bude kungiya Allah Shine Ya ke bani abunda nake taimakonsu, Hannah tayi godiya daga karshe suka dunguma wajen mota, Haisam na cewa Ramlah lallai-lallai ta dinga kwana da wata a daki ta daina kwanciya ita kadai ko nakuda kan iya tashi cikin dare, ya shaida mata ba zasu dadeba zasu dawo.
BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MANA YASA MUGA NA BADIN BADADA LFY DAGA
DAGA:the founder of littafan Hausa zallah