Gangar jikinsa na aura34

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter34
A gidan baya Haisam da Hannah
suka kame Direba na jansu suka
tafi. Sun kama hanyar garin
dashi
cikin Janhuriyar Niger, tafiya
suke kamar ba’a mota suke ba
sanyin A.C na tashi yayin da
sautin kida ke
tashi a hankali. Hannah ta
kwanto akan cinyar Haisam
cikin shagwaba ta ce “Yaya nifa
so nake inyi sati guda a Dashi
sai mu wuce Babban-Mutum
inga Iya Salmai daga can sai mu
shiga Kazaure wajen Uwar Biyu
duk muga lafiyarsu. Haisam ya
ce “Amma sati daya yayi yawa
kiyi kwana hudu dai ni zan
wuce Maradi gurin abokina in
kin gama kwanakin sai muzo
mu dauke ki mu tafi Babban
Mutum da Kazaure a raar sai mu
wuce Abuja zanje inga yadda
suke sayar mun da motoci
sannan sai
mu huta a Nicon da Sharaton,
bayan kwana hudu sai mu koma
Kano. Yayi miki ko baiyi miki ba?
Ta ce “Yayi min tunda yayi maka
Nawan. Sun isa garin Dashi
yayin da mamaki da farin ciki ya
lullube
dangin Hannah. Hannah da Hajir
suka rungume juna suna murna,
Kawu Ahmad kuwa yasa aka
shimfidawa su Haisam tabarma
a zaure suka zazzauna dangi na
ta shigowa suna yi musu sannu
da zuwa. Nanfa aka garzaya
kasuwa dan siyo kayan abinci
iri-iri wanda za’a dafawa
wadannan
hadaddun *yan gayun baki. Fura
mai dadi da kindirmon nono
mai kyau aka kawo musu kafin
a
gama dafa musu abinci. Haisam
ya sha fura da nonon sosai
kasancewar yana son fura da
nono.
Bayan sunyi sallar azahar dai-dai
lokacin abinci ya nuna sai aka
fara zuwawa ana jerewa Haisam
nasa,
direba ma aka kai masa nasa a
kofar gida inda aka yi masa
shimfida. Hannah na cikin gida
tana cin nata kawaye da dangi
duk sun zagayeta kai ka ce biki
akeyi a gidan. Haisam da Kawu
Ahmad suna cin abinci suna hira
sai godiya Kawu Ahmad yake
yiwa Haisam.
Bayan sun gama ci la’asar tayi
suka yi Sallah sai Haisam ya
shaidawa Kawu Ahmad cewar
zai wuce
Maradi sai nan da kwana hudu
zai dawo ya dauki Hannah.
Kawu Ahmad ya roki Haisam ya
kwana
mana kafin ya tafi, Haisam ya ce
ba komai ai dare baiyi ba zasu
wuce kawai. Yasa yara suka
dinga
jido akwatina suna shigarwa
cikin gidan, ya ce kuma su cewa
Hannah ta fito suyi sallama zai
tafi.
Hannah ta bude akwatin
kayansu ta cire nata, ta bar
masa nasa a cikin akwatin tasa
aka kai masa
mota. Tasa Hijab ta fito ta iske
Haisam a zaune a zaune shi
kadai, ta durkusa ta gaishe shi
ya amsa
cikin fara’a ya ce “Kinga abinda
nake gudu ya faru dani. Hannah
ta ce “Yaya, meye ya faru da kai?
Ya
ce “Daidai da rana daya bana
son in rabu da ke amma gashi
kin jawo min sai nayi kwana
hudu zan
ganki. Hannah ta marairaice ta
ce “Allah Sarki kar ka damu
GANGAR JIKINA ce kawai bata
tare da kai
RUHINA yana tare da kai sai, su
duka suka yi dariya.
Haisam ya ce “Ai ni yanzu daga
GANGAR JIKIN har RUHIN so
nake su zamana tare dani, koda
yake
babu komai tunda mu duka
muna kasar Niger din tururin
numfashinki zai dinga buso ni.
Hannah tayi dariya ta ce “Nima
zanyi missing dinka. Haisam ya
mike tsaye ya ce “Babu wani,
dadin baki ne kin sami Hajir
kuna hira yaushe za ki tuna
wani Haisam.
Hannah ta ce “Ai kuwa da kasan
irin hirar da muke da Hajir da
kace mu shekara muna hira,
domin
asalin shakuwata da Hajir
hirarka kawai take taya ni.
Haisam yayi murmushi yayi mike
ya ce “Harna
fara jin kasala zan tafi ni kadai
in bar abinda nafi so a
rayuwata. Yanzu dai abinda
nake so dake shine ki sami biro
da takarda ki rubuta duk
wadanda ki ke so a dangi a
taimakawa da jari ko kuma
wata bukatarsu da suke neman
taimako kiyi min total zan canjo
kudin Niger acan, idan na zo sai
na baki ki rarraba musu. Hannah
ta amsa masa da to gami dayin
godiya da nuna farin cikinta a
fili. Ta ce “Kuma inaso in ginawa
*yan kungiyar Aunty Ramlah ofis
wanda zai zama anan za’a dinga
yin
taro kuma duk wani mai
sha’awar taimakonsu zai iya
kaiwa can. Haisam ya ce “This is
A very good idea, sai kicewa Kawu Ahmad ya
nemo fili ya kiyasta nawa za’a
kashe wajen ginin sai a bar
masa
ya gina. Hannah ta raka shi har
cikin mota suka dinga hira har
kamar bazai tafi ba, shi dai sake
nanatawa yake bai ji dadi ba
zaiyi kwana hudu bai ganta ba,
ita kuma hakuri take bashi har
dai ta
lallabashi ya tafi sannan ta shigo
cikin gida.
<script async src=”//pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js”></script>
<!– ads1 –>
<ins class=”adsbygoogle”
     style=”display:block”
     data-ad-client=”ca-pub-1385438965160906″
     data-ad-slot=”1986751703″
     data-ad-format=”auto”
     data-full-width-responsive=”true”></ins>
<script>
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
</script>
A kwanaki hudun da Hannah
tayi ta ziyarci *yan Uwa da
abokan arziki da yawa na cikin
garin dana
wajen garin kowacce tana kawo
kukanta wasu talauci ya ishesu
sun rasa yadda zasu yi, wasu
kuma auren *ya*yansu ya tashi
basu da kudin siyan kayan daki.
Hannah ta kaiwa *yan
kungiyarta ziyara bayan shela da
akayi aka tara su
a inda suka saba taruwa. Sunyi
murna da wadannan atamfofi
da kudadan da Hannah ta raba
musu ta ce inji Ramlah ta ce a
basu, ta shaida musu wannan
kadan ne kafin ta tafi zata sake
tara su ta
raba musu kudi fiye da
wadannan daga karshe tayi
musu albishir da cewa za’a gina
musu ofis da
katafaren dakin taro wato hall
za a zuba kujeru a ciki wajen da
za a dinga yin meeting. Ta kara
da
cewa da yardar Allah kungiyar
zata bunkasa zata dinga taron
tallafi ko da yaushe. Murna
wacce ba
zata misaltu ba a wajen *yan
kungiyar sai godiya da shi
albarka suke yiwa Hannah da
addu’ar fatan
alheri. Ranar da Hannah ta cika
kwana hudu tasan daga inda
gari ya waye Haisam zai dira a
garin
gashi bata gama ziyarar *yan
Uwa ba, don haka karfe bakwai
a gidan su Inna Haule tayi mata.
Tana
shiga tayi sallama ta iske Inna
Haule da Indo suna sana’ar da
suka saba, Inna Haule tasa Indo
a gaba
tana mata fada Indo kuma tana
tikar aiki. Inna Haule ta daga kai
ta dubi mai sallama sai taga
Hannah sai ta durkar da kanta
kasa ta kasa hada ido da ita ta
mike sumsum ta shige dakinta.
Indo ta
taho da sauri ta rungume
Hannah sai ta rushe da kuka.
Hannah ta zubo da hawayen
idonta ta ce
“Indo wajenki nazo na dauka
zan ganki a wajen taro ban
ganki ba na tambaya aka ce kina
gida
baki zo ba amma na bayar da
kashinki an kuwa baki? Indo ta
ce “An bani kinsan bani da halin
fita
inje wajen taro saboda aiki.
Hannah ta ce “Bari in shiga in
gaishe da Inna in zo mu shiga
daki muyi magana.
Hannah tayi sallama a dakin
Inna Haule sannan ta shiga ta
durkusa ta gaishe da ita ga
mamakinta sai taga hawaye fal a
idon Inna Haule ta zauna ta ce
“Inna lafiya kike kuka? Haule ta
sake rushewa da
kuka tana cewa “Ina ganin ki sai
Bello ya fado min a rai, tsananin
bakin ciki da takurawar dana
haddasa masa a sanadiyyar
gallaza miki dana yi.
Bello yayi min biyayya, ranar da
zai rasu mun rabu dashi yana
kuka yana rokona in sassauta
miki
Allahu Akbar sai gawarsa aka
kawo min ya mutu da bakin
cikina a ransa, duk da ni Uwarsa
ce mai zan
cewa Allah amma Bello mai
biyayya ne nasan zai yafe min.
Hannah ki yafe min a madadin
Bello da ke kanki abinda nayi
miki. Allah kenan Ya canja miki
rayuwarki kin min fintinkau,
yanzu kira Kawunki ki zo a
araba gadon Bello a baki naki.
Hannah ta zubo
da hawayen idonta ta ce “Inna
na yafe miki daman ba Bello kika
yiwa ba ni kika yiwa shi dai
yana damuwa a ransa duk
sanda zaiga kin gallaza min.
Sannan zancen a raba gado,
Inna rike duka na yafe miki ina
ganin yanzu gadon babu abinda
zai yi min,
ma’ana baki bani kaso na ba a
lokacin da nake bukatarsa. A
yanzu haka idan na karba sai
dai na
bayar saboda babu abinda na
nema na rasa kinga da in karba
in rabaki da shi in bawa wani
gara ki
rike duka tunda ga tsufa ya karu
karfi ya kare. Mai taimakon ki ya
rasu, ni ya kamata na baki ba na
karbi naki ba. Ni a ganina da kin
koma sabon gidan can na
siminti ki bar na kasar nan Inna
ki huta
saboda kar gidan ya zama asara
shi bai zauna ba ke baki zauna
ba, Allah Ya jikan Bello. Inna
Haule ta
ce “Amin na gode. Can zuwa
wani dan lokaci babu wanda
yayi
magana sai Hannah ta nisa ta ce
“Inna shawara daya zan baki,
mai zai hana ki bar Indo ta huta
da
wannan aiki da zagi da take sha
shekara da shekaru, Inna duba
kiga yadda Indo take tamkar
baiwa ita da *ya*yanta ita ce
gona, ita ce surfe da nika. Inna
Indo bazata iya tafiya ta barki
ba, ina zata kai *ya*yan nan? A
nan dai a jikinki take
samun dan abun da zata ci da
*ya*yanta ku zauna lafiya mana
amma aikin yayi yawa. Inna
Haule ta
nisa ta ce “Hannah naji abinda
kika cemun ni yanzu jikina yayi
sanyi in Allah Ya yarda zamu
koma sabon gidan Bello mu
zauna harda Indo da
*ya*yanta ko ni kaina nasan
bani da wata *yar Uwa mai
taimakona me min hidimomi
kamar Indo,
yanzu kwanaki amai da gudawa
nayi cikin dare Indo ce a kaina
har gari ya waye ita ta wanke
kayan kashin da amai. Gaskiya
kike fada mun kirawo Indo
itama in nemi gafarar ta. Inna
Haule ta
rushe da kuka. Hannah ta
kwallawa Indo kira ta taho da
sauri tazo ta durkusa ta ce “Ga
ni. Hannah
ta gyara zama ta yiwa Indo
bayani Inna ta saduda tasan
bata kyautawa don haka ta
daina takura mata. Amma sai bayanin Hannah
ya bambanta da tunanin Inna
Haule Hannah ta ce “Indo na
taho
miki da kudi ishasshe Kawuna
zai tsaya miki a rushe
bangaranki a gina miki na
siminti kema ki
zauna da *ya*yanki za’a fasa
miki kofar shigarku daban. Zan
baki jari mai yawa zan baki ki
dinga
sana’a kina cin abinci da
*ya*yanki, na dauki nauyin
karatunsu su koma makaranta,
kema ki huta da wahala a
rayuwarki. Indo ta rushe da
kuka tana godiya, Inna Haule na
kuka itama tana neman
gafararsu tana cewa “Ai baza ayi
haka ba idan Indo ta barni
dawa zan zauna ya dinga
taimakona, ga tsufa bana iya yin
komai da kaina tunda ba gani
nake sosai ba. *Yan*yan Indo
sune aikin gonata sune suke
mun talla jikokina na cikina ko
aikensu
nayi basa zuwa. Hannah idan
kika yi haka kin raba zumunci.
Mu dai kaura can gidan siminti
da Indon
mu zauna. Hannah ta ce “A’a
Inna ai ba’a sabo da wuya,
*ya*yan Indo karatu zasu yi ba
talla ba. Indo ta ce “A dangi zaki
nemi wata ku zauna ni kam ai
nayi gaba shekara nawa ana
azabtar dani da *ya*yana an
hutar dani sai inki, ba dai ni ba
nemo wata. Hannah ta ce “Indo
ma *yar aiki zan daukar
mata ita ta kwanta ta huta. Inna
Haule ta rike baki tana
maimaitawa *yar aiki? Indo da
*yar aiki. Yaro ne ya shigo ya ce
“Wai Hannah tazo anzo daukarta
inji wani mutum a cikin mota.
Hannah ta ce musu tana zuwa ta
fito sai taga Haisam ne ta
karasa cikin motar bayan ta
gaishe shi ta shaida masa cewar
gidan su Bello Madu tazo zata
gaishe
da Mahaifiyarsa. Haisam ya
harareta ya ce “Gidan tsohon
mijinki ki ka zo ga alamar kuka
nan kinyi wato kun tuna baya.
Hannah ta tuntsire da dariya ta
ce “Kai Yaya wanda ya mutu ma
kishi kake da shi? Ba wani tuna
baya da akayi ta ganni dai tahau
kuka. Hannah ta tambayeshi
kudi tana so ta raba
musu. Wata *yar akwati ya nuna
mata a kujerun baya tana
budewa sai taga kudi himili
guda ya ce ta
dibi yadda zai isheta. Ta dibi
kamar dubu dari da hamsin
idan aka canja da kudin Nigeria,
ta ce yazo
ya shiga ya gaishe su. Bayan sun
shiga Haisam ya zauna kan wata
tabarma a dakin Inna Haule
suka
gaisa sai Hannah ta ajiyewa
Inna Haule dubu Hamsin ta ce
gashi ta sayi goro. Ta wuce
dakin Indo
ta sami Indo nata rusar kuka, ta
zauna tana lallashinta ta mika
mata dubu dari ta ce ta fara yin
jari sannan ta tabbata *ya*yanta
sun ci gaba da makaranta. Ta
kuma ce mata duk sanda take
da
matsala taje ta fadawa Hajir ko
Kawunta Ahmad zasu fada mata
a waya zata aiko mata ko nawa
ne,
kuma karshen watan nan zata
turowa Kawunta kudi a fara yi
mata ginin. Indo tayi farin ciki
tayi
murna kwarai. Ta shaidawa
Hannah cewar yau jinta take
kamar a aljannah saboda lokaci
guda an *yanta ta ta fita daga
sahun bayi. Suka dunguma suka
fito har Inna Haule suka rako
su har bakin mota suna koke-
koke suna godiya,
Haisam yaja suka yi gaba. A
zauren Kawu Ahmad aka
zazzage akwatin kudi ana hasafi
ga sunan
kowa a jikin takardar da yawan
tallafin da za’a bashi. *yan mata
goma sha biyu Hannah ta yiwa
kayan daki wasu jari ta basu,
duk an mikawa Kawu Ahmad ya
raba musu. Kudin Nigeria Miliyan
biyu
Hannah ta bawa Kawunta check,
matarsa dubu dari biyu da
Hamsin suyi jari su gina sabon
gida na
suminti, Kawu Ahmad yaji kamar
a mafarki yayin da kuka ya
barke masa yayi godiya sosai.
Haka Hajir ma tasha godiya da
kukan farin ciki. Haka dai
Hannah ta zuba kayanta a mota
suka shiga direba
Shehu shima ya shiga ya tashi
mota *yan Uwa cunkus a bakin
motar ana daga musu hannu
suka
tafi. Farin ciki fal a zuciyar
Hannah harma kamar tafi su
farin ciki saboda taimakawa
danginta data yi sun fita daga
tsantsar fatara da rashin da
suke ciki.
Sun nufi hanyar Babban-mutum
a Janhuriyyar Nigeria.
Karfe uku dai-dai a kofar gidan
Iya Salmai tayi musu.
Hannah ta shiga gidan da sauri
yayin da take kwada sallama
waige-waige take taga ta ina Iya
Salmai zata fito tayi tsalle ta
rungumeta. Wada ta gani a
bakin kofar dakin a tsaye yana
cike da
damuwa. Hannah ta karasa
gareshi cikin sanyin jiki da
dimuwa ta ce “Wada lafiya, ina
Iya Salman take?
Wada karka cemun Iyata ta rasu
. Yayin da ta fara hawaye. Wada
ya ce “Bata rasu ba gata nan a
zaune a daki tana kuka tun jiya
da yamma taki ci taki sha.
Hannah ta fada cikin dakin da
sauri ta iske
Iya Salmai tayi tagumi tana kuka
tana ganin Hannah sai ta sake
tsala kuka. Hannah ta ce “Iya
lafiya me ya faru? Wada ya shigo
ya zauna ya ce “Bansan taka
maimai meke damunta ba jiya
da rana ita da wani mutum suka
je wani gari ni dai bata fadamun
sunan garin da suka je ba sai na
ganta ta dawo da yamma tana
kuka ta ce mun wai
yau ido da ido taga Malam Habu
Mahaifinki har sunyi magana da
shi. Hannah ta zabura ta daka
tsalle ta dafa kirji ta fara ja da
baya ta fita daga dakin taje
tsakar gida ta zauna yayin da jiri
yake
daukarta bata gani sosai,
gabanta ya hau faduwa ta
tabbata lallai ciwon so ya zautar
da Iya Salmai har Malam Habu ya
fara yi mata gizau.
Uhm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE