Gangar jikinsa na aura5

Hausa novels

GANGAR JIKINSA NA AURA 


Chapter 5


 Kowa ya tambayeki yaya sunanki sai kice… Kafin ya fada Hanne cikin murna da farin ciki ta ce “Hannah Abubakar Imam.

Haisam ya tuntsire da dariya ya ce “Harma kin rike sunan kenan? Hanne ta ce “Eh, Hannah yafi dadi Allah. A dai-dai wannan lokaci suka hau barandar ajin. Haisam ya wuce gaba ya shiga ajin Hannah na biye dashi a baya. Suka shiga dukkan daliban ajin suka mike tsaye don girmama Malaminsu suka hada baki dukkan su “Good morning Sir” Haisam yayi murmushi ya ce “Morning student, how are you? Suka sake hada baki suka ce “We are fine Sir, ya ce “Thank you sit down. Kowacce ta zauna akan kujerarta. Haisam ya jawo Hannah gaban aji ya ce “Ga wata sabuwar daliba kun samu. Rauda ita ce monita ta mike tsaye ta ce “Lah, what is your name? Hanne ta daga ido tana kallon Haisam, ya harareta ma’ana ta bada amsa, Hanne ta ce “My name is Hanna Abubakar Imam. Kamar yadda Haisam ya ce ta dinga fada. Nusaiba wacce ita ce mataimakiyar monita ta ce “Ehm, nice name your are welcome Hannah. Haisam yayi murmushi ya ce “Kun fara iyayin naku ko? To maza ku saka mata kujerarta a tsakiyar ta ku  a gaba kuma kunga ita yar kucilace kamar ku. Cikin sauri Rauda taje bayan aji ta dauko kujera ta kawo ta koma ta dauko tebur tazo ta dasa a tsakiyar su a jere. Dake su duka ukun kansu daya sune yan kananan ajin sunfi kowa kankanta kasancewar akwai dingin-dingin din yan mata a ajin, musamman kabilun nan wata sai ka rantse uwa ce amma yar aji daya ce.

Farin ciki ya lullube Hannah da Haisam musamman ma Haisam yaga Hannah ta samu shiga wajen Nusaiba da Rauda wadanda su suka fi duk yan ajin kokari dan Rauda a America tayi karatun nusery da primary dinta don haka tana da bala’in kokari ga turanci daya kama bakinta. Hausa ma tana kokarin ta subuce mata. Kuma Yayanta Auwal abokin Haisam ne na kut, Babanta Alhaji Shitu abokin Baban Haisam ne, sannan Ramla yayarta ita Haisam zai aura don haka nema aka kawo Rauda makarantar saboda Haisam yana nan tazo akayi mata jarabawa ta ci shikenan aka dauketa, don haka nema take kiransa da Yaya Haisam sabanin Uncle Haisam kamar yadda sauran dalibai suke kiransa.

Nusaiba ma wata tsadaddiyar makaranta ta gama a Abuja. Ita yanzu haka ma Iyayenta suna Abuja karatu ya kawota nan amma haifaffun garin Gombe ne fulani. Rauda da Nusaiba sun zama kawaye tun ranar da suka hadu a ranar da aka kawosu makaranta, ajinsu daya suka kuma ci sa’a dakinsu daya, don haka ga gadon Rauda gana Nusaiba kuma sun hada kayan akwatinsu. Haisam ya ce “Monitor da Mataimakiyarta ku biyoni waje ina da magana daku. Rauda da Nusaiba suka mike suka bi bayan Haisam wajen aji.

Hannah na zaune babu abunda take kallo sai kallon ginin ajin da dalibai daya bayan daya taga kowacce sanye da uniform dinta tsaf-tsaf, fararen takalma kambas da fararen safa kan kowacce kitso ne tar. Hannah ta ce a ranta “Ashe da nasha kunya da ace a ranar da Baba ya kawo ni a haka na shigo ajin nan da na fita daban. Kai wannan Malami ya taimake ni Allah Yayi masa albarka. Ta ci gaba da kallon ginin ajin da irin zane-zane da akayi a takarda duk an lillika a jikin bango ga fankoki a jikin silin sunata fitar da sassanyar iska. Ginin bulo “Hannah ta fada a fili ba tare da tasan a baiyane ta fada ba.

Bayan fitar su Haisam a bayan aji suka tsaya ya kalli Rauda ya juya ya kalli Nusaiba ya ce “Rauda, Nusaiba. Su duka suka amsa ya ci gaba da cewa ga Hannah nan, kamar yadda Rauda kike kawar Nusaiba to Hannah ta zama kawarki itama, sannan kamar yadda ke Nusaiba kike kawar Rauda to ina son Hannah ta zama kawarki. Duk da ku biyu dakin ku daya to Hannah ma yar dakin kuce. Dake Safiyanu ya fada masa sunan dakin Hannah. Ya ce don haka ku uku dakinku daya, ajinku daya.

Kamar yadda a ko ina kuna tare, a hall ne a daki ne to Hannah ma ta zama kuna tare ita ma kanwata ce kunji ko? Su dukka suka amsa. Nusaibah ta ce “Uncle Haisam ko baka ce mu zama kawaye ba daman zamu zama tana burgemu Haisam yayi dariya ya juya ya kalli Rauda ya ce “Kanwata ke baki ce komai ba ke bata burgeki? Rauda ta tabe baki ta ce “Yaya Haisam rannan fa ka ce nice kadai kanwarka a makarantar nan yanzu kuma ka ce ita ce.

Haisam ya kyalkyale da dariya ya dafa kanta ya ce “Rauda kenan, ai har yanzu kina nan a matsayinki na kanwata, itama Hannah yar uwata ce kinga dole kanwata ce, Nusaiba ma kanwata ce don haka karki damu. Gata nan duk abunda bata sani ba akan karatu ku koya mata. Haka kuma magana da turanci ku rika tunasar da ita koda ta manta ta yi Hausa karku rubuta sunanta a masu yin Hausa sai a hankali zata saba itama ta ringa yin turanci sosai. Haka a daki idan bata san yadda zata yi amfani da wani abu ba kamar man gashi in zata shafa a jiki ku nuna mata na gashi ne ba ku ringa yi mata dariya ba kuna gayawa kawayenku kunji? Musamman ke Rauda kinga su Rose suna yawan kawo mun kararki wai kina yi musu tsawa kar in sake ji kina yiwa Hannah kinji ko? Rauda ta ce “Yaya ya za’ayi ta shafa man gashi a jiki sai kace bakauyiya. Haisam ya ce “A’a wai a misali nake nufi, koda a ce zata manta ta dauko man gashin.

Tafiyar wani Malami ce tasa duka hankalinsu ya juya baya don ganin mai tahowa, Haisam ya ce “To shikenan ku koma aji ga Malam Shaiya nan zai koya muku Maths an kada first period. Suka ruga aji a guje, Malam Shaiya ya mikawa Haisam hannu suka gaisa sannan ya nufi S.S.3C yana da period yana koya musu Geography.

Kamar Haisam yayi duba, da ya ce idan ta dauko man gashi zata shafa a jiki haka kuwa aka yi. Hannah babu abunda ta sani a kayan akwatinta, daga ta dauko man wanke gashi (shampoo) ta kwaba a jikinta sai ta dauko man shafawa ta maka akanta, makilin ma wani lokaci a tsagar kitso Rauda tazo ta isketa tana sharbawa. Suyi ta dariya har su godewa Allah daga karshe dai suyi mata bayani dalla-dalla, wannan ne na kaza wannan kuma a waje kaza ake shafawa. Babu laifi a sati biyu Hannah ta waye ta gane da duk kayayyakin amfani na zamani sannan ta koyi cin kayan gwangwani dana kwali, don da farko idan suka dama comflask da madara cokali daya zata yi sai ta fita a guje ta kelaya amai bata sanshi ba. Haka sadin da gesha kifin gwangwani sai taki ci tace tsutsa ce amma daga baya duk ta waye tana ci.

Hannah tana farin ciki matuka da wannan sabuwar rayuwar data tsinci kanta. Abinci lafiyayyu a akwatinta na makaranta, gashi tana cikin yara sa’aninta suyi karatu tare suyi wasa tare musamman Nusaiba tana bala’in kaunar Hannah tafi Rauda kirki don Rauda ta cika nuna isa da nuna tafi kowa kuma duk girmanka sai ta ringa daka maka tsawa. A fannin karatu kuwa ada Hannah dumame kujera take yi kawai saboda tsantsar turanci ake yi a makarantar amma sai Nusaiba ta lura da Hannah bata fahimta don haka a koda yaushe bayan Malami ya gama darasinsa sai ta matso da kujerarta har kusa da ta Hannah tayi mata bayani dalla-dalla. Haka shima Malam Haisam kullum a prep din yamma yana zuwa ya kira Hannah ya koya mata abubuwa da dama. A wata daya Hanna ta fara gane turanci fiye da yadda kuke zato.

Ranar wata asabar da daddare ranar ne ake warewa dalibai su shakata su hole rayuwarsu kamar a saka musu kidan disko su cashe wasu kuma su kada tebur da kansu suna waka wasu rawa. Wasu kuma talabijin ake kunnawa da bidiyo suyi kallon kaset duk dai abunda ransu keso shi zasu yi. Daga *yan J.S.S 1 har zuwa *yan S.S 3 wannan rana ita ake kira da “SOCIAL NIGHT” Uncle Haisam kuma shine social master wato shine Malamin da yake kula da dalibai, yake kula da C.D din da ake kunna disco da bidiyo da talabijin din da ake kunnawa. A wannan dare an yarjewa dalibai su saka kayansu na gida (personal) kowane iri ne kama daga leshi ko shadda riga da siket kai har jeans da tee shirt duk zasu iya tsukewa. 

Rauda Sarkin rawa ita har tunanin wannan asabar din wacce irin rawa zanyi don har fili ake bata kowa ya koma gefe yana kallonta rawa salo-salo har wasu suke kiranta Jenet Jacson wai kanwar Micheal Jecson.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE