Gangar jikinsa na aura6

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter6

Nusaiba kuwa ita da Hannah babu abinda suka fi so irin kallon bidiyo Hausa fim masu kyau Malam Haisam yake samowa ko Nigeria firms. Social night din wannan asabar din  bata yiwa Hanna da Nusaiba dadi ba saboda bidiyo ta lalace babu kallo sai dai C.D aka kunna aka ware kida duk mai bukata yaje ya cashe wasu na rawa wasu kuma na gefe suna kallo.
Amma wasu suna kan barandar wajen Hall din a zazzaune basa sha’awar yin rawa ko kallon masu rawa. Kungiya-kungiya kowanne da group dinsu suna waje suna zazzaune suna hirar duniya. Hanna da Nusaiba suna daya daga cikin wadanda basu shiga cikin Hall din ba wajen kida suna zazzaune a can wata barandar ofishin Malamai suna hirar duniya, hirar ma jifa-jifa suke yi saboda duk rayukansu a bace yake yau babu kallo. Kuma wani hadadden American film mai suna “Mr bones” Uncle Haisam yayi musu alkawarin zai saka musu. Nusaiba tayi ajiyar zuciya ta ce “Anya kuwa yau zan iya bacci saboda bakin ciki na kudiri niyyar ganin film dinnan, wallahi fim din akwai abun dariya muna dashi fa a gidanmu.
Hannah ta ce “Na last week ma yayi kyau ga abin dariya sosai “Osofia in London” Yaya Haisam ya iya zabo mana films masu kyau. Wata murya ce a bayansu tace na kama ku kuna gulmata. Suka juya da sauri sai suka ga Yaya Haisam ne su duka suka tuntsire da dariya ya zagayo suka matsa masa ya shiga tsakiyarsu ya zauna yayi murmushi ya ce “Kuna gulmata ko, dan yau bankunna muku kallo ba ko? Nusaiba cikin shagwaba ta ce “Yaya Haisam har kwalla nayi fa wallahi yau duk ranmu a bace yake. Yayi dariya ya ce “Kai haba harda kwalla? Ke fa Hannah kema kin yi kukan? Tayi murmushi ta ce “A’a banyi ba Uncle Haisam. Ya ci gaba da jansu da hira yana zolayarsu kamar yadda ya saba wasa da dariya da dukkanin daliban makarantar musamman da wadannan ukun. Ya ce da su “Ga Rauda can a Hall tana cashewa kuje ku tayata mana ko kuma kuyi mata liki. Suka yi dariya suka ce “Mu bama rawa, suka ci gaba da jigum. Haisam ya lura yau dai Nusaiba da Hannah babu kanta basa son magana balle doguwar hira ya ce “Nusaiba, Hannah yaya haka kowacce tayi zugum babu nishadi kamar yau ba ranar social night ba. Nusaiba ta ce “Yaya Haisam tsabar bakin cikin rashin kallon nan ne yake damunmu. Ya ce “Shi yasa baku fara’a? To yanzu daya bayan daya sai kun yimin waka da rawa tunda yau social night dole kuyi murna.
Cikin shagwaba Nusaiba ta ce “Yaya ni ban iya waka ba sai dai Hannah ta fara
tunda ita ce karama. Haisam ya kalli Hannah wacce ke murmushi har yanzu ya ce “Kinji wai inji Nusaiba ke za ki fara kece karama. Hannah tayi dariya ta ce “To bari inyi muku wakar Sarkin garinmu, Hanne ta fara tafi ta fara rero waka. Haisam ya ce “To tsaya tafi akeyi muma mu dinga tayaki muna miki amshi? Ta ce “Ai da kwarya ake kidan dan dai babu kwaryar ne.
Yasa hannu a aljihu ya zaro wannan abun busar daya karba a wajenta ya ce zai ajiye mata. Ya ce “Ga abun busarki ma ki busa mana ki kuma rero mana wakar kiwo. Cikin farin ciki Hannah ta karbi abun busarta ta hau jujjuyashi tana cewa “Allah Sarki abun busata na dade ban busa kaba, Nusaiba ta ce “Lah busa muji yadda ake yi. Hannah ta kaikaice ta fara busa abun busarta tana rera waka kamar haka.
Muyi kiwo samari, kuyi kiwo yan mata.
Kiwo baiwa ne, waka baiwa ce, haka busa ma baiwa ce.
Kuyi soyayya samari, kuyi soyayya yan mata.
Ke yar budurwa ina naki gwanin?
Ni nawa gwanin baya nan, yayi tafiya.
Amma koda bana tare da gangar jikinsa, ruhinsa yana tare da ni.
Haisam ya ce “Hanna tsaya meye koda gangar jikinsa bata tare dani ruhinsa yana tare dani? Tayi shiru can ta ce “Oho nima haka ya koya mun wakar, Nusaiba ta ce “Meye ruhi? Hannah ta ce “Nima ban sani ba, ina jin larabci ne.
Haisam yayi dariya ya ce “Yarinta mai dadi.
Kwanci tashi yau kwanan Hannah arba’in a makarantar har an kafe musu time table din jarabawa wato end of 1st term examination kasancewar daman dalibai sai da suka yi kimanin wata guda da dawowa makaranta sannan aka kawo Hanna. Babu abunda Yaya Haisam yake yi sai nasihohin da yakema yan ajinsa wato J.S.S 1A da kowaccensu ta cire wasa tasa littafin karatu a gaba don suci jarabawa. Haka kuma a wasu lokutan kan kira kannansa Rauda, Nusaiba da Hannah yana kara yi musu fada dasu dage sufi kowa cin jarabawa ya sake cewa “Hanna bana jin fargabar su Rauda kamar ke don haka ki dage duk abunda ba ki sani ba ki tambayi Nusaiba ko Rauda idan sun sani su koya miki, idan kuwa basu sani ba to kuzo ku tambayeni.
Haisam yayi musu rantsuwa da Allah a cikin su ukun nan duk wacce ta fadi jarabawarta sai yayi mata bulala kuma daga ranar data fadi jarabawa babu ruwansa da ita ya cireta a cikin kannensa. Gaban Hannah ya fadi ras dajin bayanin Yaya Haisam ta ce a ranta “Idan Yaya Haisam ya ce babu ruwansa dani aina shiga uku tunda babu mai yimin siyayyar makaranta karshenta ma karshen karatunta ya zo. Ta kudiri aniyar daga yau babu ita babu cikakken bacci zata dage da karatu don taci jarabawa, kada Haisam yayi fushi da ita.
A sati daya su Hannah suka gama jarabawarsu, jarabawa bibbiyu suke a rana daya. Don haka babu hutu ba dare ba rana kowacce ta dukufa da karatu, musamman Hannah sallah ce da cin abinci yake tashinta daga kan littafin karatunta, haka kuma ta zana jarabawar cikin sauki ma’ana da an bata question paper sai taga tasan amsoshin gaba daya. Haka take amsa su cikin sauki saboda tsabar ta gama karance Littattafanta. Hannah tasan Yaya Haisam zaiyi murna da sakamakon jarabawarta tunda tayi karatu yadda ya kamata. Hutu kuma sai wata juma’a don haka dukka wadannan ranakun babu abunda suke yi sai wasanni da raye-raye da wasannin kwaikwayo na kungiyoyi (club) din makarantar kamar English club, Hausa club, Jet club, Chemical club, Geography club, Yoroba, Igbo da dai sauransu, kuma kowacce daliba daga yar aji daya zuwa shida tana da damar da zata shiga kowanne club a makarantar. Su kuwa Malamai cikin satin nan suka dukufa da aikin making jarabawar dalibai don ganin kafin ranar hutu sun bawa kowacce daliba sakamakon jarabawarta ta tafi dashi gida Iyayenta su gani.
Ranar alhamis ana gobe hutu Haisam ya tara yan ajinsa a bakin babban dakin taron dake makarantar wato Hall don ya bawa kowacce sakamakon jarabawarta (report card). Yan ajin Malam Haisam suna da dinbun yawa don dalibai saba’in da shida ne a ajin Hausawa da Yarbawa, Igbo Musulmai da kiristoci sama da talatin, wata ko zo bata sani ba da Hausa, tun daga kudu suke babu abunda suka saka a gaba sai karatun littafinsu don shine abunda ya kawo su tun daga can uwa duniya zuwa nan kenan. Don haka babu koma baya a ciki kowacce tayi iya kokarinta matuka a wannan Jarabawa.
Haisam ya kalli fuskokinsu daya bayan daya sannan ya kyalkyale da dariya. Abun mamaki babu wacce ta taya shi dariyar kamar yadda suke wasa da dariya a aji ayau kowacce fargabar jin sakamakon jarabawarta take, musamman ma Hannah.
Tashin hankali ne mara fasaltuwa a zuciyarta  tunanin maganar da Yaya Haisam ya fada yayi musu rantsuwa ya ce duk wacce ta fadi jarabawa sai yayi mata bulala kuma babu ruwansa da ita.takeyi Hakika bata fargabar bulalar sosai tafi fargabar babu ruwansa da ita din daya fada, idan Haisam ya cire hannunsa akan Hannah waye kuma zai tsaya mata, a duniya yadda take son makarantar nan aiko hutu bata so ayi wato Hannah na daya daga cikin yan kwaleji tafi gida dadi. Abunda take ci tasha da makwancinta yafi na gidansu, ga uwa uba kwanciyar hankali wasa da dariya da kawayenta, sabanin a gidan su sai bauta, anan makaranta ma akan sasu aiki ko aike amma ba mai wahala ba kasancewarsu kanana yan aji daya dole senior zasu aikesu.
Haisam ya ce “Oh! Yau babu dariya duk kunyi cirko-cirko kuna jiran sakamako to da yawa daga cikinku kun yi kokari amma wasu basu yi kokari ba don haka wadanda basu yi kokari ba sai sun dage idan ba haka ba karshen shekara za’ayi musu repeating kowa ya wuce aji biyu a barku a aji daya ku sake maimaita shekara.
Gaban Hannah ya sake faduwa ras sai addu’a take sannan ta ji dan saukin dukan da zuciyarta take yi mata. Haisam ya ce “Yanzu zan fara kiran sunan wadanda suka yi na daya zuwa na uku sai a tafa musu zan kuma basu kyaututtuka. Sannan na kirawo na hudu zuwa goma suma zasu fito a tafa musu sune suka fi yin kokari, sauran kuma sai ku dage nan gaba. Hadiyar yawu yake ji mukut-mukut dalibai nayi don faduwar gaba dariya ta sake kecewa Malam Haisam ya girgiza kai, sannan ya bude file din dake hannunsa ya ce “Dalibar da tayi matukar kokari ta zo ta daya ita ce Rauda Shitu Muktar. Rauda ta kwalla kara don dadi sauran suka sa tafi suka juyo suna mata kallon sha’awa kowacce a ranta tana dama nice Rauda Shitu a ransu.
Haisam ya ce “Taso, fuskarta cike da fara’a zuciyarta cike da farin ciki ta zo ta tsaya gefen Haisam ya ci gaba da cewa, “Sai kuma wacce ta zo ta biyu ita ce Nusaiba Idris. Farin ciki ya lullube Nusaiba itama ta mike tazo kusa da Raudah Shitu ta tsaya dalibai na yi mata tafi raf-raf, ta uku kuma ita ce Pammella Matin Benin. Pamella ta daka tsalle don murna ana tafa mata ita ma ta fito tazo ta tsaya a kusa da Nusaiba Idris.
Hannah na lungu ta kankame gwiwarta da hannayenta ta zura kanta a matsematsin cinyoyinta yayin da kuka ya kece mata. Taga kawayenta biyu Rauda da Nusaiba wadanda suke karatu tare sun zo sun fita kokari. Ta gama saddakarwa Yaya Haisam ya cire hannunsa daga kanta tunda bata yi kokari ba. Haisam ya rufe file din dake hannunsa ya kalli sauran daliban da suke zazzaune a kasa ya ce “Kunga wadannan ukun sunfi kowa yin kokari a ajina don haka zan basu kyaututtukan da zasu je gida su nunawa Iyayensu suji dadi,

Masu yin comments godia nake Allah yabar zumunci
Marasa yi kuma!!! Kuje kune a qasa

    Yanzu fa aka fara muje zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE