Gangar jikinsa na aura8
Hausa novels GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter8
Haisam ya kalleta yayin da yaji
kamar zuciyarsa zata
fashe don tsananin tausayinta,
yayi karfin hali ya ce “Hannah
kukan meye kike don kawai anyi
hutu
zaki tafi gida? Ai na cewa uwar
biyu zata je ta daukoki kinji ko?
Zan zo inyi miki siyayya na
mayar dake makaranta, yanzu
idan kika je gida kina kuka Baba
zaice wahala kike sha a
makarantar ya ce
baza ki dawo ba. Amma ki
nunawa Baba makarantar da
dadi ga ladabi da biyayyar da
ake koya muku ga karatu da
abinci a wadace shi da
kansa zaice ki dawo, kin ji ko?
Hannah ta gyada kai ta fara
share hawayen idonta. Ya ci
gaba da cewa “Kiyi hakuri da
duk abunda Iya Abu take yi miki
hutu na karewa Uwar biyu zata
zo ta dauke ki ta kawo ki
makaranta. Sannan kullum ki
dinga zuwa makarantar
Islamiyya kina kuma duba
littattafanki na makarantar boko
don karki manta karatu kinji.
Allah Ya kiyaye hanya Hannah. Ya
juya ya tafi, muryarta yaji ta
rushe da kuka, ya juyo ya tsaya
cak
yana kallonta sai ya rasa me ma
zai ce mata sai ya juya ya tafi da
sauri. Yana mai tsananin
damuwa da
takaici, kukan zuci kawai yake.
Ba tare da ya cewa su Auwal
komai ba, ya shiga mota ya fara
tukawa. Can Rauda ta nisa ta ce
“Yaya Haisam daman Hannah
fulanin Daura ne. Ko ba daura
zasu ba?
Haisam yayi dan murmushi
kawai, Auwal ya ce “Haisam ka
cika shige-shige ina ka samu
wannan
yar buzuwar har da kakarta
kuma?
Haisam ya ce “Wai shige-shige
ni da kai za’a san mai shige-
shige naga daga zuwa har
kasan su
Naja’at Sulaiman ko banga
sanda take baka adireshinta bane
balle ni dana yi shekara a
makarantar. Auwal ya ce “To ya
isa ga wannan
zabiyar a baya ta bude kunnuwa
tana daukar rahoto. Haka dai
har suka isa Kano jifa-jifa
Haisam yake magana babu
abunda yake tunawa sai halinda
Hannah zata kasance a gidansu.
Zuciyarsa Cike da tausayin ta,
kulle-kullen yaya zaici gaba da
taimakonta yake gashi kuma ya
bar makarantar.
Har suka isa Kano. A nasarawa
G.R.A Suleman cresent gidan su
Haisam yake suka shiga cikin
katafaren get din gidan. Bayan
Auwal da Rauda
sun shiga sun gaisa da Hajiyar
Haisam sai suka yi
sallama suka nufi suma nasu
gidan da yake Lamido cresent
basu da nisa sosai.
Alh. Shitu Mukhtar sunan
Mahaifin Rauda, Mahaifiyarsu
kuma Haj, jamila sunanta.
Alh. Shitu Mukhtar haifaffen
garin Kano ne, dan unguwar
Kabara ne tare suka yi firamare
da sakandire da
Mahaifin Haisam abokaine tun
suna yara. Haj. Jamila
kuwa Mahaifiyar su Rauda
mutumiyar Chadi ce ya aureta.
Allah Ya albarkace su da ya*ya
uku, Yaya Auwal shine babba
wanda ya kammala karatun
likitansa a America yanzu
cikakken likita ne. Sai Aunty
Ramlah wacce ta gama
sakandire dinta
wannan shekarar tana jiran
sakamakon jarabawarta ta
wuce jami’a bayan an cancara
bikinta da angonta Haisam, sai
ta fara karatu a gidanta. Sai *yar
autarsu Rauda wacce yanzu
take ajin farko a sakandire.
Tsantsar *yan boko ne *ya*ya
uku sun ishesu rayuwar duniya
suna basu
cikakkiyar kulawa da tsananin
so da kauna.
Allah Yayi musu arziki mai yawa
don haka a daula suke
ta ko ina hutu, ba su fi shekara
biyu da dawowa Nigeria ba
kasancewar Alh. Shitu Mukhtar
yana aiki a embassy, shine
jakadan Nigeria a America
(abbasador) don haka duk a can
suka yi karatunsu. Har
Mahaifiyarsu Haj. Jamila a can ta
hada digirinta.
Al’amarin Hannah da uwar biyu
kuwa, bayan
tafiyar Haisam uwar biyu tayi
sauri ta sauka daga motar taje
ta yiwa Hannah siyayya kamar
yadda
Malam Haisam ya umarce ta da
ta yi. Ta dawo cikin mota da
sauri ta iske motar dai bata cika
ba, bayan
mota ta cika suka kama hanyar
tafiya. A hanya uwar biyu ta ci
gaba da lallashin Hannah tana
bata
baki dakyar tayi shiru da kukan
da take yi. Ta dade daman tana
so taji labarin Hannah da
dangantakarta da Malam
Haisam, saboda tsananin
kulawar data ga yana yi mata,
cikin wayo da dubaru irin na
manya uwar biyu ta dinga
bugun
cikin Hannah tana son jin
labarinta. Abunka da yarinya da
kuma neman agaji take yi ta
ko ina Hannah ta fayyacewa
uwar biyu komai daga farko har
karshe. Uwar biyu ta tausayawa
Hannah ta sake jinjinawa Malam
Haisam bisa jahadin da yayi
saboda Allah na taimakon
Hannah.
A garin Babban-mutum suka
sauka aka sauke musu jakarsu.
Tun da sauka Hannah ta fara
faduwar gaba tazo garin da
bawa ya fita jin dadi. Uwar biyu
ta lura da hakan sai tayi ta bata
baki tana
kwantar mata da hankalinta.
Kawayen Hannah maza da mata
*yan garin suka baibayeta suna
kallonta. Wasu kuma suna
shisshige mata har rububin yi
mata magana su ke. Masu
daukar mata jaka suka dauka
suka dunguma zuwa gidansu
Hannah. Samarin garin sai kallon
Hannah suke,
gani suke kamar ba Hannar da
ba ce da suka sani.
Tayi jawur da ita tsaf-tsaf.
Babban mamakin kambas din
data dana a kafarta suke kallo
wasu na
cewa takalmin *yan ball tasa,
wasu na cewa na faretin sojoji
ne. Mamaki ya ishe su yadda aka
yi
Hannah ta zama haka kamar
baturiya a wata guda
nan da nan, kyau na zuba duk
cikar garin da batsewarsa babu
mai kyawun Hanne da
gogewarta. Nanfa samari kowa
ya hau cewa gaskiya tawa ce
wannan, wancan na cewa na
rigaka. Kawayenta da yawa sun
kudiri niyyar suma sai sun
tuburewa Iyayensu an kaisu
makarantar
kwana irin ta Hannah don suma
su goge suyi jawur haka. Kafin
Hanne ta karasa gida labari ya
kai cikin
gidansu ance ga Hanne can
zuwa ta zama fara kal kamar
baturiya ita da wata tsohuwa.
Farin ciki ya cika Mahaifinta yayi
wuf ya fito kofar gida ya tsaya
yana murna yana jiran
karasowar Hanne (yar boko).
Budar bakin Iya Abu kuwa sai
cewa tayi watakila ciki aka yi
mata a makarantar tayi haske
don Hanne ba fara ba ce kal.
Surutai dai na hassada da bakin
ciki barkatai ta dinga yi. Hanne
na doso kofar gida ta hango
Mahaifinta sai su duk murna ta
lullubesu. Hannah ta karasa da
sauri taje ta rungumeshi kamar
yadda taga su Nusaiba suna
yiwa Mahaifansu, sai hawaye
suke ita da Mahaifinta. Iya Abu a
tsakar gida ita da *ya*yanta
babu wanda ya amsawa uwar
biyu sallamar da tayi, sai Mal.
Habu ya ce “Shigo kawai ai baza
su amsa miki ba, ya shiga ya
dauko tabarma
da sauri yazo ya shimfida mata
ta zauna a sanyaye,
cike da mamakin irin wannan
tsana da aka yiwa wannan *yar
karamar yarinya wanda ma yake
sonta an tsaneshi. Hannah taje
gaban Iya Abu ta durkusa ta
gaisheta ko ta amsa taki, ta juya
ta
gaishe da Yayyanta *ya*yan Abu
kenan suma suka mata abun
da Mahaifiyarsu tayi.
Uwar biyu ta rike baki ta ce “Oh
ikon Allah, bayin Allah me yayi
zafi Hannah nawa take? Don
Allah
kuyi mata *yar fara’a mana ko
taji dan sanyi yanzu ko dokinta
ba kwayi kusan wata biyu bata
nan. Ai ko dan
darajar idona bakuwa kwa raga
mata har in tafi.
Suka yo caaa akan Uwar biyu,
uwar nayi *ya*yan nayi, ta mike
tsaye ta juya ta kalli Hannah
wacce ta
kame a jikin katanga tana
makyarkyata hawaye ne
yake zuba daga idanuwanta
tasan yau duka da zagi Allah ne
kadai Yasan iyakarsa da zata
sha.
Hawaye ya kecewa Uwar biyu ta
ce “Hannah yi hakuri wuya bata
kisa ko anki ko anso gidan
Ubanki ne duk inda kika je sai
kinzo gidan dole. Iya Abu ta ce
“Gidan Uban nata kuma
zamansa ya
gagareta idan na so ba. Malam
Habu shima yayi jigum ya kasa
magana tashin hankali ya ishe
shi
saboda yana tausayin Hannah,
yasan wahala zasu
ci gaba da linka mata ganin
Allah ya rufa mata asiri
tayi kyau, Uwar biyu ta fita
Malam Habu ya bita Hannah ma
ta bisu da sauri, Uwar biyu tasa
gefen
gyale ta sharbe hawaye ta ce
“Allah Yana nan, Malam ni *yar
aiki ce Malam Haisam Malamin
daya
karbeta a hannunka din nan.
Malam Habu ya katseta ya ce “Eh
na gane kiyi mana godiya da
kyau da kyau na gode madalla.
Tasa hannu ta dauko kudi mai
dan kauru ta bawa Malam Habu ta
ce
“Malam Haisam ya ce a baja
nasa ne na kashin kansa bana
makarantar Hannah ba ce. Da
zarar
hutu ya kare ita da kanta zata zo
ta dauketa, Malam Habu yayi
shiru yana sauraron uwar biyu
sai
girgiza kai yake kawai yana
mamakin wannan tara
ta arziki da Haisam yake yi musu
yana fadin ashe akwai masu
halin Sahabbai a duniyar nan
masu kyautar da dukiyarsu ga
mabukata irin Haisam.
Malam Habu ya dago ya kalli
uwar biyu ya ce “Kema
daya aikoki kika rike amana
Allah Ya saka miki da gidan
Aljannah dashi da yake mana
hidima Allah Ya
bashi mai yi masa haka,
munji dadi mun gode. Ni ina
nan wata rana na gaza barci ina
tunanin ko yaya *yar Baba, ko
me take ci a makaranta na barta
babu abinci? Ashe tana can ta
fini koshi, kalli
yadda tayi bul-bul ah
Alhamdulillahi.
Mai gari ya
aiko da garin kwaki kwano biyu
da suga rabin kwano sai kudin
motar zuwa Kazaure ya ce in kai
mata makaranta, wallahi matan
nan tawa data ga garin kwakin
nan da kudin mota sai ta sulalo
ina
bacci ta sace kudin motar ta
bula ledar garin ya dinga
tsiyayewa a kasa, da naje na
shaidawa mai
gari ba kiga cin mutunci da suka
yimin ba wai daman talauci ya
ishe ni na sami kayan gwamnati
ina wadaka dashi. Su babu
ruwansu *ya dai *yata ce in
barta yunwar ta kasheta.
Nayi kuka da hawaye nazo na
zauna na hakura sai addu’a na
dinga aika mata daga nan Allah
Ya
hadata da nagari mai bata. Allah
Ya amsa addu’ata, gashi bamu
girbe amfanin gona ba shine
yasa ko
taro nakan tashi babu a
aljihuna. Uwar biyu ta ce “Kaico
haka kake rayuwa Malam?
To ni dai shawarar dazan baka
dan Allah duk rintsi duk wuya ka
toshe
kunnanka kome za’ace game da
karatun Hannah karka cire ta
daga makaranta. Babu sisinka,
ba kai
zaka dauke ta ba, ba kai zaka
mayar da ita ba, nice zan dinga
kawota ina zuwa ina daukarta
kai dai ka bata izini kawai karka
hanata saboda karatu kawai
zai farfado da Hannah ta sami
*yancinta da jin dadin
rayuwarta nan gaba, amma
azabar tayi yawa.
Malam Habu ya ce “Da gudu
kuwa zan barta, aini ba dan
za’ace na siyar da *yata ba, ko
ace na kaita birni tana iskanci
da ko hutu ma sai ince ta dinga
yi a gidanki. Amma yanzu kowa
yaji a redio an yiwa
*yan makaranta hutu ba aga
Hanne ba za’a fara titsiyeni da
tambaya a fada. Uwar biyu ta ce
“Allah Ya kyauta ni zan koma, ga
sabulai can a jakarta da
mayukan shafawa Malam
Haisam ya ce don Allah a dinga
barta tana wanka da wanki da
kitso ba
kamar yadda aka kawota ba,
kazan-kazan ina amfanin
kazanta? Uwar biyu ta fara
tafiya bayan
sunyi sallama da Malam Habu
yana godiya, Hannah ta rushe da
kuka ta bi uwar biyu da gudu ta
rungumeta su duka kuka suke
rusawa Hannah ta ce.
Uwar biyu karki tafi ki barni
wuya nake sha ni zan biki
gidanki in zauna acan. Daya
daga cikin
*ya*yan Iya Abu Musbahu shine
ya fito daga cikin gidan a guje
Uwarsa ta turo shi yazo ya
dauko mata
Hannah da yake suna labe a
zaure suna jin duk maganganun
da suke yi. Ya dauko ta aka ya
mikata
cikin gida ya rufo kofar zaure
sai kukan Hannah ne
yake tashi ya cika unguwar kai
kace rai ake zare mata saboda
irin karar kukan daga ji ba
karamin
bugu ake yi mata ba.
Malam Habu nata kokarin bude
kofar yana bugun kofar kamar
zai balla yana so yaje ya ceci
*yarsa.
Uwar biyu ta juya ta tafi tana
rusa kuka kamar ranta zai fita,
tsananin bakin ciki da tausayin
Hannah ne
ya cika mata zuciya. Tana jin
samarin dake zazzaune akan
benci suna jiyo kukan Hannah
suke
cewa “To baiwar iya Abu tazo
har an fara nada mata duka kai
wannan yarinya Allah dai Ya
rayata
kar itama wuya ta kasheta
kamar yadda ta kashe uwarta
saboda azabtarwar Iya Abu.
Malam Habu Imamu Mahaifin
Hannah haifaffan garin Babban
mutum ne Iyaye da Kakanninsa
su
suka kafa garin. Aurensa na
farko ya auri *yar uwarsa
Salmai. Allah bai basu haihuwa
ba har
tsawon shekara goma sha biyar
suna tare. Salmai da kanta ta
ringa rokar mai gidanta daya
kara aure
ko Allah Zai bashi haihuwa yaki
fur ya ce bazai yi ba, bashi da
sha’awar aure saboda baya son
tashin
hankali kasancewar sa mutum
ne mai hakuri da gudun tashin
hankali ko yaya yake.
Allah Ya bashi dan abun
hannunsa rufin asiri dai, yana
daya daga cikin masu tashen
kudi a wannan
gari nasu a lokacin. Abu wata
yarinya ce da take kawo masa
man gyada daga wani dan
karamin
kauye da yake kusa da garin
duk ranar kasuwa suna siyan
man gyada har gida take kawo
musu.
Cikin siyasa da dubaru Salmai ta
hada auren Malam Habu da Abu
aka sha biki aka kawo amarya,
da
zuciya daya Salmai take zaune
da Abu komai nata gida biyu
take rabawa ta bawa amarya, a
kullum
tunanin yau me zata bawa
amaryarta take yi kawai don
Abu ta saki jiki ta zauna ko Allah
Zai sa rabon haihuwar a jikinta
yake. Ai kuwa kafin shekara ta
zagayo Abu ta sami ciki. Tunda
ta sami ciki ita da *yan uwanta
suka tsani Salmai wai bakin ciki
take yi don Abu zata haihu ita
bata taba haihuwa ba zagi
rashin kunya kala-kala. Ta haihu
da namiji aka saka masa suna
Labaran, kafin ta yayeshi ta sake
samun ciki ta haifi Iliyasu. Nan
dai haihuwa ta bude
ta sake haifar Musbahu sai
kuma Ramatu. Rashin mutunci
yana ci gaba saida ta kai ko
ruwan gidan sai
a boye Salmai take sha kullum
tana daki zaman tsakar gida ya
gagreta. Abu da *ya*yanta su
isheta da rashin kunya. Abun
yazo ya zarce kan Salmai har shi
mai gidan Malam Habu yi masa
suke. Baro-
baro Abu take zaginsa ta cakumi
kwalarsa, tayi masa fata-fata da
dukiyarsa ya tsiyace. Duk da
haka
Salmai ta ci gaba da zaman
hakuri da Malam Habu da
kishiyarya. Amma dole da asirai
Iya Abu tayi waje da Salmai ba
don *yan uwanta sun dage da yi
mata addu’a ba da hauka zata yi
tuburan, don niyyar Abu ta
haukatar da ita, dan dole Malam
Habu ya rabu da ita. Haka Malam
Habu ya kasance abun tausayi
ya zama mijin tace sai yadda tayi
dashi idan taga dama ko abinci
ta dafa baza ta bashi ba, ko zata
bashi sai sun gama dibar yadda
zai ishe su sannan tace yaje
tukunya ya diba ya hada da
kanzo ya ci, bai kai matsayin da
zata zuba ta kai
masa ba. Bayan ta haifi Ramatu
sai ta haifi furera ta haifi *yar
Autarta Mahajana wacce ko
arba’in bata
yi ba da haihuwa a yanzu.
Wata rana Allah Ya kai Malam
Habu kasuwar wani gari mai
suna Dashi a cikin kasar Niger
ya gamu da
Habi *yar buzuwa Mahaifiyar
Hannah. Habi yarinya ce *yar
karama a lokacin shekarunta bai
wuce shekara goma sha uku ba.
kamar wasa soyayya ta
kullu Malam Habu ya aurota ya
kawota gidansu.sai Tururuwar
zuwa kallon Habi akeyi sabida
kyawunta gashinta har gadon
bayanta fara ce kyal mai kyawun
gaske. Nan fa iya Abu ta ce
dawa Allah
Ya hadani in ba da Habi ba, ta
fara azabtar da Habi.
Malam Habu kuma bai isa ba ya
hana. A haka Habi ta sami ciki,
ga ciki tsoho ga debo ruwa,
Yo ciyawa a gona karyo karan
da za’a dafa abinci sussika ita
take yi. A garin kowa tausayin
Habi yake
tayi. Wanke-wanke shara ga
duka da take sha a wajen iya
abu, solobiyun mijin nata bai isa
ya hanata
sai dai ya zauna yana taya ta
kuka abinka da abun asiri ko tak
an hana shi ya ce balle ya
tsawatar ya hana abunda take
yiwa matarsa. Cikin Habi ya isa
haihuwa ta haifi diya mace mai
kyau kamar
uwarta. Aka saka mata suna
Hannatu. Fur Iya abu
ta hana Malam Habu ya kai Habi
garinsu tayi wankan jego ya je
ya sanar musu ma cewar ta
haihu ta hana shi. Haka ta bar
Habi da danyen jego haihuwar
fari bata san yaya ake ba, badan
wata
makwabciyarsu ba data tsaya
sukayi fadi in fada da iya
Abu ba tace dole sai ta dinga kula
da Habi da haka zata barta a
daki ta rufe ita da jaririyar.!! Tun
kafin
tayi arba’ain ta zubar da
wankan, iya Abu ta fara sa Habi
aiki har su debo ruwa a rafi,
haka har Hanne ta isa yaye aka
yayeta, kwanci tashi *yan uwan
Habi dai suka ji shirun yayi yawa
babu Habi babu
labarinta har shekaru uku suka
yo kungiya suka dira a garin
Babban-mutum, tun daga kan
hanya
aka shaida musu cewar Habi ta
haihu har ta yaye *yarta sannan
yanzu a kwance take kusan
wata biyu bata da lafiya saboda
tsananin azabar da take sha a
wajen kishiyarta.
Suna zuwa gidan suka iske Habi
sai kashi a kwance akan katifa
ga *yarta itama a rame kurket a
gabanta, suka sha kuka abun
tausayi babu mai zaman jinya a
wajenta, ko awa nawa Malam
Habu zaiyi baya gida sai sanda
ya dawo zai tasheta ya bata
abinci da ruwa ita da *yar ta
babu mai basu.
Bayan zuwan dangin Habi da
kwana uku ta ce ga garinku nan
Allah Yayi mata rasuwa, sun sha
kuka kamar ransu zai fita, haka
Malam Habu yayi kuka yayi dana
sanin auro *yar mutanen da yayi
ya kawota, matarsa ta zama
sanadiyyar ajalinta. Iya Abu
kuwa da *ya*yanta suna ji a
daki ko su fito ma balle ma suyi
kukan mutuwa, ranar sadakar
uku ita
da *ya*yanta suka ci kwalliya
suna shirin fita biki,
wannan rashin Imani na iya Abu
yayi yawa, *yan uwan Habi duk
suna kallonta, suna nan sai
bayan anyi sadakar bakwai suka
shirya kayansu zasu koma
garinsu suka ce da Malam Habu
zasu tafi da Hannah. Nan da nan
ya amsa musu ya amince don
yasan idan an barta ma wahala
zata sha kamar
yadda Mahaifiyarta tasha, sai
kuwa iya Abu tayi tsallen albarka
ta ce ai babu wanda ya isa ya
tafi da Hanne wato so suke su
tafi da *yar Habu don ya dinga
zuwa garinsu ganin *yarsa daga
nan a lika masa kanwarta ya
aura ko? Dama suna ciki da ita
ai kuwa suka ci damara aka hau
masifa da iya Abu suka kuwa
taru su biyar din suka yi mata
dukan kawo wuka suka farfasa
mata baki har da cire mata
hakorin gaba guda daya, dakyar
da sudin goshi makwabta suka
karbeta. Suka ce sunma fasa
tafiya
da Hannen tama daina tunanin
suna so su sake bawa Malam
Habu *yarsu ko da kuwa
danginsu
kakaf zasu rasa miji baza su
sake bawa Malam Habu *ya ba,
mai gari yana basu hakuri da
sauran *yan gari dakyar dai aka
raba wannan fadan suka bar
Malam Habu rike da Hannah a
hannunsa da *yan
kayanta a leda yana roko su
karbeta suka ki.
Iya Abu kuwa daki *ya*yanta
suka shiga da ita tayi lambar
kwance baki ya hau ya suntuma
tana jinya.
Tun daga wannan lokaci
Hannah yarinya *yar shekara
biyu ta fara gamuwa da wahalar
rayuwa
har rana irin ta yau. Hannah ta
dandana azabar Iya Abu,