GIDAN AURE CHAPTER 1 ZAHRATEEY

GIDAN AURE COMPLETE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

*Gidan Ahmad*

Sabon zanin gadon na shimfida saboda wanda yake kai ya 6aci, ina gamawa ya fito daga kewaye yana goge jikin shi, kar6an abin gogewan nayi na goge mishi jikin sannan na taya shi saka kaya, muna gamawa na fesa mishi turare kad’an sannan na raka shi zuwa d’akin sa na masu gadi “Darling zanyi kewarka sosai, ka kulamin da kan ka sai Allah ya tashe mu lafiya” amin yace tare da sumbata ta nima na mayar mishi da martani kafin na koma cikin gida.

STORY CONTINUES BELOW

Wanka na shiga, ina fitowa na goge jikina, na fesa turare sannan na saka kaya, kwanciya nayi ina tunanin me gadina Samir, kyakyawan gaye son kowa kin wanda ta rasa, ga son gayu ga iya daukan wanka, tun ban fara son shi ba har na fara a halin yanzu, namiji ne meji da jini a jiki ga iya sarrafa mace, ban ta6a jin dadin tarayya da mijina ba kamar yadda nakeji da Samir, karewa ni ban ma san dadin aure ba balle in san dadin raya sunna sai a kan Samir wanda ya kasance me gadin gidana. Duk wata mace me karfin sha’awa irin nawa Samir shine dai dai da ita domin baya barin mace sai ya tabbatar ta gamsu da shi dari bisa dari, sai ya san kin samu natsuwa kafin ya barki ki huta.

Ina cikin tunanin gwarzo na me sanyaya zuciyata da kawar min da kishin ruwata a duk sanda na bukata, naji horn wanda ya nuna alamun cewa a gidana ne, tashi nayi na leka na hango shi yana bude musu gate, mijina ne da mukarrabansa sai wani tafiya yakeyi yana bubbudawa kamar dai shi yake da garin baki dayanta, kanshi na kara girma idan masu gadin shi suka durkusar da kan su a gareshi, komawa nayi na kwanta ina jan tsaki, shekara guda da wata biyar kenan rabona da shi wai shi yana aikin soja, ni mantawa ma nakeyi dashi a matsayin mijina, a da ina kiran shi amma a yanzu nima na share lamarinsa ne, idan ya so ya nemeni idan ya so kar ya nema duk daya ne a gurina domin na riga na samu madadinsa ko ma ince wanda yafi shi, ina jinshi sanda ya shigo ya bude kofar dakinsa ya shiga ya rufe, kamar dai yadda ya saba hakan ne ya faru, idan ba dai nashi bukatar ne ya ciyoshi ba mantawa yakeyi dani da lamarina, rayuwar daya za6a mana kenan nida shi shege ka fasa.

_________________________

*Gidan Jamilu*

Yana shiga gidan ya taras dashi kaca kaca kamar an kwato daga bakin kura, gida ba juji ba balle kuma daji, gidan dai kamar anyi yaki a cikinsa, ko ina datti amma matar gidan taci kwalliya kamar zataje party, sai tashin kamshi takeyi mace har mace son kowa kin me hassada, komai yaji a jikinta sai dai babu hali me kyau, kazanta dai kamar a kanta aka sauke shi Indai na cikin gidane, amma idan da zaka gan ta a hanya zakayi mamaki idan ka shiga gidanta dan batayi kalar kazamai ba, duk inda ta wuce sai ta bar kamshin ta.

D’aki ya shiga ya canja kaya ya fito ya gyara gidan yasa turaren tsinke sannan ya yi wanka bayan ya fito ya dafa indomie ya zauna yaci duk kuma tana zaune ta harde kafa a kujera tana kallon African magic sai dariya takeyi tana kara turo dankwali gaba tare da shewa alamun duniyar tayi mata dadi.

“Jawahir haka rayuwar mu zatayi ta zama cikin kazanta babu sauyi? Ni ba zama nakeyi ba balle kice duk muna zaman kashe kaya a gida, ban fa da hutu kwata kwata ni ban san ranar da zaki shiryu ki gane gaskiya ba, kullun ni kenan ina dawo wa daga aikin office zan kama aikin gida kamar wani house boy, yaran nawa guda biyu ma kin kasa rikesu kin kai su gidan mu dan karawa mahaifiyata wahala, sa’a kikaci kin samu sirikar kwarai wallahi amma duk da haka baki godewa Allah ba, ya miki ni’ima da dama ya baki iyaye na gari ya baki miji nagari ba yabon kai ba sirika ta gari ga y’ay’a ya baki to me kike so kuma a duniya? rufin asiri dai dai gwargwado kina cikin shi babu abin da kika nema kika rasa, baki da aiki sai yawon gidan biki da suna kina canja kaya kina nuna adonki a gari, amma gidanki kamar bola babu gyara balle kulawa bani ba ba yaran ki ba ba gidanki ba, wallahi ki guji ranar da zaki kaina bango domin zan yanke hukuncin da ba zai ta6a miki dadi ba, wai nayi aure amma ban san ma dadin auren ba kwata kwata, mutane suna aure suna murmurewa ni ina tsotsewa” ya fada yana barin falon ita kuma ta gyara kwanciya tare da binsa da harara.

_________________________

*Gidan Faruk*

Zaune take akan abin salla tayi zurfi a tunani, karan bude kofar da taji yasa ta kalli agogo, karfe biyu na dare saurin share hawayenta tayi, tanaji ya fake machine din shi ya shigo bata kula shi ba dan ta san duka zata sha, a halin yanzu da take da karamin ciki bata bukatar abin da zai ta6a lafiyar cikinta, abu ne wanda ta dade tana rakon Allah ya bata rayayyu a wannan karan ba zatayi gigin shiga lamarinsa ba balle ya kashe mata y’ay’a kamar yadda ya saba, itace da asara bashi ba dan shi yana da wasu yaran na matarsa ta farko wacce ta rasu. nad’e sallayan tayi tare dayin ajiyar zuciya ganin cewa bai kulata ba, d’aki ya shiga ya sheka mata amai tana ji taki kulawa sai da taji shuru alamun ya yi barci sannan ta shiga ta gyara gurin ta fesa turare, filo ta dauko tare da bargon ta fito falo “munafuka kin gama munafurcin kenan, Allah ya wadaran Old Man daya auro mana ke wallahi” wata yarinya ta fad’a tana wani harare harare “ke dai bari gata ba kyau ba ga guntanci ya mata yawa ga baki kamar an shafa mata gawayi ni wallahi Old Man ya mugun kwafsa mana, sai da na bashi shawaran auro kanwar Momcy Anty Wasila amma yace a’a gashi ai ya kwaso mana annabo” d’ayar yarinyar ta fada tana tunkude ta, ita dai shuru tayi ta samu guri tayi shimfidinta ta kwanta, bata da lokacin kulasu domin yaran bala’i ne yanzu zasu kashe mata aure”.

Washe gari da safe haka suka sa babansu ya gaba akan lailai sai ya auro Anty Wasila idan ba haka ba zasu bar mishi gidan shi tunda matarshi ta mallakeshi, ganin cewa da gaske suke shiyasa ya yi saurin amincewa da zancen auren amma ba dan yaso ya kara Auren ba, cikin lokaci kankani aka gama maganar auren ba tare da jinkiri ba saboda yaran sun matsa, tun daga ranar suka tasa Hamida a gaba da mugun maganganu su ala dole kanwar uwarsu zata dawo cikin gidan da zama zasu wataya suyi abin da ransu yake so.

_________________________

*Gidan Saminu*

Cikin sand’a ya shigo gidan, ta bayan taga ya zagaya ya jefa mata ledan sannan ya dawo ya bi ta kofan ya shiga, “kai Saminu ina zuwa haka baka shigo ka gaida uwar data haifeka ba? Kajimin yaro da kinibibi wato matarka tafi uwarka kenan ko, lailai ina daf da sawa ka sauwake mata domin na gaji da wannan nuna fifiko da akemin a cikin gidan nan” ta fada tana matsar kwalla.

Ganin haka yasa hankalinsa ya tashi ya fara bata hakuri, karshe dai sai da dare ya raba sannan ta barshi ya koma 6angarensa, yana zuwa ya same ta a zaune ta zuba tagumi, ta6a ta ya yi yana cewa “Faiza kiyi hakuri dan Allah” murmushin yake tayi tana cewa “babu komai mijina, meye kuma abin bada hakuri ai ni bakamin laifi ba kuma ai mahaifiyarka mahaifiyata ce idan da mutunci, dan haka dan Allah karka kara bani hakuri a kan hakan” hannunta ya kama ya sumbata sannan yace “ya naga bakici naman ba kin ajiye shi yadda na kawo miki?” Daukowa tayi ta kunce sannan tace “kayi hakuri ai bazan iya ci ba sai kana kusa dani”.

Cikin sauri ta fado dakin ta dauke ledan naman tana cewa ” munafukai wato ashe abin da kukeyi kenan a bayan idona, yanzu dan naman dani ya dace ka kawo wa shine ita ka kawo mata ni kuma ko oho ko? Wato na haifa mata ban haifa wa kaina ba, wallahi ka fita a idona in rufe kuma daga yau sai yau kar in sake ganin ka sayo abu baka kaimin na gani ba idan hakan ya faru bazan ta6a yafe maka ba shanyayye kawai” ta fada tana fita daga dakin, sai masifa takeyi. Shuru sukayi kowa da abin da yake sakawa a ransa.

_________________________

*Gidan Hafiz*

“ke Zaliha, wato ba zaki gama girki da wuri ki kawo mata ba ko? Dan bakin ciki cikin nawa ne kike so ya 6are ko me? To wallahi ki gaggauta kwashe abincin nan ki kai mata kafin raina ya 6aci dan idan har raina ya 6aci ya sai dai ki kwana a gidanku, karuwa kawai yar iska wama ya sani ko Adam din ba d’ana bane kawai kika lakamin sharri aka sa na auro ki a dole!”.

Yana shiga ciki ta fashe da kuka yana nadamar rayuwarya da biyewa son zuciya da tayi har ya kai ta ga dana sani, gashi saboda ta faranta mishi suka fara da soyayyar shan minti har aka kai ga ciki bayan ta haihu yaro ya fito da kamansa shine iyayensa masu karamci da hangen nesa suka ce dole sai ya aureta, tunda ya aureta walakanin yau daban na gobe daban kuma tun haihuwarta a waje dashi bata sake haihuwa ba, gashi har ya karo aure matar ta haifa mishi yara biyu ga cikin na uku tana fama.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE