GIDAN AURE CHAPTER 3 ZAHRATEEY
GIDAN AURE CHAPTER 3 ZAHRATEEY
Gidan Ahmad*
+
Cikin barci naji mutum yana ta6ani, ba dai zan ce 6arowa bane a gidan Soja, bude idona nayi a hankali naga ashe me gidanne, haushi ne ya kamani kamar in mishi dukan tsiya haka nakeji a cikin raina, karshe dai barinshi nayi ya yi kidin shi ya yi rawarsa, bayan ya fita a dakin na tashi nayi kukan bakin ciki sannan nayi wanka na dawo na zauna ina ajiyar zuciya a kai a kai, ban kwanta ba har aka kira sallan asuba sai da nayi salla sannan na kwanta.
Bani na tashi ba sai wajen karfe goma na rana, wanka na sake yi sannan na fita zuwa kitchen na soya kwai na had’a shayi da biredi na fito, a bakin kofan falo muka hadu ina ganinshi yana kokarin bararmin da shayi nayi saurin yin gefe na shige falon ina jan tsaki, abin da Ahmad ya tsana kenan amma dan in bakanta mishi shiyasa nayi kowa ma ya zauna da 6acin rai, har na gama karyawa na tashi bai fito daga kitchen din ba, sai bayan kusan mintina goma ya fito d’auke da tray, plate cike tam da indomie da kwai sai shayi a gefe sai tiririn zafi yakeyi, sai da ya zauna sannan na tashi na shige kitchen din dan wanke kofi da plate din dana 6ata, na samu har ya wanke tukunyan da ya yi amfani dashi komai tsaf tsaf, dadina da Ahmad akwai tsafta sosai ba kazamin namiji bane, bayan na gama wankewa na fito na wuce falon sama na kunna TV na cigaba da kallon maimaicin Frozen da akayi jiya da dare.
Ina zaune ya shigo yace min in shirya zamuje Kano gidansu, ban amsa shi ba na tashi na wuce daki na shirya tare da daukan kaya uku dan bama wuce wadannan kwanakin, karamin trolley na dauka na saka duk abin bukata aciki sannan na rufe kofan dakina na fito falo na kashe kayan kallon kafin na sauka kasa, kitchen na shiga na kashe gas da duk wani kayan wuta sannan na dawo falo nayi zaman jiranshi, ban dade da zama ba ya fito d’auke da karamar jaka irin na yan makaranta, a tare muka fita ya rufe kofan gidan sannan muka shige mota direban shi ya kaimu tashar jirgin sama.
Ko da muka isa kaninshi Fahad ne ya zo ya d’auke mu, daga gidan su zuwa filin jirgi akwai tafiya, ga kuma hold up da ya yi yawa hakan yasa sai da mukayi awa gida a hanya kafin muka isa gidan. Duk yan matan gidan suna nan har da samari. mahaifiyarsu ce kawai mata a gidan amma Allah ya albarkace su da tarin y’ay’a har goma sha biyar uku sun rasu saura sha biyu, shida sunyi aure saura shida, mata uku maza uku mazan duk sun gama karatu suna aiki matan kuma basu gama karatu ba.
STORY CONTINUES BELOW

Tarba me kyau muka samu dama Hajiya mace ce me kirki sosai da son jama’a haka zalika duk yaranta suma haka suke akwai son junansu, sai da mukayi salla sannan aka hadu akaci abinci, bayan mun gama muka shiga hira har da Ahmad kamar dai babu wani matsala a tsakanin mu.
_________________________
*Gidan Salmanu*
Yau ta tashi da ciwon kai da ciwon mara me tsanani wanda yasa ta kasa fita aiki, shima Salmanun daker ya fita daga gidan saboda damuwan da yake ciki na ganin halin da matarsa take ciki, amma Mama tayi ruwa tayi tsaki sai da ta tursasa shi ya fita ba dan ya so ba kuma tace idan har ya kuskura ya dawo da wuri zai gamu da ita tunda ba zai iya tsayawa ya kula da aikin shi ba sai aikin matarsa saboda ta shanye shi.
Bayan fitarshi haka tasa Faiza a gaba sai da ta tashi ta dafa mata shinkafa da wake sannan ta soya mata manja, Allah yaso ma tana da dakekken yaji da duk sai tayi aikin daka, daker ta iya gamawa ta had’a ta kai mata daki, ko da ta koma daki wani sabon zazza6inne ya rufeta karshe ta fito tayi ta hararwa anan ma bata tsira ba haka Mama tayi ta balai wai kawai dan bata son taci abinci shine zata zo tayi mata kazanta, ta inda take shiga batanan take fita ba haka har sai da ta ga Faiza tayi kuka sannan ta barta ta koma daki.
Ko da Salmanu ya dawo jikinta ya yi tsanani sai da aka dangana da asibiti, Mama kuwa ko kallo basu isheta ba har sukaje suka dawo bata kulasu ba sai ma mita da ta yi tayi, a gabanta aka dorawa Faiza ruwa amma sai tace wai kawai son a jawa danta asarar kudinsa shine kawai ba wai wani ciwon arziki ba, mutum sai dai yaci yaje kewaye ciki ya kasa rike d’a maganganu dai iri iri haka tayi ta ya6awa haka Faiza ta rufe idonta ruf kamar tana barci taki nuna ma taji balle taji dadin cewa tana mata kallon banza.
_________________________
*Gidan Jamilu*
Ba laifi yau ya samu gidan fes fes har kamshi yakeyi ga kuma abinci a jere a sama center table tunda ya ga haka ya san tabbas akwai abin da take bukata daki ya wuce ya yi wanka sannan ya fito falo, jollof rice tayi wanda yaji kifi sai kuma lemon kwakwa a gefe, hankali kwanci ya kwashi abinci wanda ya dade bai ci ba a gidan shi, girki dai dai-dai gwargwado ta iya babu kushewa amma tun bayan wata guda da aurensu ta fara fitowa da munanan halayyarta na kazanta da kinyi girki, idan kuma har tayi girki tabbas akwai abin da take nema a gurin shi, shimfida ne dai ba zai ce komai a kai ba dan dai-dai gwargwado yana samun natsuwa a gurinta ba shida matsala da hakan.
Bayan ya gama cin abinci ya zauna dan hutawa, fitowa tayi tana taku daya daya yadda ta saba sai zuba kamshi takeyi kamar a gidansu ake kera turaren duniya, yau abin har da gaisuwa sa6anin kullun da sai dai tace ashe ka dawo, bayan ya amsa ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke su tas sannan ta fito falon, zama tayi a kusa dashi ta sakala hannunta a cikin nashi sannan tace “bikin Hadiza fa ya kusa ina ga nan da sati guda ne kawai ya rage, kuma anko kala uku aka fitar dukan su dubu goma sai kudin dinki duka duka dai dubu hamsin da kudin dinki da kudin mota da kudin hidimar biki dana dan abin da zan bawa amarya” kallon bata da hankali ya yi mata kafin ya juya ya cigaba da kallon da yakeyi, ita bata ma lura da kallon daya mata ba ta cigaba da zuba kamar ruwan famfo, sai da aka kira sallan magriba sannan yace mata bari idan ya dawo sai suyi magana.
Farin ciki ne ya kamata ganin cewa zata samu biyan bukata, kasancewa tana fashin salla sai ta wuce kitchen ta fara had’a mishi cake da semosa, ko wanne pieces dari tayi bayan ta gama taje tayi wanka ta zauna a falo zaman jiranshi, shi kuma har bayan isha’i yana can majalisa tare da yan unguwa suna hira, bai dawo gida ba sai wajen karfe sha biyun dare lokacin barci ya gama awun gaba da ita, kitchen ya shiga ya samu tayi cake da semosa, dama ya yi tsammanin haka dan duk yana cikin bribe din ta.
_________________________
*Gidan Hafiz*
Kamar kullun yau ma sai da ta had’a mata bala’i a gurin mijinsu saboda tace tayi mata alale ita kuma tace ba zata iyayi da safen Allah ba domin zata makara zuwa gurin aiki, Allah ya so ta harta fita basu sani ba, ta san idan ta dawo akwai damuwa amma gwara dai taje aiki ta dawo sai ayi koma meye ne.
Ko da ta tashi a aiki sai da ta fara zuwa gidan Faiza ta dubata sannan ta bi gidan Nafisa itama ta dubata domin duk basu da lafiya basuje aiki ba, hakan yasa ta kara makara bata isa gida da wuri ba har sai awa guda bayan tashinta daga aiki, tana zuwa ta samu Hafiz a bakin kofa yana jiranta, tare suka shiga gida ya fara mata bala’i akan abin da tayi wa matarsa da safe, bata kula shi ba ta wuce daki ta kulle dan ta san zai iya dukanta idan ta tsaya, zage zage ya hau yi ta uwa ta uba har sai da ya gaji ya bari matarsa ta dora daga inda ya tsaya, duk tana jinsu amma tayi shurunta har barci ya kwasheta.
Bata fito ba sai bayan daya fita a gidan kusan sallan magriba sannan ta fito ta dafa dafadukan taliya da bushashen kifi, harta gama ta shiga wanka ta fito ta dauki nasu abincin bayan tayi alwala ita da yaronta suka shige cikin daki ta rufe cikin ikon Allah bai dawo ba matarsa kuma ta shiga makota, ko da suka dawo sunji haushin ganin harta gama komai ta rufe dakinta a haka suka yi kwanan bakin ciki domin basu samu damar kuntata mata ba.
_________________________
*Gidan Faruk*
Har tayi wanka ta yi shirin fita jiri ya sake dibanta ta samu guri ta zauna, wayarta ta dauka ta kira layin shugaba ta sanar mata da cewan ba zata iya shigowa ba, sanin cewa bata da lafiya jiya kuma ita ba gwanar fashin aikin bane yasa ta bata sati guda ta huta a gida, sosai taji dadin hakan domin tana bukatan hutu sosai.
Faruk ma yau bai fita aiki ba saboda shirye shiryen aurensa da yakeyi ya tsaya duba inda za’a gyarawa amarya, sosai yaransa suke farin cikin wannan aure shi kuma yake bakin cikin auren dan bashida niyyar zama da mata biyu uwa uba kuma baya son yar uwar matar shi da zai aura, kawai dai yaranshi yake dubawa da ba zaiyi wannan auren ba.
Yana gidan har Zaliha tazo ta tafi sai a lokacin ya san cewa Nafi tana gida bataje aiki ba, sai ma a lokacin ya san da gaske bata da lafiya dan ya yi tunanin kawai wani abin take kokarin hada wa dan ta ga zai yi sabon aure, duk da ya danji tausayinta amma haka yasa tayi musu abincin rana shi da yaranshi suka kwashi girki suka barta da wanke kwanoni.Satinta guda a gida ta samu lafiya, a ranar da zata koma aiki a ranar aka daura auren mijinta da yar uwar marigayiya matarsa. Abin ya mata ciwon amma kawai ta share dan karta jawo wa kanta bala’i a gurin me gida.
+
Bayan kawayenta kuma aminanta guda hudu babu wacce kuma ta san cewa mijinta zai kara aure. Yau da wuri ma ta fita a gidan saboda masu zuwa kawo wasu kayan amarya. Yaran kuwa tun da aka fara hidimar biki suka tattara suka koma gidan kakanninsu.
Tana isa asibiti ta samu Mardiyya sosai abin ya bata mamaki dan rabon ta da zuwa asibiti ta dan kwana biyu. Bayan ta kammala duk abin da zatayi ta dawo cikinsu ta zauna “manya manya ganinki sai dai a vedio call” ta fada duk duka kwashe da dariya, “to ya za’ayi ni kam ba zan iya wannan aikin wahalar ba jikina na bukatan hutu” Mardiyya ta fada tana tsotsan minti.
“Ni duk wallahi kawai dauriya nakeyi amma na rasa wani hali zuciyata take ciki, yau amarya zata tare ban san ko ita dame zata shigo ba, ga na mijina ga na y’ay’ansa idan itama irinsu ce ai wallahi na kad’e da gani har ganyena” shuru sukayi suna tayata jimamin wannan al’amari, “kawai ki dage da addua kuma ki kara hakuri, kowa da kika gani cikin mu da irin matsalarsa wanda kuma duk kina sane da hakan sai dai duk jarabawa ne wata rana zai zama tarihi” Zaliha ta fada, shawarwari suka shiga bata har zuwa lokacin tashinsu.
Bayan ta koma gida ta samu har an kawo amarya gida ya cika da jama’a, kasancewar duk suna cikin 6angaren amarya sai hakan ya mata dadi tayi saurin shigewa nata 6angaren ta shige daki ta rufe.
_________________________
*Gidan Hafiz*
A gajiye ta dawo gida duk da cewa yau batayi aiki sosai ba amma dai ta sha zama duk jikinta ciwo yakeyi. Yau gidan shuru yaronta kawai ta samu a tsakar gida yana kwance yana barci, da alama ko abinci beci ba dan ko cire uniform beyi ba, kofar dakinta ta bude ta daukeshi ta kaishi ciki, sannan ta fito tayi wanka ta shiga kitchen dan dora abincin rana.
STORY CONTINUES BELOW

Harta gama babu mijin babu matarsa, hakan ya mata dadi ta diba nasu ta kai musu daki kafin ta fito ta sake daura alwala na sallan la’asar sannan ta shiga ciki, tashin shi tayi ya cire kaya tace yaje ya yi wanka, bayan ya fito sukaci abinci sukayi salla sannan ya wuce islamiya ita kuma ta shiga kitchen ta dora na dare, tuwon masara miyar wake, cikin lokaci kadan ta gama ta dauka musu nasu ta shige daki ta kwanta dan hutawa.
Dawowan yaronta daga islamiya shi ya tashe ta, tana alwala mijinta ya shigo “sannu hakima kin samu karin matsayi, har ni zan kiraki ki wani rufe kofa har ki kasa fitowa?” Ya fada yana shakota, “ni din abokin wasanki ne, ba ma ni kadai ba matar tawa sa’arki ce da zaki raina ta? Toh wallahi ki shiga hankalinki dani a cikin gidannan domin ba zan dauki wannan sabon halin da kika fara ba” ya fada yana tunkude ta har sai da ta fadi a kasa, a lokacin kuma matarsa ta shigo ga katon ciki a gaba sai wani hura hanci takeyi ” kayimin dai-dai wallahi Hafiz ai da kayi wa shegiya duka da nafi samun natsuwa” hakuri ya fara bata sannan ya jata suka shige daki.
Ita kuma Zaliha aka bar ta da kukan bakin ciki, sa’arta daya yaran duk suna ciki basu fito ba, duk da cewa ta saba shan abin kunya a gaban su amma kuma rashin fitowarsu ya mata dadi sosai.
_________________________
*Gidan Jamilu*
Washe gari da safe kafin ta fita a gidan har ya fice kuma ya kwashe komai da tayi ya saka a mota ya wuce dashi office dan ya santa sarai yanzu sai ta kwashe abinta, sosai taji haushi data farka bata ganshi ba har so tayi taki zuwa aiki.
Gidansu Jamilun taje bayan ta tashi daga gun aiki, ko da yaranta suka ganta murna suka rinka yi gwanin ban tausayi. A tunaninsu gurinsu taje ko kuma daukansu zatayi su koma gida tare sai dai akasin hakan ne ya faru domin karan Jamilu ta kai akan yaki barinta taje bikin dangi salon yaja wo mata bakin jiki da kiyayya a cikin yan uwanta. Hakuri Maman Jamilu ta bata sannan tace mata ta sa a ranta kamar har ta tafi, godiya tayi mata sannan ta shiga dakin yaran ta duba su tare da basu kwalin alewa.
Bayan ta dawo gida ta shiga had’a kayanta a akwati na tafiya biki abin dai kamar zataje tayi wata guda. Bayan ta gama hadawa tayi mishi abinci na ban hakurin hada shi da mahaifiyarsa da tayi. Tunda ya dawo yau ma ya ga haka ya san kwanan zancen, kafin ya gama tunani kiran mahaifiyarsa ya shiga wayarsa, sosai tayi mishi fada sannan ta sa shi ya bata kudin hidima a gurin biki dan ta san idan bata fada ba, ba zai bata ba cike da 6acin rai ya amsa da to tare da kara bata hakuri.
Abincin ma 6arar dashi ya yi a kasa tsa6an 6acin rai, daren ranar ko kula ta bai yi ba haka ya kwana da yunwa saboda takaici, ita kuwa harta kira masu bada anko tace a dauka mata duka kuma a dinka mata su tana nan tafe, sanin cewa bata da nauyin bashi tsaf zata biya su kudinsu shiyasa suka amsa mata.
_________________________
*Gidan Salmanu*
Sati daya tayi a gida sannan ta fara fita aiki, a cikin kwanakin da tayi a gida duk babu rana guda daya mata dadi domin Mama ta takura wa rayuwarta ta hanata sakewa duk abin da tayi zata sha zagi ko wani abu daban, duk shayewa takeyi saboda mijinta amma abin ya isheta hakanan.
Finally dai ta samu cikin wanda aka tabbatar mata dashi a gwajin da tayi a asibiti, watanni uku da yan kwanaki aka ce mata sosai abin ya bata mamaki dan bata ta6a tunanin cewa har wai ciki ne da ita ba, a tunaninta Mama zatayi farin ciki ta kuma zubda makaman masifarta da bala’inta amma sai ta ga ak’asin haka, ba laifi taji dadin samuwar cikin amma kuma ba Faiza taso ace Salmanu ya yi wa cikin ba dan har ga Allah bata kaunar Faiza, yar kawarta taso ta aura mishi amma yaki amincewa har yarinyar tayi aurenta shine shi ya kwaso mata Faiza a matsayin wacce yake so yake kauna hakan kuwa shine yafi komai bakanta mata rai.
Tana zaune a tabarma ita da kawarta Iya Kulu suna tsunar goro suna hira ita kuma Faiza tana tuka tuwo “Idan banda shegantaka menene har sai kin zauna dan zaki tuka tuwo, yaran zamani kude kam sam bakuda kawaici, idan ba rashin ta ido ba kawai saboda ki nuna mata cewa kinyi ciki shine kike zama a kujera kike tuki kina rike baya?” Tsaki Mama taja “kedai ki barta kawai Kulu kawai iya shege ne yake damunta, bata shanye Salmanu ba ai komai ma take so zatayi babu ke iya ja da ita” 6antaran goro Iya Kulu ta sakeyi “kedai kika barta wallahi Larai da ace kin tashi tsaye kin nuna musu banbancin zamani da rayuwar da mukayi ai da ba haka ba, inace nan Salmanu ya kekeshe ido kamar na zakara yace ba zai auri Tatai nawa ba? Kuma kika kyale shi saboda shine kwalli daya namiji da Allah ya baki, ai ga shi nan tun tafiya batayi nisa ba an fara nuna miki matsayinki bai kai ba” 6acin raine ya bayyana a fuskar Mama, dama abin da Iya Kulu take bukatar gani kenan “ina waye ita kuma nawa take sannan mijin nata waye shi nawa yake, har ni za’a nunawa iya shege ai mu rashin mutunci gaba muka ba shi ba baya ba, ban haifi wanda zai yi wa yar wasu bauta ba dan haka bari ya dawo ya sameni aure zai kara ko yana so ko baya so idan ba haka ba in daga mishi nono” dariya Iya Kulu ta sheke dashi “ai sai yanzu naga ainihin kawata, haka kawai kin zauna kin zuba musu ido suna abin da suka ga dama, yanzu naji batu gwara ki had’a shi kawai da Dada ko ba komai mun had’a zumuncin da muke son hadawa” (Dada yar kanwar Iya Kulu ce).
Ba tace musu komai ba har ta gama ta kwashe na Salmanu ta kai daki na Mama kuma ta ajiye musu a gaban su dan ta san tare zasuci, bayan ta gyara inda ta 6ata ta wuce daki tayi kukan bakin ciki ta more. Ko da Salmanu ya dawo haka Mama ta sa shi a gaba da zancen auren wanda dolensa ya amince dan furucinta na zata tsine mishi, ranar dai duk kwanan bakin ciki sukayi babu wanda yace wa daya uffan.
_________________________
*Gidan Ahmad*
Ko da na koma gida a falo na sameshi yana cin abinci, sannu nayi mishi sannan na wuce daki na, bayan nayi wanka na sauko kasa na dafa indomie naci sannan na dora tuwon shinkafa da miyar shuwaka, kafin a kira la’asar na gama na jera a dinning hakan kuma ya faru ne saboda abokan Ahmad da zasu zo, shi kanshi bai san cewa zanyi musu girki ba kuma nayi hakan ne dan babu wanda ya san tsakanin mu sai me gadin gidana.
Ko da na gama na dauki nawa na kai falon sama sannan nayi sallan la’asar na zauna kallo. Ko da suka shigo duk ya rasa abin da zai yi sai dai ganin abinci a dinning ya tabbatar dana fidda shi kunya, dan dama ya so ya musu karyan ban da lafiya ne, sama ya hauro ya sanar dani isowarsu ban 6ata lokaci ba na sauka muka gaisa dasu sannan na koma sama.
Washe gari ya koma gurin aikinshi, 6angare na kuma angulu ta koma gidanta na tsamiya dan dama jira nakeyi ya tafi in samu sukuni.
_________________________