GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 15

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 15
Sadda suka fito daga wurin boka Fartsi har magrib tayi. Hakan ya sa Kursiyya ta umurci Drebanta da ya kara wutar matar, ba taso dare yayi sosai basu isa ba, kasantuwar ta san mai martaba zai bukaci ganawa da ita idan dare ya yi, game da al’amarin Gimbiya Sa’adiyya da Yerima Abu Sufyan. 
Wuraren takwas da rabi suka isa masarautarsu, kai tsaye Kursiyya ta nufi sashenta, dukkanin bayin da zasu ci karo da ita sai su zube kasa suna kwasargaisuwa. Ko kallon su ba tayi bare ta amsa gaisuwarsu, basu damu ba, domin kuwa in da sabo sun saba da hakan. Wanka ta fara yi, ta yi shiga cikin wata doguwar riga ta roba mai kwanciya a jiki, sannan ta yafa kyakkyawar lapayarta, tabi duk ilahirinjikinta da kamshi. 
Motsin Hafsa taji, da sauri ta saki sassanyan murmushi, ta bude ma Hafsa hannuwanta, da 
sauri ta shige ciki suka rungumijuna. “Umma, ashe kin dawo ban sani ba.” Bayan ta sake ta ta rike hannuwanta a cikin nata, “Banjima sosai da dawowa ba. Wanka kawai nayi ko abinci banci ba.” “Sannu da dawowa to.” “Yauwa Yarlelena. Fatar dai baki sake yin wani kukan ba bayan fita ta. ” Ta saki murmushi. 
“Ai kin daukar mini alkawarin za ki cika mini burina. Don haka kukan me zan yi? Duk Yar data same ki a matsayin uwa ba taga ta kuka ba domin kuwa zaki tsaya don ganin kin aiwatar da kaf hakkokin uwa har da doriya.” Suka sake rungumarjuna. 
“Kar kiji komai idan kika fuskanci sauye-sauye tsakanina da Halimatu. Duk wani tsari ne da neman cika miki burinki. ” 
Bata gama fahimtar Kursiyya ba, amma hakan ba zai sata tambayarta ba, don ta tabbata hakan alkhairi ne a gare ta. Don haka sai ta sake murmusawa. 
Babu komai Umma. Na san ba za ki cutar dani ba.” “Wannan gaskiya ne. Kin Ci abinci dai ko?” “Banci ba Umma. Haka kawai nakejin bana son komai ma. ” Kursiyya ta gyada kai, 
“Kar muyi haka dake Hafsa. Yaya mutum zaizauna ba tare da yaci komai ba? Mazaje ki nemi Shafa ki ce ta kai miki abinci.” 
“Umma an kai mini komai tun dazu. ” 
“Oya to jeki kici. Nima zan ciyanzu. Gashi nan tun ina wanka an kawo mini. Ko kayan 
marmari ki daure ki sha, idan ba kya son abincin.” 
Hafsa ta mike, tafi tanayin guntuwar hamma hade da fadin, “Har da barci ma inaji. Bari in tafi? Umma. Mu kwana Iafiya. ” Kursiyya ta kama mata hannun dama, “Ki tabbatar fa kin ci wani abu kafin ki kwanta.” 
To kawai Hafsa tace da ita sannan ta tafi. lta kuwa Kursiyya kankana da abarba ta sha 
sosai, sannan taji shigowar Zabbau. “Ranki shi dade, mai martaba na son ganin ki.” Murmusa idanuwa ta yi hade da tabe baki. 
“Dama na sani ai. Jeki ce da yan aiken ina zuwa. Sai na fara biyawa ta dakin matsiyaciyar 
can sannan zanje. ” 
Abin da ya kamata ke nan Fulani. Bakar mayya, aikarshenta ya kusa zuwa. Mu samu mu 
yar da kwallon mangora ko ma huta da kuda.” “Kudaje zaki ce ba kuda ba.” 
Kursiyya ta fada hade da sakin dariya. Zabbau ta mike, ta sanar da Khalili sakon Kursiyya, cewa tana zuwa. 
Sake feshe jikinta da kamshi ta yi, tajawo takalmanta flat shoes sannan ta nufi dakin Gimbiya Sa’adiyya, tana tafiya mai cike da izza da takama, wacce duk gangar jikinta ke amsawa. 
Ta samu Saadiyya duke guiwowinta a kasa, kanta da hannuwa bisa bakin gado. Da alama barci take yi wanda baijima da daukarta ba, kasantuwar har da hijabi a jikinta, da alama sallah ta gama, ta cigaba da kuka har barcin ya dauke ta. 
Murmushi Kursiyya tayi, wanda yake cike da bayyanuwar muguwar muguntarta. Ta zauna bakin gadan kusa da Saadiyya. Ta dan tauni lebonta a hankali, sannan ta hau bubbuga ta da hannunta. 
Firgigit Sa’adiyya ta tashi. Tana ganin Kursiyya ce ta daga hannuwanta aka, a take hawaye 
suka hau sintiri bisa kumcinta. 
“Don Allah kiyi mini rai Umma, wallahi ba zaki sake bani umurnin in bijire miki ba. Wannan din ma tsautsayi ne. Yerima Abu Suiyan yafi karfina na sani, ba da niya naje ba Allah, da Yaya Hafsa ya dace.” 
Kuka mai tsanani take yi, wanda duk yinin yau dama shi take sharba, musamman kuma da 
yamman nan sadda abin ya faru. 
Da hannuwanta biyu ta kama Sa’adiyya ta zaunar kusa da ita. ldanuwa ta watsa, tana tsananin mamakin abin da idanuwanta ke gane mata. K0 daigizau Fulani Kursiyya ke mata? Ta ya zata kama ta kuma ta zaunar kusa da ita abu da kamar wuya. Tun da take da ita hakan bai taba shiga a tsakaninsu ba saiyau. Yau din ma da ya daye dace abin yafi haka tsanani. 
”Ya isa haka to daina kukan.” Tsananin mamakiya sa Saadiyya dakatawa da kukan ba tare ma da ta sani ba. 
“Kawai don Yerima ya zabe ki baizabi Hafsa ba kuma sai abu ya zama na kuka? Kwantar da hankalinki, in dai don wannan ne, Hafsa ma ta bar miki Yeriman. Ta yaya mace zata auri wanda baya son ta?Ai ba zai yiwu ba. Yerima Abu Sufyan ke ya zaba, kuma ke zai aura ba Hafsa ba.” 
Kai Sa’adiyya ta hau gyadawa hawaye na cigaba da sauka a bisa kumatunta. “Amma Umma…” “Ya isa haka Halimatu. Ke ya ganiyana so fa, a kan me za a nemi tirsasa shi? Kar lki damu.” Ta saki murmushi. 
Haka kawai sai Sa’adiyya ta tsinci kanta da fargaba da tashin hankali. Zuciyarta taji tana raya mata tabbas akwai wani abu a kasa. Acan ma bata ma Kursiyya komai ba ta tsane ta ina ga yanzu da zabin yarta ke neman butulce mata saboda ita Saadiyyar kawai dai makarkashiya, Allah kadaiya barwa kansa sani sai kuma ita Kursiyyar. “Niyanzu abin da nake so dake shi ne, duk wannan kukan da kike yi ki daina shi. lta ma kuma Hafsar na mata nasiha kan cewa ta saka wa zuciyarta salama. Komaiya yi tsanani maganinsa Allah. Kuma mace bata taba auren mijin wata, kamar yadda wani baya auren matar wani. Don haka duk abin da ya faru da ma haka Allah ya tsara.” 
Shiru Sa’adiyya tayi dai haryanzu tana alajabin wannan Iamarin. Mikewa Kursiyya tayi bisa kafafuwanta. Ta dafa ma Sa’adiyya kai tace, 
”Zan tafi? wurin mai martaba in shaida masa kin amince. Gobe saiya kira Sarkin Kubaisu ya sanar da shi. Kin ga daga nan sai a fara hada-hadar daurin aure.” 
Ta kanne ido daya ganin Saadiyyar kanta sunkuye yake kasa. Duk da tana son musa ma Kursiyya sai dai ba zata iya ba. Sam bata tashi da wannan halin ba, bata iyaja-inja da babba ba. Daga nan Kursiyya ta nufi farfajiyar Sarki Sani. Bata same shi a falon nashi ba, hakan ya bata damar zarcewa turakarsa. Ta same shiyana waya, hakan yasa ta zauna bisa sofa tana bin shi da kallo. 
Yajima yana wayar sannan ya yi sallama ya kashe. Ya sakar mata murmushi sadda ya hada idanuwa da ita. 
Salbiyya ce…” ”Na sani. ” Ta katse shi. “Zata dawo ne?” 
Ya daga mata kai. “Dakyau.” Ta tabe bakinta. ”Tare dasu Anwar zasu dawojibi.” 
Bata ce dashi komai ba a wannan gabar, sai kanta data sunkuyar kasa tana wasa da zoben yatsarta. “Ki dawo nan ki zauna sosai mana.” Yayi dariyar yake, ya Iura da yanayin nata sosai, tun sadda ta fahimci da wacce yake waya ta sauya. Hakan yasa yake neman hanyar da zai faranta mata. 
“Nan ma yayi na gode.” ‘anya kuwa  Ya tambaye ta. Kai kawai ta daga masa hade da sakin murmushi. “To madalla. Maganar Yerima Abu Sufyan.” “Abin dake raina ke nan mai martaba.” Gabansa ne ya fadi jin ta fadi haka. Yana gudun abin da zai iya faruwa ga yarsa Sa’adiyya. 
“Ni a gani na, tun da dai har Yerima ya zabi Halimatu ai kuma babu abin da zamu tsaya jira k0? Yanzu haka daga dakinta nake, mun yi magana ta fahimta da ita harma ta gwada mini amincewarta. Da alama dama can ita ma din tana son shi. Don haka kawai ka sanar da Sarkin Kubaisu a fara shirye-shiryen daurin aure.” 
Ta kuma sakin murmushi. Ido bude cike da mamaki da farin ciki yake kallon ta. Sam bai 
tsammanijin hakan daga gare ta ba. Da gaske kike Kursiyya?” Ta daga masa kanta. “Babu tantama mai martaba.” 
Bai san sadda ya tallabo mata hannuwa ya sumbata ba. Daga nan suka ci gaba da daukaka soyayyarsu. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE