GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 16
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 16
Washegari da sassafe, ko fadaa mai martaba bai fita ba ya kira Sarki Abdurrahman. Bayan sun gaisa ne Sarki Abdurrahman din yake shaida masa Abu sufyan ya ce Gimbiya Sa’adiyya ce zabinsa. Ya ya gani? Hakan yayi? Sarki Saniya yi murmushi, yace da shi babu komai, ai
da Hafsa da Halimatu duk daya suke a wurinsa. Duk wacce Yerima Abu Sufyan ya zaba babu matsala. Fatansu dai AlIah ya tabbatar musu da alkhairi.
“Ranka ya dade, yaushe kake ganin ya kamata a fara shirye-shirye?” Sarki Saniya washe baki, Yayi”To yallabai ni sai nake ga ai bai kamata a tsaya wani bata Iokaci ba. Tun da dai yaran duk
sun amince dajunansu aure kawai ya dace a daura. Koya ka gani?”
”Haka ne. Kamarsati biyu yayi? Wai saboda a sassanar da mutane. Ba badon haka ba, ai da ko gobe ma saimu daura.”
Dariya Sarki Sani yayi,
“Mako biyun ma yayi ai. Allah ya nuna mana, yasa alkhairi a rayuwar auren tasu.
Zumuncinmu kuma Allah ya kara karfafa mana shi.” “Ameen ya Rabbi.” Sarki Saniya ce,
“To sai ka fada mini sadakin yar taka, domin ni sani ko nawa zan tanadar domin daurin auren dana. ”
Murmushin dattako sarkin Kubaisu yayi, Su dama haka suke da kara a tsakaninsu, kowa jan dan kowa yake ajikinsa, har ma sai ka fijan dan amininka a jiki fiye da naka dan, saboda shi ma haka zaiyi ma naka. “To yanzu yadda za,a yi, muna so a bamu jajayen rakumma guda uku, kosassun dawaki guda uku, sai kudi naira dubu dari‘ uku…”
Tun bai rufe baki ba Sarki Sani ya tulle da dariyar da yajima baiyi irinta ba. Yace”Lallai ma Abdurrahmanu. Yo to diyar taku ta zinare ce? Gaskiya ba zamu iya biyan wannan makudan dukiyar ba. A dai rage k0 mu canza sheka. ”
Sarkin Kubaisu ma yayi dariya sosai, “Ai wannan shekar ba zata taba canzuwa ba. Danka yaga yata ya rude a kanta, don haka in dai kuna so dole a daure a biya mu haka.” Waya suke mai cike da nishadi da birgewa. Tsananinjin dadi ya gama mamaye wayannan mutanen guda biyu. Wannan hadin auren sun matukar jin dadinsa. Don haka sai sukeji ma tamkar sujawo makwanni biyun su dawo gobe. A karshe suka kashe magana cewa za a ba amarya sadaki dubu dari uku da duwatsun zinare guda uku, sai doki daya da rakumi daya. Sarki Sani ya dauki alkawarin zai bayar idan anzo daurin aure. Dama babu godiya a tsakaninsu, hakan yasa suka sallame dace ma juna su gaishe da iyali. Gimbiya Sa’adiyya kuwa yadda taga rana haka taga dare bata runtsa ba hargari ya waye. Ta dai samu tayi sallolin nafila taga barcin baya da shirin zuwar mata. Wanka ta shiga tayi, ta shirya cikin bakar lapaya mai manyan flowers pink and blue. Ba ta shafa komai ba sai mai, shi ma kuma don ya zame mata dole ne take shafa shi. K0 kadan kwalliya bata dame taba. Kwalli kadai ta shafa saboda yadda idanuwanta suke wadatattu, gasu kuma farare sol, shafa kwallin ne kawai zai sa su daidaita, tsantsar kyawunsu ya bayyana.
Turare take cikin fesa wa taji taku ana shigowa, hakan ya sa ta daga idanuwanta, a nan tayi arba da Hafsa, biye da ita Kursiyya ce sun sha ado. Da saurinta ta ajje turaren hade da zubewa kasa ta gaishe da Kursiyya, sannan ta ce, Barka da safiya Yaya Hafsa.”
Murmushi Hafsa tayi hade da tabe baki, “Yauwa sannu amaryar makon gobe.” ‘Makon gobe?’ Ta maimaita a ranta. “Gimbiya Sa’adiyya yata, ya kika tashi AlIah yasa dai baki sake yin kukan ba.” Ta kirkiro murmushin dole,
Kawai ta samu ta kakalo daga kasan makoshinta. “Dakyau.” Kursiyya ta fada hade da zama a bakin gado, Hafsa ma ta zauna kusa da ita.
“Zuwa nayi in shaida miki, yanzun nan mai manaba da Sarkin Kubaisu suka gama waya, nan da mako biyu masu zuwa za a daura muku aure keda Yerima Abu sufyan.”
Zabura tayi da karfi, ta firfito da idanuwanta waje tana bin Kursiyya da kallan mamaki. “Baki shirya ba ne? Karki damu, ai nice nan mai shirya ki.” Ta dukar da kanta kasa, a take hawaye ya fara sauka a kumcinta.
“Kiyi hakuri kigafarta mini Yaya Hafsa, wallahi bada sona ba hakan ta kasance. Nasan ke keson Yerima Abu sufyan, kawai dai hali ne irin na maza. Ban da abin shi, aiya yi mini girma. Kece babba dake ya dace ba…”
Hafsa tajawo ta ajikinta tana sakin murmushin da duk wanda zaigan sa saiya gane cewa na mugunta ne.
“Ya isa haka kanwata. Ki manta da komai ki rungumi kaddararki. Dama can kece matarsa
bani ba. An gama komai daurin aure kawai ya rage.”
Mamaki sosai Sa’adiyya keyi. Irin wannan maganar ta arziki bata taba shiga tsakaninta da Hafsa ba tun yarintarsu har zuwa wannan Iokacin, sai fa yau. Wannan dalilin ne ya sa ta kasa yarda dasu duka har Kursiyyar. Ta riya a ranta cewa akwai wani abu da sukeboye
mata. Tabbas suna da wata manufar, don babu yadda za a yi duk kin da suke mata saiyau a rana daya su nuna suna son ta, bazai taba yiwuwa ba. Sai kuma taji wani kukan na sake sauko mata. In da,a ce tana da uwa da ita kadai zata iya gane idan tsakani da Allah suka dawo suna sonta. Ita ba wani makusanci ba bare ta tinkare shi da maganar ya bata shawara. Mai martaba ne kadai, shima kuma Kursiyya tafi karfinshi, saiyadda tayi da shi.
“Muna da gagarumar hidima k0 Umma? Gani yayar amarya, gani kuma babbar kawar amarya. ” ‘
Ta saki murmushi tana bubbuga bayan Sa’adiyya.
“Haka ne kam. Sai ku fara shiri tun daga yau ai. Nima akwai shirye-shiryen da zan mata, ina so Yata tayi daraja sosaiga mijinta. Amma dole sai munje tare da ita. Ai za kije ko Yata?”
Haka kawai taji bata aminta da zancen ba. Ita kanta ba ta san sadda bakinta ya kufce ba tace
aa. Cikin mamaki Kursiyya tace “A’a? Kina nufin ba zakije ba ke nan?” “Ba ina nufin haka ba Umma. Kawai dai fitar ce bana so
Shiru Kursiyya tayi, ba taso ta yi wani abu na tilasci wanda harzai iya sakawa Sa’adiyya ta gano manufarta. Hakan yasa kawai ta dan yi murmushi sannan ta mike da cewa zata tafi. Hafsa ma ta mike amma Kursiyya tace da ita ta zauna, so take yisu fara tsare-tsaren auren. Tun da ta koma daki take zirga-zirga, tana yi tana bubbuga hannuwanta, tana cika tana batsewa.
“Lallai zancen Hausawa ya zama gaskiya, da suka ce wasa da yaro shi ke kawo raini. Wato ita wannan yarinyar har ta samu fuskar da zata musa mini nace da ita mu fita tare? Yarinyar da ko yatsa na saka mata ta ciza ba zata taba cizawa ba.lallai Akwai matsala, gaskiya dole in canza taku.”
Ita kadai ta rinka tufka da warwara a cikin dakin.
Hmm