GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 20
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 20
Sadda suka isa bakin kofar gidan boka Fartsi, da karfi Sa’adiyya taji tamkar an jefa mata kibiya a saitin zuciyarta. Ta saka hannunta na dama a saitin zuciyar ta ta dafe, sannan ta daga kanta ta kalli Kursiyya da tun dazu idanta yake kyam a kanta. Ganin irin kallon da Sanadiyyar ke mata ya sa ta gaggauta tatso magana daga bakinta.
“Uhm…lafiya dai ko ‘yata?”
Shiru Sa’adiyya tayi ba tare da tace da ita uffan ba. Ta dan Iumshe idonta sannan ta sauke su ga Zabbau.
“Ina ne nan kuka kawo ni?” Maganar da sukaji tayi ke nan, tana kokarin karkata kallon ta ga Kursiyya. Cikin in ina Kursiyya ta ce, ”Uhmm…zan karbi wani sako ne sannan mu wuce. Ai zaki raka ni‘ mu shiga ciki k0?” “Ku shiga kawai, ni ina nan.”
Tsuke fuska Kursiyya tayi ba tare da tasan sadda tayi ba. Kafin a hankali ta saki fuskar, ta kamo hannun Sa’adiyya ta rike a cikin nata.
“Kina tunanin na kawo ki ne in siyar dake? Kin san bazan cutar dake ba Halimatu. ldan harzan iya cutar dake to tabbas zan iya cutar da Hafsa.”
Ta dakata daga nan tana karantar yanayin Saadiyyar.
“Taso mu shiga kinji? Sako ne kadai zan karba mu fito. Ni ma kaina sauri nake yi bana son bata lokaci.”
Ba wai don ta yarda da Kursiyyar bane, haka kawai tajiya kamata ta bita, ko ma dai miye, mutum baya tsaIlake kaddararshi. Bayan sun fita daga motar Zabbau ta rufe, fuskarta kunshe da fara ‘ar mugunta tabi bayansu.
A Iokacin da suke kokarin shiga gidan Sa’adiyya taji zuciyarta ta fara tsorata. Yanayin yadda ginin yake dole mutum saiya yi fargabar shigar shi, sai dai kaga su Kursiyya da zuwa wurin ya zame musu tamkar ibada.
Yadda Sa’adiyya ta rinkaji tamkar anajujjuya ta yasa ta tsayawa cak, gudun karta fadi. A hankali kuma hasken wurin ya fara raguwa harya koma ya zama duhu dundum, k0 tafin hannunta ba zata iya kalla ba. Dariyarketa Kursiyya ta saki, kafin ta saka hannunta ta
lalubo Saadiyya, ta riketa kyam suka doshi: hanyar dakin Boka Fartsi.
Bayan sun isa dakin nashi, kamar koyaushe sai da suka karya dajini, ban da Saadiyya da take ganin komai najuya mata, yanayin tamkara mafarki. Suka shiga daga ciki suka zauna. Sa’adiyya kuma tayi tsaye.
Lokacin da boka Fartsi ya bullo da dariya ya iso. Yana yiyana kallon Sa’adiyya, yana tafa hannuwa.
Kin cika jaruma Kursiyya. Shiyasa nake son aiki dake. Ko kadan babu dana sani a ciki. Duk taurin zuciyar wannan mayyar yarinyar ga shi saida kika yi amfani da kwakwalwa da basirarki kika kawo ta. Lallai najinjina miki. Kuma ina maiyi miki albishiri da cewa zan tsaya tsayin-daka inyi miki aiki mai kyau, wanda har adaba ba zai taba baci ba har sai idan nida kaina na warware shi.”
Dariya tayi ita ma Kursiyya, Zabbau ma ta dauki dariyar har suna shewa. Suna masujin dadin yadda boka Fartsi yajinjina wa aikin Kursiyya.
“Meya rage yanzu ya bokana?” “Aikiya rage gareni.”
Ya dunkule hannuwanshi duka biyun sai ga wani haske ya bayyana a cikinsu
A saitin Saadiyya yajefa hasken, take dukkanin jikinta ya gama mamayewa da haske. “Ina da magana ya bokana, amma kayi hakuri karta bata maka rai.”
Yajuyo ya kalle ta a fusace, sabada ya tsaniyana aiki a dakatar dashi. Cikin rawar murya tace
“Ina so a dakatar da aikin ne har sai na mayar da ita gida, in yaso saika bani na mata k0ma miye, saboda idan na koma babu ita ban san me zance dasu ba. Ko yaka gani?”
Yayi jim, Yaryatsarshi bisa Iabba alamar tunani,
“Haka ne kuma, kinyi gaskiya Kursiyya.”
Ya sake dunkule hannunshi ya bude, saiga wanigarin magani ya bayyana a ciki. Ya mika ma Kursiyya yace,
“Idan kun koma duk sadda kika so aikin ya tabbata sai a turara wannan garin a inda take, kurwarta zata dawo gare mu, gangarjikinta ce kadai zata tsaya a wurinku. Daga nan babu wani sauran tasiri a rayuwarta. Komai nata ya dawo a karkashin ikona, saiyadda nayi da
ita.” ‘ Ya saita hannunshi ga Sa’adiyya, take saiga wannan hasken na ficewa daga jikinta yana dawowa cikin hannunsa.
Motsa baki Kursiyya ta hauyi alamun tana son yin magana, amma tsabar tsoron bokan da take yi yasa ta kasa cewa komai.
“Bakinki yana motsi alaman kina son cewa wani abu.” Boka Fartsi yace da ita. “Ehh to, boka yanzu idan muka koma da ita a haka ba zata tona mana asiri ba?”
Dariya yayi da karfi yace “A sakaran tunani irin naki ne kike tunanin zata iya tabuka wani abu?” Tayi shiru kanta sunkuye a kasa.
“Ku tafi da ita kawai. Ki tabbatar cewa an mata hayakin nan, kuma da kanki zakiyi mata. Daga zarar aka yi aka gama, shi kenan komaiya kammala.”
Jikanta ta bude ta zaro dala dubu daya ta ajje a gabanshi, sannanjiki na rawa ta mike bisa kafafuwanta, ta kama hannun Saadiyya suka fice Zabbau biye da su.
Sadda sukaje bakin mota ita da kanta ta bude ma Sa’adiyya kofar ta shiga. Bayan ta zaunar da ita tace,
“Halimatu me kika gani a can ciki?” Da murmushi a fuskarta ta tace”Banga komai ba sai kaya. Umma ina zamu wuce daga nan?”
Murmushi Kursiyya tayi tana maigasgata aiki irin na boka Fartsi. Ta kalli Zabbau ita ma ta saki murmushi.
Umurtar direban tayi daya kaisu wani katafaren shagon tufafi. Suna zuwa can ta kama hannun Sa’adiyya suka shiga. lta da kanta ta hau za6ar mata manyan materials masu daraja da tsada. Sun kashe kudi sosai sannan suka nufi komawa gida.
Da isar su sun tarar tela yazo kamar yadda Kursiyya ta kira shi cewa ya iso bangarenta kafin su iso. Ta baje kaya tana gwada mishi. Suna cikin haka Hafsa ta shigo. Koda ta kalli Sa’adiyya sai da hankalinta ya tashi, don a zatanta ba zata sake dawowa gidan ba.
Da ido Kursiyya tama Hafsa alama a take kuma ta gane. Tazo da fara,a tana cewa “Halimatu ashe kun dawo.ammafa dai an zamo masu kyau?” Murmushi kawai Halimatu ta mata ba tare da tace komai ba.
Da dare tana kwance saiga kiran Yerima Abu sufyan ya shigo mata. Ta dauka da sallama kunshe a bakinta ta gaishe shi. “
“Gimbiyata ta kaina. Ya kika wuni?”
“Lafiya Iau alhamduli’llah. Ya hidimomi?”
“Kamai lafiya gimbiya Saadiyya. Ya kuma shArye shlrye an dai fara k0?” Ta saki murmushi tamkar tana gabanshi. “Ehh an fara. Yau ma munje wasu wurare.” “Wurare? Ina da ina kenan?” Ta dan yi shiru jim, kafin tace,
“Wurin farkon dai ba zan iya cewa komaigame da shi ba. Sabada tun da muka tinkari wurin ban kara tuna meya faru ba. Kawai dai zuciyata ta rinka riya min wai wurin siyan kaya ne. To amma abun mamaki shi ne ban ga komai ba. Babu wasu kaya a wurin. Na gaza fahimtar komai. ” Cike da mamaki Yerima Abu Sufyan yace,
“Wannan wace irin magana ce? Kina nufin kije wuri amma kice baki san ko meya faru ba? Ina hankalinki yake to?”
Bata san amsar da zata bashi ba don ita kanta mamakin da take yi kenan tun dazu. Jin ta
yi shiru ne yasa ya canza akalar zancen da cewa,
“Nima yau na fita zagayar gari tun safe ban samu na dawo gida ba saiyanzu. Shiyasa kika jini shiru yau ban neme kiba. Kina dai Iafiya k0?” “A Ihamdulillah! ”
Ta furta murya can ciki. “Tome ya faru kuma?” Ya tambaye ta. “Lafiya lau…uhm…”
Sai kuma tayi shiru don harga Allah akwai magana a bakinta amma bata santa inda zata
fara sanar da shi zancen ba. “Akwai magana a bakinki Gimbiya. Yanzu kina da wanda ya fini bayan abbanki?” “A’a.” Ta fada kasa kasa. ’
“Har akwai wani abu wanda zakiboye mini? Ni kuwa kin ga a yadda nake dake yanzu babu wani abu da nakejin zan iya boye miki shi. Na baki daraja da muhimmanci sosai. Na miyar dake abokiyar shawarata.”
Jin shsshekar kukanta yasa ya dakata da maganar da yakeyi.
“Ya salaam! Haba Halimatu! Don Allah kiyi shiru ki fada min damuwarki. Hala a kan wannan muguwar matar mahaifin taki ne? Meta miki? Kin san cewa zan iyajure komai amma banda digar hawayenki. Wallahi Halimatu zan iya yo tattaki gobe da sassafe inzo in kwatar miki fansa. Bana son zalunci, ba naso a zalunci wani, musammaan ma keda kike
da muhimmanci a rayuwata. Kike amanata.”
Cikin rawar murya tace,
“WaIlahi Yaya Yerima ba wani abu akayi mini ba.” “Ehen inajin ki. Keda waye to? Meya saka ki kuka? Mene ne kike son fada mini?” Tayi kokarin tsayar da kukanta.
“Haka kawai jikina ke bani wani abu mummuna zai iya faruwa dani Amma bani da tabbas. Ban
kuma san k0 mene ne ba. ” “Me ya sajikin naki yake baki haka? K0 dai kin ga wata alama ne?” “K0 kadan yaya Yerima. Ni dai don Allah wata alfarma zan nema daga gare ka.” “Huh!” Ya sauke ajiyar zuciya yana murzar sumarshi da hannunshi na dama. “Ina sauraran ki.”
Ya fada bayan ya koma ya zauna a bisa bakin gadonshi yana suararon yadda take ta famar sakin numfashi.
Hmm