GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 21

GIMBIYA SA’ADIYA 

CHAPTER 21

Sai da ta share hawayenta sannan tace

“ Ina son duk wani abu da zai faru dani ko a yanzu ko ba yanzu ba, ka dauka cewa wannan kaddarata ce. Kayi’ hakuri da k0 ma mene ne. Bawa baya taba tsallake kaddararshi. Kamar yadda na fada maka a baya, tun da nake a rayuwata ban taba ganin wanda ke sona ba bayan Abbana, amma cikin iko da kudirar AlIah saiga shi kai daga gani na ka nuna kana kaunata, baka tsane ni ba, sabanin sauran mutane.” “ 
Yayi shiru yana sauraron ta, duk saiyaji rashin kuzari a tartare da shi, jikinsa yayi Iakwas kamar ba shi ba. Baigama dawowa a duniyarsa ba yaji taci gaba da magana, 
“Sannan magana ta biyu, ta yiwu ka rinkajin wani irin yanayigame da ni. Ko a zahiri (yawan tunani) ko kuma a mafarki. Ina so a duk lakacin da hakan ta faru da kai kayi mini addu’a, sannan a karshe kayi amfani da abin dana fada maka, don ta iya yiwuwa ya zama gaskiya. ” 
Tayi shiru daga nan, tana tsananin mamakin kanta, yadda ta dage jero zantukan da ita kanta bata san yadda aka yi ta sansu ba, kai tsaye daga zuciyarta suke fitowa, sai motsin labbanta kawai da takeji. 
Goshinsa ya dafe yanajin yadda kansa ke sara masa. Mamakin kalaman da suke fitowa daga bakinta kawai yake yi. 
“A karshe, karka yarda dasu, duk wani abu da zasu ce da kai kar ka aminta.” Sai a sannan ya samu damar yin magana. 
“Wai wa ‘yanne irin maganganu ne kike yi haka Sa’adiyya? Kina magana kamar wacce jinnu suka shafa ko kuma saban shiga a hauka. Me yake damun ki? Ki fada mini matsalarki mana…” 
Yayi kasa kasa da murya cikin magiya yana rokonta, 
“Na miki akawarin zan warware miki koma wacce irin matsala ce dake tattare dake. Don Allah kar ki boye mini Halimatu, kin ga dai nine wanda zaki aura. Nine kadai wanda zaki iya tinkara da damuwarki ya warware miki. Ki fada mini k0 zuciyata zata samu 
sassauci…please!”Kukan nata ne ya tsananta. Ta dafe bakinta da hannun dama, cikin kuka tace, Ina matukar kaunarka Yaya Yerima. Hakkun zuciyata ta aminta da kai, ta yarda dakai, ta 
ta kuma mallaka maka duk wata tsoka dake cikinta. Wannan dalilin ne yasa na kasa boye maka yanayin da nake ciki, wanda ni kaina ba zan iya warware shi ba, ban san takamaimai me yake faruwa dani ba. Kawai daijikina yake bani akwai wani abu, wanda dani da zuciyar tawa babu wanda yasan shi. 
K0 ba dade ko bajima karka manta dani Yaya, karka manta da Halimatus-Saadiyya. Marainiya wacce ta tashi cikin rashin uwa, rashin gata, da kuma rashin soyayya daga dukkanin al’ummah.” 
Tana kaiwa nan ta kashe wayar, ta zare batirin daga ciki, hannunta dafe da zuciyarta tana 
kuka sosai, kuka mai tsananin karfi 
A bangaren Yerima Abu Suryan kuwa tun data kashe wayar yake kokarin kiranta amma taki shiga, sai dai ace masa wayar a kashe take. Shawara ya yanke cewa zai kira mai marraba sarki Sani. Amma sai wata zuayar ta raya masa cewa bai kyauta ba idan ya kira shi, tamkar rashin kunya ne wannan. Hakan yasa yajefar da wayar bisa gado, ya hada kai da guiwa, yanajin yadda zuciyarsa ke masa radadi, tamkarza ta tsage ta fito. Hawaye yake so su fito 
k0 zai samu sassauci a zuayarsa amma sunki fitowar. Ya gyada kanshi, a zahiriya furta, “In sha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi.” 
Tanajin karar taku na kusanto dakinta tayi saurinjawo bargo ta lullube kanta, sannan ta sassauta kukan da take yi, ta rufe idonta tamkar tana barci. Kwankwasa kofar taji ana yi 
amma ta yi shiru. Jin muryar wata kuyanga taji tace, 
SaadIyya mai martaba ke son ganin ki.” 
Banza ta mata, ta sake runtse idanuwanta gam. Jin shiru yasa kuyangar ta bude kofar ta 
shigo ciki, ganin Saadiyya a dukunkune yasa ta dora hannu a ka tace, “To badai baki da lafiya ba? Bari inje in fada masa.” Da gudunta ta bar dakin ba tare da ta rufe ba. 
Taje ta samu masu tsaron farfajiyar sarki Sani, ta isar da sakon cewa Gimbiya Saadiyya na can Iullube babu lafiya. Sadda sakon ya isar masa hankalinshi ya tashi. Ya mike da nufin zai Ziyarce ta amma Kursiyya dake zaune ta dakatar dashi, 
“Kar kaje ka tashe ta daga barcin da takeyi don Allah mai martaba. Ni nasan bata da 
lafiya saboda na biya ta dakin kafin inzo nan, na bata magani ma tace ba zata sha ba wai taji sauki. To inaji daga nan ne barcin ya dauke ta. Ka taimaka kar ka shiga ka tashe ta. ” 
Jin haka yasa ya koma ya zauna, yanajin aminta da zantukan Kursiyya dari bisa dari. Sannan kuma zuciyarsa na matukar farin ciki da ganin yadda Kursiyya ke kula masa da Halimatunsa ba kamar da ba. 
Haka Halimatu ta kwana a runtse bata runtsa ba. Idanuwanta sun mata nauyi sosai, ga kukan data sha, ga kuma rashin barci. Kanta na sara mata dukjijiyoyi sun taso mata. K0 data shiga bandaki da nufin yin alwallar sallar asubah sai ta tarar period yazo mata, Ta dafe kanta tuna cewa tun jiya ya kanata tayi, tana tajin alamunsa amma saiyau da asubah. Kama wa tayi ta kwanta. Rashin samun barciya sa tana kwanciya barcin ya sace ta mai matukar nauyi. 
Tun da sassafe Kursiyya ta tura Zabbau dakin Saadiyya don ta gano mata halin da take ciki tun da aka aiko cewa bata da lafiya. Zabbau ta same ta tana barci mai nauyi, bata ko san ta shigo ba. Tajinjina kanta da murmushin mugunta sannan ta fice. 
Dariya sosai Kursiyya tayi, tace, 
“Zan shiga dakin. A rarraba garwashi a zuba turaren wuta. Ki ware wani garwashin ki biyo ni dashi dakinta.” “To ranki shi dade.” 
Zabbau ta fada cikin bin umurnin Kursiyya. Kursiyya kuma ta lalubo maganin da Boka Fartsiya bata. Ta daga shi ta kalla cikin murmushi sannan tayi kwafa. 
“A yau din nan zan gama dake. Aikin banza aikin wofi.na gama da banzar uwarki ma  bare ke? Mtsw!” Ta saka shi a cikin hular alkyabbarta sannan ta nufi bangaren Sa’adiyya. ’ 
Duk wanda ta hadu da shi duka wa yake yana gaishe ta har ta karisa isa dakin. A hankali ta shiga cikin sanda, haryanzu dai barci sosai Sa’adiyya keyi. Tayi tsaye tanajiran isowar Zabbau. 
Bayan kusan minti sha biyar Zabbau ta iso da kaskan garwashin. Suka tura kofardakin sannan suka datse da mukulli. Kursiyya ta zaro garin maganin ta murmusa a cikin wutar sannan ta saita shi saitin fuskar Sa’adiyya. 
A cikin barci taji hayaki na mamaye ta. Ba shiri ta tashi tana ta famar tari tana bin su 
Kursiyya da idanuwa. 
“Bakar munafuka Wato ke kinji dadi kinga ina Iallaba ki k0? A tunaninki akwai ranar da zan iya sonki ne? Kinyi kadan bakar mayya. Dama babban burina shi ne in samu lago a kanki, in kawo karshen rayuwarki. Ki fadi magana ta karshe kafin in sake barbad a garin maganin nan wanda zai tafi tare da kurwarki ya barmu da gangar jikinki.” 
Ido Saadiyya ta runtse, ashe shiya sa jikinta keta bata wani abu zai faru da ita. 
“Magana daya ce zan fada miki umma. Ina so ki sani, duk daren dadewa Allah ba zai kyale ki ba. Zaiyi mini sakayya. ” 
“Hahahahaha! Ba zaiyi miki sakayya ba zaki ce Halimatu, Haka zaki ce zaiyi muku sakayya ke da bakar mahaifiyarki. Sabada ita ma nina takassara rayuwarta. Tana nan da ranta sai daigwara mutuwarta fiye da yadda take a yanzu.” Sa’adiyya ta bude bakinta za tayi magana taji ya tsaya cak. A take kurwarta ta fita daga cikin gangar jikinta, ta isa ga boka Fartsi dake can yana ta sakin murmushi, yana maraba da zuwanta a gare shi.

Hmmm
Yau dai kunjiyadda aka yi Gimbiya Sa’adiyya ta koma ita ba aljana ba ba kuma fatalwa bah. 

Akwai sauran zance. Ku biyo ni


Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE