GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 24
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 24
Kyakkyawan mari Kursiyya ta wanka wa Tabawa. Cikin rawarjiki Tabawa ta rusuna harkasa tana godiya. “Ke harkin isa ki bada minikasa a idanuwa? Niza kiyi wa karya? Tun yaushe kike ce mini kin zuba maganin a mazauninta kamar kowanne zuwa da zata yi? Yau kwanansu nawa da
zuwa haryanzu basu tafi ba? To wallahi baki isa ba! Yau-yau dinnan nan zaki bargidan nan.” Sosai jikin Tabawa ke rawa. Labbanta na kyarma ta ma rasa abin da zata ce.Tashi ni ki bani wuri. Kuma ki fara harhada kaf tsummokaranki, yau zaki bar masarautar nan, yau zaki bargarin Bilba gabakidaya, ki tafi ko ma ina ne. Masarautar Bilba ba zata iya zama da irinku masu fuska biyu ba.”
Sai a sannan Tabawa tayi nasarar shanye kukanta. “Ranki shi dade kiyi mini afwa, wallahi abin ne ya gagara yi, ba wai da son raina ba ne. ” “Ehen! Tabawa kin san ba kiyi ba me yasa za kiyi mini karya? Me yasa duk sadda zan tambaye ki sai kice mini kin saka? Nace ki bace mini daga gani tun ban sa an balla miki kafafuwanki kin zama gurguwa ba.”
Da saurinta ta bardakin, hawaye sun gama wanke mata fuska.
Ba ta ciburki a ko’ina ba sai bangaren Salbiyya. Kukan da Salbiyya ta ganta tana yi ba karamin kidimata yayi ba. Tace,
“Tabawa lafiya kuwa? Me kike ma kuka?” Cikin rawar murya Tabawa tace,
”Fulani Kursiyya ta kore ni daga masarautar nan bisa ga wani boyayyen Iaifi dana mata. Ranki shi dade, idan har kina son cigaba da rayuwa mai inganci a cikin gidan nan to ki fito gaban kowa kice baki aminta da korar da Fulani Kursiyya tayi mini ba. Domin kuwa ni hadimarki ce ba tata ba.”
Zare idanuwa Salbiyya tayi cike da mamaki, “Wace irin magana ce haka Tabawa?”
“Zan yi miki bayanin komai uwargijiyata, amma kidaukar mini alkawarin bazakizafafa mini hukunci ba. Na tabbata ba zaki barni ba tare da kin saka an daure niba. Amma gwara a mini daurin a kan na bargidan nan ba tare da fallasuwar asirin Fulani Kursiyya ba. “
A wannan karon maganar tasu bata waya bace. Sarki Sani ya gwammaciya wanke kafafuwanshi yaje masarautar Kubaisu domin yin magana ta gemu da gemu da Sarki Abdurrahmanu. A ganin shi bai kamata komai ace a waya bane. Musamman ma wannan
dashi kanshiyake ganin rashin kyautatuwar abun. Farin ciki bai kau daga fuskar sarki Abdurrahmanu ba, domin kuwa zuwa ne na ba zata sarki Sani ya masa. Bai tsammani zuwansa a daidai wannan Iokacin ba. Cikin raha suka gaisa tare da tambayar juna ya iyali da kuma bayan rabuwa, duk da cewa basu wani jima ba rabon su da juna, duka-duka a rasuwan Gimbiya Sa’adiyya ne.
Kayan marmari aka jera gabanshi, ban da cimaku kaIa-kala masu matukardaukar ido. A gefe guda kuma gasasshen bankararren rago ne jibgege bisa wani tangamemen baho. a murmushi mai martaba yayi
“Yanzu ranka shi dade ni da nayi zuwan ba zata har da wata dawainiya aka kama yi mini? Shin wai duk a yaushe ma aka yi shi daga zuwa na?”
Fara,a Sarkin Kubaisu ya fadada, Yace
“Yallabai, kar ka damu da duk wa ‘yannan. Dama akan gasa raguna domin rarraba wa mutanen masarauta. Daga ciki ne aka kawo maka.” “ “Godiya nake sosai Allah ya barzumunci.” “Ameen. Ka ci abinci sosai Yallabai.”
Kayan marmari kawaiya sha, yana yi suna dan hira kadan-kadan, kafinn a hankali yace, “Na tabbata ka yi mamakin irin wannan ziyara dana kawo maka k0?” Jinjina kai Sarkin Kubaisu ya yi, yace”Haka ne yallabai. Sai dai duba da irin amintakarmu, sai na mayar da hakan ba komai ba. Domin kuwa manyan mutane sukan kirkiri ziyarar ba zata don kawai su faranta ran wanda suka kai wa ziyarar.”
“Haka ne mai martaba. A hakikanin gaskiya magana ce tafe dani, mai matukar muhimmanci. Ina fatan ba zaka dauki maganar da wani abu ba face kokarin kyautatawa a gare mu baki daya.” Mai martaba sarkin Kubaisu ya sake jinjina kanshi, idanuwanshi kyam a kan sarki Sani.
“Rasuwar Gimbiya Sa’adiyya bai kamata ya dakatar damu daga kulla kyakkyawar alakarda muka yi niyya ba. Karmu bari, tun da dai AlIah yasa ina da wata ‘yar, me zai hana a musanya wa Yerima Abu Sufyan da ita Domin kuwa da Halimatu da Hafsa duk daya suke a wurina.” Shiru Sarkin Kubaisu yayi yana nazari. Duk da cewa zancen gaskiya ne Sarki Sani ya kawo, amma saiyake ganin bai kamata maganar ta taso a yanzu ba. Anyi gaggawa ga alamarin.
Nasan cewa za a ga kamar nayi gaggawa. Kamar bai kamata na kawo maganara yanzu ba. Sai dai abin da nake wa gudu, kar aje yaran su samu wasu abokan rayuwar a garin jinkirinmu. Kuma ba zamu so muyi musu dole ba. Hausawa sun ce wai da zafi-zafi akan daki karfe.”
“Tabbas wannan gaskiya ne. Kuma ka kawo shawara sosai.”
Murmus yayl
“Saboda haka nake ga, bai ma kamata a dauki dagon Iokaci ba. A kira Yerima Abu sufyan” idan yana nan, a ji daga gare shi. ldan harya amince to Hafsa bata da matsala. A yau din
nan ba zan tafi ba sai an daura musu aure. In yaso batun tarewa ayi shi daga baya.” Hannu Sarki Abdurrahmanu yaba Sarki Sani suka yi musabaha.
”Tabbas samun aminnai ire-irenku suna karanci a wannan Iokacin. Samun mutum mai hangen nesa kamar ka sarki Sani yana da matukar wahala. Na aminta da tunaninka, na gamsu dari bisa dari. Dama a yau ne ya kamata a daura auren Yerima da Gimbiya Sa’adiyya k0?”
Sarki Sani ya daga masa kai.
“Allah sarki! Sai mutuwa tayi musu yankar kauna. Ashe babu rabon ganin wannan rana a
gare su. Allah yajikan Sa’adiyya ya rahamshe ta.” ’ameen ya Allahu.” Sarki Saniya fada cike dajin zugin mutuwar Halimatu.
“Ni ina ga ai basai anji daga bakin Yerima Abu Sufyan ba. Tun da har shi da kanshiya zabi Gimbiya Sa’adiyya bana tunanin zaikijininta Hafsa. A daura kawai in yaso sai mu bashi mamaki. Bari a kira waziriyanzun nan a sanar da batun daurin auren na gaggawa. Ba zaka tafi ba sai da tabbacin an gama komai ranka shi dade.”
Kai Sarki Saniya gyada alamarrashin gamsuwa da batun.
“Yallabai bai kamata a yi haka ba. Yana da kyau dai mu bashi hakkinshi a matsayinshi na wanda zai zauna da matar. Ita ma don tana mace ne shiyasa, kuma na tabbatar ba zata ki shi ba. Don haka dai a daure a name shi din. Idan ma ba yanzu zai dawo ba sai mu tafi,
zuwa gobe ku same mu can a daura.” “Kar muyi haka… ” Ya dakatar da shi da hannu,
‘Alfarma ce wannan na roka yallabai. A taimaka dai aba yaron nan hakkinshi. Aji daga gare
shi sannan. ” Ajiyar zuciya sarkin Kubaisu ya sauke. “To shi kenan tun da haka ka zaba. Bari a bincika inda yake.”
Kararrawa ya buga a take saiga fadawa biyara gabanshi sun rusuna. Cikin isasshiyar muryar nan tashi ta sarauta yace,
“A binciki inda Yerima yake ace ina neman shi da gaggawa.” A tare sukajinjina kawunansu hade da mikewa. K0 da sukaje dakinshi baya nan, a rufe ne ma dakin. Suka koma cikin gida nan ma suka tambayi Fulani Maryama amma ta ce baizo wurinta ba. Sadda aka yi ta kiran wayarshi sai aka rinka jiyo ringingdinta daga cikin dakinshi alamun nan ya tafi ya bar ta.
Fulani Maryama ta kira Iambar Shaheed, bayan ya dauka ya gaishe ta ta amsa cikin girmama wa, ta tambaye shi,
“Wai Yerima lafiya kuwa? Sai neman shi ake ba a gan shi ba. Babu wanda ya fada wa inda yaje kuma wayarshi ma a gida ya bar ta. Koya fada maka inda zaije?”
Yerima Abu Sufyan dake gefenshiya gyada mishi kai da sauri, hakan yasa cikin hikima Shaheed yace,
“Tofa! Fulani ni ma kaina nemanshi nake ban ganshi ba. Tun dazu hargidan nazo ban same shi ba don a rufe na tarar da dakinshi. Niyanzu haka ma ina hanyar tafiya Birnin Banuut. Amma ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu yana cikin koshin Iafiya a duk inda yake. Kin san tun rasuwar Gimbiya Sa’adiyya haryanzu baigama dawawa hayyacinsa ba. Haryanzu damuwa bata kau daga cikin zuciyarshi ba.”
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, cikin karfin hali tace, “To ina fatar hakan Shaheed. Na gode kwarai, a sauka Iafiya.” “To Fulani nima na gode. Don Allah ki kwantar da hankalinki. In sha Allahu komai Iafiya.” Da haka suka yi sallama. Yana kashewa ya dubi Yerima fuskarshi ba yabo ba fallasa. “Amma Yerima me yasa ka zabi haka?”
“Ba zaka gane bane Shaheed. Tun dazu ina kwance cikin dakina na datse bana dan jin dadin jikina, najigittawar su Mallam Audi suna maganar sarkin Bilba, mahaifin Gimbiya Sa’adiyya ne yayi zuwan ba zata. Haka kawai sai hankalina bai kwanta da zuwan ba. Zuciyata ke saka mini cewar akwai abin da ya kawo shi. Ta iya yiwuwa a kan maganar auren Hafsa ne yazo Duk da cewa wasu sun ga fitowa ta amma babu wanda ya san inda na nufa. Don da dama wasu sun tambaye ni nace musu Iambun baya zan leka, da haka dai na samu na fita. Ba nason komawa gidan har sai dare yayi, don a lokacin na tabbata ya riga daya tafi
Idan a gabanshi ne ba Iallai in iya fadar wani abin da yake cikin zuciyata ba, saboda kwarjininsa da kuma girmansa da nake gani. Amma bayan idonsa komaizan Iya fada, duk wani abu da yake cikin zuciyata.” Shaheedya dafa kafadarshi tare da fadin
“Kuma wannan ma wani tunani ne mai kyau Oga.”
Hmm