GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 25
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 25
“Mun tattauna ni da Sarki Sani na Bilba, mun kuma yanke shawarar hada ku aure kai da Yar uwar marigayiya Sa’adiyya, wato Hafsatu. A take muka so a daura auren, sai dai shi Sarki Sani din ne yace lallai sai an ji daga gare ka, saboda ba zaiyiwu ayi babu kai ba. Dalilin da yasa aka neme ka kenan amma ba a gan kaba. Ban so ya zabi hakan ba, saboda k0 kana nan k0 baka nan na tabbata bazaka kiyi mini biyayya ba. Ba zaka taba bada mini kasa a idanu waba. Abin da duk na nuna ina so kaima kana son shi, ba tun yanzu ba, tun kana karamin yaro. Duk da hakan dai sai banki ta tashi ba, nace da shi su tafi kawai, zamu zo domin daurin aure. ”
Duk wasu kalamai da Mai martaba sarki Abdurrahmanu ya san zasu kashejikin Yerima sai da yayi su. Sai dai ko gezau basu sa Abu Sufyanu yaji zai iya yi masa wannan biyayyar ba. Jin mahaifinshi yayi shiru yasa ya dauka da fadin,
“Abba… ” Ya dan dakata, saboda nauyin maganar da zata fito daga bakinshi.
“Abba ina maijin nauyi da kuma kunyar fada maka cewa ba zan iya auren Hafsa ba. Halina da nata sun bambanta, kaman yadda babu ko hadin halayyarta dana Yar uwarta mariga
yiya. ” ldanuwa Sarki Abdurrahmanu ya zaro yana kallon Yerima Abu Sufyan da tsananin mamaki’.
“Abba ko a musulunci kanwa aka ce a hada da miji bayan matarshi ta rasu, ba wai a hada
shi da yayarta ba. Duk da dai nidin ba a riga da an daura ba, amma tamkar an daura din ne, saboda dan Iokaci kadan ne ya rage. Abba in da ace Harfsa ba yayar Gimbiya Saadiyya bace k0 bana son ta wallahi zan aure ta. Sannan Abba…”
“Dakata mini Sufyanu. Ni kake fada wa wayannan maganganun babu ko kunya a idanuwanka? Me kake nufi ke nan? Ba zaka iya auren taba? In tinkari babban aminina Sarki Sani in shaida mishi dana Yerima Abu Sufyan yace ba zai auri yarsa ba? Ina Baka isa ba Yerima. Baka isa ka zubar mini da kima ba. Baka isa kasa a rinka kallo na a matsayin wanda bashi da iko da gidanshi ba. ”
Tashi Yerima Abu Sufyan yayi ya isa gaban Abbanshi, ya durkusa durkushin kneel down, cikin sassanyar murya yace,
“Don Allah abba kayi hakuri. Ban yi dominbacin ranka ba. Sai dai bana so a samu matsala ne a gaba. Duk da nasan cewa Hafsa na sona, amma akwai matsala. Matsalar bawai iya
rashin jin son da nake mata bane, sai don rashin tarbiyyarta.” Ya dan yi shiru yana kallon reaction din Abbanshi, sannan ya dare da,
“Akwai abubuwan dana boye su ban fada maka ba, kuma na tabbata shi ma mai martaba din bai fada maka ba. A Iokacin dana fara zuwa, ba a yarda an fiddo mini yan matan biyu ba, duk da cewa ka fada mini cewa su biyu ne, a cikinsu zan zabi daya. Tun shigowar Hafsa na fahimci rashin tarbiyyarta. Mahaifiyar nata ma babu wani ladabi a bangarenta, ga son nuna isa da zakewa. Ina ganin yanayinta sai naji sam bata kwanta mini ba. A nan na nemiganin cikon dayar, tun nan sai na gane akwai tsantsar kiyayya a tsakaninsu. Abba. Halimatussa’adiyya ta fuskanci duk wata kyara, tsana gamida tsangwama daga wurin su
Hafsa. A dan zaman da nayi ranar duk na fahimci haka. Na fahimci ba mahaifiyarsu daya
da Hafsa ba. Na fahimci irin azabtarda ita da suke yi, kuma ga dukkan alamu babu wani
hukunci da yallabai Sarki keyi. Ban tabbatar da hakan ba sai dafda rasuwarta. Wasu irin
kalamai da suke fitowa daga cikin bakinta wanda suka tsoratar dani, suka kasa fice mini daga cikin zuciya. ”
Ya dan runtse idanuwanshi, ya saka tafin hannunshi na dama ya shafe fuskar.
“Abba ni zargina ma da hadin bakinsu wurin mutuwar Gimbiya Sa’adiyya…”
“Ka rufe mini baki Sufyanu.”
Da karfi sarki yayi wannan maganar, har sai da yajawo hankalin masu gadin kolarshi, wasunsu suka iso da gudu dominjin k0 Iafiya. Hannu ya nuna musu alamar su tafi da
hanzarinsu kuwa suka bar wurin.
“Tsananin kiyayyar da kake yima Hafsar harya sa kana neman yi musu kazafi? To ka rufa wa kanka asiri Sufyanu. Wallahi idan ka dauko ma kanka magana babu ruwana, ba zan shiga ba.” Gyada kai Yerima yayi,
“Wallahi Abba gaskiya nake fada maka. Dukkanin alamu sun nuna mutanen nan sune suka kashe Halimatu. Kafin ta rasu ta bani haske daya gama bayyana haka, sai dai baigama bayyanuwar ba har sai bayan ta rasu. Kuma sun yi hakan ne duk don kar in auri Sa’adiyya, tun da idan habu ranta ai dole in hakura da ita in koma wa yayarts. Abba zaka tabbatar da hakan ne idan ya kasance mai martaba sarkin Bilba ne da kanshi ya nemi hadin aurena da Hafsa, ba wai kai ka nema ba kamar na farkon.”
Shiru Sarki Abdurrahmanu yayi yana nazarin kalaman Yerima. Da gaske a wancan auren shiya fara neman su kulla zumunci, shiya kai haton Yerima Abu Sufyan a Iokacin da sarki Sanivya nemi hada Yayanshi auren zumunci da YaYayen sarakuna. Amma a yanzu da kanshi sarkin yazo neman auren, wanda ba ,a san bangaren mace da wannan ba. Ganin kalaman Yerima na niyyaryin tasirin a zuciyarshi yasa ya kuma tamke fuska.
“Yerima baka da sauran maganar da zaka fada mini a yanzu, ina ga ai ka gama zazzage duk ta cikinka k0? Sai ka tashi ka tafi. Kuma kunyata ni da kake son yi AIlah ya fika. Bazan taba kunyata ba. Ka tashi ka tafi? ka bani wuri.”
“Abba…” Ya furta cike da damuwa. “Ka tafu? kawai Yerima. Jeka ko kuma in bar kada duniya.”
Babu yadda Abu Sufyan baiyi ba don yin wata maganar amma Sarki ya hana. Hakan yasa ya tashijiki babu kwari kawai ya wuce bangarenshi. Dukkan wanda zaigan shi saiya tabbatar da akwai damuwa. Yerima da Sarki Abdurrahmanu ke tsananin so, yake ganin darajarshi, yake kyautata mishi a kodayaushe, amma yau shi ne yake ma wannan fadan,
har ma yana kin sauraren maganarshi.
Haka ya koma dakinshijiki babu kwari. Shi ma kanshi sarkin ko kadan babu tattare da shi. Fulani Maryama ta tambaye shi yadda aka yi, amma ba yada nutsuwaryi mata wannan bayanin. Hakan yasa ta dangana tayi shiru, saidai tana da yakinin Abu Sufyan bai amince ba. Domin kuwa ya kyankyasa mata kiyayyar da yake yi ma Hafsa tun zuwanshi na farko masarautar Bilba. Cikin sanyin muryarta tace
“Kayi hakuri ka yafe ma Abu Sufyanu. Na tabbata ba zaiki Hafsa haka kawai ba. Kayi mishi
uzuri, ka saurari ta bakinshi. ” Cijin damuwa ya kalli Fulani Maryama,
“Wato dama kun hada baki kenan bani da labari. To Iallai na gode da wannan sakayyar da kuka yi mini. Na gode dajuya mini baya da kuka yi Maryama. Ashe har akwai alfarmar da zan iya nema daga wurin sufyanu ku hada baki ke da shi ku kasa yi mini ita? Babu komai. Kunya dai ce naji ta, k0 ince zanji ta. Sai dai ina so ki tuna cewa ba Abu Sufyanu ne kadai dana ba. Ba Abu Sufyanu ne kadai na haifa ba. Zan kira Yerima Bukar idan gari ya waye, in umurce shi daya yikarin mata ta biyu da Hafsa. Na tabbatar bazai bada minikasa a idanuwa ba. Zai karbi zabin nawa hannu bibbiyu. ”
Yajuya ya bata baya. Cikin dakewa tace
“Amma dai ranka ya dade ya kamata kayi ma Abu Sufyan uzuri. Ka tuna a wancan karon, dawowar shi kenan daga kasar waje ka umurce shi da yaje ya zabi matar aure a masauratar Bilba, bar’ k0 musa maka ba ya amince. Duk da cewa babu tsarin aure a tattare da shi haka ya dangana, ya kuma cika maka zabinka. Ranka ya dade, me yasa a yanzu zaka ki tuna alkhairin da ya maka na baya, sai sharri kwaya daya tak da yayi maka yau? Ya kamata ka yi tunani, yadda har bai musa maka ba daga farko, tabbas a yanzu ma yana da dalili. Dalilin ne ya kamata ka tambaye shi, ba wai kayi fushi da shi ba.”
“K0 ma dai me zaki fada Maryama ki fada. Ni dai na gama maganata.”
Ba tada zabin da ya wuce tayi shiru kawai tana bin bayanshi da kallo. Ita babbar damuwarta ma Yerima Bukar da yace zai kira ya aura mishi ita. Ta tabbata daga ita har Abu Sufyan zasu kwashi takaici. Domin dama babu jituwar kirki a tsakaninsu. Yerima Bukar akwai son dizgi da wulakanci, Yerima Abu Sufyan kuma zuciya, sam baya daukar wulakanci da raini. Wannan dalilin yasa basu jituwa. Har ita fulani Maryama abun ya shafe ta.
Washe gari da sassafe sakon mai martaba ya riski Yerima Bukar. Da ma mai martaba fushi yake yi da shi bisa ga wasu talakawa daya zalunta. Yanajin kiran kuwa saiya dan ji dadi, don ya tabbatar karshen fushin yazo kenan. Baijira komai ba ya fito, tafiyar daga gidanshi zuwa bangaren mai martaba ba wani mai nisa bace, amma tsabar mulki da kasaita a bisa dokiyaje. Bayan ya sauka ya isa bangaren Sarki Abdurrahmanu. Cikin girmamawa ya gaishe shi, amma bai ko kalli inda Fulani Maryama take ba.
Atunanina babu aikin da zan sa dan cikina ya kiyi mini. A zato na k0 mutum nace dan cikina ya kashe zai kashe tare da rufa mini asiri. Sai dai ashe tunanin banza ne nayi. Ban canko daidai ba. ”
‘Dago kai Yerima Bukar yayi, don a tunaninshi ko shi ne yayi Iaifin.
“Umurni ne zan baka Bukar, idan kuma kai ma ba zaka yi ba din irin na Abu Sufyanu sai in
sani. ldan kai ma kunyata nidin za kayi babu damuwa. Sai in sama raina hakuri. ”
Yerima Bukar najin haka saiya murmusa a cikin zuciyarshi. Dama magulmata sun gulmata mishi an samu sabani tsakanin mai martaba da dan lelen yeriman nashi. Saiya karyata su, don baiga wannan ranar ba.
“Ranka ya dade, baka da wani abu da zaka saka ni wanda zai gagareniyi. Babu abin da zaka hana ni da zan ki daina shi. ”
Shi kanshi mai martaban don daiyana so Bukarya mishi aikin ne, amma ya san karya yake yace babu abin da zai hana shiya ki hanuwa. Bukar sam ba mutumin arziki bane. Mugun shaye-shaye ya gama Ialata mishi kwakwalwa. Ga tsantsar tsanar talakawa da yayi.
“Bukar, so nake ka nemi auren Gimbiya Hafsa yar sarkin Bilba, yar uwar gimbiya Sa’adiyya da Sufyanu zai aura ta rasu. Ka cika mini wannan burin kar ka bari inji kunya.” Murmushi Bukarya yi, “Babu komai Abba. Nina amince zan auri Hafsa. Na maka alkawarin cika maka wannan burin naka.”
Murmushi shi ma yayi tare da shima Bukar albarka. Jin an buga karrawar neman gaggawa yasa dukkan al,ummar masarautar Bilbah suka tsorata. Duk kiran daya kasance na gaggawa ne tsoron shi suke, saboda sai abu ya tsanan ta sannan ake yin irinshi. A fada mai martaba yake zaune yaji wannan kara. Don haka ya bude idanuwanshi yana son sanin dalilin buga kararrawara daidai wannan Iokacin, kuma ba tare da sanin shi ba. Bai kawo kowa a ranshi ba sai Kursiyya. Don ya tabbata babu wanda zaiyi wannan aikin sai ita. Gaba-gadi babu neman izini take gudanar da dukkanin uzururrukanta.
“Waziri me yake faruwa ne a masarautar nan? ” mai martaba ya gaggauta tambayar Waziri idanuwanshi kyam a kanshi.
“Sai dai a bincika ramka ya dade. Amma jikina yana bani aikin Fulani ne. Da alama akwai
gagarumar matsala ne. ” Wazirin ya furta cikin girmamawa.
Kafin kace kobo mutanen cikin masarautar sun fara hallara a babban dakin taron dake
cikin gidan, kowa da kalar abin da zuciyarsa ke kissima masa.
Da hanzari ta iso fada, Asiya, daya daga cikin hadiman Salbiyya. Kanta a kasa ta rusuna, “Ranka ya dade mai martaba, sako daga Goggoji Salbiyya, wai tana son ganin ka cikin gaggawa. Akwai matsala.”
Tana gama rufe baki waziriya umurce ta data tashi ta tafi Babu musu ta mike cikin azama ta bar fada.
“Muje farfajiyata, waziri kai kuma ku tafi dakin taro kafin mu iso.” waziri’ya mike bayan mai martaba ya bar wurin shi da dogarawa.
Tun dazu take zirga-zirga a cikin dakin tanajiran isowarshi. Jin motsinshi yasa ta duka har kasa ta gaishe shi, bayan ya zauna ta isa gare shi. “Kayi mini afuwa da neman ka da nayi kana fada ranka ya dade. Na gaza hakuri ne. ”
“Inajin ki Salbiyya. Mene ne Matsalar? ” Ya ambata cikin tsananin son sanin damuwarta.
“Nice na kira yi taran gaggawa ranka ya dade. Tabawa, daya daga cikin yardaddun hadimaina ta tazo mini da wata magana, amma ranka ya dade kayi mini afuwa, ba zan fade taba a nan sai anje dakin taro a gaban kowa.”
A tsawon rayuwarshi da Salbiyya k0 kwatankwacin irin haka bata taba faruwa ba. Bai tabaji ko ganin ta shirya meeting ba, wannan sai Kursiyya. Wannan dalilin ne ya sa bai musa mata ba, bai kuma nemi tursasa ta kan sai ta fada masa ko mene ne ba. “Babu komai Salbiyya. Allah yajishe mu alkhain‘. ” Da murmushi a fuskarta ta amsa da amin. Kursiyyaha kuwa rike baki ta yi, gabanta na tsananta dokawa. Jiran isowar Zabbau da taje dauka mata rahoto kawai takeyi. Tana cikin wannan tunanin kuwa saiga ta ta iso har da shesshekar sauri take yi. “Ranki shi dade, wannan kira na gaggawa dai ba daga mai martaba bane. An tabbatar mini da cewa aikin Goggoji ne. Ban dai san dalilin yin saba. Inda najiyo wannan din ma kansu basu san dalilin kiran ba. ”
Mamaki karara a luskar Kursiyya. Ta tauni labban ta cike da gadara tace, “Komai ya zoda
sauki dai tun da ba daga mai martaba bane. Takaicin dai shi ne a ce mai martaba yayi
kiran gaggawa ba tare da sanina ba. lta waccan ban damu ba. Na tabbata ba wani abu mai tsanani ba ne. Fiddo min bakar alkyabbata sannan kije dakin Hafsa kice ta shirya yanzu mu tafi dakin taro.
Da azama Zabbau ta aikata abin da Kursiyya ta umurce ta. Sannan suka tafi
Girman dakin taron ya wuce gaban a misalta. Domin kuwa wanda ke zaune gaba sam ba zai iya hangen na can bayanshi ba. Zazzaune suke kowa yayi sit, dakin ya cika makil tamkar ba yanzun nan ne akayi kiran ba.
Daga kujerun gaba, masu fuskantar al’umma, sarki ne da kaf iyalanshi, banda Kursiyya da Hafsa dake daidai shigowa yanzu. Idon kowa ya koma a kansu, domin kuwa abun mamaki
ne a ce anyi kiran gaggawa irin wannan kuma ba daga Kursiyya ba ne. Kujeru biyun da suka rage Kursiyya ta zauna, daga gefen haggun mai marraba sai Hafsa kusa da ita.
Munkaila ya dauki Iasifika tare da furta, “A madadin mai martaba da iyalinshi, ana muku barka da wannan Iakaci tare da fatan duk kuna cikin koshin lafiya. Wannan kira ne wanda daga ni har ku babu wanda ya san dalilin yin shi, duk da dai cewa ba bakon abu bane a wurinmu. Don haka zan isar da sifika ga maigirma Goggoji, kamaryadda aka umurce ni. ”
Da azama ya isa ga Goggoji ya mika mata sifikar sannan ya koma ya zauna. Ta karba da faraa kunshe a fuskarta tayi sallama. “Da farko dai ina mai baku hakuri na tara ku da nayi a wannan wuri zuwan kwatsam, wanda na tabbata wasu daga cikinku sun razana. Kafin in ce komai, ku bani sakan talatin za a shigo min da wata baiwar Allah. ”
Tana gama rufe bakinta saiga Tabawa an shigo da ita an daure hannuwanta. Da an gan ta dai an san mai laifi ce. Daga gefen ajje masu Iaifi aka wulla ta. A tsorace Kursiyya ta darara idanuwanta ga Tabawa da aka kumburar ma fuska. Salbiyya ta kalli reaction din Kursiyya sannan ta murmusa, ta dora da fadin, “Na tabbatar da ni daku muna mamakin yadda rayuwar ni da ‘yayana tayi karanci a masarautar nan. Idan yau muka dawo gobe zamu yi sha’awar tafiya, babu wanda ya san dalili. Idan muka tafu? din kuma sam hankalinmu baya kadowa ga gida, tamkar wasu wayanda aka ma kurciya haka muke. Duk da abun yana matukar damu na, amma ban taba kawo komai a raina ba. Sai dai na cigaba da fada ma Allah dare da rana babu gajiya wa, harya karbi du’a,ina a wannan karan, wato gaskiya ta
baiyana… ”
Cikin kidimewa Kursiyya ta mike da idanuwanta suka canza launi. “Salbiyya wane irin maganganu ne kika tara mutane kike yi karamar wata karamar yarinya? Ya kamata ki san akwai maganar da a iya cikin gida kawai ake yin ta.”
Tamkar bada ita take yi ba, Salbiyya ta shashatar da ita tare daci gaba, “Tabawa ki fadi duk abin da kika sani tun daga farko har karshe, sannan ki sani, ke hadimata ce, nike da damar zartar da hukunci a kanki. Idan kika boye wani abu zan miki hukunci daidai da zunubinki.“
Sifikar aka isarga Tabawa, cikin rawar murya ta fara kokarin magana amma ta kasa. Idanuwan mutane kadai sun ishe ta. Da kyar ta iya daga Iabbanta tace, “Goggoji, ki sani, ba za a taba hada baki dani a cuci Fulani Kursiyya ba. Ba zan iya aikata abin da kike soba. ”
Idanuwa bude Salbiyya ke kallon Tabawa. Tama kasa furta komai sai tsananin mamakinta da take yi.
“Fulani Kursiyya kigafarce ni. Ina tsoron fadin abin da Goggoji ke son na fadi game dake.
Don Allah kiyi min rai, amma ba za a cuce ki dani ba. ”
Cike da al’ajabi maimartaba ke kallon abin dake faruwa. Ya gaza fahimtar komai sai bin su yake da kallo daya bayan daya.
“Tabawa kiyi bayani yadda za a gane, da alama kowa yana cikin duhu ga maganarki. ” Munkaila ya fada ganin yadda kowa ke bin ta da kallo. “
Ta share gumin dake tsattsafowa bisa goshinta. Cikin marairaicewa tace, “Goggoji ce ta same ni ina zaune ta bukaciyin sirri dani. Wai tana son hada ma Fulani Kursiyya makirci wanda zata kasa fitar da kanta. Tana so ta hada baki da ni wurin wannan aika aika. Na tsorata sosai kaina sunkuye ina tunanin ta yadda zan ce mata ba za a iya cin amana dani ba. Can naji tace “so nake na bayyana wa kafatanin al’umma cewa Fulani Kursiyya ce ta mana asirin rashin zaman mu a masarautar nan. Ta yadda kowa zaigane sasai.” na daga kai na kalli Goggoji, nace “To ni kam ta yaya zan shiga cikin wannan batun Goggoji? ” Ta kwantar da muryarta, cike da son na aiwatar mata da aikin ta ce, “Ina so ki fada wa al umma cewa dake take hada baki wurin yi mini asiri. Ke idan ta kama ma kice ke kike karbo mata asirran. Ni zan kare ki daga Kowanne irin hukunci.” Na tsorata sosai har na rasa abin da zan yi. Daga farko kamar ince mata ba zan iya ba, sai kuma na tuna cewa idan har ban amsa mata ba to zata iya zuwa wurin wata tayi mata, a cuci Fulani Kursiyya ba taji ba bata gani ba. Don haka sai na amsa. Shi ne aka kai ni dakin hora aka ajiye ni, jiya kenan. Goggoji ta min alkawrain tarin abun duniya, In takaice muku zance, ta alkawarta hada auren danta Yerima Anwar da ‘yata Shamsiyya. ”
Tun da Tabawa ta fara maganar jikin Kursiyya ke rawa. Ganin kamai take tamkara mafarki. Ba haka suka yida Tabawa ba. Bata shiryajin kalar wannan karyar ba. don ba itace taba ta tattara mutane ba. Innalillahi take ambata a fili, tana kallon fuskar dattiju war matar data kusa sa ‘ar mahaifiyarta amma ta dage tana sharo karya tamkar an shirya mata.
Cece-kuce da surutan mutane ne suka yawaita, har wurin ya dauki hayaniya. Cikin bacin rai mai martaba ya runtse idanuwanshi, bai san sadda ya saki tsawa mai karfi ba, wacce ta gigita kusan duk wanda ke dakin taron. Hakan yasa duk akayi tsit, wurin tamkar ba a taba yin magana ba.
Kuka Kursiyya tasa mars kara, ta saka dukkanin tafukan hannunta tana murzar hawayen karya, wanda da kyar ta samu ta kirkiro su. “Me nayi wa Salbiyya? ” Ta taka ta isa har inda Salbiyya take, daga gefen daman mai martaba. Ta rusuna har kasa idanuwanta cikin na Salbiyya, ta ce, “Salbiyya me nayi miki dana cancanci wannan kazafin daga gare ki? Me yasa kika zabi ki kunyata ni bisa Iaifin da ban san dashi ba?
Idan kunaji ana cewa speechless, to haka Salbiyya ta tsinci kanta. Cikin dakiku kadan ta fara tunanin yadda sukayi da Tabawa shekaranjiya. Bayan sun gama magana da Tabawa, tace tana son fallasa sirrin KurSIyya a gaban kowa, amma don Allah idan ta fallasa din ta sassauta mata hukunci. Salbiyya ta tsare Tabawa da cewa ta fada mata k0 mene ne, daga fari taki fada mata, cewa ta bari dai har sai anje gaban mai martaba din. Amma Salbiyya ta nace kan Iallai sai Tabawa ta fada mata. Hakan ya sa tace,
“Kamaryadda kika sani, shekaruna talatin cif a cikin masarautar nan, wato daidai Iokacin da aka auro ki. Da zuciya daya nake zaune da ke, k0 da wasa ban taba tunanin cin amanarki ba. Sai dai daga lokacin da Fulani Kursiyya ta zama matar mai martaba, ta fahimci kyautata wa da amincin dake tsakanina dake, sai ta nemi illata rayuwar aurenki ta hanyata. Ta nunar min da tana son tayi’ aiki dani, amma a sirrace. A take ta bani kyautar dunkulen zinari mai matukar nauyi. Ban taba mallakar dukiya kamar wannan ba. Hakan yasa na amince mata, ta bani wani kullin magani cewa in ajje shi a bisa kujerar zamanki. Ban musa mata ba na karba na aikata kamaryadda ta umurce ni. Babban abun mamaki, kina zama a ranar baku kwana a masarautar nan ba, daga ke haryaranki maza biyu. Kuma tun daga nan baki sake zuwa kasar nan kin zauna ba. Saboda da zarar kin zo ake sabunza aikin, har sai kin fita kuma. ‘
A wannan karon ta bani sai ban saka ba. Har asirina ya tonu ta gane ban saka din ba, shi
ne ta kore ni daga masaraular nan kwata-kwata.”
Tana kaiwa nan ta daga kanta ta kalli Goggoji, hawaye ta gani wanke a Iuskarta. Bata hana ta ba, saboda zaluncin ya kai mizanin da za a iyayin hawaye ma. Sunjima a haka kafin Salbiyya ta ce, “Sosai naji haushin Kursiyya amma duk da haka bai kai haushinki da naji ba Tabawa. Kin ci amanata kin zalunce ni. Kuma Allah ba zai taba barin ku ba, saiya mana sakayya ni da yarana.”
Cikin kuka Tabawa tace, “Shirye nake da karbar duk wani hukunci naki. Sannan kuma a shirye nake domin fallasa wannan sirrin a gaban kowa. Amma ina mai rokonki daki sassauta mini hukunci, sannan kar ki kore ni daga masarautar Bilbah.”
Zaluncin ya zaluntu, cutar ta cutu kwarai, ace tsawon shekara talatin an raba zuciyar Salbiyya da mijinta. An raba ta duka da masarautar. A ranar haka ta kwana ta wuni tana kuka. Taso washegari tayi kiran gaggawar, saiya zamana Sarki Sani baya nan, ya tafi? Kubaisu nema wa Hafsa auren Yerima Abu Sufyan. Da gariya waye ne da rana tasa aka karkada kararra wa domin wannan taron na gagawa.
Kuka SaIbryya keyi sosai, tanajin wani irin radadi sosai a kalbinta. Wannan sharri’ har ina? Ita da aka zalunta amma sai gashi a karshe an mayar da abun kanta. Da sauru da sauri zuciyarta ke bugawa, a hankali ta rinka ganin komai na juye mata, da ba a zaune take ba da tun tuni ta fadi. A hakan ma saida mai martaba ya tallabeta ta fadi ajikinshi ta rijib‘