GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 3
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 3
Cike dajarumta ta sauko daga bisa gadonta. Ko kadan babu alamar wani tashin hankali a tattare da ita. Sai dai kuma duk da yakinin da zuciyarta ke bata kan cewa babu abin da waccan aljanar za ta iya yi mata, hakan bai hana ta jin fargaba a zuciyarta ba. dan kyafta idanuwanta tayi sai kamannin sun fado mata a rai. Haka dai ta samu ta kawar da komai daga ranta, gudun kar al‘ummar masarautarsu su fahimci wani abu. A bisa tafin kafafuwanta da suka sha zanen lalle harzuwa saman kafarta ta mike, ta mike hannuwanta a daidai lokacin da mika ta zo mata. Cikin takun isa da kasaita ta fara ajje kafafuwanta har lokacin data bar dakin. A daidai isar ta falonta ta ci karo da hadimarta ta rusuna tana zaman jiran fitowar ta. A lokacin da Kurskiyya ta fito ne hadimar ta sake zubewa a kasa, cike da girmamawa take fadin,
“Ranki shi dade tun dazu nake nan ina jiran ki. Ga shi har rana ta fara fitowa baki fito ba. Allah ya sa dai lafIya. Da girman kujerarki.” Ba ta furta komai ba sai tabe bakinta da tayi. Ko kadan hadimar ba tayi mamaki ba. Kadan kenan daga cikin izza irin ta uwargijiyarta.
“Ranki shi dade, takawarki lafiya, na hada miki komai a wancan dakin, kiyi wanka ki karya.”
Sai a sannan tayi magana, “Ki gaggauta kira mini Zabba,u. Kice inajiran ta a wancan dakin.”Da rawarjiki tajinjina kanta, sannan da gudunta ta bar dakin domin kiran Zabba’u. Wancan dakin Kurskiyya ta koma, ta hakimce bisa wata kawatacciyar kujera, ta dora daya
Alamar takun da taji ne ya tabbatar mata da cewa Zabba’u ce. Hakan ya sata sauke ajiyar zuciya, daidai shigowar Zabba,u cikin dakin. A bude ta bar kofar hade da zubewa kasa cikin girmamawa. A zabure Kursiyya ta mike tsaye, tace, “Yi maza ki rufe kofar can Zabba,u, akwai gagarumar matsala.” Dajin haka sai Zabba’u ta tabbatar cewa akwai damuwa mai tsanani. Ba komai bane ke saka yanayin Kurskiyya canzawa haka ba. Amma a yanzu kam kallo guda za ka mata ka san cewa akwai abin da yake damunta.
cikin rawarjiki ta tura kofar, sannan ta dawo jiki na rawa tace,
“Ina fatar wannan matsalar ina da maganin ta, ina fatan ina da maganin warwaruwar kowacce irin matsala taki ranki shi dade.”
Gyada kai Kursiyya tayi, daidai lokacin da ta bude bakinta zata yi magana taji komai ya gagara Fitowa daga cikin bakin nata. Rawa labbanta suka hau yi, bilhakki take son yin magana, amma ina, ta neme ta ta rasa. “Ranki shi dade lafiya? Me kike son fadi?” Zabba’u ta fada a firgice, idanuwanta duk sun firfito waje tsabar kidima.
A nan din ma kokarin magana Kursiyya tayi ta kasa. Ta saka dukkanin hannuwanta ta shake wuyanta, amma ina, sai wani irin ruwa dake fitowa daga cikin bakinta. Hakan ya kara tayar da hankalin Zabba’u. Jikinta ya hau karkarwa tana sake tambayar Kurskiyya abin daya same ta, amma ina, sai ma tsananta da abun yayi.
Hannunta tasa ta tallabe ma Kursiyya wuyanta bayan ta matsa kusa da ita, sai dai a firgice ta sakar mata wuyan nata saboda wani irin mugun wari da ya daki hancinta. Hannunta na haggu ta saka ta dode hancinta. Tunda take a rayuwarta bata tabajin wari ko mai kama da wannan ba. Ga wata irin kala da yawun yayi, tamkar kwata. Cikin lokaci kadan bakinta ya karkace.
Suna a cikin wannan halin ne sukaji an kyalkyace da wata irin muguwar dariya, wacce ta amsa dukkanin bangon cikin dakin. Duk inda sukajuya sai suji kamar daga nan ne dariyar ke fitowa. A hankali kuma suka koma ganin gabbanjiki, idan sun ga ido a wancan gefe, Idanuwa Zabbau ke zarowa sosai, tana tsananin mamakin wannan al’amari. Tsoro ya gama mamaye kaf ilahirin jiki da zuciyaryarta. Ji take kamar ta tashi ta zura da gudu, sai dai kuma
ba hanya, ita da kanta tasa sakata ta rufe kofardakin, yanzu kuwa kafin ta bude tama in abun kashewa ne har an riga da an kashe su. Ta inda hanci yake sai ga hancin da kanshi ya baro bangon yana kokarin isowa inda suke, da haka dukkanin gabbanjikin mutum suka hadu wuri guda, suna dunkulewa, sai ga wannan fatalwar wadda boka Fartsi ya fiddo daga kwalba ta cibre wuri guda, a hankali tana takowa zuwa wurin su. Atsawon wannan lokacin kam Zabba,u ta gama kidimewa, sun makalkalejunansu ita da Kursiyya, duk tsananin warin da Kursiyya ke yi Zabba,u ba taji shi ba a yanzu. Tashin hankali ya mamaye ta.
Dum! Dum! Dum!!! Sautin takun ke ratsawa harcikin kunnuwansu. Ji suke tamkar ana zuba musu narkakkiyar dalma tsabar azabarda ke shiga ta kofofin kunnuwansu. Basu kara shiga tashin hankali ba sai sadda ta fara yi musu magana da wani irin sauti, wanda sauraron shi ma kadai ya ishi mutum zurawa da gudu. Kamar yadda na fada miki a daren jiya Kursiyya! Keda tashin hankali kun zama aminnan juna. Haka kuma sai kin fuskanci tsana da tsangwama daga wurin mutane, ciki kuwa har
da makusantanki. Bazan fasa daukar fansa a gare kiba. Ba zan taba tausaya miki ba. Haka kuma ba zan taba gajiyawa ba.”Ta zura dogon hannunta ta cafko fuskar Zabba,u, da karfi tayi jifa da ita, tana fadin, Sai kuma ke! Bakar munafuka. Da hadinn kai da goyon bayanki, da kuma bakaken shawarwarinki ne aka zalunce ni. Banji ba ban gani ba aka illata mini rayuwa. Sannan ku kuka dawo kuka ci gaba da rayuwarku mai kyau da nishadi. To baku isa ba Wallahi kuma sai kun dandani makamancin abin da naji.” Ta dalla tafin hannunta daidai inda tayi jifa da Zabba’u, a take sai ga haske ya bullo daga hannun nata, ta yarfa shi da karfi, sai ga wasu irin kananan halittu na fitowa daga ciki. “Ku shiga cikin jikinta ku illata mini ita a yinin yau kawai. Kafin dare yayi” a
Buuuuu! Kwarin suka isa inda Zabbau take. Mamaye ta suka yi a hankali suna shiga cikin jikinta. Atake ta hau soshe-soshe tana murzar jikinta ta ko’ina. A tsayin wannan lokacin kam babu kukan, sai ruwan hawaye mai gumi kawai dake tsatssafowa daga kwayar idonta. Zufa na ketowa ta kowacce gaba dake cikinjikinta. Ta kanannade tamkar gammon kifi, tana fitar da nishi sama-sama. ’
Dariya fatalwar ta sake kyalkyalewa da ita, kafin a hankali ta saka hannuwanta ta damko gashin Kursiyya da yatsunta guda biyu. “Ke da gashin kai har abada!“ Ta sake fashewa da wata dariyar da karfi. Da akaifunta ta ringa sakawa da karfi tana cizgar sumar Kursiyya. Sai dai Kursiyyar ta rumtse idon cike da jin azaba, da haka har ta gama tsinke kaf gashin kan Kursiyya. Da karfl ta sake kyalkyacewa da wata dariyar, wacce har sai da bangon dakin ya amsa. Kursiyya ta ringa jin kamar ana sama da kasa da ita. Ga kuma Zabbau can gefe guda a kanannade jini na fita daga ko’ina na jikinta.daidai, tamkar babu wani abu daya faru a lokacin.
Kuka ne ya sake kufce ma Kursiyya, ta sake yunkurin yin magana a tunaninta ko yanzu za ta iya, sai dai kakari kawai data ringa yi, wanda takejin wata irin azaba tun daga cikin cikinta har izuwa bisa harshenta. Ta sadakas, ta cire tsammani a yanzu. Ashe dai haka aikin sharri yake? Dama Hausawa sunce, idan zaka gina ramin mugunta ka gina karami, gudun karka fada a ciki. Ga shi dai ita ta gina babba, mai matukargirma. A lokaci guda ta afka a ciki, afkawa mai wuyar fltowa.
A rayuwarta, bata taba tsammanin akwai irin wannan ranar ba. Ko kadan ba ta taba kawo ma ranta cewa akwai ranar da rayuwarta zata wulakanta har haka ba. Magana ta dauke mata cikin ‘yan lokuta. Ga wani irin yawu da take fitarwa, wanda ita kanta warinsa takeji, har tana ji kamar za tayi amai. Awani bangaren kuma baki daya sumar kanta babu ita. Duk jikinta babu abin da tafi ado da shi sama da sumar kanta. Saboda Allah ya bata halittar gashi. Duk wanda ya san Kursiyya to ya santa da gyaran gashinta sosai, kuma ta Fiddo shi waje tayi ado dashi.
Kwankwasawar da taji anama dakin ne ya dawo da ita daga dogon tunanin data jefa kanta a cikinsa. Ta yiwu Shafa’atu ce, hadimar nan tata. Amma me zata fada mata idan ta bude mata ta shigo ta same su a wannan halin? Ga kanta a bude, fatalwar tayi jifa da mayafinta bama tasan inda yake ba bare ta nemo ta rufe kan nata.
“Ranki shi dade, mai martaba ne yayo aike tun dazu yana son ganin ki. Na tsaya jira ne k0 Zabba,u zata fito na sanar mata, amma naji ku shiru, kuma ga shi sai kara yin aiken yake yi. Yanzu haka ga Mallam Kabiru nan tsaye yana jira. Me zan fada masa?“ Durum‘. Ta sakejin faduwar gaba. Shin tana da wata mafitar data wuce ta bude dakin? Babu! Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa.