GIMBIYA SA,ADIYA CHAPTER 33
GIMBIYA SA,ADIYA
CHAPTER 33
Shi kanshi dreban bai san hanyar Yankin Banii Hashim ba. Tafiya dai sukeyi idan sun yi nisa saisu yi tambaya. Sun dai gane basu kauce ma hanya ba. Hakan ya sa ya cigaba da taka motar.
Fira sukeyi jefi jefi Kursiyya da Zabbau. Dukkaninsu basu da wata nutsuwar kirki. Tsoro hade da tararrabi ne cike da zukatansu.
Har dare yayi basu isa ba. Suka tambayi wani mutumi a kan baburya tabbatar musu da cewa suna da sauran tafiya, kuma ga shi hanya! babu kyau idan dare yayI’. Ya basu shawara cewa su nemi muhallin barci su kwana harzuwa safe sannan su tafi.
Kursiyya ta tsure jin an ambaci hanya babu kyau. Har sauri take tama mutumin godiya hade da tambayarshi inda za su iya samun masauki.
Su dai ba Hotel suka sani ba, babu ma shi a wancan lokacin. Sai dai irin gidaje haka su nema su kama haya na kwana daya kacal.
Mutumin yace zai musujagoranci wurin wani abokinshi su samu gida. Ya tuka babur dinshi suna biye da shi har suka isa gidan mutumin. Basu wani bata lokaci ba suka samu gida mai dakuna biyu, wanda komai akwai a Clkinshi daidai gwargwado. Kudin Kursiyya ta biya sannan aka musujagoranci har kofargidan, aka bude musu suka shiga.
A nan suka kwana. Washegari ma ba asubanci suka yi ba, saboda tabbatar musun da aka yi har da asubah ana ta ‘addanci a hanyar. Sai da gariya waye sosai sannan suka bargarin hade da kama hanyar yankin Bani Hashim.
Da fara isarsu yankin tun ba a fada musu ba suka gane. Saboda tsananin girman garin, da kyau da tsaruwarshi. Ga shi ko’ina shuke shuke ne. Wannan shiya tabbatar musu da cewa
akwai wadatar kayan abinci, manoma ne sosai a yankin.
Gaban Kursiyya ya fara bugawa da karfi sannan na Zabbau yabi bayanshi. Kallonjunansu suka yi be tare da sun furta komai ba suka cigaba da tafiya. Kursiyya tace da dreba ya tambayi inda masarautar garin take.
Dreba na ganin wasu mutane ya faka kusa dasu. Bayan ya yi musu sallama sun amsa ya tambaye su ina ne masarautargarin.’ Cike da mamaki samarin suka kwatanta musu. Suna barin wurin wani cikin matasan yace “Daga ganin su dai sunyi doguwar tafiya. Ko daga inama suke AlIah masani. ”
Tun daga nesa suka fara hangen ginin masarautar. A fuska kadai tayi ukkun masarautar Bilbah, bare kuma a yi maganan zurfinta. Kai tsaye suka shiga ta babbar kofar, ba tare da tuhumar komai ba aka bar su suka wuce.
Sai da suka ketare manyan kofofi biyar, a ta shida aka dakatar da su. Wani basamuden mutumi fuskarshi babu alamun imani yaCe “Meke tafe daku?”
Kursiyya taji wani irin zafi a zuciyarta. Duk matsayi da mulkinta wai yau ita ce wani kaskantaccen mutumi yake mata wannan tambayar.
“Daku nake magana.” Ya sake maimaitawa dajajayen idanuwanshi.
Cikin in-ina Kursiyya tace ”Mun zo wurm sarauniya ne. Ni matar Sarki Sani ne, Sarkin BIlbah. Mun zo tane musamman domin zantawa da ita. Amma kafin komai ka fara zuwa ka sanar da ita sannan kazo mu shiga.”
Wani dake can daga gefe yana sauraren su yayi saurin gyada wa wancan katon mutumm kai. Ya daga musu kai hade da basu izinin shiga kawai. KurSiyya ta yi nannauyar ajiyar zciya sannan ta koma cikin mota suka shiga. Daga nan din ma wata sabuwar tafiya ce. Sun yi tafiyar da akalla zata kai kilomita biyu sannan suka isa wani gini da aka kayata shi da zanen hannu kalar. Ginin mai kyau sosai da daukar ido. Cikin zuciyar Kursiyya tace ‘ashe a kauye muke mu kam. Masarauta na inda take.”
“Ranki shi dade da alama daga nan ne iya amfanin mota ya kare.” Cewa tayi zoka bude min kofar mu fita.” Ya fito hade da bude mata ta fita. Zabbau ma tabi ta. Kanta ta daga sama tana kallon tsawon ginin wurin, wanda taga tsayinsa sosai, da alama tsawon benen ya haura wa goma. Ta kofar farko suka shiga. Suka ci karo da mutane kowa na aikin gabanshi. Babu wanda ya kalle su, hakan yasa su ma din ba su tanka ma kowa ba.
Harsuka yi nisa basu ci karo da mai tanka musu ba. Sun daiga yadda bayi ke ta hidima. Da kuma kuyangu kowa na harkan gabanta. Suka gaj‘i suka dakatar da wasu yanmata.
“Don Allah muna tambaya ne. ldan baki suka zo masu son ganin sarauniya ya suke yi?“ Cike da mamaki suka kalli Kursiyya da tayi maganan “Ta san da zuwanku ne?”
Kallon kallo Kursiyya da Zabbau suka yi. Hakan yasa yanmatan suka fahimci Sarauniya bata san da zuwansu ba. Dayar tace “Babu komai kuzo in kai ku dakin baki. Idan munje akwai mai tsaron kofa. Shizaku fadawa kun zo, shi kuma ya sanar da aminin Saraumya. Sai ta fitar da ranan da zata zanta daku.”
Lokacin da sakon isar su ya riski Sarauniya Maimounatu tayi mamaki. Hakan yasa ta runtse Idanuwanta na sakan talatin, sannan ta bude hade da sakin murmushi. Ba lakacin tashinta daga fada bane. Saboda ko la,asar ba ta yi ba. Amma ta mike bayan ta dafe sandar zinarinta. Da sauri hadimanta ma suka mike. Aka bajejan kafet din da take takawa har zuwa duk inda za taje a cikin gidan.
Mata ce kyakkyawan karshe. Wacce ta tattara duk wata hali na mace wadda za ,a so. Fara da Ita ga yalwargashi. Jikinta sanye da wasu bakaken kayan fata maigashi-gashi.
Tafiyar da bata wuce ta minti biyar ba amma sai da ta dauki kusan minti ashirin da biyar
A daki kuwa Kursiyya sai take. Zabbau tace “To wai ma fa babu tabbas idan zata gan mu a yan Iokutan nan.kenab Idan ta yankar mana kwanaki kafin ta gan mu ina za muje mu zauna?”
Kursiyya tayi jim, sannan tace “Ke kar ki wani damu. In harba ta samu ganin mu ba dole ta bamu masauki. Musamman ma Idan taji daga inda muke. Duk da dai ba a yarda da uwar kishiya. Yo to uwar kishiyar diyarta mana.” Ta kyalkyace da dariya.
“Toni dai kam ma tsoron matar nan nake ranki shi dade. Sosai na tsorata dajin Iabarinta. Ina
fatan mu samu nasara dai.”
Kafin Kursiyya ta kuma cewa komai taji alamun gayyar mutanen da suka yo gaba Sarauniya na bm su. Kansu suka daga, ganin yadda aka malalejan kafet ya sasu mamaki. Basuyi tsammaci zasu ganta a dai dai wannan Iokacin ba. Hakan ya sa sam basu zaci ita bace Har sai da wani dattijo ya shigo yaCe “To ga Sarauniya nan isowa yanzun nan. Ku koma kasa ku zauna.”
Da sauri suka koma kasa din suka zauna. Sunajin iso warta duk suka sadda ka wunansu kasa har ta nemi wuri ta zauna. Hannu kawai ta daga duk mutanen suka tafi. Sun gane cewa privacy take bukata. Don haka aka bar dakin daga Sarauniya sai Kuyangu da Zabbau. Tayi gyaran murya.
Tace cikin Iakaci kalilan da bai wuce sakan ashirin ba na gano abin da yake tafe daku. Ban
san ke wace inn mutum bace ba Kursiyya. Kin zarce duk tunanina. Duk hatsabibancinki ban zaci zaki zo nan da nufin Iubbata ta ba. Ya aka yi kwakwalwarki ta dode har kika yi zaton ba zan gane komai a kanki ba?”
Da sauri da sauri sukejin gabansu na faduwa. Tun ma kafin aje ko’ina baki daya abin ya
Ialace musu. “Zan kaiku hargaban Uwar biyu. kaman yadda kuke so. Ku tashi mu tafi.” Zare idanuwa sosai Kursiyya tayi. “Me kike nufi? damu Sarauniya Maimounatu? Bayan duk kin san abin da nazo yi din kuma zaki kai mu inda babu wani mahaluki da zaije wurin ya
da wo da ranshi?”
Dariya sosai Sarauniyar tayi, wacce ta dade bata yi irinta ba. “Tun ban taba ganin ki ba na sanki Kursiyya, na san makirCI da hatsabibancinki. Zan kaiki gaban Uwar biyu ba don ni kaina na san daIilin hakan ba. Sai dai inaji ajikina wani abu zai iya faruwa. Ku tashi mu tafi.”
Babu musu suka Mike. Sai dai hankalinsu sosai a tashe yake. Ta mika hannunta daya ga KurSIyya daya ga Zabbau. A take suka bace daga dakin.
Wani irin gunji-gumji suka rinkajI a Iokacin da suka bullo cikin dajin da babu alamun akwai abu mai rai a cikinsa. Suka karisa bude I’danuwansu, saiga namun dawa a gabansu. Da zaki Kursiyya ta fara arangama. Cike da kidima ta kudundune a jIkin Sarauniya Maimounatu. “Ki taimake ni karya cinye ni.” lta ma Zabbau ta kudundune Sarauniya Dariya kawai tayi tace “Babu abin da zasu yi muku tun da tare nake da ku. Da dai ku kadai kuka zo da yanzu babu k0 bishi bishinku. Ku saki jikinku kawai mu karisa bukkar Uwar biyu. Duk da sunji ta fadi hakan amma hankalinsu baigama kwanciya ba. A hankal: suke takawa, rike dajikin Sarauniya Maimounatu.
A gaban wata bukka suka Isa, wadda a kiyasce sai suce ba zata iya daukarsu ba saboda karanta. Sai dai suna shiga ciki sai suka ga sabanin haka, Wani irin girma gare ta mai ban mamaki. Gadon kara ne guda uku ajere, sai tabarmar kaba daga gefe a shimfide.
“Ku zauna inje gidan kasa in kira ta.” Sarauniya Maimounatu ta furta hade da sakar musu murmushi.
Wannan dakin ba kadan din tsorata su yayi ba. Abubuwan al’ajabi da ban mamaki ne sosai a cikinshi. To sai kin dawo.” Kursiyya tayi kalan halin fadi, jIkinta sai faman karkarwa yakeyi. Babu jimawa Sarauniya ta dawa ta zauna. Saiga Uwar biyu biye da ita. Tsohuwa ce sosai mai dan karamin jiki. Gashin kanta hargadon bayanta. Fuskanta cike da saje tsage. Da gaske Uwar biyu ba mutum bace. Saboda kallon halittarta kadai zai tabbatar da haka. Bata zauna ba sai da ta zagaye su har sau uku, sannan ta dafa musu kawuna ta saki dariya mai karfi, ta koma ta zauna. “Kursiyya da Zabbau. Yunwa ma kukeji k0? Malmoon me yasa baki sa an basu abinci ba kafin ku taho?”
Cikin mamaki Kursiyya da Zabbau suka kalle ta. Yun wa sukeji sosai, rabonsu da abinci tun a kan hanya da suka ci. Sai dai kuma ba abun mamaki bane, laakari da cewa ita mayya ce.
“Kursiyya matar Sarki Sani, uwa ga Gimbiya Hafsa. Muguwar mace mai tarin mugun abu a cikin zuciya. Da gaske a kalar bil,addama ban taba sanin akwai irinki ba. Ban taba sanin akwai wacce za tayi tunanin fafatawa dani ba. Ke, ban ma san akwai wacce ta san ni ba.”
Kursiyya sai faman kyakkyaftun ido take yi kanta sunkuye cike da tsoro. ”Kursiyya ‘yargidan boka Fartsi.“ ta kuma sakin dariya Kursiyya ta zabura ta hada Ido da Uwar biyu. “Boka Fartsi na da dadadden sani a wurina wanda shi kanshiyake tsoron arangama dani. Shi ya baki Iabari a kaina k0? Don yafi kowa sanin kaidina. ” Ta sake kyalkyacewa da dariya. Yar karamar mace amma sai shegen dariyar tsiya.
“Ba shiya fada miniba Uwar biyu. Sai dai shiya fadada mini bayani a kanki.” KurSiyya ta amsa cikin rawar murya.
“Kursiyya zan yi amfani dake ta hanyar gumawa Boka Fartsi takaici. Dake zan cusa mishi
haushi. Akwai wani aljanina da nake mugunji dashi, amma sai da Boka Fansi yayi yadda
zaiyi ya rabani da aljanin nan. Naji haushi sosai. Duk kanrfin tsafina baiyi tasiri ba. Bai sa aljanina ya dawo gare ni ba.
Kursiyya, idan har kika goyi bayan wannan abun dari bisa dari na miki alkawarin wani abu. Zan zama jagararki a dukkan komai. Zan zame miki garkuwa. Zan zama mai cika miki burikanki. Zan amsa duk wata bukata taki.” Murmushi Kursiyya tayi jin hakan. Tace na amince Uwar biyu.” ta gaggauta fadi. Zabbau ta kalle ta ta zaro idanuwa, tana tuna ranar da Kursiyya tama boka Fartsi alkawarin ba zata taba butulce masa ba.
“Wane abu ne Boka Fartsi ya taba yi Wanda kike tunanin idan babu shizai shiga kunci? Ina
nufin wani aiki nashi da yayi maizafi.” Shiru jim, Kursiyya tayi kafin hali tace”Akwai aiki da ya taba yi min a kan wata mata, matar mijina. A yanzu haka tana gida acikin ban dakin dakina. Duk wani tsafi? nashi mai karfi yakan sani in taimaka mishi da wannan matar, saboda tana tattare da abubuwan da yake da bukata sosai a tsafinshi.” “Da kyau.“ Uwar biyu ta furta bayan ta mike tsaye. Ta hau jeka ka dawo a cikin dakin. Kafin tace “Zan yi maganinshi da wannan. Zan mamaye daidai inda take. Zan hana shi ganin ta, zai dauka cewa bata wurin ma duka. Da wannan ne kadai zan iya rama abin da yayi min.” Kursiyya bata damu ba sam. A ganin ta me ake ci da boka FartSI bayan ga Oganniya ta samu? Ta saki murmushi. “To amma Uwar biyu me yasa yake jin tsoronki sosai.”
Uwar biyu ma ta saki dariya. “Na fada Miki tsaron kaidina yake Yana tsoron ya shigo hannuna,ne ya san abin da yayi min.”
Kursiyya na son yin wata magana amma ta kasa, bakinta sai matsiyake yi. Tana son fadi amma tana jin tsoro don bata San abin da zai faru ba. Sarauniya Maimounatu tayi dariya tace “Bakinki yana motsi Kursiyya. Ban san me zaki fada ba. Kina son yin magana ne a kan halin da ‘yarki take ciki ko? Nice nan na mata. Shekara nawa da auren Gimbiya Jiddah da Yerima Bukar ko bari bata taba yiba. Amma daga zuwan diyarki Hafsa ta samu. Juna kina tsammanin sai in bar shi?” Tsoro sosai Kursiyya taji. Ta kasa fadin komai sai mazurai. Take