GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 6
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 6
“Sharadin ai ba wani mai tsanani bane. Mallam Khamis ya fadi hakan tare da sakin murmushi. Yaci gaba da fadin, . “Zan mata aiki, matukar bata da alhaki a abun.” .
Cike da mamaki Waziri ya kalle shi. Bai gane inda sharadin ya dosa ba. Hakan ya sa ya tambaye shi,
“Allah gafarta mallam, alhaki kamar ya kenan?” Mallam Khamis yace, “Kamar yadda na san halin Kursiyya, haka kai ma ka sani. Ta yiwu wani ta zalunta shine abin ya koma kanta. Amma fa ba wai nace dole haka bane. Zan iya ganewa matukar hakan ne.
Da fara,a a fuskarsa kamar koyaushe ya hau tattara karikitan gabansa, sannan ya gyara lagen rawaninsa, saboda yanayin sanyi da ake ciki.
“Tafaddwal Yallabai.” .
Mallam Khamis ya fada bayan ya mike. Waziri ma mikewar yayi shi da mutum biyun da suke tare.
Dafda magrib suka isa gidan sarki. Ko da suka isa fada mai martaba baya nan. Dama waziri ya kawo hakan a ranshi, saboda tsananin rudewar da mai martaban yayi, baya jin cewa zai iya zaman fada yau. ‘
Masallaci suka fara dosa, sai da suka yi sallah sannan suka isa bangaren Sarki Sani. A bakin kofa masu tsaron kofar suka tabbatar musu da cewa mai martaba baya ciki, yana bangaren Kursiyya tun dazu. Hakan yasa suka juya akalar tafiyar su, suka doshi bangaren
Kursiyya. Afalo suka samu mai martaba, tare da fadawan da akalla zasu kai mutum takwas zuwa goma. Yana ganin su ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sannan ya mike tsaye, ya mika
hannunsa na dama ga mallam Khamis tare da yin musabaha. ‘ “Barka da zuwa Allah gafarta mallam. Mu isa daga cikin dakin da take k0?” Babu musu yabi bayansa tare da waziri kawai, suka karisa cikin dakin. Sosai Kursiyya ta fige a yini guda, tamkar zautacciya haka ta koma. Musamman ma idan aka yi dubi da kanta da yake kwa-kwal babu ko disin suma a kai. Da kuma yadda bakinta ya karkace, tana fitar da ruwa mai matukarwari. ‘
Tun daga isar shi dakin Mallam Khamis ke kallon Kursiyya. Tana hada ido da shi tayi saurin janye kallon ta daga gare shi, hade da sunkuyar da kanta kasa tana watsa idanuwa. ‘
Murmushi Mallam ya yi hade da gyada kansa. Yace, “Babu gaskiya a nan waziri.”
Mai martaba bai fahimci komai ba sai waziri. Waziri yace,
“Kamar ya babu gaskiya Allah gafarta mallam? Na gafa shigowar ka kenan.”
“Hmm! Kasa hada ido da Kursiyya tayi da ni kanshi wani tabbacin rashin gaskiyar ne. Amma ina zuwa. Ina ne ban- dakin nan? Zan sake alwalla, akwai abin da zanyi.”
Da jin Mallam Khamis ya fadi haka Kursiyya ta gaggauta mikewa hartana cin tuntube. Magana take kokarin yi amma ta kasa. Sai dai da hannu take masa nuni da kar ya shiga. Sannan a karshe ta koma bakin kofar ban-dakin tayi tsaye cak, tana sauke ajiyar zuciya. Wani murmushin Mallam Khamis ya sake yi. “Babu abin da zanyi abandakin dama. Na yine kawai don in gwada ta. Kun ga dai alamun Kursiyya bata da gaskiya ke nan. Idan ba haka ba, me zai sa ta hanani shiga duk da kuwa cewa ita nake kokarin nema wa lafiya?” Sosai waziri ya gamsu. Sai dai ya rasa gane dalilin da yasa Kursiyya za ta yi haka. Tun da suke a gidan babu wanda zai ce ga ranar da ya leka wannan bandakin na Kursiyya. Sai dai ita da Zabbau kacal. “Yallabai ni zan tafi. Sai dai ko a gwada zuwa wurin wani malamin wata kila a dace. Ni dai bana goyon bayan zalunci, haka kuma ba na zalunci. Ayi mini afwa ranka shi dade. Na barku lafIya.”
Ya bar wurin sarki da waziri cike da mamakin abin daya faru. A zahirin gaskiya shi kanshi sarki ya san cewa Kursiyya bata da hali. Sannan kuma yanaji ajikinsa akwai wanda ta aikata ma wani abu shine abun ya dawo gare ta. Musamman ma da abun bai tsaya a kanta ita kadai ba har da kawar shaidanancin tata. .
“Ai shi kenan. Waziri yanzu miye abun yi?” Shiru waziri ya yi, kamin yace, “Yallabai dama dai Mallam Khamis ne kadai nake tunanin samun mafita daga gare shi, to kuma ga abin da ya faru. Ni ina ganin me zai hana a hakura kawai a zuba wa sarautar Allah ido? Insha Allahu zata samu lafiya.”
Cikin gyada kai sarki ya ce,
Haba waziri! Taya kake tunanin zan iya barin matata taci gaba da rayuwa a haka babu
magana? Kaji yadda wari ke futowa daga gare ta. A haka za tayi ta zama waziri? Don Allah ka kawo wata shawarar mai bullewa.” “To yallabai, insha Allahu zuwa gobe zan duba, zan san abin yi. Sai kuma mu dukufa da addu’a. Allah ya ba ta lafiya.”
Cikin sauri ya fadi maganar, sosai ya matsu ya bar dakin, ko don tsananin warin da dakin keyi‘ A nan suka tafi suka bar su, sannan aka kawo musu abincinsu na dare ita da Zabbau.
Basu bari kowa yaga komawar su gidan ba. Kai tsaye suka nufu sashen Kursiyya, Zabbau na fadin, “Na yarda da boka Fartsi. Na tabbata in dai an aiwatar da aikin nan a yau, to a yau din zai mayar dake dakinki. Hehehe Ai babu wadda mai martaba zai iya rayuwa da ita sama dake. Ehh, ki kwantar da hankalinki rankishi dade.” Sassanyan murmushi Kursiyya ta saki. Shiya sa take kaunar Zabbau da zuciya guda. Tana son ta da alkhairi, ba tun yau ba, tsawon shekaru da dama na daga rayuwarta. ‘ A dakinta suka yada zango. Jikarta ta ajjiye kasa, sannan ta saki nannauyar ajiyar zuciya. Jikar tata ta zuge, ta fiddo silin akaifar da boka Fartsiya bata, tace,
“Zan aiwatar yanzu. Ki samu don kar,a gane wani abu. Ki turo min Shafa da abinci.”
Mikewa Zabbau tayi ta fita, Kursiyya kuwa ta shiga asirtaccen bandakin nata, wanda ita kadai ta san abin da ke cikinsa. Tajima a ciki kafin ta fitoo fuskarta cike da zufa, sai sauke ajiyar zuciya take yi.
Zaman ta kenan Shafa ta shigo dauke da wani babban tray, wanda kekunshe da kuloliguda uku masu matukar kyau, da wasu kuyangu biyu biye da ita; guda ta riko kwandon kayan marmari, gudar kuma ruwa ne da Iemuka iri-iri a hannunta. Bayan sun ajje suka gaishe ta cike da girmamawa, sannan suka nufi hanyar fita. A kofarsu ta fita daga sashen duka ne suka hadu da Haroun ya tambaye su Kursiyya na ciki? Suka amsa masa da ehh. Shafa ya umurta kan ta shiga ta shaida mata cewa mai martaba na neman ta, yana
sashensa, yace yanzun nan taje. Da saurin Shafa ta koma ta sanar da ita. Murmushi Kursiyya ta saki, maikunshe da ma ‘anonin da ita kadai ta barwa kanta sani. Sannan tace ace dashi tana zuwa. Ta tabbatar cewa aikin boka Fartsi ne yayi tasiri. Takudira a ranta ba zataje yanzu ba, sai ta
gama ,,,,, masa aji sannan. Kayan marmarinta ta hau sha sai murmushi take sakarwa kanta. ‘
Da kyar take dibar abincin tana kaiwa bakinta. Fiye da rabin wanda ta dibo zubewa kasa yake yi, saboda yadda hannunta yake kyarma. Bayan ta gama duka ta ture shi da kafa, ya isa hargaban Zabbau. Mai hali dai ba ya barin halinsa. Atunanin Zabbau Kursiyya zata matso kusa da ita ta bata abincin a baki, saboda tsananin yunwa takeji, har tana jin kamar babu kayan ciki a cikin cikinta. Bata san yadda za tayi taci abincin ba, sai cewa tayi “Ranki shi dade ki taimaka mini ki bani a baki. Yunwa kamarza ta kashe ni.” Wani irin mugun kallo Kursiyya tabi Zabbau dashi. lnda tana da bakin magana a lokacin watakila sai ta zagi Zabbau din. Sai dai kuma a yanzu kam babu.
A cikin wannan halin da suke suka fara jin wata irin tsuwwa a hankali, tun daga nesa take tasowa, har ta fara karisowa inda suke. Gabansu ne ya hau duka, yayin da fitsari ya fara
sauko ma Kursiyya a wando. Ta tsakanin ginin dakin wata bakar mage ta ratso, mai jajayen idanuwa, sai bindinta mai matukar tsawo. Halittar magen babu wanda zai ce ya taba ganin irinta a duk cikinsu. Kallo daya mutum zai mata hankalinsa ya nemi gushewa. Musamman kuma idan ta bude bakinta, zara-zaran hakoranta suka bayyana, harshenta mai tsananin tsawo ya sauka har bisa kafafuwanta. Ga kuma tsuwwar dake fitowa daga cikin bakin nata.
Da gudu Kursiyya ta isa inda Zabbau take. Tana son tsala ihu amma babu bakin magana. Zabbau ma dake da bakin kasa fasa ihun tayi, ga kuma magen sai dada kusanto su take yi.
A lokacin data iso daf dasu ta tsaya cak Taci gaba da zura musu idanuwanta masu ban tsoro. Harshenta ta sake zurowa ya isa daidai saitin Zabbau. A take ta warware daga halin da take ciki, ta dawo zaune daram, tamkar babu abin da ya taba samun ta.
A hankali ta fara mikewa tsaye, har ta koma fasalin aljanar nan. Da karfi ta tulle da dariya, kam cikin mummunan sautinta madukaki ta fara watso kalamanta masu matukar razanarwa.
“Kar kiyi tunanin kin kubuta Zabbau! Karki taba ‘sammanin na gama da kene. Ina so ku saka a ranku cewa bama mu fara wasan ba. Ku saka a ranku cewa sai rayuwarku ta
muzanta, sai tafi tawa rayuwar muzanta.” Tafin hannunta ta saita daidai fuskar Kursiyya, sannan ta sake saita shi a fuskar Zabbau. Haske ne ya fito a idanuwansu. Sannan suka mike, suka rinka bin ta a baya, tamkar wanda remote kejuya su. Kamar yadda aljana Sadiyya ke taku a hankali, haka suma ke takun a hankali, kuma har yanzu hasken bai fice daga idanuwansu ba.
Lokacin da ta isa bakin ginin saita sake canza halitta, ta koma halittar magen nan ta dazu. Daga bakinta ta feso musu wani abu, sannan ta bace. Tana bacewa suma suka bace. A wani kasurgumin daji suka bullo, wanda babu alamun akwai halittar rai a cikinsa. Sai daidaikun tsirrai jefi-jefl, wasu sun fara bushewa, wasu kuma a lokacin suka dasa fitowa. Sadda suka bullo suna ganin haske, amma cikin kankanin lokaci haske ya bace bat, wurin ya zama duhu dundum, wanda ko tafin hannuwansu ba zasu iya gani ba. Kursiyya ta fara jin an jawo ta da karfi, kamar an zira mata kaca a wuyanta. Da karfi ake fisgar ta, yayin da akejan ta a kasa, kururrubai na gurzar ta, hakukuwa na cakar ta. Ihu take sonyi babu hali. Sai wata irin gumza da take saki tamkar tsohon ragon daya shekara baici abinci ba. Azaba takeji wuyanta na mata zafi, ga matsarta da karfen yayi a
wuya.
a Abangare Zabbau kuwa can aka bar ta. Sai dai wani irin radadi da takeji saboda wutar da takejin ana yayyafawa a jikinta. Ihu take mai hade da kururuwa, tana murzar jikin nata da hannuwanta, duk inda ta gurje sai ya gwalje, saboda kunar da tayi. Idan ta runtse idanuwanta sai ta rinka ganin mugayen namun daji na tinkaro ta, suna bude bakunansu tamkar zasu hadiye ta. Idan kuma ta bude sai ta rinkajin wani irin ruwa mai zafi na fitowa daga cikin idanuwanta. Tama rasa me zata yi taji dadi. Azabar duniya ta ishe ta. Ji take dama mutuwa tazo ta dauke ta a daidai wannan lokacin, da ta ji dadi sosai. Kursiyya kuwa wani wuri aka kai ta aka ajje, wurin na kama da tsohon ginin da yayi shekaru ba a shige shi ba. Bata iya gane komai dake wurin, kasantuwar tsananin duhun dake akwai a cikinsa. Ta jima a wurin tana sauke ajiyar zuciya, sannan haske ya bayyana a wurin. A take sai ga boka Fartsi ya bullo gabanta. Yana sakin wata irin muguwar dariya, dukkanin gabban jikinta na amsawa, sai dai ko alamar dariya babu a fuskarsa. Ya dauki kimanin minti talatin yana dariyar, kafin ya tsaya cak daga yin ta. Wurin yayi tsit, babu wanda zaice akwai mai rai a cikinsa. Yar yatsarsa karama ya soka daidai bisa cibiyarsa, ya lakuto wani bakin abu daga cikinta. Ya matso daf da Kursiyya, ya singa yatsar daidai makoshinta, sannan cikin mummunar muryarsa yace, “Yi mini magana Kursiyya. A zaton ki ana cin amanata a zauna lafiya ne?”
Bata taba tsammanin maganar zata fito ba, saidai tana yi taji kamar wasa maganarta ta fito. “Kayi mini gafara boka Fartsi. Nayi nadama!” Ya sake tuntsirewa da wata dariyar da karfi, yana sake bin Kursiyya da kallo.
Yace”Kursiyya ki sani, rayuwa da komai naki yanzu sun dawo a karkashin ikona. Idan da kin kawo yarinya, wacce bata da alhakin komai, an azabtar da ita, an cutar da ita, to yanzu abin ya juyo gare ki. Reshe ya juye da mujiya. Na rantse da bokancina da nayi gado a wurin Babana Shazbu, sai na lalata miki rayuwa. Gimbiya Sadiyya da kanta zata kwatarwa kanta fansa, kamar yadda kika ga ta fara yanzu. Ina so yanzu idan na mayar da ke, ki bayyana komai a fada. Ki tona ma kanki asiri a idon duniya; tun daga kan abin da kika aikata ga mahaifiyar Gimbiya Sadiyya, har zuwa yanzu. Idan kuma ba haka ba…” “Karya kake yi boka Fartsi!” Kursiyya ta fada da karfi hade da zaro idanuwanta. Shi kanshi bokan sai da yayi mamaki. Halin Kursiyya ya sha bamban da na sauran mutane. Ko kadan Kursiyya ba ta da tsore. A zaton ka don ka ganni a haka tamkar na tsorata shi zai sa na karaya? Ban karaya ba, ba kuma zan taba karaya ba. Na san ka boka Fartsi, na san ko waye kai, na san komai naka…” “Naji dadi da baki manta ko waye boka Fartsi ba!” Yayi saurin tarar ta, “Baki manta kaidina ba. Baki manta cewa ni mai aikata duk abin da nace zan yi bane. Bana son kashe ki a yanzu Kursiyya, da tuni kin bakunci lahira. Bana son kawo karshen zamanki a cikin masarautarku, da tuni kin dawo a nan, karkashin ikona. Nafi son komai zai same ki ya same ki a can. Na miki sanya ko? Hahahaha!” Dariya yake mai karfu, sai dai fuskarsa babu annuri ko kadan a cikinta. Kwaryar gabansa ya debo abin dake cikinta, ya watsa shi ga Kursiyya. A take idanuwanta su kajuye tamkar babu kwayar ido a cikinsu. Bakinta yayi tsawo sosai har yana iya tabo habarta. Kunnuwanta su kayi tsawo. Kallon fuskar Kursiyya kadai kan iya jefa mutum a tsananin rudani.
Hmmm