GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 7

GIMBIYA SA’ADIYA 
CHAPTER 7
Cikin takun isa da kasaita ta isa bakin kofar dakin. A bisa al’adardakin sai an cire takalmi sannan a shiga cikinsa. Hakan tayi itama. Ta shiga da isasshiyar tafiyar ta wacce kejijjika kafilahirin gangar jikinta. 
A tafkeken falanshi ta same shi. Ya kishingida bisa tum-tum, idanuwansa na bisa talabijin, yana kallon labarai. Da sallama kunshe a bakinta ta isa gabanshi. Saurin mayar da kallon sa yayi gare ta, ya saki tattausan murmushi, sannan ya tashi zaune. 
“Barka da hutawa mai-martaba.” Ta furta bayan ta zauna kusa dashi. ”Yauwa, sannu Kursiyya.” Ya fada cike dajin dadi da farin cikin ganin ta. “Ka aika a kira ni tun dazu, to kuma ina wani uzurin ne saiyanzu na gama.” Fara ‘a bata kau daga fuskarsa ba, ya ce, “Babu komai ai. Dama tun da naji ki shiru na san akwai dalili.”a “Haka ne Yallabai. Allah daiya sa Iafiya.” Sai da ya dan gyara muryarsa, ya kankance ta sannan yace, 
“Neman afwarki zanyi Kursiyya. Don Allah kiyi hakuri abin daya faru, sharrin shaidan ne. Harga Allah banso faruwar hakan ba. Amma ina so komaiya wuce, hakan ba zata sake faruwa ba.
Sai data saki shu’umin murmushi sannan tace, “Dama dai kai ne ka dauki abin da zafi mai martaba…” “Bana son tashe-tashe don Allah Kursiyya. Kigafarta mini. Komaiya wuce. ” “Komaiya wuce daga gareni‘ ranka ya dade. Sai dai Hafsa, dama ita ce ka bata ma rai.” 
Sai daya dan yi shiru, ya kasa furta komai, da zarar ka kalle shi ka san akwai abin da yake damun shi, sannan yace, 
“T0 yanzu ya kike so a yi?” Ta dan tauni Iebenta, sannan tace, “Hakuri zaka bata.” “Hakuri?” Ya zaro idanuwansa cike da mamaki. 
“Hakuri fa. Haryanzu yarinyar nan bata da walwala tun sadda abin nan ya faru. In banda kuka babu abin da take yi.” 
“Ta amma Kursiyya baki ga kamar raini zaikara shiga tsakanina da Hafsa ba? Dama ba wani kunya ne take dashi ba,” “Hmm! Mai martaba kenan. Amma inda ace Halimatu ce ai ba zakaji komai wurin bata hakuri ba. Ba waiyau aka fara ba. Kai kanka kasan na sha kama ka kana bata hakuri. Amma dayake wannan bora ce, dole kace raini zai shiga.” ‘ 
Jim! Yayi na tsawon lokaci, ya rasa abin dake masa dadi. Bai san ranar da Kursiyya zata so Gimbiya Sadiyya ba. Bai san ranar da Sadiyya za tayi farinjini ba. Shi kadai ke son yarinyar. Wannan dalilin ne yasa yake fifita soyayyarta a kan kowa. Yake kokarin ninka kaunar da yake mata, har da ta uwa data rasa tun tanajinjira. Idan babu wata maganar ni zan tafi.” 
Maganar Kursiyya ta dakatar da shi daga tunanin da yake yi. Kaunar da yake yima Kursiyya, da yadda yakejin ta a cikin ransa yasa ya rasa mafita, bai da yadda zaiyu‘, bai da zabin da ya wuce ya amince da bukatarta. Zai ba Hafsa hakuri kamar yadda Kursiyya ta bukata. “Dawo kizauna Kursiyya. Zan ba Hafsa hakuri.” ‘ Dawowar kuwa ta yi ta zauna, tana watsida idanuwanta ga mai martaba, tana yi masa frin kallon dake dada fizgar sa a koda yaushe. 
Hadiminsa dake tsaye can nesa da falon ya kwala ma kira, da hanzarinsa ya iso haryana cin tuntube. Ya rusuna cikin girmamawa, hannunsa a sama alamar jinjina, Yace”Ranka ya dade.”
 “A kira mini Hafsa ‘yarbaba.” Mikewa yayi da hanzarinsa ya bardakin. Mai martaba ya fuskanci Kursiyya da murmushi a fuskarsa, 
“Ba dai Hafsa ’yarbaba kike so inba hakuri ba? To an gama! Yanzun nan zan aiwatar, in dai har hakan zai faranta miki’ rai, ki amince mini ki dawo dakinki. ” ‘Murmushi ta yi wanda har hakoranta suka bayyana, tana murmusa idanuwa cike da 
kisisina. “Me zai hana, ranka ya dade? Ka dai aiwatardin kawai.” Takun Hafsa ne yasa su yin shiru basu kuma furta komai ba, ta nemi wurin zama ta zauna kusa da Kursiyya, kanta sunkuye a kasa, fuskar nan tata ko kadan babu annuri a cikinta. Gyaran murya mai martaba yayi, sannan yace, 
“Hafsatutu ‘yarbaba. To ayi murmushi mana yarlelena.” 
Yanayin yadda yake maganar duk wanda ke kusa da shi dole ya tausaya masa. Magana yake tamkar wani dolo. Ko kadan baiyi kama da sarki ba. Sarki Sani wanda ya gaji sarauta tun iyaye da kakanni. “In a kan abin da ya farune jiya, kiyi hakuri kinji yarlelena? Na miki akawari hakan ba zata sake faruwa ba. Daga yanzu na baki dama, duk abin da kike so ki aiwatar. Ki hukunta duk wanda ya aikata miki ba daidai ba.” 
Dago kanta tayi ta kalle shi cike da mamaki. Ya daga mata kai alamun yana bata tabbaci kan maganar daya fada. In ko haka ne, tabbas ba a haka nan Fulani Kursiyya ta bar mai martaba ba. Akwai dai wani abu a kasa. “Kiyi mini magana ‘yarlelena. Bana son ganin bacin ranki. Kuma na baki hakuri, da izinin Allah hakan ba zata sake faruwa ba.” 
Sai a sannan ta saki murmushi, wanda ya sake bayyana asirtaccen kyawunta. “Babu komai maimartaba, komaiya wuce.” Hannunsa na dama ya mika mata, ita ma ta mika masa nata su kayi musabaha. 
“Kije ki hukunta su na baki dama. Kuma daga yanzu duk wanda ya kawo miki wargi ko rainin wayo ki hukunta shi, da iznina. ” Mikewa tayi a bisa kafafuwanta. Ta fara taku a hankali cike da takama. 
“Na gode sosai rankayadade. Sai dai na tabbata ba za kaji kyakkyawan labari ba…” 
Bai bari ta karisa maganar tata ba yace, “Kar ki damu ’yarlelena. Kiyi komai kike so.” Hada ido suka yi ita da Kursiyya, suka sakar majuna murmushi. Daga nan ta kama hanyar barin farfajiyar dakin, kafarta sanye da rufaffun takalman fata, an kawata su da zanen filawa mai kalar baki. 
Kursiyya ta kama hannun sarki Sani. Cikin salo take tattaba hannun nashi, tana wani Iumshe idanuwa. Ajiyar zuciya sarkiya sauke, yace, 
“Yanzu kuma sai me ya rage?” 
“Na amince ka komar da ni dakina.” “Na dawo dake a matsayin matata.” Ya fada cike da shaukin soyayya. Murmushi ta saki, shi ma haka. Sukaci gaba da Hira mai cike da soyayyar junansu. 
A cikin hirar tasu ne maimartaba ke labarta ma Kursiyya cewa Hafsa ta zabiyarima Abu sufyan a matsayin wanda zata aura, sai dai ba yajin hakan zaiyiwu, saboda ba lallai bane ba yaron ya kaunaci Hafsa, saboda wayewarsa ba zata barshi ya amince da auren hadi ba. 
Kursiyya ta daure fuska babu alamar wargi a maganarta, tace “Idan har Hafsa tace Yerima Abu sufyan takeso, babu makawa dole sai ta aure shi. Babu abin da tilon ’yata zata nunar da tana so wanda ba zata same shi ba.” Maimartaba ya danyi shiru jim, kafin yace “Bani da tabbacin ba zai,amince din ba. Tun da har mahaifinsa ya aiko da hotonsa, ina tsammanin yasan zai amince din ne.” Sai a sannan Kursiyya ta saki fuskarta. “Yanzu naji magana.” 
Ta furta hade da lumshe idanuwanta. 
Da dare bayan Kursiyya ta koma dakinta, Hafsa ta same ta ta hakimce bisa babban kafet, jingine da tumtum, Zabbau daga gefenta alamun magana suke yi. Ja tayi ta tsaya, ta san ka ‘idar  Fulani Kursiyya da Zabbau, matukar suna yinta to babu mai kusantarsu. 
Al’adarsu ce wannan tun ba yanzu ba. Akwai yarda mai tsanani a tsakaninsu. “Shigo Hafsa, ai mun gama.” 
Jin kalaman Zabbau yasa Hafsa karisowa cikin dakin, kanta sunkuye a kasa tana wasa da ‘yan yatsunta. ‘ 
“Gimbiya Hafsa. Tabbas akwai damuwa. ” Kursiyya ta fada, saboda karantar yanayin ‘yarta da tayi cikin Iokaci kadan. 
“Tace Umma, wani mummunan mafarki nayi a daren jiya game da zabina, wanda ya matukar tayar mini da hankali.” Dan taunar lebo Kursiyya tayi, ta kama hannun Hafsa ta zaunar da ita kusa da ita, “Mafarki ai ba gaske bane ‘Yata Hafsa. Kar kiji komai, koma mene ne, babu abin da zai faru. Ba zai taba tabbata ba. ” 
“Umma kina ganin kamar Yerima Abu sufyan ba zaice Halimatu yake so ba?” 
Ido Kursiyya ta zaro, mamakin kalaman ‘yar tata take yi. Wannan wasu banzayen kalamai ne ke fitowa daga bakinta, wanda ba zasu taba yiwuwa ba. Taya tana raye Yerima Abu sufyan dan sarkin Kubaisu zai auri wacce ba ‘yarta Hafsa ba? Kuma ya rasa ma wa zai aura sai Gimbiya sa’adiyya? ‘ 
Ta saki murmushin mugunta, irin wanda take ga kamar abin ba zai taba yiwuwa ba. 
Tace Ban labari ‘yata. Me kika gani a mafarkin?” “Umma…wai fa ita ya zaba da yazo…” 
“Hahahaha!” Kursiyya ta tulle da dariya, Zabbau ma ta taya ta. 

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE