GIMBIYA SA’ADIYA CHAPTER 9

GIMBIYA SA’ADIYA

CHAPTER 9

Washegari da dare bayan Sarki Sani ya nemi ganawa da Kursiyya a turakarsa ne take masa tadin auren Hafsa da Yerima Abu Sufyan.
“Ba na tunanin yaron ya kammala karatunsa fa. Idan ma daiya kammala, to dakyar idan ya dawo gida. Munyi magana da mahaifinsa a waya, yake shaida mini ya kusa kammalawa dai. Amma ban sani ba, dayake an kwana biyu da mukayi maganan”
Shiru Kursiyya ta yi tana wani nazarin, kawai sai zuciyarta ke nunar mata da cewa komaiza suyi kamata yayi a gaggauta, basu san me jinkirin zai haifar ba‘ “Amma Maimartaba, haka zamu zira wa ‘yar nan idanuwa haryanzu babu aure?
Kamata yayi ace mu kokama aurar da ita. Tun da dai ta samu wanda take so kuma me za mujira?”
Hannunsa na dama yasa ya shafi? fuskarsa, ya dan lumshe idonsa ya bude, sannan yace
“Zan yi magana dashi Sarkin Kubaisu din, haryanzu ma ban shaida masa cewa Yerima Abu sufyan ne zabin Hafsa’yarlelena ba.”
Ya dan saki murmushi, irin yana so ya faranta wa Kursiyya ranta din nan, musamman da yaga alamun yanayinta ya dan canza a take. “Yanzu ya kamata ka kira shi, don komai za a yi nafi son a yi da hanzari.” “Yanzu kuma dare ya yayi Fulani Kur…” Ta dakatar da shi tun bai karisa ba.
“Kar muyi haka da kai maimartaba. Ka kira shiyanzu bari in miko maka wayarka. Ba kaji me Hausawa suka ce ba? Da zafi-zafi kan daki karfe. Ka ga yanzu ne daidai ka kira. ”
Duk da bai so hakan amma ba shi da zabin daya wuce ya amince da abin da Kursiyya ke so. Dare ya yi, tun da har tara ta wuce. Ajiyar zuciya kawai ya sauke bayan ta miko masa wayar, ya Iatsa kiran Sarki Kubaisu.
Bugawa hudu tayi da sallamarsa ya dauka. Fuskarshi a sake tamkaryana gaban Sarki Sani din ne. “Rankayadade barka da dare.” Sarki Saniya fada shi din ma yana sakin murmushi. “Yauwa, barkanmu dai rankayadade. Ya gida ya Iyali? Fatan komai Iafiya.” ”Lafiya Iau alhamdulillah, saigodiya. Ya masarautar taku?AIlah daiya sa komai Iafiya,” Sarkin Kubaisu ya amsa da komai lafiya, sannan ya dora da fadin,
“Yau din nan dan naka ya dawo kuwa, har ina batun in turo shiya gaishe ka, daga nan ya duba ‘yan matan wacce ta masa a cikinsu.”
Murmushiya saki najin dadi, kamarya san dama dalilin kiran nashi ke nan.
“Ah to masha Allah! Naji dadi sosai wallahi. Allah ya albarkaci karatun nashi, ya albarkaci rayuwarshi baki daya. “Ameen rankayadade. Idan ya huta gabe, jibi insha Allahu zan turo shi. Zanyi magana da shi goben, na tabbata ba zai bada min kasa a ido ba. ”
Sarki Sani ya murmusa, harga Allah yaji dadin kalaman na abokinshi’. Sai daikuma gabanshi ya fadi, jin cewa bai fada ma Yeriman cewa Hafsa ce aka zaba mishi ba.so alama dai a cikin ‘yan matan biyu ne ake so ya zaba. Yana son Halimatu so mai tsanani. Sai’ dai yana guje mata wahala. Sosai yake guje mata halin da zata shiga ciki matukar Yerima Abu sufyan ya zabe ta bai zabi Hafsa ba. Sauki guda ya samu a zuciyarsa, yadda Halimatu ta kasance mai bakinjini, ya tabbata Yeriman ba zaizabe ta ba. “Rankayadade Iafiya dai k0?”
Dirar maganar Sarkin Kubaisu yaji a kunnuwansa, ita ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula.
“Uhmm…lafiya…lafiya Iau rankayadade. Dama kiran ka kawai nayi mu gaisa. Na gaishe ka,saida safe, na gode.
“Ni ke da godiya sosai. Na matukarjin dadin wannan zumuncin. Ina fatan kulla yaranmu auratayya ya kara mana dankon zumunci da kusanci dajuna. Sai da safe. A gaishe da iyalin.”
Bayan sun yi bankwana ya kashe wayar, ya sakar ma Kursiyya murmushi hade da fadin, “Yanzu shi kenan ai k0?” Ta murmusa ita din ma,tace “Shike nan kam. ” “To ma sha Allah!”
Ya fada cike da farin cikin Kursiyya kuwa ta fada duniyar nishadi. Kallon ta kawai idan mutum yayi zai tabbatar cewa tana tsaka dajin dadi. Ita kuwa babbanjin dadinta shi ne ta faranta ma Hafsa rai.
Washgari Sarkin Kubaisu ya kira mai martaba sarki Sani, ya bashi tabbacin gobe da safe Yerima Abu Sufyan zai taso daga Kubaisu. Sosai Sarki Saniyaji dadi, sannan a karshe suka yi sallama. Lokacin da ya fada wa Kursiyya yadda suka yi, ba karamin dadi taji ba. Daga nan ta fara shawara da zuciyatta, na irin tarbar da za suyi ma Yeriman, ko don ‘yarta ta kara yin daraja a idanuwansa.
A dakinta ta aika aka kira Zabbau, bayan ta iso Hafsa ma ta iso. Cike da faraa ta ce,
“Gabe i warhaka Yerima Abu Sufyan angon ‘yata Gimbiya Hafsa yana nan gidan,zaizo ganin kyakkyawa kuma ’yarlelen Sarki Sani.”
Ido bude cike da farin ciki Hafsa ta rungume Kursiyya, tana tsananinjin dadi a cikin zuciyarta. “Umma…da gaske gobe Yerima zaizo?” Kai Kursiyya ta daga, tana mai tabbatar mata da maganar.
“Umma ban ma san me zanyi ba, gashi kuma ban shirya ma tarbar sa ba. Mene ne abin
yi?” Murmushin kasaita KurSIyya tayi,
“Karki damu ‘yata. A cikin yinin yau komai zai iso, ina nufin kayan adonki. Ina so kiyi kwalliya wacce za ta tayar wa Yerima Abu Sufyan hankali. Kwalliyar da dukkan namijin da zai ganki sai kin shiga zuciyarsa, kin yi fatali da duk wata macen da yake so.”
Hafsa ta kara kankame Kursiyya, tanajin nutsuwa na sauka sosai a cikin zuciyarta.
“Zabbau na bar ragamar komai a hannunki, na dangane da kayan ciye-aye. A tabbatar da an shirya komai a cikin tsari. Ina so ko da Yerima Abu sufyan zai iso an gama shirya komai, don ya tabbatar cewa yazo masarauta maigirma da daraja, saboda ’yata ta girmama a cikin zuciyarsa. ”
Tun daga nan shirye-shiryen tarbar Yerima Abu sufyan suka kankama. Da yamma Iikis wata mata maizubin Larabawa ta iso masarautar Sarki Sani, biye da ita yaranta ne maza da mata mutum biyar, kowannensu dauke da babbarjaka. Kai tsaye Zabbau ta musu iso zuwa bangaren KurSIyya, domin dama ta san da zuwansu, su ne zasu kawo kayan da za a zabar wa Gimbiya Hafsa.
Fiffiddo kayan aka yi daga cikinjaka, sannan Kursiyya ta umurci Zabbau da ta kira Hafsa, ta zabi wanda take so
Ba tajima ba ta shigo dakin fuskarta kunshe da murmushi, Zama tayi, daga inda take yaran waccan matar suna daga mata kayayyakin tana gani. Duk wanda aka dago sai tace besu mata ba, har aka zo kan wata gwaldin din riga, wacce taji adon duwatsu masu
matukar kyalli da daukar ido. Tana gani tace su ajje a kusa da ita, sannan suka cigaba da daga wa.
Wata alkyabba ce baka ta zaba a karshe, wacce ta kure duk wani kyawun da ake bukatar akyabbar yar sarki ta kasance.
Daga karshe bayan an sallami matar suka yi magana cewa da safe za ta turo wacce zata
shirya Gimbiya Hafsa, ta yi kyau sosai.
Tun safe Gimbiya Sa’adiyya ke kwance bisa gadonta, ba taje k0 ‘ina ba sai dai idan lokacin sallah yayi ta tashi tayi. So take taje dakin Hafsa ta gaishe ta amma tana tsoro. Saboda abin nata kara yawaita ma yakeyi. Tsanar data mata a kullum ta ‘azzara takeyi.
Hannunta tasa ta share hawayen dake binta, a bayyane ta furta,
“Ya Allah ka kawo mini karshen wannan halin da nake ciki. Rashin uwa cuta ne…”
Ta fashe da kuka mai cin rai, tanajin kewar mahaifiyarta na shigar ta. Duk da ba ta san dadin uwa ba, ba ta san komai game da uwa ba, shayarwa mai raino ce aka kawo ta shayar da ita tun tana ‘yar watanni shida da mahainyarta ta rasu.
Allah ka yaye mini wannan muguwar tsanar da kowa ke gwada mini, ya Allah ka kawo
ranar da nima zan zama wata abar alfahari, wacce kowa zai kaunata. Allah ka sani bani da
mugun kuduri game da kowa. Zuciyata fes take da kowa. Ba na nufin kowa da sharri. Amma niga ni bani da mai sona sai mahaifina.”
Kuka sosai takeyi, wanda ya haifar mata da zafinjiki, jijiyoyin kanta duk suka mike.
Motsin kofa taji alamar ana kokarin shigowa, hakan yasa ta gaggauta shanye hawayenta. Ba ta dago kanta ba, sai dai ta sani k0 ma waye ba zai wuce Gimbiya Hafsa ko kuma Zabbau ba. Su din ma kuma ba alkhairi ne tafe dasu ba. ldan har aike ne daga mai martaba ba za a shigo ba, sai dai daga bakin kofa ‘yar aiken ta isar da sakon.
Taku taji a hankali, da alama maiyin takun ko kadan bata son taka kasa, kamar dole ya zame mata.
Ji tayi an bubbugo ta a hankali, hakan yasa ta dago kanta, ta murza idanuwanta da suka kada suka yijajur, tana bin Fulani Kursiyya da kallo. Sanyin hali irin na GIMBIYA Saadiyya, sai ta saki murmushi hade da furta,
“Ga wurin zama Umma, kizauna.” Ko kadan babu annuri a fuskar Kursiyya bare har Halimatu tasa ran da alkhairi ta shigo. Ta zauna a bakin gadon dafda Saadiyya.
Tashi ki rufe mini kofar can da na bari a bude.”
Taji KurSIyya ta fada cike da izza da takama. Da saurin ta   ta mike ta rufo kofar, tanajin yadda gabanta ke tsananta faduwa. Ta tabbata sai ranta ya baci kafin Kursiyya ta bardakin, sanin halinta da tayi, cewa abin arziki baya hada su.
“Halima! Halimatu!! Halimatus-Saadiyya!!! Sau nawa kikaji na kira sunanki?” Kanta sunkuye tanajin yadda hawaye suka taru a cikin idanuwanta tace, “Sau uku.” “Dakyau.” Kursiyya ta fada, ta dora da,cewa
“Umarni nazo baki, ba neman shawararki na zoyi ba, sannan kuma ba rokanki na zoyi ba. Ki saurare ni da kunnen basira”

Hmm ko wanne irin umurni ne wannan
Muje zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE