GIMBIYA SA’ADIYA COMPLETE

GIMBIYA SA’ADIYA 





CHAPTER 28




Yana hada kayan hawaye na sauka a kumatunshi. Cikin sanyin jiki ya kammala duka. Ya fara kokarin‘jan trolley dinshi. Kamar daga sama ya farajiyo sauti na tinkaro inda yake. Can kuma saiga haske ya bayyana. Ya runtse idanuwanshi, sai yanzu ya tuna da zuwan da tsuntsu ya mishi kwanaki. Ko daya bude idonshi kuma saiya ga tsuntsun nan na ranan a gabanshi, ya tsura mishi jajayen idanuwa. 
“Ni dai don AlIah ka fitar dani daga wannan maganar. Mu mika komaiga Allah. Da alama babu wanda zai saurare ni. Kursiyya ta riga data gama da kowa saiyadda tace. Ba najin wata magana ta wa zatayi tasiri, bama za a tsaya a saurare ni ba bare har a yarda cewa da hadin bakin Fulani Kursiyya a wurin mutuwar Gimbiya Sa’adiyya.Tsuntsun bai ce komai ba saijefo ma Abu Sufyaan takarda da yayi kaman yadda yayi na farko, sannan ya tashi ya mamaye da haske ya bar dakin. Sai da Abu Sufyan yasa tafin hannu ya shafe fuskarshi sannan ya ambaci sunan Allah ya dauki takardar. Wannan din ma da ajami aka yi ta. Ya fara karantowa, “Alhakin Gimbiya Sa’adiyya ba zai taba barin duk wani da yake da hakkinta ba. Kar damuwar da kake ciki tasa kajanye jikinka daga kokarin tabbatar da gaskiya. Sai dai ba zanga Iaifinka ba idan kayi kokarin janjikin naka. Albishirguda daya ne tak zanyi maka. Sa’adiyya bata mutu ba. Kurwarta tana wurin wani gagarumin boka. Gawarta kuma tana tare da mahaifiyarta ana tsaface su. Duk daren dadewa zata dawo. Naso ace nayi iya kokarina amma ba zan iya ba, aikin yafi karfina. shi yasa na sako ka a ciki ka taimaka mini mu yi tare ko da karfun adduoi ne.
Sunana Suad, ni aljana ce. Nayi 
alkawarin zan cigaba da bibiyar al’amarin Gimbiya Sa’adiyya harzuwa ranar da zata kubuta. Ina maka fatan alkhairi dare da rana.” 
Yana kaiwa karshe a karatunshiya sauke nannauyar ajiyar zuciya, ya share hawayen daya sake sauka mishi. Sosai yake alajabin wannan abu, yana nanata kalaman cikin wasikar. “Komawa yayi miki wannan abu Allah yabi miki hakkinki Halimatu. Allah ya kawo ranar 
da wannan gaskiya zata bayyanu a gaban al,umma.” 
Yajawo akwatin nashi hade da ficewa yabar dakin. Ko da yajeyiwa maimartaba bankwana ko kallon arziki‘bai samu ba. Ya samu daiya amsa gaisuwarshi sannan ya mishi 
fatan sauka Iafiya. Ya koma wurin Fulani Maryama. “Fulani har na fito ma tafiya.” ta kalle shi cike da kulawa. “Tun da sassafe haka?” Ta fada tana kalIon shi da murmushl’ kunshe a fuskarta. “Tunjiya na samu na kammala komai, da karfe goma na safen nan jirginmu zai tashi. Na kira Jaheed zai kaini filin jirgi, harma ya iso 
yana waje zaman jirana.” Isowa ta yi ta shafa kanshi, “Ina maka fatan alkhairi dare da rana. Allah ya kaiku Iafiya ya dawo min da kai cikin aminci. Ayi karatu sosai, sai wani Iokacin.” “Ameen Fulani. Na gode sosai.” 
Haryajuya ya tafi ta kira sunanshi’. “Kayi wa mahaifinka sallama dai k0?” Ya amsa da “Ehh can na fara zuwa sannan nazo nan.” “To A1hamdulillahi.Allahya kiyaye hanya.” Ya fice zuciyarshi cike da kunci. Baya son tafiyar amma dole ta zame mishi. Yanaji a ranshi watakila idan ya tafi yayi nisa da kasar zai samu sassauci a zuciyarshi. Kunci da damuwarshi za su tafi. Sannan a wani bangaren kuma kila idan yayi nisa da maimartaba zaiyafe mishi Iaifin daya tafka. Yana fita daga dakin Fulani Maryama Jaheed yaja akwatunanshi guda biyu suka tafi. Yerima Bukar cike da farin cikin takaicin da Sarki Abdurrahmanu ke kunsa wa danlelenshi 
Tun daga lokacin da Sarki Saniya sanar wa Kursiyya maganar auren Hafsa sai suka hau shirye-shirye. Sune can sune can wunin Siyayyar abubuwan aure. Maigyaranjiki ma ta musamman aka dauko tun daga Sudan domin ta gyara amarya Hafsa. lta kuwa amaryar sai rawarjiki take zata zama amarya ga rabin ranta, abar kaunarta Yerima Abu Sufyan. 
Ana gobe daurin aure maimartaba Sarki Sani na dakinshi duk abin duniya ya dagule mishi Kursiyya ta shigo. Da sauri ta zauna a gefenshi. “Ranka ya dade lafiya dai na gan ka kamar a cikin halin tunani?” 
Yayi saurin daidaita nutsuwarshi. “Lafiya kalau Fulanina. Kawai dai na tuna da Gimbiya Sa’adiyya ne. Da yanzu ita ce ake tayi ma hidimar nan, k0 kuma ince da tuni ma anyi an gama. ” 
Kursiyya ta dan bata ranta kafin ta gaggauta saituwa. “Da ma ai kana naka Allah na nashi. Yanzu dai ba wannan ba. Maimartaba haryanzu fa babu wata magana daga bangaren anguna. Ya kamata ace ango ya kira amarya yaji abubuwan da take so na shagalin biki. Amma fa nice nake komai ranka ya dade. Walima da za a yiyau da yamma ma nice na hada, babu maganar ango. Kana ganin babu matsala kuwa?” 
Sarki Saniya saki guntun murmushi. “Babu matsakar komai. Ai kin ga dole a samu haka, saboda magana ta gaskiya duk inda auren hadiyake ba lallai a samu yadda ake so ba. Ina tsammanin al’adar masarautarsu daban tamu daban, watakila su basa yin hakan ne.” 
Tabe baki Kursiyya tayi. ”Shike nan ai. ” ta mike a bisa Iafin kafafuwanta da suka sha lalle mai matukar kyau. 
“Fulani Kursiyya.” Ya kira sunanta. ”Naam maimartaba.” Ta amsa hade dajuyowa tana kallon shi. 
“Ki turo min Hafsa ‘yarlele.” Da fara’a ta amsa da to sannan ta fike tabar dakin. 
Ta same ta ta fito daga wanka ana mata gyaran gashi. Ta murmusa tana kallon yadda Hafsa ta kara kyau sosai, fatar jlkinta ke sheki tsananin gyara data sha. “Wani abu sai kyakkyawar 
‘yata. Gaskiya dole in karawa mai gyaran nan kudi, k0 don gyara min tilon ’ya da tayi.” “ Murmushi duk suka dauka kafin ta shaida wa Hafsa taje kiran maimartaba. 
Cike da isa take taku har ta iso dakin maimartaba. Bayan ta zauna a bakin gado ta gaishe shiya amsa mata da sakin fuska. “Hafsatutuna amaryar gobe.” Ta rufe fuskarta alamunjin kunya. 
“Yar guntuwar nasiha ce zanyi miki Hafsa game da zaman aure. Kin ga auren nan da kike jin shi ba abun wasa bane. Zaki koma ne wata sabuwar rayuwa, tare da mutumin da bai san halinki ba baki san nashi ba. Zaki koma rayuwa a masarautar da baki taba kai mata k0 da Ziyara ba. Masarautar da da dama al’adunta suka sha bamban da ta Bilbah. Don haka sai kin riki hakuri, ki daure, tare da daura damararyiwa mijinki da kafdanginshi biyayya. Sannan wannan halin naki na son girma dole ki rage shi, ki rage mulki, ki rage raini, sannan sai kiga kin zauna da kowa Iafiya Hafsa. Kinfi kowa sanin ba mu san wani abu wai shi saki ba a gidan sarauta, duk dalilin da yasa aka yi saki to ki duba shi, saiya girmama. Don haka sai kiyi kokarin nisanta kanki da girman abin da zaijawo miki saki. Matukar aka sake ki kuwa kinjawo wa wannan masarautar surutu, wanda har diyan diyanki ba zai daina bibiyarki ba. A takaice ma, idan har kika tafka zunubin da zaisa a sake ki, kar ki tinkaro wannan masarautan Maganin kar ayi kar a fara. Ko yaji ban yarda da shi ba. Zuwa ganin gida ma kanshiyana da ka’ida. Akwai Iokacin da ake warewa na zuwa gida, za a hado ki da tawaga ki zo kiyi iya adadin kwanakin da aka dibar miki sannan ki koma. Saboda haka sai kin kula sosai. Ki girmama mijinki da iyayenshi. Rashin kunya da fitsara duka ki daina. Kar inji kar in gani. ” 
Yana kaiwa nan ya dakatajin shesshekar kukanta. “Abba bama zanyi abin da duk zaija wo wannan ba. Na maka alkawrain ba zan taba kawo wani kokegare ka koga Ummana ba. Zan ma Yerima Abu Sufyan Iadabi sosai. ” 
Gaban maimartaba ya sake dokawa. Bai san abin da zai faru ba idan Hafsa ta gane ba Abu Sufyan bane mijinta. Dole dai tayi hakuri. Ya ayyana a ranshi. Kuma shi haryanzu babu wanda ya,,,, bakinshi wai ga wanda Hafsa za ta aura. Kursiyya ce ta yanke nata hukuncin. Kuma dama can ba shi da niyyar fada musu din. Da kanta ta samar mishi hujja. Koda an tashi dai zai ce baiyi da kowa ga wanda Hafsa zata aura ba. 
Daga nan ta tashi ta tafi. Suka hau shirye-shiryen walima. Yadi ne ta saka kalar baki, wanda a kiyasce zai kai kimanin dubu sittin. Yaji ado tun daga saman rigar har kasanta. Sannan ta dora alkyabba mai mayafi Ita ma kalar baki’, amma an mata ado da kargolden. Fuskarta ta amshi kwalliya. Ta saka takalmigolden mai tsini sosai. Sannan an bazo sumarta dake kyalli a saman goshinta. 
Bayan ta gama shiri aka zo aka fita da ita farfajiyar da ake gudanar da walimar, inda aka ci aka sha.saida Kaf al ‘ummar masarautar Bilbah suka shaida Iallai ana bikin ‘yargata. Abinci babu 
wanda bai ciyayi guzurinshi ba. 
Sai magrib sannan aka tashi walimar. Tana daki tana cire kayanjikinta Kursiyya ta shigo ta zauna kusa da ita. “Hafsa dazu maimartaba ya kira ki, Ya kuka yi da shi?” 
Ta zayyane mata kafyadda suka yi. “Gaskiya ya fada miki Hafsa. Kinga dai nice mai goyon bayanki ko? To ba zanjuri zuwa yaji ba. Ba zanjuri saurarenki ba idan kika kawo min karar mijinki. Ya zama dole kiyi hakuri da duk halin da zaki tsinci kanki. Ba Iallai ba ne ki samu yadda kike so ba. Abin da kika ga maimartaba yana yimin keba Iallai naki mijin ya miki irinshi ba. Maza kala-kala ne. Sannan dole ki rage wulakanta mutane. Can ba nan bane. Babu tabbas idan zasu goyi bayanki. Bare kuma wannan rasa kunyar yaron, fitsararre da alama ba Iallai ku shirya ba. Sai‘ kin kula.” 
A ran Hafsa haushin Kursiyya taji. A kan me zata aibunta abun kaunarta kuma angonta? Ta yamutsa fuska tana kallon ta. 
“Hafsa k0 kiso ko kiki wannan yaron rasa kunya ne kuma sai na fada. Ke kika ce kina so, don haka dolenki ki dauki duk halinshi.” 
Mamakin mahaifiyarta take yi. Ta yadda yau din nan take mata fada ta wannan sigar. Kodayake dai, aure ba wasa bane. Kursiyya na gamawa ta fice daga dakin. Hafsa kuma ta daga kafadarta alamun ko’inkula. A ganin ta k0 ma wanne irin hali Yerima Abu Sufyan gare shi ita taji zata iya zama da shi. Zata ba mara da kunya. Don haka babu bukatara fada 
mata yadda za tayi rayuwa a gidan, sai kace dai sabon shiga a gidan sarauta.Washegari!!!!!!!! 


Shin kun fahimci wani abu mai matukar muhimmanci a wannan chaptern? Idan kun 
fahimta menebe shi.’ Drop your comments. ! 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE