GIMBIYA SA’ADIYA
GIMBIYA SA’ADIYA
CHAPTER 17
Gimbiya Sa’adiyya tana zaune saiga sako ya riske ta daga mai martaba, cewa yana son ganin ta. Agogon dakinta ta duba, karfe tara da rabi na dare, har ta yi shirin kwanciya ta mike. Dogon hijabi wanda keja harkasa ta saka, sannan ta zira takalminta ta nufi farfajiyar Sarki Sani. A bakin kofa ta gaishe da masu gadin wurin, ta cire takalminta hade dajan hijabinta ta debo ta har bisa goshi, sannan ta shiga dakin. Ba ta same shi a falo ba, hakan
ya bata damar zarcewa dakinsa da sallama kunshe a bakinta. “Wa ‘alaikissalam. Shigo ciki yata. ”
Mai marteba ya fada sadda yaji muryarta. Cikin nutsuwa ta isa dakin, ta zauna a kasa kanta sunkuye ta gaishe shi.
“Yata ina fatar dai kinji sako daga wurin Fulani Kursiyya game da batun aurenki.” Shiru tayi tanajin idanuwanta na kokarin kawo ruwa.
“Ki kwantar da hankalinki yata. Na tabbata Yerima Abu Sufyan zai kula dake, zai baki cikakken gata watakila fiye da wanda kike samu a nan. Ki cigaba da hakurin nan dai wanda na sanki da shi, wanda nake baki a kodayaushe, insha Allahu komai na dafda zuwa karshe, da zarar kin bar masarautar nan shike nan. Za ki samu gata sosai a masarautar
Kubaisu. ”
shesshekar kuka takeyi sosai, sosai takejin nutsuwa a kalaman da suke fitowa daga bakin mai martaba. Tana fatar hakan, tana ji a jikinta ita ma, kila karshen rayuwar kuncinta ne yazo. Al’amarin Allah babu ta inda baya zuwa. Ta yiwu dalilin zuwan karshen kuncinta ne ya
Sa Yerima Abu Sufyan ya zabe ta a matsayin wacce zai aura.
karamar waya na nan na siya miki, an saita komai, idan kin koma daki ki nemo Yerima lambarsa na nan na saka miki har ma mun yi waya da shi. Ku yikokari a Cikin makwannin nan biyu ku kara daidaita kanku. In sha Allahu za kuji dadi a rayuwarku.” ’
Yajawo wata drawer ya mika mata kwalin wayar Cikin Ieda, sai kuma ya dauko wayar daga bisa side dra wen
Da hannuwanta biyu ta karba, cikin rawar murya ta furta, “Na gode Abba, Allah ya kara arziki mai albarka.” ‘ameen Gimbiyata. Ki tashi kije kawai AlIah yayi miki albarka.”
“Ameen abba.”
Ta furta bade da mikewa.zata fita mai martaba yace mata,
“Kin ga na manta ina son fada miki, gobe da rana jirgin su Salbiyya zai sauka. ”
Cikin zaro ido tace, “To fa! Tafiya haka kwatsam?” “Aikuwa. Amma ni tunjiya ta sanar dani, har da Anwar da Adnan duka zasu dawo. ” Sa’adiyya ta dafe kirjinta, fuskarta ta nuna alamun walwala. “Allah daiya sa sun dawo kenan ba zasu koma ba.” Sarki Sani yayi murmushi, “To Ameen. ”
“Bari in tafi Abba, sai da safe.”
“Allah ya bamu alkhairi.” Ya furta hade da jawo radio dinsa ya kunna Iabarai.
A daidai fitar ta tayi kiclbis da Kursiyya zata shigo. Kanta ta sunkuyar kasa tana kokarin fita. Kursiyya ta kalli ledar hannun Sa’adiyya sannan cikin murmushin makirci tace,
“Yata Halimatu har zaki fita?An gama hirar kenan?” Sa’adiyya ta kirkiro murmushi hade da daga kai. “To shi kenan sai da safe.”
Sa’adiyya ta bardakin. A ran Kursiyya sai tsine mata take yi, tsananin haushin Sa’adiyya da takeji kara ninkuwa kawai yake yi. Tama rasa ta hanyar da zata bullo mata don ta kaita wurin Boka Fartsi.
Sa’adiyya na komawa daki ta kunna wayar. A dialled numbers ta ga lambarsa anyi saving da Yerima. Kamar ta kira, kamar kuma kar ta kira haka takeji. Wata zuciyar ce tace mata ta kira din, jiki sabule ta latsa kiransa. Kashewa yayi ya sake kira. Hannunta harkyarma yake mata, tana tunanin abin da zai shiga tsakaninsu idan ta dauka.
”As…assalamu alaikum.” Ta fada cikin rawar murya. “Wa alaikissalam. Gimbiya Sa’adiyya barka da dare.” ”Uhm…ina wuni?”
“Laliya Iau. Ya kike ya gida? Ya kuma ciwon kai? Na tabbata kina nan kina fama da shi saboda kukan da kika sha.”
“Hmm
Kawai Sa’adiyya tace da shi. “Uhm? Kin yi shiru. Ko bakiyi kukan bane?” “Na daina ai.” Ta fada cikin wata murya mai kama da shagwaba. “Good girl. To ya kike miye Iabari? Kin dai fara shirye-shirye k0?” “Name fa?” Ta katse shi. Murmushi yayi wanda har ita kanta saida taji shi.
“Na tabbata an sanar dake kin kusa zama mallakina. Ki cire tsoro da duk wata kunya, ki
sanar dani gaskiyar abin da yake cikin zuciyarki. Shin kina so na?” Dafe kanta tayi tana tunanin amsar da zata bashi.
“To idan ma nace bana sonka kana da wani abun yine? Naga ai su Abba sun gama magana har an fitar da rana.”
“Hmm! ldan kika ce ba kya so na me zai hana ni fitowa na fada musu gaskiya ba sAi Iokaci ya
dade da wucewa na auren dole ba. Feel free and tell me, what’s in your mind?”
Shiru ta danyi, bata son shi, haka zuciyarta ke karantar a’a ita. Sai dai kuma ba tajin haushinsa, saboda shine mutum na farka da yaso ta bayan mahaifinta. A ranta tanaji, shi’ ya kamata ta mallaka wa dukkanin zuciyarta, shiya kamata yaja ragamar rayuwarta. Ko babu komai ya zama zakka, ya karya karatun karyar da zuciyarta tajima tana mata, cewa ba zata taba yin aure ba har abada, saboda ba zata taba samun masoyi ba.
Kin yi shiru Halimatu. Kar ki cuci kanki, nima kuma ki cutar da ni.”
“Ba zan boye maka kamai ba Yaya Yerima, tun da nake a rayuwata, bayan Abbana babu wanda ya taba cewa yana sona. Ba a maza kadai ba, hatta a mata yan uwana bani da masoya, kowa ya tsaneni babu gaira babu dalili. Ba kuma abune na yanzu ba, ya samo asali tun yarin tata har na girma. ”
Sai kuma kuka ya kufce mata. “Subhanallahi! Ya isa to daina kukan.”
“Ta yaya zan kimutumin da ya kasance shine farkon wanda ya nuna yana so na? Ya zama
dole na fadi’ maganar nan, ko da kuwa hakan zai zama silar da zaka goranta mini nan
gaba…” Bata karisa maganarta ba ya dakatar da ita,
“Ki daina fadin haka Halimatu. Ba zan taba goranta miki ba har abada. Kuma na tabbata akwai wani abu a kasa, kowa ba zaiki ki ba haka kawai. K0 da a as wani mugun hali kike dashi dai ai dole ki samu kawayen da zasu soki, bare kuma ba haka kike ba. Dan zuwan da nayi kawaiya tabbatar mini da cewa kina da farar zuciya, haka kuma kina da kyawun hali. Mai martaba yace mini mahaifiyarki ta rasu k0?”
Ta kokarta shanye kukanta. “Tun inajinjira.” “Allah sarki! Allah yajikanta ya gafana mata. A karkashin mahaifiyar Hafsa kika tashi ke nan?” Ta saka tafin hannunta ta share hawayen dake sake sintiri a bisa kumcinta.
“Ba .a karkashin kowa na tashi ba. Ni kadai na tashi a karkashin kaina, da kuma taimakon Abba.”
Cike da mamaki Yerima Abu sufyan ya zaro ido tamkaryana a gabanta. Yace,
“Ba ki tashi a karkashin kulawar uwa mace ba kike nufi? Ta yaya hakan ta kasance? Ina Abba yake da ya kasa nema miki ko da uwar raino ce?”
Murmushin takaici Sa’adiyya ta saki,
Ban san komai a kan yarintata ba, ban san yadda aka raine ni ba. Sai dai nayi wayo da sanin Umma Kursiyya aka wakilta ta kula dani, sai ta samu damar muzguna mini, taci zaralina, ta cutar dani…”
Kuka sosai Saadiyya keyi, wanda yasa Yerima Abu Sufyan ya hakura da tambayoyin da yake rattabo mata, duk kuwa da cewa yana tsananin sonjin amsoshinsu.
“Ya isa to daina kukan. Insha Allahu komai yazo karshe. Kema zaki tsayu a kan tsayayyar rayuwa. Zaki samu farincinki kamaryadda kawacce mace take samu. Allah ya fisu, zai kuma saka miki. ”
Sosai Yerima ke rarrashinta harya samu nasarar saka ta dariya. Daga nan suka sallame, ta kashe wayar sannan ta kwanta barci.
Hmm