GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 30

GIMBIYA SA,ADIYYAH






CHAPTER 40






Khalili ya tafi da sauri sai gashi da ashana,ya mika ta ga Mallam Khamis.
Mallam ya kyasta ma zaren ashana, karon farko bai kama da wuta ba her sai da ya sake kyastawa. A take zaren ya kama da wuta sosai, sai gashi sai kara girma yake yi, yana fitarda wani irin kauri mara dadi. Yajima yana ci da wuta,sai can ya bada wani irin fas! Da karfin gaske, wanda duk sai da suka gigita a wurin, banda Mallam Khamis da fatalwa Saadiyya. Yana gamawa kuma sai ya koma toka, kamar babu abin daya faru.
Kafin Indo ta gama dawowa hayyacinta sukaji muryan Saadiyya tana fadin “Boka Fartsi meya kawo ka nan din? Nace me ka zoyi a nan? K0 ka zo ne ka karisa kashe min mahaifiya? Ka tafi da gaggawa. Ka tafi boka Fartsi tun kafin na illata ka a nan.” Agabanta ya duke, dukiyar kneel down. Ya hade hannuwanshi biyu a wuri daya sannan ya
dora a saman kirjinshi. cikin kuka yace, “Inaji ajikina karshena ne yazo a yau. Komai ya tashi ya cukurkude mini. Bani da kamin komai a halin yanzu, duk na tattare shi gare ki. Naji ciwon hakan sosai, sai dai bai kai mini tsananin dacin abin da Kursiyya da Zabba’u suka min ba. Bai kai mini zafin cin amanar da suka yi mini ba.A shirye nake da daukan koma wanne irin hukunci ne naki Saadiyya. Sannan zan yi muku wani albishir, cewa zan mayar dake ainahin yadda kike, zaki koma
hakikanin mutum din ki, amma kafin nan ina so sai kin lallasa mini mutanen nan guda
biyu. Ki gama daukar ma kanki fansa dani kaina, sannan ki koma mutum Saadiyya. Ki koma asalin halittarki.” Dukkaninsu suka zura idanuwansu ga tsohon mutumin da kai da fuskarshi suke cike da furfura Suna tsananin mamakin kalaman da suke fitowa a tsakanin labbanshi. Kalaman da sukejin su sunzo musu a bazata, domin kuwa har shi Mallam Khamis din bai taba kawo ma ranshi cewa Saadiyya na raye ba. Cike da al’ajabi Mallam Khamis Ciro ya isa gare shi, cikin daurewar fuska yace “ldan karya ka mana ka kuka da kanka boka Fartsi . Sannan kuma idan da gaske ne ka mayar mata da kurwarta yanzu-yanzun nan. Mu mutane ne masu taushin zukata, wanda basu farlanta daukan fansa ba, masu barwa Allah lamurranSa.
Yau ke Saadiyya ce a raye na tabbata ba zata ce lallai da kanta zata dauki fansa ba. Saadiyya yarinya ce mai tsoron Allah da tawakkali. Yarinya mai hakuri dajuriya. Na san zata barwa Allah komai, ta bar su da duniya, sannan ta barsu ga mai kowa mai komai.
Ba wai na ce dole sai ka kyale su ba. Mu duk ba wannan ne a gabanmu ba. Kawai ka mayar mata da kurwarta a gangarjiki, daga nan sai kayi duk ma yadda kake so dasu, mun sallama maka su din.“ Boka Fartsi duk sai yajijikinsa yayi sanyi da kalaman Mallam Khamis. Yace, “Hakika kana cikin mutanen da nayi wa muguwar tsana, a da, Kursiyya ta kawo mini sunanka da nufin nayi aiki a kanka tun wasu shekaru da suka shude a kan wani yar hatsaniya daya taba shiga tsakaninku. Sai dai nayi duk iya kokarina amma abun ya gagare ni, sai ma neman wahala kawai da nayi. Tun daga nan ne na tsane ka. Amma a yanzu sai abun ya sha bamban. Kalaman nan naka suka karyar mini da zuciya. Ko don wannan kadai zan mayar mata da kurwarta, zata dawo da rayuwarta, kuma mutuwa sai idan lokacin tane yazo”
Kursiyya sai mazurai take yi, tana kallon yadda abin da ta gama gasgatawa yake kankance a gaban Mallam Khamis, yana neman ruguza dan farin cikin da yayi saura na daga
rayuwarta. Da karfi ta saka hakora ta cizgi fatar hannunta da sosai, sai ga jini na malala. Wai ita duk tsananinjin haushi ne. Still ba ta nadama ba
Boka Fartsi ya duka a wurin hade da sunkuyar da kanshi kasa. Babu jimawa sai ga abubuwa sai bullowa suke a gabanshi, dukkanin kayanshi na tsafi. Su dai kam sai kallon sarautar Allah suke yi, har sai da wurin ya cika tsaf da abubuwanshi. Sannan sai ya hau fadin wasu kalamai da duka wurin banda Kursiyya da Zabba’u babu wanda zai ce ya taba jin su. Da karfi gawar Saadiyya ta bullo gabanshi, hancinta toshe da auduga, idanuwan nan nata a rufe,jikinta sanye da likafani kamaryadda aka rufe ta a kushewarta. Ya saita idanuwanshi a saitin nata idanuwan, sai ga jan haske na fitowa daga cikinsu, yana saituwa a idanuwanta, hasken yana dira a cikin nata idanuwan. Numfashi na shigarta, numfashi na fita daga waccan fatalwar. Sannu a hankali har sai da ya gama shiga duka,
sannan ita kuma fatalwarta fadi da karfu a wurin, a take ta hau dagargajewa tamkar kankarar da aka buga a kasa da karfi. Sai da duk ta malale a wurin sai kuma ta daskare, lokacin ita kuma Saadiyya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya hade da yin barci a wurin. A lokacin kuma Boka Fartsi ya dawo daidai. Yace,”Wannan ita ce ainahin Sa’adiyyarku. Wacce lokacin mutuwarta baiyi ba da karfi da yaji muka raba ta da shakar iskar duniya.” Cike da mamaki Sarki Sani ke kallon lamarin, yana son yin magana amma tsananin al’ajabi bai bar shi cewa k0 uffan ba. Sai ya kalli Saadiyya, sai kuma yajuya ya kalli Indo.
Dukkaninsu biyun farin cikin rayuwarshi ne. Kallon su kadai na kara shigar da shi wata duniyar jin dadi. Sai dai kuma a yanzu ya gaza gasgata halin da yake ciki. Ya gaza tantance shin a farin ciki yake ko kuwa a bakin ciki? Farin cikin sake sabuwar rayuwa da iyalinshi mafi soyuwa a gare shi. Bakin ciki kuma na yardar da yayi da Kursiyya ashe tana nan tana cin amanarshi a kasan kasa. Abin da bakinshi ke son tambayar boka Fartsi ne yaji Mallam Khamis ya furta.
“Amma ni abin da ban fahimta ba, wannan yarinyar ta rasu kuma har an binne ta. Yaya aka yi gawarta tazo gare ka?” Boka Fartsi yace,
“Hakika gawar Halimatu ce aka binne. Sai dai kuma abin da baku sani ba shine, ko barin
masu binniyar daga makabarta basu yi ba tsafina ya dauko mini gawarta ya kawo ta gare ni. A lokacin tuni kurwarta ta jima a cikin katuwar kwalba, najefa ta a kasan kogin gidana. Na ajje gangar jikin kawai a tare dani, ba tare da ina amfana da ita ba. A lokacin da Aljani Maharazkhan ya ceto ni daga zaluncin Uwar biyu, a lokacin ne ni kuma na hayaka da cin amanata da Kursiyya tayi, na karya dadadden alkawarinmu da ita ta hanyar fiddo kurwar Saadiyya daga cikin kwalbar sihiri, na mallaka mata dukkanin karfina har ma dana zoben da aljani Maharazkhan ya bani, kawai don ta kwatar mana fansa a wurin Kursiyya da Zabba’u.
Ayau din nan na tabbata rayuwata tazo karshe. Domin kuwa duk ranan da boka ya tona asirin kanshi (confessing) a gaban wasu, to lallai a ranan ba zai kwana duniya ba. Kuma koma ba wannan ba, na jima da sanin ta dalilin yarinyar nan Sadiyya ne mutuwata za tazo Ba tun yau ba, na san dole zan mutu ne a silarta. Duk da cewa mu kanmu bokaye masu aiki dajinnu ba mu san gaibu ba, sai dai Allah da ikonSa yake ba mu haske, mukeji ajikinmu idan wani abu zai faru damu.
Babbar damuwata ma ita ce ni na san dauwamammen dan wuta ne, kasantuwana mushriki, tun yarintata har na fara manyanta, har izuwa yau din nan dana zama tsoho tugut
Kar ku taba tsammanin na tuba ne, babu tuba a rayuwata. Ban yi nadama ko da na sanin kasantuwana boka ba. K0 ba komai na kafa tarihin da babu bokan daya taba kafa shi a duk yankin nan. Na zama boka daya tamkar da dubu.
Ni zan tafi inda mutuwata take. Zan riski ajalina ba zan so ya riske ni a gabanku ba, don ma kar ku bada labari.”
Ya mike zai tafi ke nan yaji wani irinjiri na diban shi, ba shiri ya koma ya zauna. Ya kuma sake mikewa zai tafi, ya daure duk da neman faduwa da yake yi, amma ina, tsayuwa ma ta gagare shi bare tafiya. A hankali yakeji idanuwanshi najuye mishi, yana ganin komai bibbiyu, da karfi ya fadi a wurin timmmm!
Babu wanda ya yi yunkurin zuwa inda yake, sai dai kallon sarautar Allah kawai da suke yi. Nan take boka Fartsi ya hau cije-cije, yana wani irin kakari sai sabbatu yake yi. ‘ “Ku zo ku taimaki dan wuta. Dan wuta zai mutu jamaa! Ku taimaka mini.“ “
Kalaman da suke fitowa ke nan daga bakinshi, da kuma wasu marassa dadinji. Bakinshi yayi ta fltar da kumfa, idanuwan nan sun firfito waje zuru-zuru, numfashi sai sama da kasa yake mishi.
Daga haka malakul-mauti ya iso gare shi. Ya zare mishi ranshi da karfin gaske, bayan ya gama zayyana ma mutanen wurin cewa shi dan wuta ne.
Wa iya dhu billahi!. Ya Allah ka sa mufi karfin zukatanmu. Allah ya raba mu daga aikata shirka.

Kursiyya da Zabba’u fa?
Wait for it

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE