GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 36
GIMBIYA SA,ADIYYAH
CHAPTER 36
Boka Fartsi ya karbi zoben ya soka a yaryatsarshi. Sannan ya hada hannayenshi biyu alamun godiya ga aljani Maharazkhan. Da sauriya kama mishi hannuwan yana kokarin hana shi.
“Ka wuce duk wannan a wurina Boka Fartsi. Kawai ka cigaba da ayyukan gabanka. Ka dauki fansa ga duk wanda ya cizarafinka. Kar ka raga wa Kursiyya, ita ce tajawo komai daya faru. Sam Kursiyya bata cancanci ka sassauta mata ba. Ka daukar mata hukunci mafi muni a rayuwarta.” Boka Fartsr‘ kai kawai yajinjina. Har a lokacin bai da karfin yin magana. Zaman wuri daya da yayi na tsawon shekaru bai sake shi ba. Jin komaiyake ya zame mishi bako. Babban burinshi kawaiya dauki fansa ga Kursiyya. Ya nuna mata iyakarta, tare da tabbatar mata da cewa shi ba wawa bane. Aljani Maharazkhan yace “Nizan tafi gidan aure na. B lallai ba in sake dawowa a dan wannan lokacin. Ka san yadda tsarinmu yake na aure. Yanzu haka ma satar jiki nayi na taho. Na tabbata a duniyarmu ana can an fara jajena. Na baro matata da kewa sosai. Don haka ni zan tafi Ina maka fatan alkhairi. Ina maka fatan nasara a dukkan komai naka.Yana gama fadan haka ya bace daga wurin yabi iska. A kan hanyarshi yaji wata irin guguwa ta cigabanshi. Hayaki ya taso mai matukarzar yawa wanda yasa ya gagara k0 da motsi. Tsayawa yayi cak, yana sauraren sarautar AIlah. Bai ankara ba yaji an Shake wuyanshi da karfin gaske. “Waye a nan?” Ya furta cike da azaba.
Da karfi ta kyalkyace da dariyar nan tata. Sannan ta dunkule hannunta, dukkanin hayakin ya Iafa tamkar ba ayi shi ba.
“Uwar biyu wai me yake damun ki ne?” “Meh yake damu na?” Ta maimaita maganarshi cike da mamaki. “Kina da matsala sosai. Ni ki sakeni ki bar ni in tafi,inda zanje. ” “Karyarka ta sha karya Maharazkhan. Kai kanka ka san ni Uwar biyu ba zan kyale kaba. Ka aikata abu mafi muni a gare ni, abu mafi cin zarafi da cin mutunci. Ban taba tsammanin akwai ranan da zaka minjan ido ba saiyau. Ban taba tsammanin akwai ranan da zaka nemi cin zarafina da zobenka za tazo ba, sai a yau na tabbatar. Amma babu komar’. Yanzu duk ba Iokaci bane ba na maimaita abinda ka riga da ka san shi. Ba Iokacin tsayawa cece-kuce da wanda bai kamace ni bane. Yanzu ina zoben yake? Nace ina zoben yake Maharazkhan?” Ta zaro idanuwanta duk suka zazzalo waje. Sosai Maharazkhan ya tsorata, sai dai k0 kadan baiyarda ya yiyadda za ta iya fahimtan ya tsorata dinba.
“Babu shi Uwar biyu. Na damka shiga wanda ya fini bukatanshi a daidai wannan lokacin.
Naba boka Fartsi shi domin ya kwaci fansa a inda ya dace.”
Ta tabe baki tace “Kafishi bukatan wannan zoben a yanzu Maharazkhan. Domin kuwa sallama shiga boka Fartsi daidaiyake da tsayawar numfashina Daka sani ka rike na wani lokaci, har sai ka ga komaiya sanyaya. Amma dayake kana da toshewar basira sai ka bayar. Don haka ni ma zan nuna maka da cewa ina da nawa karfin ko da ace babu zabe. Zan Iashe maka kayan ciki, kaga illa irin tamu ta mayu. Ka tabbata cewa mu mayu mun fiku jinnu illah.”
Yayi dariya sosai Maharazkhan, sannan yace ‘a shirye nake da karban duk wani hukunci
naki. Bana tsoro k0 fargaban zaluncinki Uwar biyu. Na shirya, ki Iashe ‘yan cikina ki bar gangar jikin a nan. Ko ba komai na zamajarumi. Za a yi alfahari dani cewa kasurgumar mayyar nan ta ta kashe karamin alhaki kama ta.”
Yana kai aya a zancenshi ta hau zazzala harshenta waje. ldanuwanta ta watsa a saitin cikinshi. Ba a yi cikakken minti daya ba Maharazkhan ya fadi kasa hade da sakin ‘yar kuwwa. Wata irin kara Uwar biyu ta saki da karfin gaske, wacce ta amsa kaf ilahirin dajin.
“Wayeya ce dani bani ba.Nima na ce dashi bashi ba. Nafi karfin aja dani. Nafi karfin wanda ya fisu ma balle su. Wo hohoho Uwar biyu kayan zalunci. Uwar biyu gayyar masifa da bala’i. ‘yar karamar da ta gagari manya-manya. A tashi a bar ki uwar tagwaye, uwar
mutum da mayya. Mayya matar bIl,Adama. Kin zarce Aljan kin zarce mutum. ” Ta sake ky a lkyacewa da dariya. Bata san sadda tajijikinta ya mata nauyi ba. Tayi kokarin motsawa amma ta kasa. Tayi-tayi ta daga hannunta yaki daguwa. Hakan ya sa mamaki ya cikata. Tayi gaggawar bude idanuwanta da ta rufe tun a sadda take ma kanta kirari. Zare idanuwa tayi a lokacin da taga baki daya jikinta an nade shi da ankwa. Ta dora idanuwanta ga gangarjikin aljani Maharazkhan ta gan shi a kwance babu alamun motsawa. Ta sake kallonjikinta, mamaki bai kau daga gare ta ba. “Kina mamaki k0?” Ta tsinkayo wata zazzakar murya ta daki dodan kunnuwanta.
Kamar inuwa ta fara hangen dirarriyar mace na tinkaro ta. Bayan ta iso gabanta ta rikide ta koma aljana. Kyakkyawa da ita da yalwargashi. Ta barbazo sabon kitsonta har bisa mazaunanta.
“Uwar biyu kike k0 wa? Kin cuce ni kin zalunce ni. Tun da nake a rayuwata ba a taba ci min zarafi kamar wannan ba. Ban taba kawowa a raina cewa ba zan yi tsawon rai da mijina ba saiyau da kika shiga tsakanin’. Rabuwata da Maharazkhan ashe rabuwarmu ce ta karshe ban sani ba. Ashe muguwar mata na nan zata raba ni da rabin raina. Wallahi wallahi wallahi kema sai kin mutu. Ban taba kashe kowa ba, hasalima ban taba k0da shigajikin bil’adama ba tsabar adilanci. Sai dai ayau zan yanke wannan alkawarin nawa. Zan aikata abu mafi muni a gare ni. Zan kashe ki Uwar biyu. A yanzun nan zan kawo karshenki a daron duniyarki, kamar yadda kika kawo karshen nawa mijin, kika yanke masa zama a duniyarshi. ” Uwar biyu kasa cewa komai tayi sai rawar jiki da take yi. Gashi an daure mata duk wata gaba tata da ankwa bare tayi gigin yin lsafi ta bace. Da gangarjikin nata ne dama take
amfani, ga shi kuma ba zai moru ba a yanzu.
“Ki taimaka mini kar ki kashe ni. Ina son rayuwata, bana son mutuwa. Ban tashi barin
duniyata ba. Ki taimaka mini ba don halina ba.”
Rufaida ta tamke fuskarta tamau tamkar bata taba yin dariya ba. Tace “Ashe baki san kowa haka yakeji ba .a yayin da aka tabbatar mishi da za a kashe shi?A yau kin sani ai. Kinji yadda mijina yaji.”
Ta dunkule hannunta da karfi sannan ta bude shi, ta saita a daidai zuciyar Uwar biyu.
“Yau nayi amfani da karfin tsafin sarautata, wanda ban taba amfani dashi ba tun sadda kakana sarkin Aljannu ya bani shi. Kinja miniyin azumin kaffara Uwar biyu, saboda rantsuwar da nayi har abada ba zan yi amfani da shi ba. Amma babu komai, azumin kaffara ya fiye minisauki a kankici gaba da rayuwa bayan kuma kin kashe mini farin cikin
rayuwata. Kin yanke mana kaunar da muka ci burin yi mai tsananin tsawo a cikinta.”
Ta karisa maganar da fashewa da kuka mai karfi. Sannan ta bar Uwar biyu dake ta zagwanyewa tana daddarewa, gabbanjikinta suna rabuwa dajuna.
A gabam gawar mijinta ta koma. Ta dora hannuwanta a saman zuciyarshi, hawayenta masu dumi suna sauka a bisa farar rigar jikinshi. “Ban so ka tafi ka bar ni ba ya mijina. Ka tafi ka bar ni cikin kunci da takaicin rashinka. Ban san ya rayuwata zata kasance a yanzu da ka tafi ka bar niba. Ka dawo gare ni Maharazkhan’ Ka taimaka ka dawo gare ni.”
Kuka takeyi sosai, ta fita hayyacinta ma sai famar girgizar gawanshi takeyi. “Tafiyar nan kawai da kayi ka barni na shiga kuncin dana gaza samun sukuni har sai dana biyo ka. Ashe abin da idanuwana za su gane mini ke nan‘ Ashe gawarka zanyi tozali da ita rabin raina.”
Zama yayi in banda huci babu abin da yake yi. Tunanin ta inda zai bullo ma Kursiyya ya guma mata kawai ke kai kawo a cikm zuciyarshi. Duk ranan daka kama ni da cin amanarka k0 kuma na butulce maka ka hukunta ni, hukunci mai tsananiya Bokana.’ ‘
Maganar Kursiyya ce ta fado mishi a rai. Ya kara tsuke fuskarshi hade da mikewa.
“Zan miki hukunci mafi muni kamaryadda kika zaba ke da kanki Kursiyya. Zan karya alkawarin dana jima da daukarshi. Kijira ni kawai.” Ya saki murmushi a daidai wannan lokacin.
Kogin gidan kasa ya isa. Kanga zobenshi kawai yayi saiga kwalba katuwa ta iso gare shi. Ya bar wurin domin dawowa dakinshi, haka ita ma kwalbar taci gaba da bin shi har sai da yazo daidai inda yake son tsayawa.
Runtse idanuwanshi yayi sannan ya bude, ya kalleta da ido yanajiran abin da zai faru. ‘
Na tabbata daga nan kun gama fahimtan komai. Kun gane yadda kamaiya faru ko? To ma shaa Allah. Wanda ma suka manta sai su koma farkon labarin su duba, zasu ga fitowan Gimbiya Sa,adiyya daga cikin kwalba har bibiyar su Kursiyya data fara yi. ‘
Wasu da dama haryanzu sun kasa fahimtan yadda labarin yake. Har da masu cewa wai ba Sa,adiyya bace ba fatalwar nan? Kuma me yasa ta sake mutuwa? Ina fatan dai yanzu kun gano kan labarin. Ma shaa Allah!
Tafiyar kwan-gwaba kwan-baya ta kare. A yanzu zamu koma tsamo-tsamo cikin labarin Gimbiya Saadiyya. Zamu dasa daga inda muka tsaya. Wadanda suka manta inda muka tsaya su duba shafunan baya su tuna.
Ku daure damararku masu karatu. The game is coming to an end. Really? Kuna so ya kare? Okay Ok Still da sauran labari. Karku manta haryanzu Baka
Fartsi bai san inda mahaifiyar Gimbiya Sa,adiyya take ba. Uwar biyu tayi mummunan
aikin da babu wanda zai iya warware shi sai ita da kanta. Kuma babu ita yanzu haka,
ta mutu.
K0 yaya wannan Iamarizai kasance?
Ina Hafsa mai fama da bari?