GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 38

GIMBIYA SA,ADIYYA





CHAPTER 38





Saadiyya ta saki haske ya isa saitin bakin Kursiyya. A take bakinta ya daidaita tamkar ba shi ba‘ Amma duk da haka sai kunya ta hanata yin magana. “Ki yi magana Kursiyya tun kafin raina ya baci‘ Don idan ya baci ba zata mana da kyau ba.”
Kursiyya ta daure fuskarta tamau tace “Duk abin da kike ganin zaki iya kiyi Saadiyya. Ba zan taba fada muku inda lndo uwarki take ba. Wallahi kiyi mini abu wanda yafi wannan muni amma ba zan fada ba Dukkanninsu dake wurin mamaki ya cika su. Wannan wace irin zuciya ce Kursiyya gare ta? Duk abin da take cikinsa amma haryanzu taki nadama. Da karfi Saadiyya ta kyalkyace da dariya. Sannan ta sake daure fuskanta tace “Kina daukan komai tamkar a wasa ko Kursiyya? Ina so kisan wani abu, a yanzu babu Uwar biyu, ita data daure miki gindi kike sheke ayarki. An kashe ta har lahira. Baki da wani mai tsaya miki sai Allah. Allah kuma kin dade da barin shi. Kin dade da barin Allah Kursiyya.“ Mallam Khamis Ciro yayi gyaran murya sannan yace “Kursiyya‘. Kin sanni ba tun yanzu ba. Haka ni ma najima da sanin ki. Sosai nake da hanyoyin da zan magance kaf matsalolin nan. Sai dai kuma ba zan yiba. Ina so ne komai ya warwaru ta cikin ruwan sanyi. Ki fito ki fadi gaskiyan abin da ya faru. ldan ba haka ba kuma dukkaninmu a nan zamu barki da ita
Daga ke sai aminiyar munafurcin taki Zabba’u. Ta maganance mana taurin kanku.”
Zabba’u na jin haka cikin rawar murya tace “Ni kam zan fadi gaskiya. Wallahi ba zan iya jurar kalar azabar fatalwar nan ba. Ni kadai na san halin dana shiga sadda ta tafi wata duniya damu. Bazan so ta sake tafiya dani ba. Ba zan soba k0 kadan Mallam.“Da sauri Kursiyya ta kalle ta cikin damuwa sosai. “Karmu yi haka dake Zabba’u. Kar ki karya dadadden alkawarin da yake tsakaninmu. Ki tuna aminicinmu. Ki tuna alkawurran da suke tsakaninmu. Ki rufa mini asiri karki fada musu. Ki yarda muyi juriyar duk wata azaba tata, amma ki sani, bata isa ba ta kashe mu idan lokacinmu bai yi ba.” ” Zabba’u zaro idanuwa tayi tace “Idan kuma bata kashe mu ba ai za mu sha wahala ko? Ni dai kamfa ba zan iya daurewa ba, sai dai kawai kiyi hakuri. Yau zan fallasa dadadden sirrin da daga ni sai ke sai boka Fartsi ne kadai muka san shi.” Tajuya ga mai martaba Sarki Sani, ta sunkuyar da kanta kasa. Zata fara magana ke nan taji da karfi Kursiyya ta dode mata baki hawaye wanke a saman fuskarta. Na roke ki kar kice komai Zabba’u. Ki rufa mini asiri ki duba halaccin dana miki a rayuwa…” Kafin ta rufe baki mai martaba ya daka mata tsawar da sai da ta gigita ta. A kaf tarihin rayuwarta kalarwannan tsawar bata taba shiga tsakaninsu ba sai yau. Ta tsorata sosai, hakan ya sa ta koma ta ladaftu wuri guda sai faman sauke ajiyar zuuya take yi.
Zabba’u ta share kwallar data sake fito mata, tace, “Kimanin shekaru ‘talatin da biyu da suka wuce. Watarana ina kwance a dakina ina firfita, kasantuwar Iokaci ne na zati. Sai naji motsi a cikin dakina. Na tashi ina tambayar ko waye,
a zatona ma mijina ne amma sai naga ba shi ba ne. Fulani Kursiyya ce tafe taci ado tamkarwata dawisu tana taku. Da mamaki na kalle ta, ina tunanin abin data shigo yi a kaskantaccen dakina. Mamakin na kawar hade da sakar mata murmushi ina gwada mata wurun zama. “Wannan zuwa haka na bazata ranki shi dade Allah dai yasa lafiya.”
Ganin ta sakar mini murmushi yasa na tabbatarda ba matsala bace ta kawo ta. Na gaisheta cike da girmamawa ta amsa a mutunce.
“Zabba’u!” Fulani ta kira sunana. Na yi saurin amsawa hade da kallon ta, ina sonjin abin da bakinta zai furta.
“Zabba’u wata yar matsala ce ke tafe dani. Kuma na tabbata kece kadai zaki iya warware mini ita. Wannan dalilin ne yasa nazo gare ki, ki taimaka ki fitar dani daga wannan matsalar. Domin kuwa idan har ban fita ba zan ji takaici kwarai da gaske.”
Cikin rawar murya nace “Ki fadi ranki shi dade, na yi alkawarin duk yadda zanyi, zanyi don ganin na fitar dake, in dai har ina da yadda zan yi din.“
Fulani Kursiyya ta sake gyara zama sannan tace, “Dazun nan ne mai martaba yazo da murnarshi yana shaida mini wai lndo na dauke da juna biyu. Cikin farin cikinshi yake shaida mini wai Shl bai taba shiga farin ciki kamar wannan ba. Kin san ita ce uwar gidanshi. Tsawon shekara tara kenan da aurenta amma ko bari bata taba yi ba. A bayanta harya auro Salbiyya ta haifi Anwar. Ga shi nima ya auro ni bayan Salbiyya na haifi Hafsa shekarar da ta wuce. Wannan dalilin ne yasa yake cike da nishadi harya kasa boyewa.
To ni kuma magana ta gaskiya Zabba’u ba zan iya jurar ganln Indo ta haihu ba. Don na tabbata sai ya gwada wa abin da ta haifa din soyayya fiye da wadda zai gwada wa namu yaran. Don haka nake so ki taimaka mini Zabba’u. Ki taimaka ki kai ni wurin wannan bokan da kika taba yi mini tayinsa kwanaki. In dai harkin gasgata aikinsa ki kai ni. Ina so yayi duk yadda zaiyi in dai za a zubar da cikin da kejikin Indo, sannan a lalata mata mahaifa baki daya
Na kalle ta cikin mamaki na tuna sadda na mata tayinshi. Nima na samu labarinshi ne a wurin wata aminiyata mai suna Uwani. Don haka na kai ma Fulani zancensa a lokacin da suka samu wani dan sabani ita da mai martaba. “Babu komai ranki shi dade. Duk sadda kika shirya sai ki min magana kawai mu tafi Amma
sai kin tanadi kudi. don Uwanl ta fada mini yana karban kudi sosai.” Fulani Kursiyya tayi murmushi bayan ta mike tsaye. “A shirye nake k0 yanzu don dai dare yayi ne da mun tafl. Amma gobe da sassafe ki zama cikin shiri. Zancen kudi kuma kar ki damu. Ni kudi ko kadan ba matsalata bace.”
Daga nan ta tafl ta barni bibiye da inuwana har ta bace ma gani na. Nayi mamaki kwarai, domin kuwa hadaddiyar mace mai ji da aji kamar Fulani Kursiyya da mamaki ace za taje wurin boka. Musamman kuma idan na tuna yadda ta kore ni a lokacin da nakai mata tayin boka Fartsi.
Washe gari wuraren goma na safe muka bar masarautar Bilbah, muka nufi wurin boka Fartsi. Mun sha gwagwarmaya sosai a lokacin shigarmu gidanshi. Domin kuwa surkulle ne
kala-kala, ga azaba da muka fuskanta kafin muka samu isa dakinshi. ‘ A lokacin da ya bayyana gabanmu ya iso da sassanyan murmushi. Yace “Maraba da zuwa wurin boka Fartsi. Sannunku da zuwa fadar boka Fartsi. Ku raya a ranku cewa kun samu abin da kuke so. Zan muku komai, zan zame muku garkuwa ga dukkan komai. Fatana kawai ku dora yardarku a kaina. Ku gasgata ni. Ni kuma na muku alkawarin biya muku dukkanin bukatocinku.” Fulani KurSiyya tayi bayyanannen Murmushi hade da cewa “Tun kafin aje ko’ina na gama yarda da kai ya bokana. Kursiyya da Zabba‘u sun gama yarda da kai.”
Boka Fartsi yayi tsafi sai ga kwarya ta bayyana a gabanshi Clke taff dajini. Ya fara mika ma Kursiyya yace ta sha kaman rabin jinin sannan ta bani in karisa shanye rabin. Ya kara da cewa “Don yana farkon zuwanku ne yasa nace ku sha da yawa haka. Wani zuwan ba zai kai
haka yawa ba. Ina sone yabi jikinku, ku saki jikinku sosai dani.”
muka saki gyatsa muka dora kallon mu gare shi.
Bai bari kowaccenmu ta kuma cewa komai ba yayi gyaran murya. “Ita wannan matar da kike so a zubar ma da cikinta ba zai yiwu ba. Matsalarda aka samu mu munfi yin irin wannan aikin ne ga karamin ciki. To ita kuma duk zaman nan ta san tana da cikin amma sai bata sanar da kowa ba. Sanin cewa karamin ciki ba a tallar shi har sai idan shi ya bayyana kanshi, gudun sharrin masu sharri. Abin da ta guda din kenan ta kame bakinta, har shi kanshi mai martaban sai daya gane da kanshi, harma ta kusa haihuwa. Karki wani damu amma. Na miki alkawari akwai abin da zanyi da sai yafi zubar mata da cikinta muni.
Abu na farko da zan miki shi ne zan isar da kibiya ga cikin Indo. Ita wannan kibiyar ita ce zata isa daidai cibiyar abin da yake Clkin cikinta. Zai fito mai mugun bakin jinin da kowa zai kishi‘ Har sai idan an samu nasaran fitar da wannan siririyar kibiyar daga cibin jinjirin. Matukar ba a ganshi an fitar ba a haka zaici gaba da rayuwa babu wanda zai so shi. Sai kuma ranan da ya mutu.
Sannan abu na biyu, bayan ta haihu akwai yiwuwar mu mayar da ita butum butumi, bayan 
mun batar da ita, ko mu nisantar da ita daga masarautar duka. Amma ya kika ce?” 
Murmushi Kursiyya ta saki tana mai tsananin jin dadin hukuncin da boka Fartsi ya yanke daukan ma Indo. “Komai kace haka za a yi ya bokana. Na amince da wannan din. Ka Mata duk abin da kaga 
ya dace.” Boka Fansi ya sakejawo kwaryarshi ya kifa ta, sannan ya sake budewa, abun mamaki sai ga inuwar mace mai ciki a cikin kwaryar. Ya murza yatsunshi biyu akaifa ta fito yajefa ta a 
saitin cikin matar. Da karfi ya saka hannunshi ya kashe kwaryarta yi ratsa-ratsa. 
“An gama komai. Nan da yan makwanni kadan za ta haihu. Bayan ta haihu da wata uku sai ku sake dawowa.” Fulani Kursiyya ta bude Jakarta ta fitar da makudan kudade ta dire a gabanshi. Bai ko kalle su ba yace “Mun gode. Ku tashi ku tafi an sallame ku.” Haka wurin fita ma muka rinka haduwa da abubuwan ban tsoro har dai muka yi nasarar fita. Inda muka ji dadin aiki da Boka Fartsi babu wani abu da ya bayar wai a saka mata a abinci ko kuma a turara ko dai wani abun. Shi da kanshi ne ya aikata. 
Bayan mun dawo Fulani Kursiyya tayi mini kyautar lapaya kalan nata da take sakawa guda uku, sai kuma turamen atamfofi guda uku. Naji dadi sosai, na karba kayan na koma dakina. 
Tun daga nan amintaka ta kullu a tsakaninmu. Ta dauki yardar duk duniya ta dora a kaina. 
Haka nima na mayar da ita uwar dakina, nake tinkaranta da duk wata matsalata. 
Bayan kwana ashirin da biyar cif da dawowarmu daga wurin boka Fartsi lndo ta haihu, ta haifi Halimatu. Kyakkyawar yarinya mai cikakkiyar lafiya. Haka ita ma lndo din ta haihu da 
Iafiyarta sosai, bata wani sha wahala sosai ba 
Sai dai abun mamaki babu wanda zai kalli Halimatu sau daya ya sake kallon ta. Dukkanin wanda za suje wurinta sun tsane ta. Tamkar dodo haka ta koma, ko ince mujiya, ita ce dai uwar bakinjini. 
Wannan shi ne silar bakin jinin Gimbiya Saadiyya. Shine dalllin da yasa ta tashi babu mai kaunarta sai mahaifinta kadai. Wanda shi din ma babu yadda boka Fartsi bai yi ba don 
ganin ya cire masa kaunarta amma ya kasa. Kaunar nan ta da da mahaifi tayi tasiri gare su.‘ 
Lokacin da Halimatu ta Cika wata uku ne muka kama hanyar komawa wurin Boka Fartsi kamar yadda ya umurce mu. 

Hmm’ Da gaske ba a son tallar karamin ciki. Ba karamin ciki kadai ba, har ma da neman aura. An fiso sai kamai ya tabbata sannan a bayyanar wa mutane. Saboda babu wanda ya san kudurin wasu. 

Allah yasa mu dace

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE