GIMBIYA SA,ADIYYAH CHAPTER 39

GIMBIYA SA,ADIYYAH
CHAPTER 39

Bayan mun isa wurin Boka Fartsi ya tarbe mu da aminci. Ya bamu abun kari muka karya, watojini. Yace, “lndo gyatumar Halimatus-Saadiyya tana da karancin addini . Bata wani damu da yiwa jikinta da yarinyarta addua ba. In tazo baccin haka ai da tun wurin gashin cibi ta gano kibiyar da najefa ma diyarta.
Don haka ita kanta lndo din aiki a kanta ba zaiyi wahala ba. Sannan kuma na gano wani haske gare ni mamaye da ita. Ina ji a jikina zan more ta, sosan gaske. Najima ina neman wacce ke bima yan biyu rayayyu guda uku, sai kuma yan biyu na bari guda biyu. lndo tazo a daidai lokacin da nake son ta. Zan yi amfani da ita wurin wasu daga cikin tsaface-tsafacena.”
Fulani Kursiyya tayi murmushi hade da cewa “Ni fa ban wani damu ba da duk abin da zaka yi mata. In dai har Indo za ta wulakanta to shi ke nan.“
Boka Fartsi yace “Ki saka a ranki har an gama komai.” Ya hau busa bakinshi sai ga wani irin suraci na futowa daga ciki yana bin iska. Iskar suracin wurin lndo duka bai fi minti daya ba. Duk muna kallon abin da yake faruwa a cikin kwarya. Halimatu ke hannunta amma tayi gaggawar sauke ta ta dora bisa gado. Tamkar mahaukaciya haka ta bi iskan nan, ya zartar da ita cikin ban dakin Fulani Kursiyya.
Daga nan Boka Fartsi ya dago kanshi ya kalle mu, da murmushi kunshe a fuskarshi.
“Zamu ajje musu gawar karya, iri daya sak da ita. Ku tafi kawai. Kuna komawa za kuji sanarwar mutuwarta. Ni kuma zan ci gaba da tsafi da ita a can cikin inda na kai ta. Sai dai akwai sharadi mai tsauri gare ki Kursiyya. Sharadin shi ne ko da wasa kar ki bari wani ya shiga bandakinki, sai dai ke ko aminiyarki Zabba’u. Domin kuwa duk ranan da kika yi sake wani yaga Indo, to tabbas ranan asirinki ya tonu. A ranan Indo zata fito, kuma a matsayin rayayyarta.”Fulani Kursiyya tace “In don wannan ne kar ka wani damu boka Fansi. Zanbi umurninka, zan kuma kiyaye. Na maka alkawari.”
“Ku ajje kudi ku tashi ku tafi.” ya furta ba tare da ya kalle muba. Fulani Kursiyya ta zaro kudinsa ta ajje sannan muka mike muka barwurin cike da farin cikin samun nasararmu. Fulani Kursiyya sai faman shi mini albarka take yi. A ganin ta ta silana ne ta samu wannan mafitar, har ga shi komai yazi mata a yadda take son shi.
A ranan ne zancen mutuwar lndo ya bade ko‘ina. Duk inda ka gfta a cikin masarautar za kaji ana zancen mutuwar Indo, mutuniyar kirki mai matukar son mutane da kyautatawa. Kowa nata ne sam bata da kyamar talaka. Duk da cewa diyarta na da bakinjim’ amma sam hakan bai shafe ta ba. Wannan halin nata na kirki yasa kowa ya yi kukan rashinta. Babu wanda zai bude baki ya bata shaidar banza, sai dai makiyinta‘ K0 makiyin nata ma sai mara tsoron Allah. Domin kuwa ita kowa nata ne, da masoyi da makiyi duk tana jan shi a jikinta. Wannan bai ishe mu ba, bayan Salbiyya ta haifi Adnan haka muka kai sunansu wurin Boka Fartsi, ya musu aikin da dole sai da suka tafi kasar Lebanon daga inda mai martaba ya auro ta. Idan ta dawo ma haka za mu sake zuwa ya mata wani aikin da a ranan za suji tsanar Nigeria su tafi Wannan dalilin ne yasa sam Salbiyya da yaranta basu da shaawar zama Bilbah. Da sunzo zasu koma.
Muggan asirran da boka Fartsi ya rinka dirka wa mai martaba har basu da adadi. Baki daya Fulani Kursiyya ta gama shanye shi. Idan ta zana layi ta ce karya ketare shi wallahi ba zai taba ketare shi din ba. Idan ya ga tana son abu jikinshi na rawa yake aikatawa.
A yanzu haka da komai yajuye mana, ina tsammanin rana dayar nan tak ta barawo da ake fadi ce ta zo kanmu. Ashe bamu da labari Uwar biyu ma ta rasu, ita ce kadai gatanmu, da ita kadai muka dogara.
Yanzu haka maganar nan da nake muku, lndo tana nan ciki bandaki, kuna lekawa ta can ciki zaku gan ta tsaye tamkar gunki. A haka take tsawon shekara talatin. lta ba rayayya ba ita ba matatta ba. Iyakacinmu da ita idan Boka Fartsi ya bamu wani sako da za muyi aiki da ita, sai mu cusa shi a cikin bakinta, kafin mu fito har aikin ya tabbata.
Labari daya ne ya rage ban baku ba, wato yadda aka yi muka kashe Gimbiya Sa,adiyya. Wannan kuma ina so ne Fulani Kursiyya da kanta ta fada muku. Inga karshen taurin kai irin nata.”
Murmushi Mallam Khamis Ciro ya yi sannan yace “In dai wannan matar mai bakin taurin kai ce ba zata taba confessing don kanta ba. Taurin kan da bai da amfani ke nan, na banza, domin kuwa komai tsananin taurin kai da girman kanta ba ta kai Shaidan ba. Kuma a karshenshi la’anannen Allah ne, wuta ita ce sakamakonshi ranan gobe kiyama. Yanzu dai duk ba wannan ba. Mu samu a fito da baiwar Allah‘n nan mu ga halin da take ciki. Kodayake dai kun ce idan wani ya bude ya gan ta zata dawo daidai. Muje ko mai martaba.”
Tsananin tashin hankalin da Sarki Sani yake ciki bai sa ya iya ko motsawa ba. Zaune dai yake amma tamkar ba shi ba. Jin komai yake tamkar a mafarki, wai shi ne ke ganin wannan ranar da ko a mafarki bai taba tunanin akwai ta ba.
Ganin tamkar ba shi a cikin hayyacinsa yasa Waziri da Khalili suka bi bayan Mallam Khamis suka zarce bandakin.
Babba ne sosai yana da ciki da falo. Daga can ciki suka hangi mace sanye da riga da zani na atampa, bakinta a bude sai idanuwanta rufe. A kame kam tamkar gunki. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Shine abin da su duka ukun suke furtawa.
“Ban taba tsammanin da gaske ana aikata irin wannan zaluncin ba. Ashe da gaske mutum yana zaluntar dan uwanshi mutum saboda wani abu na duniya?”
Maganar da Waziri yayi kenan yana jin saukar hawaye a bisa kumcinshi. Mallam Khamis ya yi murmushi. “Mu wannan duk ba bako bane a wurinmu, mun sha haduwa da shigen haka. Sai dai bambancin kawai gaskiya ban taba haduwa da rayayyen da aka mayar haka ba. Zaluncin yayi yawa. Shekara talatin da kusan biyu a garkame wuri guda? Astaghfnrullah!” Kamar ance Mallam Khamis Ciro ya rufe bakinshi sai Indo ta fara wata irin kara kankara keyi idan ana farfasa ta. Duk inda ya kame din yana darewa,jikinta yana saki, a hankali tana komawa daidai.
Duk suka yi tsaitsaye suna kallon sarautar Allah. Kafin a hankali komai nata ya gama daidaita. Fuskarta ma ta saki. Bakinta ne ya fara rufewa, sannan ta dan kyafta idanuwanta hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Rijif! Ta fadi kasa da karfin gaske. Da sauri suka yi kanta, Mallam Khamis sai tofe ta da addua yake. Ganin cewa bai kyautu yana ambatar sunan Allah a cikin bandaki ba yasa yace dadu Khalili su taimaka mishi su ciccibe ta a koma cikin daki da ita. Bayan sun ciccibe ta kai tsaye suka fito da ita. Da sauri mai martaba ya mike tsaye cike da mamaki. He couldn’t believe wai lndo uwar gidanshi ce yau ga shi gata, bayan rabuwa da yayi da ita na tsawon lokaci a matsayin ta mutu, shi da kanshi ya saka kanta a cikin kabari. Mallam ya budejakarshi ya dauko wani garin magani, ya debi kadan a hannunshi sannan ya zuba wannan ruwan nashi na ciki gora duk atam hannun,ya murje sosai, ya shafe shi a fuskar Indo. Firgigit ta zabura hade da kara sauke ajiyar zuciya.
Ya kara diba ya shafe mata fuska a kalo na biyu, a take ta bude idanuwanta sai kallon su take yi tamkar wacce ta tashi daga wani dogon barci. “Maimartaba matso kaga ikon Allah. Zo kaga Indo ta bude idonta. Lallai lamarin Ubangiji sai Shi. Tabbas babu karfi babu dabara face a wurin Allah madaukakin sarki.” Tamkar kafafuwanshi ba zasu iya daukar gangarjikinshi ba haka ya doso inda suke. Ya kalli lndo dta kafe ceiling da kallo idanuwanta a bushe kyam. nunawa yayi a gabanta, ya saka tafin hannunshi na dama ya dan shafi idanuwanta suka rufe. Sannan ya dafe kanta ya hau tofa mata addu’o’i iya wadanda ya sani. Shi yana yi Mallam Khamis nayi, sai Waziri da Khalili ma suna yin nasu.
Daga haka sai ta hau yunkurin amai da karfi, tamkar fitar rai. Mallam Khamis yace “Mu kokarta a tasar ta zaune. Ina ga dole sai ta amaye abubuwan da aka rinka cusa mata a bakinta. Ma‘tsalar yanzu da muka shiga da mun sani kafin komai an kwakulo abubuwan cikin bakinta. To sai ba muyi ba kuma harta hadiye. Don haka dole sai ta fitarda su sannan komai zai daidaita. Kar kuma mu fasa addua. Babu abin da yafi karfin addua. Ke kuma Kursiyya ki saurare ni kawai.”
Duk abin nan da yake faruwa fatalwar Saadiyya na nan zaune sai zubarda hawayen jini take yi. Tana kallon mahaifiyarta cike da tausayi, sannan tana kara tsanar Kursiyya da Zabba’u, hade da tunanin mummunan hukuncin da zata daukar musu.
cikin kakarin aman da Indo keyi har dajini. Maimartaba yace ko ruwa za a bata? Amma Mallam Khamis yace kar a bata tukunna, a dan dakata harta gama hararda komai na cikin. Sunfi minti sha biyar tana yunkurin amai kafin a hankali saiga wani dan guntun zare ta fiddo, wanda ba zai wuce tsawon gabar yar yatsa ba. Fari tas da shi.
lkon Allah kuma tana fiddo shi tamkar ba a yi ba. Ta daiyi lakwas na wahalan aman da tayi, amma aman ya tsaya.
Khalili yace “To Mallam ji dan aman, ko dai bashi kenan ba?” 
Mallam yace “shi kenan  Dukkan abubuwan da aka ba ta sune suka dunkule suka zama wannan dan zaren. Yi sauri ka samo min ashana kuga ikon Allah.” 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE