Trending

GIRMA YA FADI COMPLETE HAUSA NOVEL

GIRMA YA FADI COMPLETE HAUSA NOVEL

 

 

 

KAUYEN GWARZO, 1988
Sunan da na taso da shi tun ina karama shine Zaynab Aliyu Gwarzo. Asalin mahaifina mutumin garin GWARZO ne da ke cikin jihar Kano da ake kira Malam Ali Mai Almajirai. Malam Ali, sananne ne a ciki da wajen kauyen Gwarzo da ya shahara wajen ba da maganin cututtukan da suka shafi aljanu daga Alkur’ani mai tsarki.
Bayan magani da yake bayarwa yana karantar da dubban almajirai, kuma fitaccen manomi ne, makiyayi. Ya mallaki manya-manyan gonaki guda biyar, tirken dabbobi zuwa tsintsayen gida irin su kajin gidan gona, agwagi, talo-talo, jimina, gada, zabbi, akuyoyi da sauransu.
Haka nan Malam Ali mutum ne mai cikar mutunci da tsananin kyauta, duk wanda ya kwana ya tashi a garin Gwarzo ya san da hakan. A garin Gwarzo baki dayanta Malam Ali fitacce ne da ake matukar girmamawa gami da ganin kima da mutuncinsa. Daga inda duk ka ce kana neman gidan Malam Ali, za a ce da kai “Mai Almajirai?” Daga ko’ina a cikin garin Gwarzo za a rakoka har dakalin gidan Malam Ali Mai Almajirai.
Matan Malam Ali na aure uku ne, amma cikinsu babu wadda Allah ya baiwa haihuwa sai uwargida Inna Dubu da ta haifi Umar-Faruk shi kadai ya tsaya. Sai da ta yi haihuwa tara duk mutuwa suke tun suna jarirai wato (wabi).
Daga Inna Dubu sai Inna Rakiya, sannan Innata, Rabi. Rabi matar Malam ta karshe Buzuwa ce fara sol, ita ce mahaifiyata kuma a hannunta na taso.
Asalin auren Innata da Malam ya samo asali ne daga kawo ta neman magani, kasancewar Malam mutum mai ta’ammali da mutane daban-daban daga ko’ina cikin kasar Hausa da kewayen ta, manyan ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan boko da manyan ma’aikatan gwamnati kan zo neman taimako wajen sa a kan harkokin su, kuma suna ganin nasibi na hakika cikin taimakon sa, daga garuruwa daban-daban ana kawo marasa lafiya wadanda ya ware musu sashe guda a gidansa.
Ya kan bada lakani na kasuwa, cututtukan da suka dami bil’adama, musamman wanda ya shafi aljanu zuwa cututtukan yau da kullum. Hakan ne yasa kullum za ka ga kofar gidanmu cike da motocin zamani wannan ya shiga wancan ya fita.
To hakan ce ta hada shi da Alhaji Sani Buzu, shahararren dan kasuwar fata kuma dan siyasa daga garin Yamai ta kasar Niger. Ya zo Kano ne musmaman domin nemawa ‘yarshi maganin tabin aljanu da ta samu, tare da kanwarta Nuratu.
A cikin Kano ne ya samu labarin Malam Ali ta hanyar wani abokinsa dan kasuwar Niger zuwa Kano, wanda shima ya sha zuwa amsar taimako hannun Malam Ali. Alhaji Sani bai san kowa a Kano ba, karewa ma ko zuwa bai taba yi ba sai a kan lalurar Rabi. Akwai kauna sosai tsakanin shi da ‘ya’yanshi biyu Rabi da Nuratu, wadanda mahaifiyarsu ta mutu ta bar mishi, tun rasuwar ta bai kara aure ba.
Ya kawo su Rabi Kano da zummar neman magani ne kawai. Malam Ali, ba wai warkar da mahaukata yake ba, illa in lalurar kankanuwa ce ta kuma shafi aljanu bata gagararshi, ya kan raba mutum da su cikin ‘yan satittika daga ayoyin Alkur’ani mai tsarki.
Ya kawo Rabi da kanwarta Nuratu gidan Malam Ali tsayin sati biyu ana yi mata magani, anyi sa’a lalurar tata karama ce, cikin lokaci kankani Malam Ali ya raba ta da su.
Don farin ciki Alhaji Sani ya ce ya fadi komai yake so in dai bai fi karfin sa ba shi ko ya yi mishi. Budar bakin Malam Ali sai cewa ya yi, ai ko baka bani komai ba ka bani auren Rabi Mana? Ya fiye mini duk abin da za ka bani, bana karbar ladar aiki sai sadaka a inda ake da bukatar ta.
Jikin Alhaji Sani ya yi sanyi, don bai taba kawo ma ranshi bukatar da Malam Ali zai nema kenan ba, da ko kusa bai fara wannan subutar bakin ba.
Hankalinsa ya tashi matuka, yaran da basu ma taba zuwa Kano ba, ko kalmar “zo” da Hausa basu sani ba, gashi daya ba ta iya rayuwa sai da ‘yar’uwarta, akwai kauna da shakuwa ta hakika tsakanin Rabi da Nuratu.
A can Yamai suna tare ne da mahaifiyarshi, yana sa ran yin aure cikin wannan shekarar kamin ayi zaben da yake nema a Jihar su (Damagaram).
Ya yaba da rayuwar Malam Ali da iyalinshi, ko kadan bai raina musu ba, suna cikin suttura da cima mai kyau da rufin asiri, amma ita Rabin yake ji ko za ta amince, da yadda zai tafi da Nuratu babu Rabi.
Abin mamaki da aka tuntubi Rabin farat daya sai ta amince, wannan ba karamin abin mamaki bane, domin a haife Malam Ali ya haifi ukun Rabi.
Ita ko Nuratu ta ce kafarta kafar Yayarta wato ba za ta bi Baban ba. Shima Malam Ali ya yi alkawarin rike Nuratu tamkar Faruk har auren ta.
Alhaji Sani bai tafi ba sai da ya yankawa Malam Ali sadakin Rabi ya biya. Allahu Akbar! Ashe karshen rayuwar sa kenan, sallamar shi kenan ta har abada da ‘ya’yansa Rabi da Nuratu.
A kan hanyar shi ta komawa gida Niger, cike da zullumin bayanin da zai yiwa mahaifiyarshi da ‘yan’uwansa a kan auren da ya yiwa Rabi babu saninsu babu yardarsu, cikin jinsin da ko a tunani basu taba yin na tsintar kansu a ciki ba, a kasar da basu ko sani ba, jirginsu ya fadi a wani tsauni kafin a kai Niamey, babu maganar mai rai a ciki.

Ni dai na taso bani da labarin NURATU. Gidanmu cike yake da ‘ya’yan riko, domin kowacce cikin matan Malam tana rikon ‘ya’yan ‘yan’uwa, don haka gidan Malam Ali da albarkarsa ba za ka ce ba a haihuwa ba.
Na tashi tashin gata kuma tashin sangarta, kasancewata auta, wadda ba ta zo ba sai bayan haihuwar Faruk da a kalla shekara goma sha biyu, bayan ni kuma ba a samu wata ba. Don haka suke kira na “Kyauta” wato Kyautar Allah. Inna ta Rabi kadai ke ce dani “Abu” shi ko Malam “Zaynabu-Abu” ne baya ragewa.
Bayan Inna Dubu Innar Faruk Inna Rakiya ba ta haihu da Malam ba, ‘ya’yan kanwarta ne take riko. Rayuwarsu cikin mutuntaka da sanin ciwo kai ce, domin kowacce cikin su ta mallaki hankalin kanta, babu rashin jituwa ko kadan a tsakaninsu. Dukkan su sun hada ‘ya’yan ‘yan’uwa da almajiran Malam sun rungume a matsayin ‘ya’yansu, sai dai a kan ce wane dan dakin wance ne, wance ‘yar dakin wance ce.
Akwai Yaya Halima da Inna Dubu ta rike shekarun baya ne aka yi auren ta, Lami da Laure da Inna Rakiya ta rike suma duk Malam ya aurar dasu sun haihu a gidan mazajensu.
Ina da shekaru goma Ya Faruk ya kammala sakandire, inda duk za shi ka ganshi rike da hannuna, ko me ya ci a waje sai ya rago mini, idan makaranta ya je ya dawo sai ya kawo min tsarabar rake, gurji, gyada da makani. Ina son Yayana Faruk, domin halayen sa dake burge kowa.
Da fari dai Faruk shiru-shiru ne, miskili na kin karawa, da wuya ka ga yana hira in ba dani ba ko Rabi, haka da wuya ka ga ya daga ido ya dubi mai shigowa sai dai ya amsa masa sallama ba tare da ya dago ba.
Akwai aminci da mutunta juna na hakika tsakanin Ya Faruk da Rabi, ta yadda duk wata damuwar Faruk Rabi ta sani, komi nashi da ita yake shawara, haka duk wata ajiyar shi mai muhimmanci a dakinmu take, kai ba za ka ce kishiyar Mamansa ce ba.
Halin dattaku irin na Ya Faruk daban yake da na kowa cikin gidan, yaro ne a zahiri, amma halinshi na manya ne, tun ina yarinya a ban san komi ba, na san Faruk kyakkyawa ne, dana kan karkace kai in bata lokaci ina ta kallon sa, shi din bai sani ba.
Idan ya juyo muka hada ido sai ya ce, “Kyauta yaya ne kike kallo na?”
Mai hazaka da mai da kai, kuma mai nasara a kan duk abin da yasa gaba. Faruk tun yana shekaru goma ya haddace Alkur’ani, haka har girmansa da shigar sa babbar makaranta bai daina zama yana daukar karatun buzu ba wajen Malam.
Faruk ne mai taje min dogon gashina tun ina shekaru uku, ya kallabe shi kalba biyu, hagu da dama, shi yake zabar min kayan da zan sanya, ya kuma goya ni a bayan keken sa ya kai ni makaranta, in an tashi ya je ya dauko ni dai-dai da rana daya bai taba gazawa ba.
In Innata na mun wanka, sai ya girka kujera ya zauna yana azalzalarta ta daina cudawa da karfi, fatar Abu bata da kwari, ba kya gani ja ce ne? Inna sai ta tsage jini ya fito? Rannan ya ce,
“Inna Rabi daga yau kada ki sake yiwa Abu wanka ni zan dinga yi mata, don na lura wallahi da gayya kike cudawa da karfi, ba kya tausayin fatar Abuna”.
Rabi ta yi dariya ta kira Malam ta ce ya raba wannan rigima ta Faruk. Malam ya ce, “Faruku namiji baya yiwa mace wanka ka yi hakuri. Daga yau babu mai kuma yiwa Zainabu-Abu wanka da soso”.

Tun tasowata na san Innana Rabi na fama da wani bakin ciki na shekara da shekaru, wanda in har ya ciwo ta, takan shiga daki ta yi ta kuka. A irin wadannan lokutan, Faruk kadai ke iya tausarta da kwantar mata da hankali. Na kan gansu suna ta kus-kus, na ita damuwar da ke damun Inna Rabi, wadda yawan shekaru da yanayin rayuwa bai taimaka ba ko kankani wajen gusar mata da wannan damuwar ba.
Ta kan ce da ni,
“Kyauta rayuwa abin tsoro ce, haka zuciyar mutum sau tari makiyarshi ce. Ta kan umarce shi ga abin da ta san ba dai-dai bane kuma Allah ya yi hani da shi. Ki guje ma sharrin zuciya, kuma ki tsarkake zuciyar ki, daga sabon Allah komai kankantarsa.
Ki nisanci ZINA, ki kiyaye al’aurarki, mutum da kike gani abin tsoro ne, musamman wanda kika taimakawa, dama kuma Annabi (S.A.W) ya ce, “Ka ji tsoron sharrin wanda ka kyautatamawa”.

A wadannan shekarun, bana damuwa da irin wadannan kalaman nata, kamar yadda bana fahimtar komai a cikinsu, domin hankalin bai isheni ba. Abinda na sani ko kuma na fahimta kawai shine, Inna Rabi rayuwarta daban ce da ta sauran matan Malam, komi baya faranta mata. Haka mafificiyar kaunar da Malam ke gwada mata, bata burgeta.
Tana da wani mummunan kullaci a kan mutane da al’amarinsu, haka gaba dayan rayuwarta cikin kunci take. Sau daya na taba ganin ta tayi dariya a tun tasowa ta, wato ranar da Faruk ya ce ba ta tausayin fatata. Kokarin Malam da Faruk a kullum shine farin cikin Rabi da farin cikina, amma hakan baya hanata zubar da hawaye a yawancin lokuta.
Duk wata kulawa ta uwa da uba kusan in ce na same ta ne daga Ya Faruk, yana sona, yana kulawa dani tamkar ‘yar da ya tsugunna ya haifa. Haka nan komi nawa mai muhimmanci ne a awurin Faruk, shirme ne ko akasi.
Ire-iren mutanen birni da ‘yan boko da kan zo wurin Malam, ba zan iya iyakance alhairan da nake samu daga garesu ba, kullum cikin sabbin kaya, kayan wasa, sabbin dinkuna, kayan zaki da kayan kwalam nake saboda farin jinin da Allah ya yi min. Wasu kuwa kan ce kyawuna ne yake sayo min farin jinin, kowa ya ganni sai ya tanka, ya kuma tambayi Malam game dani, don ko a farcen kafa bamu yi kama ba (komi nawa irin na mahaifiyata ne) tamkar ta yi kaki ta tofar. Amsar da Malam ke bayarwa a kullum shine, nayo Innata ne, wadda take Ba’abziniyar Niger.
Ni kaina na san ni da Inna ta daban ne a cikin gidan, haka muke wal! Sai ka ce tocilan don haske a cikin jama’ar gidan, ko kuma ka ce wata ne a cikin taurari.
Sai dai abin da yake matukar burge ni da rayuwar gidanmu shine, ba za ka taba ganin an nuna wariyar launin fata ba, da ni da su Indo da Hafsisi da su Dubu ke riko, duka su Inna Dubu sun dauke mu daya ne babu banbanci. Sai dai Malam da Ya Faruk a kullum, a komi kuma a ko’ina, su kan nuna nice ‘yar gaban goshinsu.
Halin Innata da irin rayuwar ta kam ya riga ya zame min jiki, har baya damuna, ba ni kadai ba haka duk kishiyoyin ta babu mai nuna damuwa da yanayin rayuwar ta, don in da sabo sun saba. Sai ta wuni ba ta yi magana ba sai bin kowa da ido, haka kullum daren Allah cikin yi min nasihohi da tsoratarwa a kan ZINA take.
Ni a lokacin ma ban san mene ne zinar ba, ban gama tantance ma’anar kalmar zinar ba. Abin da na fahimta kawai shine; zina wani abu ne da Innata ke matukar kyamata, kuma wani abu da Allah ya yi kakkausan hani da shi.

 

DOWNLOAD BELOW 👇

GIRMA YA FADI complt

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE