HARSASHEN SO CHAPTER 1
HARSASHEN SO
CHAPTER 1
Ah Ah wayyo, wayyo Allahna, sai nishi takeyi cikin yanayi na jigata da wahaltuwa sai dumamiƙe wata “yar tsofuwa takeyi tana kuka, cikin tausayawa take bata hakuri tare da mata sannu,
Tafiya yake sai faman gyara zanin daya yafa a saman kafadar sa yakeyi, zugar “yan daba ne biye a bayansa kowa da wuka a hannunsa wasu kuma gorori ne yayin da wasu ke rike da “adda a hannayen su, A kofar dakin da matar take ciki ya dakatar dasu, cike da izza ya harbi kofar dakin da kafar sa ta bude ya shige ciki rai a jagule, Kwance take a saman gado cikin yanayi na nakuda banda zufa babu abinda takeyi, sai kuka takeyi tare da hada hannayenta biyu alamar neman gafara, kallon mijinta tayi cikin kuka tace don girman Allah kayi hakuri, Gyara rikon bindigar hannun sa yayi sannan yace sassauci daya zakiyi ki fanshe kanki a wurina, shine haihuwarda namiji, dan na dade inajiran zuwan wannan ranar,
Sake yafa zanin daya lullube jinkinsa yayi sannan yaci gaba da cewa, tun a daren dana tabbatar kin samu ciki nake miki gargadi da kada ki haifo min diya mace, a daidai lokacin data saki kara alamar abinda ke cikinta yana gab da fitowa duniya, Da sauri ya matsa kusa da ita ya ida jawo abunda ta haifa da kansa, wani irin harbi yakai mata yayin daya ga abinda ya samu, kallonta yayi sannan yace dan ubanki duk gargadin da na miki saida kika haifo min mace?……. Cikin kuka tace don girman Allah mai gida kayi hakuri, cikin tsawa yace rufemin baki dan ubanki, maza ki mayar da ita a cikin cikinki kice namiji kike so shegiya, cikin rawar murya “yar tsohuwar tace haba Mansir mi kake yi haka? Babu ruwanki mama, sai kawai ta rasa abinda zata haifo min sai mace? Bayan tasan makiyana suna zageye dani kullum burinsu suga bayana, nayi alkawari dan da nahaife shine zai ciromin kan Bashirya kawomin gabana wannan shine mafarkina kullum kuma shine tunani na!
Cikin fushi ya juyo ya kalli matar sa dake kwance cikin jini, daka mata tsawa yayi sannan yace zaki mayar ko kuwa sai na mayar miki da kaina matsiyaciya? Cikin kuka da rawar murya banda kyarma babu abinda jikinta yakeyi tace kayi hakuri ikon haihuwa kadai Allah ya bamu, bamu da zabi namiji ko mace wannan duk shine yake bayarwa, kuma ko a tarihi
ban tabajin wanda ya aihu ya sake mayar da dan da sunan a canja masa wanda yake so, Saida ya sauke mata mari biyar sannan yace to ina so yau ki kafawa duniya tarihi, inyi alfahiri dake ki zamo mace ta farko a duniya kin samu mace kin canzo namiji dan cika umarni mijinki, idan kuma baza ki iya ba ni bara na mayar miki da ita sai ke kuma kiyi kokari ki haifo min namiji kinji,
Idan har kika cika min burina nayi miki alkawari ko bakya raye saina kawata kabarinki da furanni duk safiya zanje na gaishe ki inyi miki ban gaji da haihuwa,
Tabata yayi jin yana ta hauka shi daya amma tana kallon sa tayi shiru, ke bakyaji na ne? Shiru yakeji, dan yatsan sa ya saka cikin idonta amma ko motsi daya batayi ba, kecewa yayi da wata irin dariya sosai saida ya samu natsuwa yace shegiya ta zabawa kanta hukunci mafi sauki, taga tafiya lahira yafi mata sauki tasan horona zafi gareshi ai da baki mutu ba
yau din nan wallahi dasai diyar ta koma cikin cikinki karamar mara kunya,
Kallon mahifiyar sa yayi sannan yace mama, ki rufe min wannan sirrin namiji na haifa ba diya mace ba, kallonsa mahaifiyar tasa tayi sannan tace ban gane namiji ba? Tsawa ya daka mata cewa ‘NAMIJI’ na haifa ba ‘MACE’ ba to mansir namiji ka haifa, Dariya yayi sosai tare da cewa maza daukarta a wuce a shiryata cikin kayan maza, Babu dadewa mama ta dawo rumgume da jaririya a cikin shiri kamar yanda danta ya umurceta, amsar jaririyar yayi sannan suka fita a dakin da gawar mama tana biye bayansa kamar bindin sa,
Ihu Yaransa suka dauka tare da daga wukake sama, shi kuma sai yashe baki yakeyi, bayan kowa ya saurara ne mansur ya fara magana cewa, faduwa tazo daidai da zama yayin da karfina yake neman karewa na samu babban jarumi a gidana, gaba daya suka kara cakumewa da ihu ……..
Bama kajin karar komai sai usir da suke busawa, hannu ya daga musu alamar su saurara, bayan sun sake natsuwa, mansiri yace dan cikar jarumtar jarumin uwarsa ya fara kashewa sannan ya fito duniya dan ganin bayan makiya na, ihu suka kara dauka lallai jarumi barka da zuwa duniyar makiya, Saboda haka kai balaga maza ga wasika zuwa ga bishir ka kai masa, cikin girmamawa wanda aka kira da balaga ya anshi wasika ya hau doki ya Flta dan cika umarnin mai gida, Saida mansur ya gama murnar haihuwar jarumi sannan aka shirya Maryam dan kaita makwancinta,
Balaga a gidan Bashir wanda yaransa na ganin sa sukayo kansa kowa ya cire wukarsa daga cikin kubenta, bashir ne ya dakatar dasu, kowa ya tsaya ba dan ransa yaso ba, balaga ne ya isa gaban bashir sannan ya bashi takardar da mansurya aiko da ita, Murmushi barshir yayi sannan yace ni bana taba duk abinda ya fito daga hannun makiyi na, dan haka warwareta ka karanta muji abinda dan shegiyar yace, bude takardar yayi ya fara karantawa kamar haka,
Na san a yau zakayi baccin bakin ciki domin makashin ka yazo duniya, yazo da na”un azabobi iri iri, kuma yayo dakon mugunta ta kashemin kai a cikin ruwan sanyi, ina maka albishir da gidanka ya kusa zama tarihi a doron kasa jarumi,jarumi da uwarsa ya fara saida
ya kasheta sannan yazo duniya daukar sa hatsari ne domin hannuwa yake gundilewa, mutuwar ka, mutuwarka ta doso ka fara kidaya shekaru 25 masu zuwa sanan ka yanki makabarta_
Dariya sosai bashir yayi bayan ya gama jin sakon makiyin da duk duniya baida kamar sa, sannan ya kalli yaransa yace kunji wani hauka wai “yar cakukuwar jaririn da aka haifa yau
Shibe ya fara kirga shekarun mutuwa ta, da sauri ya mike tsaye tare da daure fuskarsa sosai yace ka fadawa ubangidanka nine ajalinsa shida abinda yake alfarin yazo duniya dan ganin bayana, ka fadawa makiyi ni bashir nace dashi da dan nasa da dukan yaransa duka gangar
jikinsu tawa ce, ya daki gabansa tare da buga kafarsa kasa harsai da kura ta tashi,
Juyawa balaga yayi yahau dokinsa ya bashi linzami sai diddige yake masa doki ya dibi hanya sosai, maza ku tattara min kasar da daya taka kuje kofar gidansa ku zubar, ……..
Mama zaune a gaban danta rokonsa takeyi da ya taimaka ya bawa jaririyar nan suna, amma fur yace sunansa ‘JARUMI’ cikin lallashi tace fadamin sunan sirrin nata, na bata sunanki, sannan kuma idan har kika riketa a zaman namiji har abadan duniya bazata gane ita wacejinsi bace, zatayi ta zama a matsayin namiji, yana fadin haka ya mike a wurin ……
Bayan shekaru goma, ‘JARUMI’ ne zuge a cikin kayan koyon fada, mansur yana daga saman bene hawa na ukku a cikin katafaren gidansa, tuffa ne a hannunsa yana ci yana kallon
karon batta tsakanin jarumi da sauran garadan daya hadasu fada …….
Wata irin shareriyar wukace a hannun jarumi wanda mahaifinshi yayi masa lakabi da ‘SHALELE” banda dariya babu abinda mansur keyi ganin shalelen sa yasan salon cuta da mugunta,
Saidai shalele yayi zamiya yakai sara, idan kuma aka kawo mata suka saidai ta zuke, a cikin fafatawarsu da wani babban jarumi a cikin jaruman mansur duk lokacin da zata kai suka mansur ganinta yakeyi kamar wani dan matashin zaki,
Yaba kokarin nata yasa shi mikewa tsaye yana tafa hannunsa ganin shalelen tasa tasan makwantar cuta, nuni yayi da duka yaransa su shiga ciki shalele ta kara dasu, gaba daya suka zagayeta ita daya tal a cikin filin karan batta, dariya mahaifinta yayi sannan yace wuta…
Bakajin karar komai sai kukan wuka cakau cakau kau kau kau, sai kallin wuta ke ‘tashi, wata irin dariya mansur keyi saboda lallai yaga diyarsa ta horu da irin horon daya horar da ita!, Ganin ta gajiyar da yaran ne, yasa mansurya sauko daga saman benen, dukawa yayi ya dauki wuka sannan yace shalele kara da babanka, ya karasa maganar yana murmushi..
Ja tayi da baya baya, cikin salon irin na fada, tirjiya tayi da kasa a bayanta,tana dan tamawa mansur kuma shima yana gyarawa dan fara karawa da diyar tasa, sun dade suna gwabzawa amma shalale bai gaji ba, mansur ne ya gaji dan haka aka ajiye makaman yaki, yaja hannun diyarsa suka wuce ciki, A gaban katon hoton bashir mansur ya tsaya, sannan ya dauki wata wuka ya cakawa hoton jikinsa har kyarma yakeyi saboda masifa, cikin siririyar murya shalele tace mai gida wannan hoton waye? Saboda wannan suna shine mansur yace wa shalele ta rika kirasa dashi,
Kusa da babanta ta matsa tare da gage masa hawayen idonsa, tace mai gida shine bakin cikinka ko? Cikin sanyin murya yace shine, amma kafin ya jika shalele ina so ka gama min da bayan dansa,
‘Da daya tak yake dashi a duniya ya dauki son duniya ya dora masa, sannan kuma saboda ni ya raba yaron nasa da garin nan ya turasa zuwa can kasashen turai, shalele ka taimaka min kafin ka kashe min bashir ina so ka dasa masa tsoronka a zuciyarsa ka gama min da bayan dan daya dade yake ma hidima a duniya ka ciro kansa ka kai a gabansa…. Ka kafa tarihi a kauyen nan ka zama tsoro mai sa tsoro a zukatan makiyana, Murmushi mai gida yayi sannan ya daki kafadar shalele yace ina alfahari dakai dana, murmushi shalele yayi tare da cewa ina alfahari dakai mai gida,
Mama ce ta futo tare da cewa shalele kazo kaci abinci kayi wanka, to mama ya fada tare da cewa mai gida sai anjima, sai anjima shalele, yana tsaye mama taja hannunsa suka wuce ciki ………
Hmm