HARSASHEN SO CHAPTER 10

HARSASHEN SO 
CHAPTER 10
Saida ta dauki tsawon mintoci sannan ta leko daga wurin data buya a hankali, bataji motsin kowa ba kuma bata ga kowa ba, 
Ajiyar zuciya tayi sannan ta fito, igiyarta ta dauka sannan ta wurwurata ta riko wani karfe dake Cikin gidan, duk wannan wayar da aka saka wanda ta zagaye gidan baisa shalele ta gane hadari bace a gareta, 
Babu ilimin sanin birni da abubuwan “yan birni itadai burinta kawai taga Mubarak shine kawai kudirinta, Kama igiyar tayi taja ta da karfi dan taji igiyar zata iya daukarta, saida ta tabbatar igiyar zata dauketa sannan ta kama ta fara hawa, Duk sojan dake bakin get motsi kawai yakeji karfe nayi dan a cikinsu babu wanda yayi bacci fira sukeyi, duk lokacin da shalele ta riko igiyar nan da karfi ta taho sai karfen nan yayi motsi, Uban waye nan? Wani soja ya tambaya, shalele dake bayan katanga ta zaro idanuwa tare da dakatawa ta daina tahowa, sai raba idanuwa takeyi kamar tayiwa sarki karya, Wata murya daban bata farko ba taji ance jawo ko wane dan iska ne ya gundule ukku kafin ya shigo cikin gidan, da sauri shalele ta daga kanta tana kallon wayoyin har wata jar danja suke fitarwa ga wani katako an sa hoton kan mutum ya gulle hannu daban kafa daban, 
Da sauri shalele ta saki igiya ta silalo kasa ai bata gama dirowa ba taji an fito, a daidai lokacin data fado kasa daf, da sauri ta mike ta kwalkwala da gudun bala”i, wannan soja kuwa ganin shalele ta ruga shima ya bita da gudu yana cewa ihu barawo, itama shalele ihu barawo take cewa tayi haka ne dan duk wanda ya taho ba ita zai kama ba tunda soja yana bin bayanta, Mutane suka fara Fltowa daga wurare daban daban amma shale|e tayi nasarar fecewa, wannan soja kuwa yaji bakin ciki da bai kama wannan shegiyar yarinya ba, dan harya tanaji irin horon azabarda zai mata saboda tunda yake a gidan Abak { Mubarak } bai taba ganin dan isa irin mai hijabi ba, amma duk ranar daya kamata saita ci uwata, haka ya hakura ya 
koma cike da bakin ciki a zuciyarsa. ‘ 
lta kuwa gudu takeyi harta isa gida, a kofar shiga gida ta tsaya tana sauke numfashin wahala, saida ta sarara sannan ta tattaro natsuwarta, magana tayi a bayyane cewa lallai shiga gida ya tashi daga sama { ta katanga ko bango }ya dawo ta kofa, lallai aiki sabo, A wahalce ta shiga cikin gidan dan dama ba rufewa sukeyi ba tunda gida ne na “yan tasha, shige da fice akeyi har safiya ta waye, Cikin bacin rai ta shiga dakinta dan taso idan ta shiga gidan Mubarak sai asuba zata flto zata zauna tayi ta kallonsa ne har gari ya waye! 
Daren yau bacci kona minti daya baizo ba a idon shalele zanen hoton Abak ta kurawa ido sai kallo takeyi babu ko kyaftawa, saida lokaci lokaci takan ajiye ajiyar zuciya, A gidan Abak kuwa tashin hankali sosai a tsakiyar daren nan bakajin komai sai khadija dake ta dure duren ashariya dunkulawa takeyi tana kara murzawa abinda kuwa ya kawo wannan tashin hankali shine…, 
Shidai yana sallah ne, ita kuwa ta farka danyin Fitsarin dare, bata dade da shiga toilet ba wayarsa ta fara kuka tana bukatar a bata dauki, Fasayin fltsarin tayi ta fito da gudu ta dauki wayar dan ganin mai kiransa a tsohon daren nan, Hafsat, haka ta gani kuma shima haka ya rubuta mata, da sauri ta dauki wayar jikinta har kyarma yakeyi ta fara kwalalawa uwar Hafsa ashariya. Zagi takeyi sosai itama Hafsa ta fara ramawa dan dama haushin khadija takeji sosai tunda kusan sati 1 idan ta kira Abak baya daukar wayarta idan ta tura sako babu reply wannan dalili yasa itama ta shiga dirkakawa uwar khadija zagi, yanajinsu dukansu amma baiyi magana ba, 
Bayan zagi gore gore ya fara tashi, amma Hafsa tayiwa khadija mai zafl sannan ta kashe wayarta tana maiyin dariyar rainin hankali, wani irin ihu Khadija tayi tare da jefar da wayar saida komai na cikin wayar ya tarwatse, da sauri ta matsajikin dressing mirrow tajawo inda Abak yake ajiye bindiga, Da sauri ta saita bindigarta fara barin Harsashe Mubarak yana kallonta baice mata ta tafasa bare a sauke, cikin kuka take cewa saina kasheki saina kasheki …… Wani irinja tayiwa lumfashinta tunda ta tafi bata dawo ba ta fadi kasa somammiya, Kallo yabita dashi tare da cewa Allah ya sawake dan wannan dama shine aikinta dan matsawa yayi ya dauki sauraran wayoyinsa ya flta daga cikin dakin! Cikin damuwa ya isa palo dan har kanshi ya fara ciwo shidai bayasan hayani kuma bayansan tashin hankali wannan masifa inaga ya auri Hafsa kuma? ‘Dan gajeran tsomaki yayi sannan ya fara kiran wayar Hafsatu. Bayan ta dauka ta sassauta murya cikin kissa da kwarewar bariki ta fara magana cikin kuka, kayi hakuri babu mai laifln nan saini da ban kira ba duk da haka bata faru ba, ni bansan kayi bacci ba, dan naga da rana baka da lokacin wayane bansan madam tana kusa ba, gaskiya na aikata babban kuskure amma kayi hukunci a gareni dan batawa matarka rai da nayi Shiru yayi harna tsawon minti 3, sannan Hafsa ta ce hello? Ummmm ai inajin ki, Abak ya fadi haka tare da sakeyin shiru, cikin tattausar murya Hafsat ta sake cewa kayi hakuri don Allah insha Allah haka baza ta sake faruwa ba, yayi kyau haka kawai ya fada tare da kashe wayarsa. 
Shalele da Khadija wannan dare ya zamar musu daren bakin ciki dukansu, ita dai babban bakin cikin shalele rashin ganin Abak dan taso a daren nan yau ta fada masa tana tsananin sansa san da duk a fadin duniyar nan bata ga wanda yake masa san da take masa ba, itace kadai ta dace da rayuwarsa, idan har Abak ya aureta a matsayin matarsa hakika yayi mata ya kuma dace zai kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarsa! Har garin Allah ya waye Shalele tana cikin kuncin rayuwa, da bakin ciki tare da tsinewa sojan daya ganta albarka amma lallai ya zama dole ta nemi Mai Nasara dan ya warware mata komai, 
A bangaren Khadija kuwa Abak bai sake bi ta kanta ba, dan dama idan ‘ta suma itace take dawowa tunda ya hanata sumar nan bata bari, shi kuma baisan ba itace takeyin hakanba zuciyarta ce dan duk lokacin da taji mace tayi magana dashi ji takeyi kamar zata mutu shi yasa take suma. 
Shalele bata koma gidan Abak ba har kwana biyu dan gani takeyi tana zuwa za”a ganeta amma yau tasha ta dubu mutuwa ko rayuwa duk wanda yazo a gareta tana maraba dashi. Kasuwa ta koma ta sake siyo waya babba mai kyau wai zata dauki Abak hoto idan ta shiga cikin gidansa. Daga kasuwan gidan ta nufa kai tsaye bayan taje ta zauna a inda ta saba zama 
dan sojojin wurin sun fara saninta sosai saboda yawan zaman da takeyi a wurin idan tazo zata gaishesu sai ta shari wuri tayi zamanta, “ Kurawa get in gidan ido tayi kamar tana kallon wani abun arziki dan tasan lokacin fltowar Abak ya kusa, kara kallon takardar hannunta tayi sannan ta sake kallon kofar gidan. 
Bude get in gidan taga anyi dan haka da sauri ta mike tsaye tare da gyara nikaf in fuskarta motar dayace ta fito kirar ‘G-Wagon’ haka ya tabbatar mata da Abak ne dagashi sai Mai Nasara yana tukawa. Ta dubu tasha tayi wurin motar tana daga musu hannu babu wanda ya saurareta sukaci gaba da tafiya, da gudu shalele ta ruga taje ta shiga gabansu ta inda motar zata wuce amma mai nasara bai daina taflya ba, ganin haka yasa shalele kwanciya a kasa wai idan zasu bi takanta subi su wuce, Mai Nasara sake take motar yayi da gudun bala”i Abak yace dakata, ka gani k0 waye baida niyar tashi karkayi kisan kai kana da alhaki har a wurin Allah kayi kisa da gangan wanda kuwa ya kashe da gangan shima a kasheshi. 
Shalele tana ganin sun tsaya ta taso da sauri saitin inda Abak yake ta tsaya sauke glass yayi tare da cewa ya akayi ne? Ba tare data tayi magana ba ta flto da takardar hannunta ta mika masa, kallonta yayi sosai amma bai anshi takardar ba. 
Mai Nasara ne yace ke ya akayi ne wai? Cikin rawar murya tace ba dakai nake ba da uban gidanka nake, cikin masifa Mai Nasara yace ke karki min rashin kunya zan ci uwaki. Saka takardar tayi da sauri cikin motar ta kwalkwala da gudu. Binta da kallo Abak yayi harta Dace, tsaki yayi sannan ya dauki takardar ya warware fara 
karantawa yayi kamar haka! _So mahadine idan da gaskiya idan ya shige ka ya wuce ƙaya!_ Murmushi Abak yayi tare da maimata kalmar a bayyane, sakeyin dariya yayi sannan ya kara 
kallon takardar yana mai dubawa sosai. 
‘Dan gajeran tsaki yayi tare da girgiza kansa, Mai Nasara yaja motar suka tafi. Yinin ranar nan wannan kalami ya tsayawa Abak a zuciya sai maimaita wa yakeyi, 
So Mahadine idan da gaskiya idan ya shige ka ya wuce ƙaya._ Cikin farin ciki Shalele ta isa gida ranta fayau. Tayi alkawari kuma bata sake komawa sai bayan sati daya, komai nata cikin farin ciki takeyi tanajin dadi fiye da tunanin mai karatu. Cikin farin ciki ta dauki makerta rubutu tayi a ajikin bango maganarAbak ta rubuta kamar haka! Ya akayi ne?_ Dariya tayi sosai tare da kwantawa saman kafet tana maijin farin ciki. 
Kamar yanda tayi alkawari sai bayan sati daya zata koma to bata koma ba, sai yau take da niyar zuwa dan yaune satin ya cika, wani dan karamin wuri ta samu ta da rezarta sabuwa ta yanka hannuta ta tara wannan dan wurin jinin yana diga a ciki, 
Saida jinin ya taru sosai sannan ta daure yatsan nata da kyalle, takarda ta dauka da gashin kaza ta fara rubutu da jininta amma daga wurin tsinin takeyin rubutu ba wurin jikin gashin ba! 
Bayan ta gama ta tashi sabuwar hijabi ta saka amma bata saka nikaf ba. Napep tahau ta nufi gidan Abak bayan sunje ta sallami mai napep, ita kuma ta nufi kofar gidan kai tsaye, bayan sun gaisa ne tace don Allah tana neman mai nasara. 
Lafiya kike neman sa? Eh lafiya qalau amma kawai kace masa ina neman sa, to we za’ace masa? Kace masa kawarsa tana neman… Bata karasa magana bama ya iso wurin. Cikin sakin fuska yace ah sannu da zuwa, yawwa shalele ta fada, Mai Nasara yace shigo mana saida taji faduwar gaba sannan tace tou. Cikin tsoro ta shiga ciki tare da fara waige waige Mai Nasara yana gaba tana biye a bayansa suna taflya, 
Wuri ya samar musu suka zauna, bayan gaisuwa Shalele ta fara kwararawa Mai Nasara karya dan taki yadda ta fada masa gaskiyar lamari. Suna zaune a wurin har aka kira la”asar tace zatayi sallah, “ 
Wani wuri yakaita dan tayi alwalla ai sai tace saita kama ruwa, dan nazari Mai Nasara yayi sannan yace tou kibi nan ki mike sosai zakiga BQ a wurin ki shiga akwai matar mai gadi a wurin, yawwa nagode ta fada tare da fara taflya, dan juyowa tayi tace don Allah kayi hakuri ka aramin wayarka zan kira gidanmu. Ciro wayarsa yayi shalele tazo ta ansa sannan ta wuce ciki, bata ida isa BQ inba ta fara daga kanta sama tana kalle kalle
Ko akwai C C T V camera a wurin babu dan haka ta fara duba wayar contacts ta shiga ta fara dube dubenta ganin bata iya gano abinda take nema ba yasa ta dawojerin kira. Mai gida Abak shine sunan da Mai Nasara ya rubutawa Mubarak a wayarsa da sauri ta fara kwashe number bayan ta gama dauka ta fara kiran daya daga cikin layinka data siya tafa san a kashe yake haka tayi ta kira saida ta gaji sannan ta shiga BQ in ta gaisa da matar tace mata sallah nayi ne a nan kina ciki baki ji ba, matartace Allah sarki, ita kuma shalele ta sanar da ita haka ne koda anzo bincike daga baya zata fada cewa ta shigo idan akace me tayi? Zatace tayi sallah ne, 
Godiya shalele tayi tare dayi ma matar alkairi dan hausawa sunce alheri mai hana mugun suna, shalele ta fadawa matar cewa sunanta shalele zata dawo wata rana kawo mata ziyara, matar tace Allah ya yadda, shalele tace kina da waya mu rika gaisawa ne? Eh ina da ita shalele tace yawwa sakamin numberki a nan, ansa matartayi ta rubutawa shalele number wayarta shalele tace ngode saina kira. Godiya matar tayiwa shalele ita kuma ta flto! Bakin get ta dawo inda Mai Nasara yake zaune cikin ladabi ta bashi wayar tare dayin godiya, ansa yayi ita kuma ta zauna tare da fara magana cewa gidan nan yayi kyau, Mai Nasara yace wallahi kuwa, kallonsa shalele tayi sannan tace tou yanzun gidan nan ina mutum zai iya gano dakin matar gida dashi mai gidan kansa? Wannan aisa ciwon dimuwa ya kama mutum. Murmushi mai nasara yayi ba tare daya ce komai ba, gyara zama shalele tayi sannan tace ai ko kai dan gidan nan baka san inda dakin mai gidan yake ba, dariya sosai Mai Nasara yayi sannan yayi tsaki yace kinga can nanne hanyar palonsa kina shiga nan zai sadaki dako ina da ina na gidan amma ba ta nan madam dinsa take shiga ba shi kadai yake shiga ta wurin sai kuma idan yayi baki, tanan yake shiga tanan kuma yake fitowa, Jinjina kai shalele tayi tare da cewa kasan gaskiya sai an baka lambar yabo, hira sukaci gaba dayi har aka kira magrif, cewa yayi to ki tafi gida nima masallaci zanje, mikewa shalele tayi tare da cewa bara na koma nayi sallah nima saika dawo, tafiya yayi ya nufi masallacin cikin gidan, ita kuma ta nufi wurin palon ta saka takardar da tayo rubutu a ciki. Wayarta ta ciro ta rubuta sako kamar haka! Barka da hutawa ya jama’a? Idan har ka shigo cikin gidanka kafln ka shiga ciki a bakin kofar palonka sako yana nan na ajiye maka!_ Tana gama rubuta sakon ta kashe wayarta tare da cire layin ta karya shi. A daidai lokacin da mai nasara ya iso wurin. Godiya tayi masa sannan ta kama hanya dan tafiya gida….
Abak kuwa dake hanyar dawowa gida yaga wannan sako ya shiga kokonto dan haka yana isowa gida ya fara dubawa inda akace an ijiye masa sakon, takarda ya gani dan haka ya fara zarewa sannan ya bude palonsa ya shiga, Saman kujera ya zauna da mamaki yake kallon takardar ya akayi aka shigo har gidan sa aka ajiye masa wannan iskanci ba tare da kowa yaga mai wannan sakon ba, tsaki yayi sannan ya bude takardar ya fara karantawa kamar haka. Masoyina Abak tunda nake ban taba ganin kyakkyawar fuska kamar taka ba!_ 
Duk kyawon kyau baikai kyawun fuskarka ba, Abak ina san na bayyana maka kaina Abinda ban sani ba shine daya ko zakaci gaba da sona idan kaga fuskata?_ Nasan cewa dai a halin yanzu kaima ka fara tunani na domin ina tare dakai inajin kalamanka masu dadi._ Saidai matsalar sani na ne bakai ba, to bansan yadda zata kasance inka sanni ba ban taba soyayya ba Abak shi yasa nake tsoron bayyana maka kaina._ Abak kadai san halin da mutum yake shiga a soyayyarsa ta farko, mutum yana zamantowa ne kamar yaro mai koyon rarrafe, ina so ka sani wannan wasikar da jini na na rubuto maka ita, kasan soyayyar jini tana dawwamane har abada Nagode, na barka lafiya daga mai kaunar ka boyayyah

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE