HARSASHEN SO CHAPTER 11

HARSASHEN SO 
CHAPTER 11
‘Dan gajeran nishi Abak yayi tare da komawa ya kwantar da bayansa a jikin kujera! Kara kallon takardar yayi yana mai sauke ajiyar zuciya, dan lumshe idanuwansa yayi sannan yayi magana a bayyane cewa, Wace ce ke kuma? Miye nasabarki da Abak har kike ikirari kin rubata wasika da jini, wace soyayya ce wannan ta yarinta kuma? Bude idonsa yayi tare da saka wasikar cikin kujera ya mike ya wuce ciki. Kai tsaye ta tunkari kofar gidan da take haya, amma idan hankalinta yayi dubu ya tashi ta shiga damuwa ta kidime gaba daya ta rude ganin mahaifinta tsaye dashi da tawagarshi! Cikin tashin hankali da tsoro tace mai gida? ‘Dan tabe baki yayi tare dajinjina kansa, murmushin karfin hali shalele tayi sannan tace da kanka haka? Tabe hannunsa yayi sannan yace da kaina mana ko kayi bakin cikin gani na ne? Ko daya mai gida. 
Saidai kawai nayi mamaki ya akayi ka gane inda nake ne? Dariya yayi sosai sannan yace shalele kenan ai karka samu wani damuwa kawai dama dai na biyo ne domin nayi maka jaje, Jaje mai gida meya faru ne? Saida mai gida ya sake shekewa da dariya sannan kalli yaransa yace kunji wani rainin hankali wai yanayi kamar baisan komai ba! ‘Daure fuska mai gida yayi tamau sannan ya juya bayansa rufe idanuwansa yayi tare da daga hannunsa na dama dan yatsansa manuni ya nuna sannan ya fara magana cikin rashin mutunci. Da farko ina miki albishir da bazance ina maka ba ina miki zan fada domin kin gama tonamin asiri na kuma kin gama lalata min shirina kinsa makiyina yazo har gidana yayi farin ciki kuma ya fadamin maganganu masu zafi saboda tabarbarewa yau diyar dana haifa har take san dan makiyina wanda bai sanki ba baima san kinayi ba, Wani jiri jiri shalele taji lokaci guda kuma zufa ta karyo mata harsai da ta cire hijabinta lumfashinta ya fara ja sama sama lokaci guda kuma ganinta ya dauke wani abu mai kama da mutuwa ta fara jiyo kamshinsa cikin wahala ta dafe daidai zuciyarta tare da lalabo bango ta dafa shi, hawaye ne suka kwaranyo daga cikin idonta ta kalli 
mahaifinta dakel wanda bata iya tantance kalarsa. Maganar mahaifinta takeji sama sama wanda bata iya tantance abinda yake fada, lallai idan har Mubarak dan bashir ne tun yanzun ta yafe lumfashi mutuwa itace kawai tafi cancanta da rayuwarta, 
Sai yanzun kunnuwanta suka dawojin abinda mai gida yake fada, me nayi miki shalele? Wannan wace irin kiyayyace ai ban taba tunanin zaka haifl da ya zama makiyinka ba sai a wannan karnin, 
Wata irin shaka mai gida yayi wa shalele ya shaketa sosai idanuwansa na tsiyayar da hawaye yace me nayi miki me nayi miki ne ……………….. ? Cikin muryar wanda yaji Shaka shalele tace kayi hakuri mai gida! 
Cikin murya mai kama da zan mutu mai gida yace wallahi bazanyi hakuri ba kuma bazan yafe miki ba, kayi hakuri wallahi ba laifina bane zuciyata ce, saida mai gida ya kwadawa shalele wani irin mari wanda yasata harta wurwure kamar an gyara ranfa sannan ta fadi kasa, tattakata mai gida yayi harsai da tayi amai sannan mai gida ya dagota. Yace Dan uban zuciyar miye amfaninta, tara hannunsa yayi saitin bakinta sannan yace amayota zuciyar dan ubanta, cikin kuka shalele tace bata fitowa mai gida, cikin tsawa yace saita fito dan amfanin zuciya a jiki aiki da ita, ke bakya amfani da taki dan da kina da zuciya irin tawa duk namijin duniya da bai baki sha”awa ba. Saboda na haifeki kawai na auri uwarki da bata mutu ba saina sawake mata aurena danni bansanjin dadi ba bansan so ba tun ina matashi na rayu da kiyayya na tashi a cikinta na girma da ita kuma kema dana haifa sai kin soke duk abubuwan dana soke a rayuwata, kai balaga ku wuce muje zuwa gidan dan iskan yaron nan! Cikin motar da suka zo da ita mai gida yajefa shalele kamar wata akuya, haka sukaja motocinsu suka tafl dan mai gida yasa Balaga ya gama binciken komai akan Abak kamar yanda Bashir yayi akan shalele dan tunda yaji labarin ta taho birni yasa aka biyota bincike sosai akai masa tare da hadin guiwar Mai Nasara ya dan fadi iyakar abinda ya sani A kofar gidan Mubarak kuwa masu gadi sun hana su mai gida shiga, dan haka mai gida yasa aka fara fafatawa tsakanin sojoji da yaran mai gida, 
Hayani ta kwaure a wurin sai masayar hannu akeyi, fada sosai tsakanin hukuma da kuma wanda ba hukuma,ba sudai hausawa cewa sukayi hukuma sai lallashi amma a bangaren mai gida babu! 
Fitowar mai gida yasa suka daina fafatawar domin sunsan mai gida ko waye a wurin Mubarak kuma shi Abak din ya fade musu cewa karsu kuskura su shiga fadan da ba nasu ba dan shima baya ciki kuma duk abinda shi mai gida zaizo yayi su barshi girmansa ne tunda kanin mahaifinsa ne uwa daya uba daya. Jan shalele yakeyi har suka shiga ciki yayin da yaransa suka tako masa baya, banda kuka babu abinda shalele takeyi. Suna tsaye a wurin suna neman ta hanyar da zasu bi 
Mubarak ya fito dan yaga komai, Cikin aji da natsuwa Mubarak ya fara magana cewa, sannunku da zuwa, gaba daya yaran 
mai gida suka juya suka kalli mai gida danjin abinda zaice, murmushi Mubarak yayi da gefen bakinsa sannan ya maida dubansa ga shalele yace me kike ma kuka ne ke kuma? lta kallon mai gida tayi bayan wani lokaci kuma ta dawo da kallonta wurin Mubarak, mai gidane ya fara magana, Kai dan karamin dan iska inajin idan baka taba gani na ba kana da labarina a wurin ubanka, tunda aka kagi duniya har zuwa yanzun nan da nake magana ban tabajin dadin fadin sunan makiyi ba magana mai dadi tausasa murya da kuma kallo mai sanyaya zuciya, tsakani na da makiyi sai kallo mai tada hankali magana mai sa firgici daga karshe kuma nayi kisa! . Dafa shalele yayi yana mai kallon Mubarak sannan yaci gaba da cewa yau da ana sake zuciya da saina sake zuciyar wannan dakikiyar yakai duka saman kan shalele wanda harsai da jini ya biyo mata ta hanci, mai gida yace dakai da ubanka da wannan diyar tawa duk duniya kune abinda na tsana a rayuwata ganin bayan dukanku ya zama wajibi a gareni, ita 
tana da dama har yanzun sassauci daya zatayiwa kanta shine ta ciremin kanka yanzun nan. Murmushin karfin hali Mubarak yayi sannan yace: hakan da zatayi yana nuni da cewa zai kawo zaman lafiyarku kaida Babana? ldan har haka zai gyara zumincinku na sadaukar da rayuwata ke Suleim sunan shalele kenan na gaskiya Ummu suleim zoki ki cire kaina. Ya fadi maganar yana mai durkusawa saman guyawunsa, 
Yana mai ci gaba da cewa san zuciya rudin duniya rashin sanin darajar zuminci yasa kunyi facali da fadar Allah, rudanin duniya tsagwaran san abun duniya ya lalata zumunci uwa daya uba daya, 
Yau ina so ka dauki takobin nan da kanka ka cire kan dan dan uwanka uwa daya uba daya nasan ko bayan bana numfashi nadama zata ziyarci dukan zuciyoyinku dan zuminci shima rai garesa duk wanda ya kashe shi zai tadda Allah idan har ka kasheni ko kasa an kasheni banajin komai kuma banajin bakin ciki nasan nida na tafi banyi gaggawa ba kuda kuke a raye bakuyi jinkiri ba, shawara daya zan fada muku wannan itace magata na karshe Mai gida ya katse shi ta hanyar cewa shawarar banza tufff da bakin bakin matsayacin nan, zumunci dani da matsiyancin ubanka tuni na kashe zumunci nayi jana’izar ta na binne shi saida na kunna masa uwata na hada da barkono tsidagu naci gaba da balbala fetiri harsai da kasarwurin ta bace saboda azaba, Juyawa yayi ya kalli shalele dajini keta diga ta hancinta hannunta ya riko ya mika takobin sannan yace kansa kawai nake so ki kawomin a gabana yanzu yanzun nan! Cikin kuka shalele ta rike takobin ta tunkari Mubarak wanda tunda ta taho ya sadda kansa kasa yana jiran saukar wuka. Lallai tana sansa so mai tsanani wanda data kashesa kamaryanda mahaifinta ya fada gara ta burmawa kanta wuka, Yayin da wata zuciya take umarta ta tayi amfani da damarta tunda tana a gabansa ta fada masa kawai tana sansa idanma tsireta mai gida zaiyi ya tsireta tadai fada masa tana sansa kuma ko bayan bata rayuwa zaiyi alfaharl’ da haka, kallonsa ta sakeyi a daidai lokacin data tsaya a gabansa, Goge hawayen idonta tayi sannan tayi magana a zuciyarta! 
Abun da ciwo kaso mutum ba tare da wanda kake so yasan kanayi ba, amma kuma bana tunanin akwai abinda yafi ciwo kamar kaso mutum ka kasa samun kwarin guiwar furtawa wanda kake so cewa kanasan sa, ubangiji yana jarabtarmu da soyayya ta karya cike da tarin rudani daga bisani kuma ya nufemu da samun soyayya ta gaskiya saboda mu fahimce wane irin ni”ima yai mana a gaba Hadiyar yawu tayi daqer wanda tajishi kamar ta hadiye mutuwa ne a makoshinta, ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi magana a bayyane cewa! Soyayya ta gaskiya tamkar fatarwa ne wanda kowa yake yawan maganarta, kuma kalilan ne suka ganta, soyayya ta gaskiya bata rabuwa da farin ciki har abada kuma sannan bata da karshe ku sanyawa ranku aminci da kuma soyayya kawai sai kuci gaba da tafiya, abinda kawai na fahimta soyayya tsakanin da namiji da “ya mace tilas ne in ba haka ba ko mutuwa ta wajaba ga daya daga cikinsu, duk ranar da wani masoyi ya rabu da masoyinsa ina da tabbacin walwala tayi bankwana da rayuwar wannan masoyin._ 
Dukawa tayi ta ajiye takobin a gaban Mubarak sannan tajuya ta kalli mai gida wanda baiji abinda tacewa Mubarak ba amma shi Mubarak yaji ta. Cikin sarkewar murya tace kayi hakuri bazan iya ba, 
Cikin fushi mai gida yacewa yaransa kuyi ta dukanta harsai kunji baya numfashi, gaba daya sukayo kan shalele suna kokarin rufa mata Mubarak ya mike tsaye tare da cewa kai ku kiyayeni. Dakatawa sukayi, ba tare da sun sake motsin kirki ba, kusa da shalele Mubarak ya matsa sosai har tana iya jiyo bugun zuciyarsa cikin sassanyar murya yace me kike cewa dazun nan da kika tsaya a gabana? A hankali ta daga idonta da niyaryin magana amma kafin tace wani abu tuni taji saukar wani gungumen abu a saman kanta tuni jini ya barke da sauri takai hannunta saman kanta ta tabo, jini ta gani kuma gashi yana ta kwararowa a saman fuskarta. Murmushin karfin hali tayi yayinda taji zuciyarta tana mata wani irin azaba, A galabaice ta sake matsawa kusa da Mubarak sosai hannunta dafe a saman kanta murmushi dauke a fuskarta tace kayi hakuri na bata maka lokaci ban baka amsa ba, abinda ta fada din ta sake maimatawa a wannan lokaci kowa yaji abinda shalele ta fada. Sauko hannunta tayi daga saman kanta ta rike hannun Mubarak tajashi shi kuma ya bita cikin tausayawa, Da jinin dake zuba a saman kanta ta rubuta a bangon kofar palonsa, ‘INA SAN KA“ a daidai lokacin da mai gida yazo ya fizgeta a hankali ta fara rufe idonta tana sauke numfashi haryanzun murmushi takeyi haka mai gida yajata har hannunta ya zame daga cikin hannun Mubarak. Har suka fita waiwayen Mubarak takeyi tana murmushi, haka mai gida ya sankama shalele a motar suka dibi hanyar gida zuciyarsa cike da nadama dama wannan dalilin yasashi shiga tashin hankali kar a haifar masa mace dalili kuwa shine! Abinda ya faru shekaru 17 domin abin nan ya tsaya masa a zuciya babu rana bare kuma lokaci da zai manta da wannan bakin mafarki ba. Kwance yake yana bacci lokacin sanyi ne sosai wanda komin lullubinka sai kaji sanyi. Dare ya raba tsakiya daidai matarsa Maryam ta farka daga bacci cikin tsoro danjin yanda 
mijinta yake kai mata duka, kuma koda ta tashi taga lallai bacci yakeyi baisan yana dukanta ba. Sai maganganu dake flta daga bakinsa kamar haka. Na rantse da Allah bazai yuwu ba mama baki da rabo ko daya akan diyar nan nine ubanta kuma wallahi data koma gidan makiyi na gara na kasheta, haka kika ce k0? Tou shikenan a tsagata biyu a bawa kowa kasonsa nawa kason zan bawa karnuka naki kuma naga yanda zakiyi dashi! . Tashinsa maryam ta farayi dan har zufa yake duk bala”in sanyin da akeyi zufa ce ke fita daga jikin mai gida, yana tashi kuwa ya kwararawa maryam mari tare da tambayata anya kinyi aiki da maganin nan daidai? Lallai an samu matsala domin nasan malam zakiru bayamin karya wallahi yace a daren dana tabbatar kin samu ciki ki fara amfani da wannan maganin ya bani tabbacin da namiji zaki aifa wallahi. ‘Dan murmushi tayi saboda tana da da’a da biyayyar aure kauda kanta tayi a gefe sannan tace Allah ya huci zuciyar mai gida ka kwantar da hankalinka insha Allah baza”a samu matsala ba, cikin fada yace idanma an samu kanki zata kare domin nayi mafarkin kin haifi diya mace harta girma kuma ta koma tsagin ‘MAKIYI NA!“ Bayan dawowa tunani, Ajiyar zuciya mai gida ya sauke tare da cewa wato kinsan abinda kika shirya shi yasa kika lallaba kika mutu, tou wallahi karya ne baya yuwuwa ………. 
Zuciyarsa cike da bakin ciki suka isa gida! Jini jagejage da jikin sit din da aka ajiye shalele amma wallahi ko tausayi daya bai zo a zuciyar mai giba ba.Nan cikin motarya barta kuma ya hana kowa ya fiddota dan yace su barta harsai jininta ya kare ta mutu bata da wani amfani, Mama ce ta fito tayi ta fada ta inda take zargawa bata wurin take sakawa ba kuma bata da karfin flto da shalele daga cikin motar kwata kwata tunda jiki ne na tsufa su shalele kuwa sabon jini ne. Mubarak kuwa tunda su shalele suka tafl bai samu natsuwa ba haka babu kwanciyar hankali a ransa dan iyakar tausayi shidai yaji tausayinta a ransa. Ciki ya koma ya nufi dakinsa danyin wanka saboda jikinsa ya dan baci da jini dan shalele ta rike masa hannunsa kuma ya shafa a jikinsa bai sani ba babu wani dadewa ya fito, shiga mai kyau yayi ya saka kaya masu kamala da burgewa turare yadan matsa ajikinsa ba wani mai yawa yana gamawa ya nufi dakin uwar gida khadija. ‘Kwance take saman gado ta harde kafa daya saman daya kanta yana kallon sama tana yin “yar waka wanda baka iya jin abinda take cewa dan sautin baya fitowa sosai. 
Cikin maganarsa mai saka zuciyar mutum shiga taitayinsa yayi sallama ya shiga, bata amsa ba kuma bata kallesa ba. Jikin madubi ya matsa dan daukarwayoyinsa amma babu ga mamaki ya sake dubawa bai gani ba. Ba tare daya kalli Khadija ba yace ranki ya dade kinga wayoyina kuwa? Ya karasa tambayar yana mai ci gaba da dubawa a inda ya ajiye. Murmushin mugunta Khadija tayi sannan tace na gansu. Har yanzun bai kalleta ba yace a ina kika gani ne?. Saukowa tayi daga saman gadon taje har inda Mubarak yake tsaye saida ta sumbace shi 
sannan taja hannunsa suka fita daga dakinki. Kicin ta nufa da Mubarak haryanzun hannunsa rike a hannunta shidai baice mata komai ba yana dai binta ne da ido har suka tsaya. Tunkuya ce a saman wuta sai turirin ruwan zafi ke fita, kallon kyakykyawar fuskar Mubarak tayi sannan ta mayar da kallonta a cikin kyawawan idanuwansa masu daukar hankalin mata. Murmushi dauke a fuskar Khadija idonta a cikin na Abak tace yanzu idan akace wayoyinka ne a cikin nan ya zagayi dani ne? ‘Dan tabe bakinsa yayi sannan yace mefa zanyi? Dariya Khadija tayi sosai bayan ta sarara ta daure fuska tana mai ci gaba da cewa wayoyinka ne anan ta bude tukunyar dan ya gani. Taci gaba da cewa wannan dakikiyar yarinyar ta kiraka da wata jakar da bansan ko waye ita ba. Wannan hukunci zanci gaba dayi ma duk wayoyin daka canja idan har mace ta kiraka a cikin gidan nan wallahi. Murmushi,,,, Mubarak yayi tare da jawo Khadija a jikinsa yace sannu da kokari Allah kuma ya baki sa’a danni bana nemar miki sauki, zanje gida yanzu Baba yana nema na. Na barki lafiya ya saketa daga jikinsa ya fita daga kicin din. 
Wani irin ihu Khadija tayi tare da baro tukunyar daga saman wuta har ruwan zafin saida ya taba kafafuwanta ihu takeyi hauka takeyi tare da duddurawa Abak zagi wanda baiji ba kuma baima san tanayi ba! 
Shi kadai yake tafiya a motar iyakar baci ransa ya baci yana cikin fushi mai fushi zuciyarsa sai turiri takeyi tare da tunzurashi sosai akan Khadija amma ya dake danshi a rayuwa bayasan yaga shine ya zama silar batawa wani ko ayi kuka dashi yana dai kokari yaga bai shiga rayuwar kowa ba ya batawa wani wannan dalili ya hanashi aure tun tunin duniya ashe Khadija kurace ta lallabo wa Abak da fatar Akuya lallal’ yayi danasanin aure shi baya 
san raini shi yasa ya tsani mace ma a rayuwarsa. Ajiyar zuciya yayi tare da mayar da hankalinsa akan hanya sosai harya isa garinsu. Ta bayan gari ya shiga a can nesa da gidansu shalele yayi parking ya fita a kafa yaci gaba da tafiya dan shiga cikin gidansu shalele. Kansa tsaye ya shiga amma ga mamaki babu kowa saboda dare ne. Tsaye yayi a wurin dan baisan ta ina zai fara neman hanyar da zata sadashi da mutane ba kuma babu wanda zai tambaya. Ya dade tsaye a wurin yana sakawa yana warwarewa wanda ya rasa mama dan haka ya tunkari hanyar bene kansa tsaye yake tafiya babu tsoro ko fargaba a zuciyarsa harya haye sama. 
Shalele dake kwance tana bacci kamshin turare Abak ne yakai mata har cikin hanci Shaka tayi sannan ta rikeshi sosai a cikin ruhinta dan karya fita, Shi kuma yana tsaye a waje har yanzun wata zuciyar tace masa yayi sallama dan ya fito da “yan gidan gaba dayansu idan yaso suka gansa kawai yace musu yazo ne ganin shalele da jiki, idan sunyi hauka yayi musu duka dukansu ya tafi da ita dan yasan zata temaka masa wurin ganin ya gyara zumincin da abin duniya yasa ya rabe.  wata zuciyar tace masa tare dayi masa gargadi ta tuna masa da matsayinsa koshi waye ta kara jaddada masa yin hakan taka sharia ne, yana wannan tunanin yaga an tunkaro sa da fitilar kwai, bude manyan idanuwansa yayi tare da kurawa wurin ido, saida ta tsaya gabansa sannan tayi magana cikin muryar tsufa cewa waye kai? Meye ya kawoka gidan nan? Murmushi yayi a ransa, sannan yayi magana a bayyane cewa nine ke wace ce ke kuma? Jin muryar Mubarak yasawa Mama jin faduwar gaba tare da kara daga fltilarta kara haskawa murmushi Mubarak yayi danshi baisan dalilinta nayin haka ba, daga shi har Mama sun dade a haka shine yayi karfin hali cewa. am da Allah ina neman Shalele ne kasa magana Mama tayi tadai nuna masa hanyar dakin shalele Mubarak ya wuce ita kuma ta 
koma nata dakin. Tabe bakinsa yayi sannan yaci gaba da taflya har zuwa kofar dakin Shalele yana taba kofar yajita a rufe, dan haka kawai yaci gaba da dukan kofar, firgigit Shalele ta tashi tare da dafe kanta dake mata wani irin azaba dan dukan da mai gida yayi mata da wani katako, saida ta rike kan sosai sannan tayi magana a hankali cewa waye? Kai tsaye yace nine Mubarak, idanuwa Shalele ta zaro sosai tare da rage hasken futilar kwai saboda tsoro ya kamata tasan dai babu abinda zai kawo Mubarak gidansu har abadan duniya saboda Iyayen kowa sun shata babban layi sun raba duk kuma wanda yaga dan wani a gidansa shekewa ce kawai babu sassauci. A hankali ta koma ta kwanta tare da kara rike kanta da dukan hannayenta ga ciwo ga tsoro, shi kumajin shiru yasashi yaci gaba da dukan kofar dakin, cikin tsoro shalele ta kara jan bargo ta lullube. 
Mubarak kuwa cewa yayi zoki bude kofa mana magana zanyi dake, wayyo Allahna haka Shalele ta fada da karfi tare da cewa aljannu, duka ya sake kaiwa kofar dakin da karfi? yace kizo ki bude nace, jin tahowar mutane yasashi ya tashi daga kofar dakin da sauri ya sauka daga benen ya boye a karkashin bene, da gudu yaran mai gida suka fara wucewa ji yakeyi 
kamar duk yacicci ubansu amma zuciyarsa ta bashi hakuri dole ya hakura har sukaje dakin Shalele. Cikin tsoro tazo ta bude kofar jin yaran gidansu, cikin kuka ta fara magana cewa aljannu ne tana magana tana dafe da kanta, Balaga ne yace ina aljannu suke ne? Cikin muryar wanda ya walhatu tace naga aljannin yana sauka ta wancan benen, ta nuna da hannunta, Murmushi Mubarak yayi tare da gyara tsugunninsa, Mama duk tana jinsu amma tayi shiru shi kuma mai gida haushin shalele yakeji shine dalilinsa da bai fito ba, Muje ki nuna mana inda yake, to tace suna gaba tana bayansu tana binsu babu wanda yasan akwai mutum a kasan bene dan haka wasu da dan saurinsu suka flta sai balaga, Balaga yana wucewa saitin Mubarak shi kuma ya fito da sauri ya tare Shalele tare da rufe mata baki da hannunsa, kuka ta farayi cikin irin yanayin na wanda aka rufewa baki amma Balaga ya riga daya fice, Gabe daya jikinta ya dauki kyarma saboda tashin hankali lallai ta yadda aljanni ne tunda bai tare su Balaga ba amma ita ya riketa, cikin kuka ta fara kiciniyar cire hannun Mubarak daga saman bakinta amma ta kasa saida ta gaji sannan ta tsaya, murmushi yayi sannan yace dan uwanki ne koma muje ciki magana zamuyi, babu gardama ta koma dan ita har yanzun bata yadda shine ba. 
‘Dakinta suka koma bayan sun shiga Abak ya kulle kofar da kanshi suka wuce ciki, Shalele tana gaba yana bayanta har suka shiga ciki a gefen gado ya kwanta da takalmansa bai cire ba yace ma shalele kema zoki ki kwanta anan. Hawa tayi saman gadon adan nesa dashi ta kwanta, murmushi yayi sannan yace zoki ciremin takalmi na yau nima a gidanmu zan kwana, idanuwa ta zaro tare da cewa ka rufamin asiri mai gida ya siyo sabuwar bindiga yace zai kasheni da ita idan har na sake 
tunawa dakai a rayuwata. Dariya yayi sannan yace ke kinajin tsoron mutuwa ne? A daidai lokacin daya gyara kwanciyarsa ya lumshe idanuwansa, Shalele batayi magana ba taji maganar Balaga yana 
cewa Shalele ya kika dawo ne? Kallon Mubarak tayi amma ta kasa cewa komai. 
Kara yin magana Balaga yayi dan haka Mubarak ya make murya zuwa irinta Shalele yace kuje kawai ku kwanta ashe ma mafarki ne nayi sai yanzun na tuna, Balaga zaiyi magana Mubarak yace saida safe ….. , Balaga ya sake cewa babu dai wani damuwa k0 karamin mai gida? Eh babu wani damuwa zaku iya tafiya Murmushi Balaga yayi sannan ya juya ya tafi. Kunna wanca hasken mana Mubarak ya fada bayan ya tabbatar da Balaga ya tafl, Shalele sauka tayi ta kara kunna hasken fitila sannan ta zauna a gefen gado cikin yanayin damuwa. Menene? Mubarak ya tambayeta yana mai matsawa kusa da ita, cikin shashshekar kuka tace wannan wane irin hali ne harma kasa kafa ka biyoni har cikin gida, Murmushi Mubarak 
yayi sannan yace ya kamata na kasance anan ne shi yasa ma na kasance, Shalele tace kaga malam ka tafi kawai, Mubarak yace A, a, Shalele tace kaga malam ka kama gabanka kawai ka bace a wurin nan kaga idan har wani ya gano ka zaka shiga cakwakiya, Mubarak yace wayyo ……. cakwakiya ta bayyana a nan gata nan kuma a gabana, yayi maganar ne a cikin sakata ya karasa maganar yana mai lumshe idanuwansa, sannan ya bude hannuwansa. yaci gaba da cewa ni kuma gani a shirye nake na zamo shekakke 
domin wannan cakwakiyar
Goge hawaye Shalele tayi ta kalli Mubarak tace masa katangun gidan nan kunne garesu, Mubarak yace da gaske? Shalele tace kuma duk mutanen dake bayan katangun nan dukansu masheka ne, Mubarak yace haba? Amma a tanan wane masheki ne zaikai ke? Kuma koma dai mene ne nazo a sheke ni, Juyowa Shalele tayi ta kalleshi tace wai kai me kake nema ne Eye? Matsawa kusa da ita Abak yayi sosai sannan yace wata “yar karamar …….. harkallace, a bani gishiri na bada manda ki karbi zuciya ki bani zuciya, Shalele tace kaiwa Allah ka tafi kafin mai gida ya fito, gyara kwanciya yayi sannan yace Ohoho to zan tafi kuwa amma bisa sharadi daya kwallin kwal. Ajiyar zuciya Shalele tayi tace wane sharadi ke nan? Mubarak yace kimin alkawari zamu hadu gobe. zakizo!! Jinjina kai tayi alamar amincewa Abak yace zaki zo kenan k0? Murmushi tayi ba tare da tayi magana ba, saukowa yayi daga saman yana cewa tou ina jiranki a bakin rafi gobe da marece kuma karki bata lokaci kinji Shalini na? Bata sake magana ba har Abak ya fice daga dakin, Mama tana lekensa ta window harya sauka daga saman benen ya fice daga gidan, goge hawaye tayi koba a fada mata ba tasan wannan jikanta ne dan maganarsa da tafiyarsa duk irin na danta Bashir ne. A hankali ta koma ta zauna bayan ta tabbatar da Mubarak yabar gidan. 
Shalele kuwa sauke ajiyar zuciya tayi cikin farin ciki ta koma ta kwanta, maganar Mubarak ta fara dawo mata lokacin da yake kwaikwayon maganarta yana magana da Balaga murmushi tayi tare dajan bargo ta lullube jikinta., 
A hanzarce yake tafiya harya isa wurin motarsa cikin sauri ya bude ya shiga yaja dan komawa gida ba tare dayaje gidansu ba, Lokacin daya koma gida Khadija tayi bacci hannunta a dunkule kamar zata kai duka wa wani, matsawa yayi bakin gadon ya durkusa guiwarsa a saman gadon a hankali ya kama hannunta ya bude sauke ajiyar zuciya tayi saboda tasha kuka harta godewa Allah, layikan wayarsa ne rumtse a hannunta dan gajeran murmushi yayi sannan ya kwashe layikansa ya fita a dakin. Da safe kuwa shalele bata fito ba kwata kwata, shima mai gida bai nemeta ba dan duk a duniya yanzu idan akwai abinda ya tsana bayan shalele yake da take neman ta wulakanta sa kuma take nema tajuya masa baya ta zabi dan makiyinsa akansa amma yasan mai fishe 
sa, Suna zaune a tebirin cin abinci dashi da Mama babu maima wani magana har mai gida ya gama abinda yakeyi ya mike Mama ta kira sunansa dawowa yayi ya zauna cikin damuwa, cikin muryar rarrashi Mama tace Mansur ka sauke gaba akan kai da diyarka ka gogeta daga cikin zuciyarka da tambarin bakin fenti daka shafa mata. Cikin iskanci yace naji zanyi nazari akai.yana fadin haka ya tashi a wurin, Mama tabi bayanshi da kallon harya kule. 
A bangaren Mubarak wayoyi ya samu saboda wancan wayoyin gaba dayansu sun tashi aiki duk wani abu mai amfani daya ajiye a wayarsa yake so Khadija ta wulakanta wayoyin nan saukinsa daya ma layinka sa data cire, saida wayoyin suka ibi wuta sosai yasa wani yaronsa ya saka masa layikansa, Bayan ya gama saka masa  ansa wayoyin yayi ya shige ciki, agogo ya kalla bayan yaje dakinsa yaga 03:39pm
 ajiye wayoyin yayi ya shiga toilet danyin wanka saboda tafiya wurin 
Shalininsa, shi kowa yana cewa Shalele amma shi kuma yace wai Shalininsa. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE