HARSASHEN SO CHAPTER 13

HARSASHEN SO
CHAPTER 13
Tashi tayi ta nufi toilet wanka tayi da wani ruwan rubutu wanda saida ta zazzaga garin magani a ciki, cikin wata kwarya mai kama da akushi ruwan maganin suke, 
Bayan ta gama wankan ta fito ta dauki wani garin magani ta kwabashi a cikin ruwan turare ta shafejikinta tsaf dashi, wata “yar karamar laya ta dauka ta makala a kasan harshenta, sannan ta farayin magana kamar haka! Ya  ka sawa Mubarak tashin hankali da zarewa ya samu warwarewar tunani idan ya rufe idonsa Ummu Suleim kadai zai rika gani baya da magana sai tawa duk bayan dakika daya ya tuno dani  ka hana masa zaman lafiya da kwanciyar hankali harsai yazo ya ganni gobe goben nan, Tana fadin haka ta kwarara wani ruwan rubutu tun daga tsakiyar kanta har ya sauko a jikinta gaba daya, bayan ta gama ta cire layar ta koma ta kwantajiran tsammani, Mubarak kuwa bai kwanta ba harsai da aka kira sallah asuba yaje masallaci yayi sallah saida ya dawo gida yayi karatun alkur’ani mai girma har 7:09am yana karatun alkur’ani sai 
8 ya gama yayi addu’oi ya kwanta dan yin bacci. Maryam kuwa tunda safe ta taho gidansu Asma’u suka fara shirye shirye dan tasan yau Mubarak dole saiya zo dan ta yadda da aikin gobe da nisa danshi ko kisa aka sakashi yayi kafin ma ki dawo gida ya karya wuyan mutum ya sheke zuwa lahira, Wanka tasa Shalele tayi da wani garin magani mai dan karan kamshi bayan ta fito Maryam da kanta tayi mata kwalliya kaya masu kyau daban sha’awa Shalele ta saka aka caba ado na daukar hankali ana zaman jiran zuwan Mubarak! 
Shiru babu Mubarak babu dalilinsa har aka kiran sallah isha’i Maryam tace kai baya yuwuwa wallahi an samu matsala a wurin aikin nan Shalele tace wallahi yanda kikace nayi haka nayi ban bata ba, 
Maryam ta bugawa gobe da nisa waya ta fada masa yanda akayi kuma sun jira Mubarak har yanzun babu wani bayani, gobe da nisa yace su bashi minti goma yana zuwa, Suna zaune jigum daga Asma’u Maryam har Shalele suna jiran cikar minti goma, lokacin yana cika gobe da nisa ya kirawo, Maryam ta dauka yace gaskiya nayi bincike kwata kwata ma hankalinsa baya nan naga taflya a cikin bincikena yauma yabar nigeria amma ban bincika inda ya tafl ba, Maryam tace tou yanzu miye abun yi ne? Gobe da nisa yace gaskiya Maryam sai kun saki aljihu sosai dan aiki da aljannu akwai wahala ga turarukansu ga jini sai kuma abinda za’a 
basu na sadaka, Maryam tace kada muyi haka dakai kaga bugun farko bamu samu nasara ba domin Allah yanzun kuma sai mu sake bayarda wasu kudin ai gara dai ka sake maimaita mana aikinmu da wancan kudin da muka baka muga ko an samu nasara a karo na biyu, Gobe da nisa yace Maryam aiki fa anyi an wuce wurin tsohon lissafi ne yanzun sabo za’a dora san kudinki yayi yawa idan har kin gani baza ki iya ba ki bawa yarinyar nan number wayana ni saina temaketa.Maryam tace wallahi bazan hadaku ba idan ka shirya yi mana aiki shikenan idan kuwa bakayi ba wannan matsalarka ne sai mu nemi wani yayi mana, to babu damuwa nasan duk inda kikaje saikin dawo min, ba tare da Maryam ta sake magana ba ta kashe wayarta, Cikin daren nan suka fita da Maryam da Asma”u sai Shalele Maryam ta daukesu a motar 
suka tafi gidan wani malaminta…. Bayan sunje suka gurfana a gaban malam Maryam ta kora masa bayani matsalar data kawosu, tashin farko ya fara buga musu kasa abinda ya fada musu cewa shine gaskiya Mubarak bayasan Shalele hankalinsa zuciyarsa da tunaninsa kwata kwata wallahi baya kanta. Da sauri Shalele ta girgije kasar tare da cewa karya kikeyi kasa malam sake bugawa mu gani, murmushi yayi tare da sake watse kasa ya zanata, kallon Shalele yayi sannan yace 
hakika baya sanki kuma bakya ransa karshe ma baisan ki ba, Shalele tace wallahi kasa karya kikeyi, malam zana man kaina ka gani ina san Mubarak ko bana sansa? Ci gaba yayi dayin rubutu a saman yashin bayan ya game ya kalli Shalele yace ‘SO’ lallai ‘so mai tsanani ma wanda idan har kika rasa shi mutuwa zakiyi. Tashin hankali haka kawai Shalele ta fada saida ta goge zufa a kasan zuciyarta sannan ta kalli malam tace tou yanzun miye mafita? Malam yace maflta daya kiyi hakuri dashi dan gaskiya duk malamin da yace zai miki aiki akan wannan mutum karya yakeyi damfararki kawai zaiyi! Ajiyar zuciya Shalele tayi tare da kallon Maryam, murmushi Maryam tayi, tare da bude jakarta kudi ta bawa malam tare dayi masa godiya suka tashi suka flta, 
Kuka Shalele ta farayi tare dakai hannu saman kanta tace kalu bale gareki Shalele wace irin mutuwa zakiyi kai Allah ya tsinewa malamin nan albarka, dama naga sama sama yakeyin sihirin nan bayayi da karfi shi yasa dan daya hau kasar nan da karfin tsiya aradu dasai ta nuna masa komai, Juyowa Maryam tayi ta gogewa Shalele hawayen idonta tace kwantar da hankalinki yanzun wurin wani malami zamuje bara muji abinda zaice mana shi kuma, Cikin shashshekar kuka Shalele tace akwai wani boko a garinmu shi bacewa ma yakeyi yana zama maciji yana zama iska mai gida ya taba aikena a wurinsa amma ni banma san ina yake zama ba, Maryam tace karki damu manta da waccan tunda mai gida ya aikeki wurinsa kinga kenan bokansa ne idan har kika yadda yasan wannan damuwar taki mai gida zaisa yayi miki asiri wanda bakisan ya zaki kare ba, Shalele tace haka ne fa, motar suka shiga suka dunguma sai gidan wani malam babangida, shima dai bayani sukayi masa yace tou suje zaiyi istihara kome kenan zai kira Maryam da safe ya fada musu, lta dai Shalele ba haka taso ba, cikin bacin rai ta dawo gida taso ace taji matsayarta. 
a bakin get Maryam ta ajiyesu ta wuce gida, daren nan Shalele ta kasayin bacci a kagare take gari ya waye taji miye matsayinta a wurin Mubarak. Tunda safe Shalele tasa Asma’u ta kira Maryam dan suji sakamako, Maryam tace musu domin Allah sunyi waya da Malam Babangida yace Shalele tayi hakuri da Mubarak wannan abu baya yuwuwa wallahi kuma taurarinsu ma basu hadu ba, Wani irin bakin ciki Shalele taji makoshinta har wani daci daci yakeyi, tace Maryam ki rufa min asiri mu canja wani wuri, Maryam tace gaskiya akwai wani malami da na sani aikinshi wallahi Shalele cin kudi gareshi kiyi hakuri kawai Allah zai baki wani amma ki manta da maganar wannan Mubarak, 
Din Shalele tace shin ya iya aiki ne? Maryam tace sosai ma danni lambar mota ma kadai na basa saiya kawomin namiji wallahi dan ko lambar mota na gani na fada masa saiyayi aiki tukuru wurin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu. Shalele tace muje a jaraba rashin tayi yakansa abar arha, Maryam tace gaskiya idan dai kin samu kudi zan rakaki domin dai tashin farko sai kin ajiye masa miliyan 2 karanci dan gwamnoni yakeyi ma aiki malamin “yan siyasa ne, Shalele tace tou yanzu dai kizo sai musan abinyi, Maryam tace tou babu damuwa saina zo din, suna gama wayar Asma’u tace Shalele karki kuskura Maryam ta koya miki hali nabin malam tsibbu kiyi hakuri duk abinda yayi farko zaiyi karshe da yardar Allah, Murmushi Shalele tayi tare da cewa baza ki gane saitin ba, da bindiga idan har aka saitaki bulet saiya fasa jikinki sannan ya shiga cikin sokar jikinki zakiji zafl sosai yayin da yake a cikin jikinki, amma a lokacin da aka cire miki wannan ‘HARSASHEN‘ zakiji dadi Jinya ta “yan kwanaki kadai zakiyi wurin ya warke kin manta da wannan ciwon da kuma zafin da kikaji yayin da wannan ‘HARSASHEN’ ya shiga a cikin jikinki, amma duk zafin ‘HARSASHE’ bana tunanin akwai wanda yakai zafin ‘HARSASHEN SO’ kiyi hakuri Asma”u addu”a kadai zaki min. 
Tsaki Asma”u tayi tare da cewa tunda har kinyi imani ana cire ‘HARSASHEN‘ bindiga lallai shima ‘HARSASHEN SO’ za”a iya ciresa, Shalele tace Uhum kin tabajin wanda akayi wa tiyatar zuciya kuwa? Asma”u tace sosai ma kuma sun rayu, Shalele tace amma tunda kike a duniya kin taba samu labarin wanda akayiwa tiyatar so? Asma”u tace gaki nan za’a fara a kanki, 
Murmushi Shalele tayi tare da cewa, uhum da za’a bayyana kuncin da zukata suke shiga a sanadin soyayya da na tabbata da al’amara da yawa sun canja, karki yanke kauna da rahmar ubangiji nasan soyayya alkairi ce, karkiyi kokarin bata zuciyar da tarin sirrikan da suka boyu a cikinta! Karkiyi sanadiyar zubar da hawaye a idanuwan al’umma da yawa da suke natsuwa da walwalta, idan har kika tirsasa zan biye idan har na mutu nasan farin ciki yayi ban kwana da zuciyar mai gida, idanuwansa sunci gaba da zubar da hawaye har tasa mutuwar ta riske sa,Asma”u batayi magana ba Maryam ta shigo da sallama, gaba daya suka amsa Maryam ta samu wuri ta zauna a gefen katifar dakin Asma”u, bayan gaisuwa Maryam tace Shalele yanzu ya ake ciki ne? 
Shalele tace a gaskiya ina san ayi min aiki sosai akan Mubarak ina sansa fiye da tunanin mai tunani ina san na ganni na zama matarsa ta sunna tunda nake a duniya ban taba san wani ba a zuciyata ba saishi, dashi ta bude dashi kuma ina fatar na mutu da sansa, 
Ajiyar zuciya Maryam tayi sannan tace to ga mafita daya, gyara zama Shalele tayi tare da cewa inajinki, Maryam tace muje na rakaki wani wuri ki anso bashi, babu wani damuwa Shalele tace suje, a gaggauce sukayi shiri suka dunguma zuwa wurin da za’a basu bashin kudin, a saman jikin kofar shiga wurin an rubuta ‘LAPO‘ su duka suka shiga ciki kuma sun samu ganin mutumin wato shugaban kungiyar ‘LAPO’ gaisawa sukayi sannan suka fara rattafa bayani, ‘ Bayan bayani da Maryam tayi da kuma adadin yawan kudin da suke so a basu bashi inyamirin yace tou Maryam kinsan fa ba‘acin kudin ‘LAPO’ a zauna Iafiya, Maryam tace ta sani, mutumin yasa akayi hotuna wa shalele passport bayan bincike ya kuma bukaci a nuna masa mazauni su Shalele wato gidansu, Gidansu Asma”u Shalele ta nuna a matsayin gidansu, bayan ya gani yasa akayiwa gidan kudi yaji kudin sun linka adadin kudin da Shalele ta amsa, ma’ana idan Shalele bata biya kudin ba zai siyar da gidan ya dauka kudinsa ya basu ciko. Account in Asma”u a ciki aka turawa Shalele kudi naira miliyan ukku tare da mata kashedi duk satin duniya zata bada kudi naira dubu hamsin harta biya adadin yawan wannan bashin data ci, Shalele kuma ta amince duk satin duniya zata bayar da wannan kudin, daga nan kuma suka wuce wurin malamin da zasu bawa wannan kudi, shima bayani Shalele tayi nasa sannan ta fada mishi yanda takeso ayi da Mubarak yace babu damuwa amma shi gaskiya aikin da zai mata lallai saita ga Mubarak ido da ido zai kamashi, Shalele tace ai baya nan, malamin yace nemosa zakiyi a cikin duniya ba bukatarki kike so ki biya ba? Shalele tace Ey, yace tou kije idan har kika tabbatar da inda zaki gansa ki fadamin zan baki sakonki insha Allah, godiya Shalele tayi malam yace karki damu Mubarak kin kamashi a hannunki, dadi ya baibaye zuciyar Shalele tace Malam nawa za”a baka ne? Cika fuska yayi sosai sannan yace miliyan hudu zaki bayar, ldanuwa Shalele ta zaro sosai tare da rufe bakinta da hannunta sannan tace haba malam kudinfa rancensu na samu dakel Maryam kiyi masa bayani mana, Maryam tace ai 
tun kafin muzo na fada miki kuma kikace kinji kin gani to wane bayani kuma? Ba siyen atamfa bane bare mu tsaya ciniki ba karaya bace ko gocewa da sai muce idan zamu dawo zamu kawo masa cikon kudinsa, Mu koma can ‘LAPO’ a kara mana cikon miliyan daya,jigum Shalele tayi bayan wani lokaci kuma tace Asma”u miye shawararki? Asma”u tace ai na bayar da tawa kin raina, Shalele kallon malam tayi sannan tace masa don Allah kayi hakuri ka anshi 3miliyon din. Kallon Maryam yayi ita kuma ta kyara masa ido, kallon Shalele yayi sannan yace gaskiya haka zaki bayar idan har bazaki bayar ba kawai ki barshi a tari gaba, ajiyar zuciya Shalele tayi sannan tace to babu damuwa zan cika insha Allah, malam yace to dadai yafi, ‘LAPO‘ suka koma aka ida cika kudin suka koma miliyan biyar, Haka Shalele ta kyarkyare kudi miliyan hudu ta bawa malam, miliyan daya kuwa ta cire dan tafiya neman Mubarak ba tare da sanin Alhaji Abbas ba dan duk wannan fitarduniya da ake kullawa baisan anayi ba, Haka Shalele ta shirya tayi tafiyarta Abuja ta siyi sabuwar wayana da layi, koda taje Abuja Bobo mai napep ta nema shine ya tayata ta shiga ta futa harta samu number Mubarak, wannan karon a cikin kanta ta rubuta ta gudun karka samu matsala. Saida Shalele tayi wata biyu cir a Abuja babu Mubarak babu labarinsa kuma babu wanda yayi mata cikakken bayani ina yake ma kwata kwata, ga kuma fitina kwance ta bari a cikin garin katsina bata biya kudin ‘LAPO’ ba, Alhaji Abas ya fito da safe dan taflya kasuwa inda yake neman dan abinda zal’ rufawa 
kansa asiri yaga mutane tsaye a kofar gida “yan sanda da kuma dillai sai cinikin gidansa akeyi. ‘ Hankalinsa ya tashi sosai dan haka ya tambaya k0 lafiya? Babu wanda yabi ta kansa suka ci gaba da cinikinsu, Alhaji Abbas ya fara fada sosai tare da mimmike duk wasu jijiyoyi na jikinsa abokinsa ya bugawa waya ya rattafa masa iyakar abinda ya sani yace babu damuwa yana zuwa wurin bada jimawa ba da yake babban dan sanda ne, 
Babu dadewa kuwa ya iso wurin, duk wani dan sanda dake wurin saida ya girmama, da kansa ya tambayi yanda akayi, inyamirin ya fada masa komai, hankalin Alhaji Abas ya tashi sosai ina Shalele ina cin bashi har naira miliyan biyar? Me zatayi dasu ne? Wannan abu ya daure kan Alhaji Abbas dan haka ya koma cikin gidansa da tsananin bacin rai. Sashen su Asma”u ya nufa bata nan dan itama tashin hankalin yasa tabar gida kuma ta lallaba Shalele cewa ta dawo katsina asiri yaci har Mubarak sunzo shida mai gida, tou Shalele tace mata ta taho katsina yau, wannan dalilin yasa tabar gida tun asuba tana tasha tana jiran zuwan Shalele dan ta fada mata halin da ake ciki, dama ita Maryam tunda Malam ya bata miliyan biyu ta kama gabanta, bata sake bin ta kan Asma”u ba, 
‘Dan sanda shine yace tou babu dalili a kama gidan mutum a siyar babu hannun Alhaji Abbas sannan kuma baisan anyi ba hasali ma diyar amininsa ce ba diyarsa ta cikinsa ba, kuma ko diyarsa ce daya haifa a cikinsa babu dalili a siyar da gidansa tunda bashi bane yaci suje can su nemi Shalele, Basu da yanda zasuyi suka bar kofar gidan suka shiga gari dan neman Shalele, hotunanta aka watsa sosai a gari ana nemanta, duk wani wuri lungo ko sako neman Shalele akeyi, Shalele kuwa sai la’asar likikis ta shigo Katsina, a lokacin har Asma”u ta gama kufulewa, tana ganin Shalele tace Shalele kin dora mana bala”i da tashin hankali ni nasan akan wannan matsalar Baba yana iya tsinemin albarka mu tafi kawai kikai kanki hannun hukuma, 
Tsaki Shalele tayi tare da cewa haba da Allah ni nama sha wani abun arzikine saboda wannan “yar guntuwar matsalar zaki wani daga hankali sai kace ance za”a kwakwale miki idanuwa, ita kuma hukuma  tajirani zanzo gareta ko bayau ba amma shi Mubarak kullum nisa yakeyi a cikin duniya …… Ai Shalele bata gama rufe bakinta ba motar “yan sanda ta tsaya a gabansu, kallo daya Shalele tayiwa motar taja baya, saida da taga sosai ita zasu kama sannan ta sharari hanya ta tsula da gudu, a guje “yan sandan suka bita yayin da mai tuka motar yaja yabi bayansu da gudu tare da sakin jiniya irinta “yan sanda wa wa wa wa ……….. Kuuuuuuuuu, kwa kwa …… Haka suka reta a cikin garin Shalele tana ta neman hanyar tsira dan tasan mai gida yaji wannan labari 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE