HARSASHEN SO CHAPTER 16

HARSASHEN SO
CHAPTER 16
Da sauri Shalele tace Ey, dauke kansa yayi tare da cewa me yasa kike so muyi aure dani dake ne? Shalele tace nidai kawai kamin a rayuwata ina sanka sosai kuma idan har kace baka sona zanyi hakuri saboda bana san na ganka a cikin damuwa zan fita daga rayuwarka dan saka farin ciki a taka rayuwar! Tabe bakinsa yayi tare da jinjina kansa yaci gaba tukinsa har ya isa inda zaije bai sake magana ba, itama shiru tayi amma idonta akan Mubarak bata gajiya da kallonsa ummm hausawa sukace so hana ganin laifl …… , 
Parking mai kyau yayi sannan ya fita yabar Shalele a motar ya shiga ciki, ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe idanuwanta a hankali ta koma ta kwantar da bayanta a jikin kujerar motar sosai, 
Allah sarki asma,u nasan kin farka bana nan ta fadi maganar a bayyane a daidai lokacin da Mubarak ya shigo cikin motar, kashe motar yayi tare da cewa mata muje, A hankali ta bude motar ta zura kafarta ta fita, saida ta fita sannan ya sake kunna motar ya dage glasis din motar sannan shima ya fito tare da kulle motar. Iyakar gajiya Shalele ta gaji ta wahaltu ta galabaita dan haka ta kasa taflya saboda tanajin dinkinta kamar ya bude ma haka takeji ajikinta dan haka tayi tsaye a wurin ita batayi gaba ba kuma batayi baya ba. Saida ya kusa shigiwa ya juyo yaga babu Shalele ta baya baya yadan dawo tsaye ya hangonta tana kuka, ba tare daya dawo ba yace mene ne? Ciwona yanamin ciwo ne, iyya yi hakuri taho a hankali tou. Daga kafarta tayi a wahale wata irin kara ta saki saboda ciwo kuma ance mata karta sake tayi tafiya harsai likita ya bata izini, ita dadi so ta wani kama hanya ta taho, daga inda yake yace kiyi a hankali fa, ‘ Cikin kuka tace nifa bazan iya zuwa ba, Mubarak yace me yasa ne to? Wahala nakeji, wayoyinsa yasa a cikin aljihu daya a hannunsa tunda kananan kaya ne ajikinsa wanda ya rike bata samu damarshigewa ba babu wuri, 
Wurin Shalele ya dawo hannunta ya rike sannan ya fara tafiya da ita a hankali, ihu takeyi danji take kamar “yan hanjinta zasu zubo kasa, da sauri Mubarak ya duka ya daga wurin ciwon,jini ne kawai yake ratata sosai, Hankalinsa ya tashi da sauri ya dago ya kalli Shalele wanda takejinta gab da mutuwa take, cikin tausayawa Mubarak yace yi hakuri in mayar dake meta ne? Shiru Shalele tayi dan bata san wane zata zaba ba, lafiyarta? Ko kuwa zama da Mubarak, yarinta kenan cewa tayi ita bazata koma mota ba, agogon hannunsa ya kalla har ukku ta wuce, Aiba  zaki tsayawa ba? Shalele tace Ey dan bata lankwasuwa duk yanda yayi da ita kuka takeyi, sakin hannunta yayi yaje ya dauko mota a gabanta yayi parking daidai ta inda zata shiga, fitowa yayi ya bude motar ya kwantar da kujerar motar a hankali ya shigarda ita tana ihu sosai dan gaba daya dinkin ya gama budewa,Hankalin Mubarak Idan yayi dubu ya tashi shi bama fita da ita ba idan ta mutu ya zaiyi? Ina zashi da ita duk wanda ya ganshi da ita idan har Babanshi yaji labari akwai matsala sosai, Dogon nazari yayi wanda shi kadai yasan tunanin me yayi jinjina kansa yayi alamar gamsuwa da abinda zuciyarsa ta fada masa, motar ya shiga yaja da gudu yabar gidan ……. Asibiti mai kyau da tsada yakai Shalele saida aka sake sabon dinki sannan aka bata gado tayi jinyar kanta harta samu sauki, bayan an gama komai Mubarak yazo gaban gadon da take kwance kusa da ita ya duka sosai ya dafa hannunsa a saman gadon idonsa a cikin nata yace, Kiyi hakuri zan tafi gida tunda dai kinsan komai ki kula da kanki zan turo wata mata ta zauna dake karki sake kiyi magana da kowa ki zama kurma duk wanda yayi miki magana tambaya ko wani abu daban kiyi kamar bakyajin kowa kinji ko? To Shalele ta fada, Mubarak yace zan rika zuwa ganinki ko wane karfe 2 na dare zan zauna dake bazan tafi ba harsai asuba haka yayi ko? Shalele tace Eh, to yi murmushi ya fadi maganar tare da rage kallon idonsa hannunwan sa duka a saman fuskarta, murmushi Shalele tayi tare da kauda kanta gefe saboda kunya, ‘ Allah ya baki lafiya kanwata na tafi saina dawo, cikin siririyar murya tace amin Yayana, bai sake magana ba ya fice daga dakin. Yana fita Shalele tayi wani irin ihun jin dadi daga kwance take rawar farin ciki, cikin murna take cewa Allah yayi maka albarka Mai gida daka sokamin wuka wannan ciwo ka zamar min alkairi kayi ta zama ajikina karka sake ka warke in zauna da Yaya Mubarak harya yadda ya soni. Sai iskanci takeyi daga kwance. Allah na gode maka tunda kaine ka tsaramin haka a rayuwata, saida ta sakeyin ihu sannan tace duniya sabuwa yau gani a cikinta, wiwiwiiiiii na samu kula kuma ya bani gata, rayuwa ta kaine garkuwata Allah yanda ka nunamin wannan rana ka nuna min ranar da zai fada da bakinsa yana sona, wallahi duk ranar da Yaya Mubarak yace yana so na wallahi sai nayi azumi 60, niko nace kamar kinyi kisan kai ……. 
A gajiye ya koma gidansa saida ya dan watsa ruwa sannan ya dauro alwallah don yin ibada kamar yanda ya saba a ko wane daren duniya ….. , Asma”u kuwa bata san babu Shalele ba saida asuba data farka danyin sallah, idan hankalinta yayi dubu ya tashi da guda guda ya tashi, tun tana ganin abun kamar wasa harta yadda da gaske ne, dan haka ta tashi hankali tare da kwarara ihu dan duk wanda yake asibitin nan yaji ihun Asma”u, Kowa fa yaji mamakin rashin ganin Shalele dan kowa yasan bazata iya tafiya ba, haka ya tabbatar musu da lallai sace Shalele akayi Asma”u tasha kukanta harta godewa Allah, haka ta hakura ta kama hanya dan zuwa ta sanarda mai gida halin da ake ciki. Tashin hankali sosai mai gida ya shiga a lokacin daya samu labarin batar diyarsa, baida mafita dole ya hakura dare yayi yaje ya sanar da boka idan ma wani ne ya sace ta zai fada masa, kallon Asma”u yayi tare da cewa kije kiyi wanka kici abinci, tashi tayi ta wuce dakin Shalele babu natsuwa a jikinta ko kadan, Mubarak kuwa Hafsa ya tura taya jinyar Shalele ya fada mata cewa kanwarsa ce uwa daya uba daya, dan haka ta kula da ita sosai wurin ganin ta faranta ran Mubarak, rainin hankali, IKamar yanda yayi alkawari biyun dare zaizo, to yazo duka zukatan masoyan guda biyu suna cikin farin ciki, ita Shalele tasan saboda ita Mubarak yazo, itama Hafsat tasan dan ya ganta yazo, tunda babu wanda yasan kowa yana san Mubarak a cikin su biyun nan, tunda dai ita Hafsa tasan kanwarsa ce ai tasan babu wata soyayya ita kuwa Shalele batasan wace ce Hafsa ba da kuma matsayinta zuciyarta yanda ta dauki Mubarak ba, 
Wasu irin kattin ledoji ne Hafsa tayi ta daukowa daga motar Mubarak tana shigowa dasu a dakin da Shalele takeyin jinya duk wani abu wanda Shalele zata bukata daga ita har Hafsat babu abinda babu tunda ba abinci yake sa a kawo musu ba, dan idan khadija ma ta samu labari har asibitin tana iya konawa ita tana can london ya barota a can takeyin karatu ba tarema da ita ya dawo ba, Hafsat a kusa da Mubarak ta zauna bayan ta gama jido ledojin, da sauri Shalele ta rumtse idonta tare da kauda fuskarta gefe wannan ma wane irin danyen iskanci ne? Haka Shalele ta fada a ranta, niko nace kaji wani sakarci keda kika kasa ma har yanzun ba”a taya ba. Surutu Hafsa ta farayi wa Mubarak wanda babu kwaba babu aya ba daga layi saiyi takeyi tana dariya ita burinta yayi dariya amma hankalinsa yana kan wayarsa saida yace uumm to, daga Shalele har Hafsa kowa idonsa akan Mubarak, Cikin damuwa Shalele tace Yaya, da sauri ya kalleta dan yacewa Hafsa Shalele kurma ce, idanuwa ya zaro sosai yanda yayi mata kallon yasa ta shiga taitayinta, akwai wani abu da yake so ya gano ne akan Hafsa shi yasa ya kawota tayi jinyar Shalele yasan tunda tasan 
Shalele batajin magana zata rika sakin layi tanayin wasu abubuwa a bude, Cikin tsananin bacin rai Mubarak ya mike tare da wankawa Shalele mari harsai da tayi gyatsarwahala kamar zatayi amai ta maidashi ta hadiye, cikin tsoro ta kalli Mubarak amma ta kasa magana, lta Hafsa bata ji abinda Shalele tace ba tadai ga Mubarak yana dukanta, cikin damuwa tace ranka ya dade meye haka? Me tayi maka ne? Tsaki yayi tare da kwashe wayoyinsa yama fita daga dakin cikin bacin rai, niko nace irin haka ai bayani akeyi. 
Da gudu Hafsa ta bishi tana cewa kasan kurman mutum wahalar sha”ani garesa hakuri akeyi, sai yanzun Shalele ta tuno ance ta zama kurma, tsaki tayi a ranta tace wallahi yau da bakaine kamin wannan iskanci ba dasai naci uwar ko waye, Jiki a sabule Hafsa ta dawo tare dayin maganganu wanda suka tadawa Shalele hankali tsoro ya bayyana kirikiri a saman fuskarta ji tayi kamar ta tashi ta zungura da gudu. Wani lumfashi Shalele take fitarwa wanda duk mai hankali yasan na tsoro ne. 
A zuciyarta tayi magana wayyo Allahna na shiga 3 na kawo kaina inda za”a tsafeni . kuka Shalele ta farayi kamar tace wayyo Allah, kallonta Hafsa tayi tare da cewa shegiya kema zaki ci ubanki, ita dai Shalele kukanta takeyi ita Hafsa a tunaninta dukan da Mubarak yayi mata take kuka akai dan tasan Shalele bata ji. 
Shi kuwa Mai gida yana can gurfane a gaban boka kuma a bude yake fada masa cewa Shalele tana tare da Mubarak kuma hankalinta kwance bata da wata damuwa, yayi niyar zartar da wani hukunci amma dole ya fasa tunda yayi ma Mama alkawari dan duk duniya ya tsani ta koma gidan Bashir, ‘ Kallon boka Mai gida yayi tare da tambayarsa da Shalele da Mubarak zasu yi aure ne? Boka yace babu aure gaskiya shidai baiga aure a tsakanin Shalele da Mubarak ba, wannan magana yasa Mai gida ya kwantar da hankali, godiya yayi tare dayi wa boka babban wanka 
da ruwan kudi, cikin farin ciki ya koma gidansa. Satin Shalele biyu a asibiti kuma ta samu sauki sosai dan yanzun tana iyayin komai da kanta amma Mubarak yace kada a basu sallama kuma bai dawo ganinsu ba yamayi tafiyarsa dubai, Hafsa kuwa tafiyarta takeyi ta daina zama asibitin. Shalele tana cikin damuwa ta gaji da zaman asibitin amma saboda bakar kwakwa taki taflya, babu dai abinda ta nema ta rasa haka ta zauna a asibiti har tsawon wata daya, yau kam Hafsa ta dawo asibiti dan yaune ranar da take sa ran dawowar Mubarak, Duk abinda tasan Mubarak zai gani wanda zaiji babu dadi ko zuciyarsa ta sosu Hafsa tayi kokari wurin ganin ta kauda shi, ita dai Shalele tana kallon ikon Allah an hanata magana da karfin tsiya, sai bin Hafsa takeyi da kallo cikin tsoro, saida ta gama duk abinda takeyi sannan ta kwanta a saman katifa taja katon bargonta ta lullube. 
Ajiyar zuciya Shalele tayi tare dakai dubanta bakin kofa dan an tabo kofar alamar za’a shigo, da sallama ya shigo cikin dakin da sauri Shalele ta kalli agogo 9:34pm amma Hafsa basarwa tayi kamartana bacci. Kuka Shalele taci gaba dayi amma babu damartayi magana dan da an bata izinin magana kawai zatace Mubarak don Allah ita dai su tafi. Kallonta yayi tare da nuna mata tayi shiru Hafsa so daya ya fada daga haka bai sake magana, Wata mikar rashin kunya ta farayi wai ita a dole bacci takeyi, cikin irin muryar masu bacci ta fara magana, mamaki ya kama Shalele sosai ta kalli inda Hafsa take kwance sannan ta kalli Mubarak, zoki ki kwaso muku kayanku a motar, Saida tayi hamma sannan tace Ehum sannu da zuwa, yawwa yace a takaice, tashi tayi tazo ta ansa makullin motar sannan ta fita, kamarjira Shalele takeyi ta fita ta kara yage baki tana kuka sosai, murmushi yayi tare da cewa yi magana fadamin miye? Jikinta har kyarma yakeyi ta fara korawa Mubarak bayani a daidai lokacin da Hafsa tazo shigowa dan haka ta dauke magana zuwa nunawa da hannu, ajiye kayan hannunta tayi bayan ta shigo tare da kallon Shalele tana so ta gano wani abu, murmushi Mubarak ya sakeyi tare da dan matsawa ya jingina da jikinsa ajikin bango yana kallon Shalele sosai dariya yake so yayi amma bayayuwa dan yaga itama ta iya munafirci lokaci daya, ta burgeshi sosai yanda takeyin irin abun kurame, Cikin kissa Hafsat tace me take nunawa ne? Tabe baki Mubarak yayi tare da cewa Oho tambayeta gata nan ni kinsan ba duka yarenta nake ganewa ba, Itama Hafsa dariya tayi tare da sake fita daga dakin, Da wutsiyar idonsa yabi Hafsa da kallo harta wuce, kina fadamin, Shalele tace nidai wallahi tsoro nakeji don Allah ka rabani da ita, to ba kince na aureki ba? Dakel Shalele ta hadiye yawun bakinta tare da cewa Ey, kallonta Mubarak yayi sannan yace to kiyi ta kasancewa da Hafsat harsai kin gano min abinda na kasa ganowa shekaru ukku da suka wuce, cikin kuka Shalele tace mene abun? Nima ban sani ba Mubarak ya fada, wanda hakan yayi daidai da sake dawowar Hafsat, zama tayi a gefen gado itama bayan ta ajiye kayan data dauko, kallonta Mubarak yayi sannan yace don Allah dubamin kamar nabar dayar wayana a mota. Tashi tayi ta sake fita ba tare da tayi magana ba, Shalele taci gaba da cewa idan har nayi haka kayimin alkawari zaka aureni, kallonta yayi ido cikin ido sannan yace ban miki alkawari ba kiyi abinda nace kawai, Mi yasa baza kayi alkawari ba? Saboda bana da sha’awar auren mace biyu a rayuwata itama dayar addu”a nakeyi Allah ya rabani da ita in huta, ba tare da Shalele ta sake magana ba ta sauko daga saman gado dauke kansa yayi gefe dan yaji ajikinsa tafiya zatayi, 
A bakin kofa suka hadu da Hafsa ita zata shigo Shalele zata fita, da sauri ta rike Shalele tare da nuna mata ina zataje ne? Mubarak yace barta tafiya zatayi taje ta fadawa Baba inayin soyayya dake, ban gane ba, Hafsa ta fada, Mubarak yace ai ta zauna dake tasan kirkinki da mutuncinki wai daga muna magana nace bazan aureki ba shine tayi fushi zata tafl gida, Murmushi Hafsa tayi tare da nunawa Shalele tayi hakuri murmushi Mubarak yayi tare da kallom Shalele da kyau ya nuna mata wai tayi hakuri su zauna tare, girza kai tayi tare dayin nuni da hannunta, idanuwa Mubarak ya zaro tare da kallon Hafsa yace wai kinji bazata zauna dani ba gidanki take so ki tafi da ita. Cikin kuka ta nunawa Mubarak ba haka take nufl ba, dariya yayi sosai tare da cewa ni babu wani damuwa wallahi kije kawai babu komai tunda dai kina santa ba damuwa, buda baki tayi da niyar yin magana dan ita Allah ya sani bata san rabuwa da Mubarak sannan kuma bazata iya bin Hafsa gidanta ba saboda tsoronta takeji kamar zata mutu. Saukowa yayi daga saman gadon yazo kusa da Shalele hannunta yaja suka fita waje, cikin damuwa Hafsa tabi bayansu da kallo har suka bace, Mubarak kuwa mota ya shigar da Shalele sannan shima ya shiga ya zauna, dan rungumota yayi kadan ajikinsa bawai kadaddabeta yayi ba, kadan ya riketa da hannunsa na dama ta dan shigajikinsa kadan sannan ya fara magana,Suleim na yadda dake 100% ban tabaji a jikina zaki cuceni ko so daya ba, ke “yar uwata ce tajini karki duba halin da iyayenmu suke ciki baki koya ba baki iya ba kuma nayi imani bazaki iya ba, inajinki daban da sauran mata a zuciyata, nasan kina so na, ….. sai kuma yayi shiru, daga kanta tayi ta kalleshi sannan tace kaima kana so na ne? 
Girgiza kansa yayi alamar A, a, wani irin bakin ciki Shalele taji ya sokar mata zuciya wanda bazai yuwu a kwatanta ba, baka so na ta tambaye sa? Da girarsa ya bata amsa alamar Eh sannan ya saketa daga jikinsa yace zakimin abinda nake so ko A, a,? 
Dakel ta iya mayar da numfashi sannan tace zan maka insha Allah, Mubarak yace saboda me zaki min ne? Shalele tace saboda Allah, zuminci da kuma san da nake maka, to na gode sosai, hannunsa yasa a aljihu ya ciro wani zobe mai kyan gaske ya lalubo hannunta ya saka mata a yatsanta, karki sake ki rabu da wannan zoben koda wasa na fada miki kinji k0? To Yaya ta fada idonta a cikin nasa, waya ya Ciro mai kyau da tsada ya bawa Shalele bayani yayi mata wanda banji abinda yace ba, amma tayi godiya, yace yawwa zaki 
Iya fita ki jirata anan zata zo ta tafi dake, 
Jiki a tsabule ta fita daga motar murmushi mai daukar hankali yayi mata wanda tajisa ya shiga cikin jikinta da gudu yabi duk wasu sassa najikinta wanda yasa gaba daya ta manta 
da damuwar da take ciki, da kallo tabi motarsa harta bace. Waya yayi ma Hafsa cewa ga Shalele nan su tafi tare, bata so haka ba amma ta hakura 
haka suka tartaka duk wani abu da suke so Hafsa ta dauketa a motar suka tafi gidanta ….. 
Saida yaje gida sannan ya turawa Shalele sako cewa kiyi hakuri kuma ki kwantarda hankali ni ina tare dake. Saida safe karki kiyi bacci ba’a bacci a gidan sannan kuma ki rika kasancewa a cikin alwallah da kin tabbatar babu maza ki canja wata, ki rike sallah akan lokaci da safe zanzo in taho dake kiyi bacci da daddare zan mayar dake, ina miki fatan alkairi ki huta, dan uwanki, Mubarak BashirAbak, ki goge sako idan kin gama karantawa, Kan Shalele ya daure me haka yake nufi wai? Ita Hafsat wace ce ita to? Miye alakar Mubarak da ita? Meye yake so in sani wanda shi ya kasa ganewa? Wannan wane irin rayuwa ne? 
Abinci wani mutum yazo ya ijiye a gaban Shalele wanda kallo daya tayi masa gabanta ya fadi, murmushin karfin hali Shalele tayi masa tare da nunawa da hannunta sannu take nufl, shima murmushin ya mayar mata sannan ya flta daga dakin …… Mubarak zaune yake a saman kujera Zseater yadan rabe irin dai zaman manyan mutane ya wani dan bude zaman nasa irin nasu su masu kudi, saida ya shafa sumar kansa sannan ya 
kalli wayarsa, sakon daya turawa Shalele ya gage shi daga cikin wayarsa, ‘ Shalele kuwa gaskiya hankalinta ya tashi dan wannan abincin da aka kawo mata bata yadda tacishi ba, ga maganganun da takeji anayi a palo iyakar tashin hankali ta shiga lallai son maso wani koshin wahala ita kuwa har abadan duniya bata taba tunanin Mubarak zai kawota wannan wuri ba wai da sunan ta kamo masa mai laifl, ita ba soja ba, ba “yar sanda ba haka kawai ya dauko bala”i da mutuwa ya dora mata, wato idan ta mutu shi baya da bakin ciki bare asara sannan yama ce baimin alkawarin zai aureni ba, goge hawayen idonta tayi tare da cewa Ya Allah ka ciremin san wannan bawa naka a zuciyata ka bani hakuri da dangana ka mantar min dashi daga cikin zuciyata, Sai yanzun ta gane tayi murnar banza da tace ta godewa Allah da Mai gida ya caka mata wuka, sai yanzun tayi rashin godiya dan jinta takeyi kawai tazo lahira ne da kanta, Har safiya ta waye Shalele tsoro ya hanata bacci, Mubarak kuwa daga masallaci ya wuto gidan Hafsa waya yayi mata cewa ta turo masa Suleim, tace bazai shigo ba? Yace sauri yakeyi zai dawo, tambayarsa tayi ina zasu je ne? Yace babu wani wuri da zaije kawai dai tazo yanzu yanzun nan, Hafsat tace bacci takeyi ai, tsaki Mubarak yayi tare da kashe wayarsa. Da sauri ta tashi taje ta fara tashin Shalele wanda dama ba bacci takeyi ba, kwana tayi tana kuka saboda tsoro, saida ta tashi zaune sannan Hafsat tayi magana cewa kema saura kici gaba da kwana a gidan nan, wani irin kugi cikin Shalele yayi amma saita danne dole, tabi Hafsa da kallo kamo hannun Shalele tayi suka fita daga dakin, Har motar takaita ta gaishe da Mubarak amma bai amsa ba, Shalele na shiga yaja motarshi yayi tafiyarsa, gidansa ya nufa da Shalele a dakinsa yayi mata masauki tana hawa gado bacci yayi gaba da ita, shi kuma fita yayi ya kama harkokin gabansa, Shalele kuwa hankalinta kwance tasha baccinta sai bayan azaharta farka jigum tayi a gefen gado tana tuno maganganun su Hafsa lallai matar nan tana da hadari sosai to amma shi 
Mubarak miye alakasar da wannan mutane dan gajeran tsaki tayi tare da cewa lallai sai ya sanardani komai idan har yana san na bashi taimako gaskiya, kuma insha Allah dana kamo masa bakin zaren zan kama gabana in Allah ya yadda, 
Tana wannan tunanin ya shigo ba tare daya kalli inda take ba yace kina jin yunwa ne? A, a, banajin yunwa, yayi,, yace tare daukar wasu takaddu zai fita. da sauri ta tashi tsaye tare da cewa Yaya, tsayawa yayi ba tare daya juyo ba yace meye? Gaskiya babu wanda ya isa yasa na sake komawa gidan nan ko waye shi, to Mubarak yace, ita kuma tace ko kaine baka isa ba, murmushi yayi tare da cewa to, kuma wannan ai cuta ce ashe kasan matar Da sauri tace A, a, Yaya wasa fa nakeyi dama dan inji yanda zakace zanyi zamana tare dakai sannan kuma zanyi ta komawa harsai nima an kasheni …… Tafiya yayi ya kyaleta ita kuma tabi bayanshi tana ci gaba da cewa wallahi zan koma gidan. Har suka fito palo hakuri take bashi amma yace ta wuce ta tafi gida idan ba haka ba wallahi ranta zai baci, cikin kuka
 tace haba Yaya kai baka san wasa ba, ai kasan inaji dakai wasikar dana taba rubuto maka kwanakin baya ma da jinina na rubuta, taya zaka rika raba jini da jiki kayi hakuri wallahi na bari,
Shiru yayi ya kyaleta yana kokarin flta tabishi da gudu, tsayawa yayi yace ki fito in kinqi Baba zaizo yayi miki dukan fitar hayyaci gara ma ki rufawa kanki asiri kawai ki koma tun kafin wani yasan kina gidan nan, Dan tada hankali tayi sai yanzun ma ta tuna da tabar Asma”u a asibiti tun wata daya daya wuce, wayyo Allah haka ta fada tare da ture Mubarak tayi waje aiko zata ci ubanta a wurin Mai gida, da sauri Mubarak ya rikota ya maido ta cikin palon yace ina zakije ne? Kai kyaleni Mai gida, dariya yayi tare da maida ta ciki ya kulle kofar da makulli yayi tafiyarsa, dafe kai Shalele tayi tare da karanto ta shiga ukku yanzun ta tuna ma jinya ta kawota cikin gari kai amma lallai Mai gida zaici ubanta wallahi. Kai amma lallai bata da hankali, 
Sai bayan la’asar Mubarak ya dawo, shima zama yayi a daya daga cikin kujerun palon Shalele ita kuma tana zaune kasa da kofin tea in data sha komai babu abinda ta dauke a wurin ta barshi, ko kallonta baiyi ba ya zauna yaci gaba da wayarshi, saida ya gama sannan tace don girman Allah Yaya ka fadamin mine ne matsayina a wurinka? Sannan mi yasa ka hada alaka tsakani na da Hafsa? Bayan kasan ita mai cutarwa ce? Kuma kace baka sona, mi yasa kayi min haka ne? 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE