HARSASHEN SO CHAPTER 18

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 18
Ko inda take bai sake kallo ba kuma bai mata magana ba, Shalele kuwa banda kuka babu abinda takeyi, babbar nadama tayi na sanin Mubarak amma dukwannan abun da yayi mata baisa taji haushinsa k0 kadan ba a ranta tadai jingina abunne kawai a matsayin kaddara. 
Shalele sai shashshekar kuka takeyi kamar ranta zai fita da gefen hijabinta take ta goge hawayenta, ban gare daya na zuciyarta kuwa tunanin Mai gida takeyi da halin da yake ciki, Idan har aka kai‘ta gidan yari wane irin makudan kudi zai biya wurin anso ta? Idan haryaji labarin ta sake haduwa da Mubarak tana cikin bala’i kuma itace ta isko Mubarak da kafafuwanta. Tana san ‘ayi magana amma tanajin tsoron Mubarak dan ta lura yana da saurin fushi, dole ta hakura batace komai ba har suka iso gidanshi, a motarya barta ya fita. Bai wani dade ba ya dawo, bude murfln motar yayi daidai inda Shalele take zaune. A hankali yakeyin magana cewa kibi sannu ki fito ki wuce ciki karki yadda ki bari kowa ya ganki, cikin mutuwarjiki Shalele ta fito zuciyarta cike da tsoro dan bata san yadda zata kare ba idan suka shiga ciki Cikin munafirci take tafiya harta shiga cikin palon tayi tsaye, Khadija dake bacci amma saboda tsabar masifar kishi saida taji kamshin mace ta shigo cikin gidanta, wukil ta bude idonta tare da fiffido su sosai, maganar Mubarak tajiyo shima cikin rashin gaskiya yana cewa kije ki kwanta ki huta. Ni zan tsaya anan sallah zanyi, Da gudun bala‘i ta sauko daga saman gadon tayo palon a guje, a lokacin tuni Shalele ta shige inda tayi baccin safe jiya, itama ranta a bace dan haushi ma Mubarak ya bata wallahi duk girmansa duk kyansa wayewarsa ajinsa gogewarsa tunaninsa kudinsa budewar idonsa kwarjininsa da kuma zafinsa ace yana jin tsoron mace? 
To wallahi saita fita saidai yau ya kasheta, maganar sa taji yana cewa karki daga min hankali ina ruwanki da wanda nazo da ita ne? Khadija tace ai naga nema ma abun naka yake ya zarce misali duk can da kakebinsu bai isheka ba har saika fara kawo min mata har a cikin gidana saboda tsabar rainin hankali? Mubarak yace me kika daukeni ne? An fada min neman mata nakeyi da zaki rika magana ina nemansu a waje? a Kafin Khadija tayi magana Shalele ta fito wurin tazo ta tsaya tare da cema Khadija sannu sannan ta mayarda kallonta wurin Mubarak tace wai’ mene ne aketa hayaniya an wani hana mutane suyi bacci? Khadija tace ubanda ya haifi uwarki ta daddana wani lafiyayyen zagi tare dakai ma wuyan Shalele shakara, 
Mubarak baiyi magana ba, dan haka Khadija ta shiga dukan Shalele amma Mubarak yayi zaune saman kujera kafa daya saman daya. Wannan abu yayiwa Shalele bakin ciki dan haka ta dauki Khadija tayi sama da ita tare da dannawa kasa ita, saman ruwan cikinta ta durkusa taci gaba da dukanta kamar tana dukan wani kato. Mubarak na ganin Shalele ta kayar da Khadija kasa ya tashi da sauri ya daga Shalele daga jikin Khadijar amma sai wani kara kaiwa Khadija harbi takeyi, wani irin mari yayiwa Shalele saida tayi tagal tagal zata fadi ta dafe bango da sauri. 
Wani irin halbi yakai mata shima ta kara tafiya tangal tangal tare da dafe inda yakai mata harbin dan wurin Ciwonta ne, fizgota ya sakeyi ya Kara marinta saida ganinta ya dauke, ni zaki dakarwa mata a gaban idona, kinsan yanda nake santa kuwa? Murmushin karfin hali Shalele tayi tare da goge daidai inda ya mareta harsai data shafo gefen bakinta ta goge jinin dan gefen bakin nata ya fashe saboda marin da yayi mata.A hankali takai dubanta ga Mubarak sannan tace bazance baka da adalci ba, kana da adalci kuma hakan da kayi shine hukuncin gaskiya, dan koni aka daki makiyina a gaban idona banajin komai, amma duk mai san yaga bacin raina hakika ya tabo abinda nake matukar so a rayuwata, tofa lallai anan ne mutum zaiga bacin ran Shalele ta karasa maganar cikin nuna tsananin bacin ranta. Tana fadin haka tajuya dan komawa daga inda ta fito, Khadija tace karki koma min dakin miji shegiya mayya, Shalele tace banajin abinda kike cewa amma ki iskoni biyoni dakin ki fadamin tana maganar tana mai ci gaba da tafiyarta. Shalele tace uwarki ce mayya zama daram a gidan nan ko mai gidan bai isa ya rabani da gidan nan ba idan dai bani na tafi dakaina ba. 
Cikin kuka Khadija tacewa Mubarak ni wallahi idan na zauna da ita Allah ya tsine min albarka, dukma cikin “yan matan da kakeyi ban tabajin wanda na tsana ba kamar waccan tsinaniyar yarinya, Mubarak yace karki kara tsine mata ki kiyayi kanki bar ganin na daketa kice zaki rika aibata ta a gabana wallahi ranki zai baci. Maganar zama kuma kada ki zauna idan kin tafi nace miki zan fasa rayuwa ne? Macenmi Allah na tuba. 
To idan kanajin kai mace ba komai bace ba ka sakeni, shidai Mubarak baice mata komai ba, nan tayi tsaye tayi ta tsiyaya ruwan rashin kunya, amma k0 inda take Mubarak bai sake kallo ba dan yama kaddara bata a wurin hankalinsa yana kan wayarsa. 
Ita kuwa Shalele ta kasa bacci bawai tsoron Khadija ba A, ita tashin hankalinta zuwa gidan yari, sai kuma kisan da taga anyi a gabanta, sai zuciyarta dake kara mata kashedi haduwarta da mai gida. Idan hankalinta yayi dubu a tashe yake. 
Shi kuma Mubarak tunanin yanda zai shigar da Shalele gidan yari da irin rayuwar da zatayi yake tunani, dan lallai zuwa gidan yari a cikin tsarin aikinsa ga Shalele yafa zama dole, sai taje dole babu makawa, amma yana tunanin irin dabi”un da zata dauko a gaskiya idan har yayiwa Shalele haka bai mata adalci ba kamar yanda ta fada, amma fa gaskiya sai tayi hakuri. Khadija kuwa saida ta kare masifarta sannan ta koma dakinta, wayarta ta dauka ta kira 
shahararren malaminta ta sanar masa da duk abinda ya faru a tsakaninta da Shalele, yace babu damuwa zaiyi binciken komai zai kirata zuwa safiya in Allah ya yadda. Mubarak kuwa saida yayi sallah asuba sannan ya shiga dakinsa. Shalele kwance a saman abin sallah tana bacci, gabanta ya durkusa sannan ya fara tashinta, a hankali ta bude idonta ta kallesa so daya sannan ta sake rufewa ita dai batasan ko haushi ya bata ba oho. Suleiym, ya kira sunanta cikin rarrashi, ba tare data sake bude idoba ta tashi zaune tace inajinka, wata katuwar takarda ce ya warware sannan ya ajiye a gabanta, yace bude ido ki gani, gaba daya ta bude idonta yanda tayi abun harsai da tsikarjikin Mubarak ta tashi, bin idanuwanta yayi da kallo yana murmushi, itama murmushin tayi wanda saida yaji sa har cikin ransa. “Yar dariya yayi mai sauti sannan ya maida kallonsa a jikin takardar, wannan zanen hoton waye? Ya tambayi Shalele tace ban sani ba k0 waye. Duba sosai da waye yayi miki kama lye? Nidai baimin kama da kowa ba, ni ina kama da mutum dake cikin hoton ne? Kara kallo tayi sannan tace gaskiya A, a, kalla da kyau ki gani. Shalele tace nidai ban wani ga kamarku ba, to yayi kwanta kiyi bacci. A hankali ta koma ta kwanta shi kuma fita yayi daga cikin dakin. Tunanin hoton takeyi a zuciyarta tare da kara karantowa amma ta kasa gano ko waye. Shi kuwa Mubarak mota ya koma, mutumin daya bashi zanen ya mayar da takardar sannan yace ka tabbata yana raye? Na tabbata wallahi amma bansan inda yake zaune ba yanzu, ita dayar matar tasa kace tana gidan yarin katsina k0? Sosai ma na tabbata da haka amma na tabajin labari kwanaki ance kamar ta samu tabin kwalwa an kaita asibitin mahaukata kamar yanda naji labari amma banda tabbas ta dawo ko kuwa bata koma gidan yarin ba shine dai ban sani ba. Jinjina kai Mubarak yayi tare da cewa to gaskiya bana tunanin Shalele zata iya, dan akwai yarinta cikin kanta danyen kai gareta har yanzun, ni na tabbata idan har Baba yaji muna bibiyar matar nan ni saina fi kowa shiga matsala, mutumin yace nima karyata ta kare, Mubarak yace kuma dukanmu a cikinmu sai Shalele tafimu shiga damuwa, to jira ma mu ina ruwanmu da wani gyaran zumincinsu kaga kawai mu bar wannan matsalar can ta matse masu
A, a, kada kayi haka tunda har kayi niya nayi alkawari zan baka goyon baya 100%, Mubarak yace kasan yanda za”ayi ne? Kawai zansa a fito da matar in yaso sai muyi mata tambayoyin da zamuyi mata, mutumin yace maganar fiddota wurinka bazai yuwu ba domin shi babanku akwai wanda yasa yake kula da duk wani motsinta wallahi idan har yau akaje wurinta wallahi sai yaji labari, haka shima Mansur. Ajiyarzuciya Mubarak yayi sannan yace wane laifi ne yakaita gidan yari iye? Mutumin yace gaskiya sharrin kisan kai akayi mata, Mubarak yace to babu damuwa, sundai dan dade suna maganganunsu daga baya kowa ya kama gabansa. Zuwa 9am labari ya bazu a cikin gari na kisan da akayi ma wani dalibi wanda dama an dade ma ana nemansa bayan ya Fito daga hannun “yan sanda, to wasu wanda ba’asan ko su waye ba suka kashe sa aka zo aka jefardashi her a cikin makarantarsu. Shalele bata san duk wani kulli da akayi ba aka zo har gidan Mubarak aka nannadeta, tambaya takeyi lafiya meya faru amma babu wanda ya saurareta koya bata amsa, abinda akayi a garin abuja amma saboda makirci aka nufi katsina da ita. Shalele tsugunne a cikin motar gidan yari sai kuka takeyi ta rasa inda yake mata dadi a rayuwarta, kuma ta bude idonta sosai taga ba “yan sanda bane sojoji ne, su kuma me tayi musu, me suke nema a wurinta ne? Kuka takeyi sosai kamar zata shide, lallai ta yadda duniya makaranta ce mai wahalar karatu, baka gama wani karantun ba wani darasin yake riskarka. Tunani barkatai takeyi a zuciyarta wanda ta rasa mafita itakam taga ta kanta. Haka suka sharari tafiya daga garin abuja har zuwa babban birnin katsina ta dikko dakin kara, kunya garesu basu da tsoro, kai tsaye aka wuce da Shalele gidan yari aka ajiyeta. lta dai bata san abinda tayi ba, sannan kuma bata ga laifin da tayi masu ba har suka kawo ta gidan yari. Wannan abu akwai azazza a kasa saboda tasan ba’a zuwa gidan yari kai tsaye saidai idan alkali ne ya kawo ka, lta da zata bada shaida meya  hada ta da gidan yari? Kai lallai akwai abinda yake faruwa wanda gaba daya tunaninta ya tsaya. Allah yayi min sakayya da duk wanda yake so yasa damuwa a cikin rayuwata ko waye shi, haka ta fada a bayyane. 
Mike tsaye tayi saboda motar ta shigo cikin gidan yarin, mutane cirko cirko ta hango a lokacin da aka bude motar, tsaye tayi ta kasa saukowa daga saman motar saboda kacocin dake jikinta tun daga kafarta aka sagalosu ta wuyanta sannan aka hada da hannayenta aka datse da kwado, kuka kawai Shalele keyi dan bata san laifin da tayi ba karshen tuzarta dai an tozarta fiye da tunanin mai tunani, kunyar ma hada idanuwa takeyi da mutane dan haka ta rufe idanuwanta hawaye naci gaba da digowa daga cikin idonta masu zafin bala’i,. Fizgota akayi harta fado kasa, sannan wasu mutane da bata san k0 su waye ba suka jata tafiya takeyi amma bata san inda suke zuwa ba tunda bata ganin hanya. Daga bayansu akayi magana cewa karku ajiye ta a dakin nan ku wuce gaba da ita. Wata murya taji daban wanda ba wanda taji ba daga farko yace gaskiya wannan dakin za’a ajiyeta ai duk magana ne na kisan kai a barta anan har zuwa lokacin da za’a yanke mata hukunci daidai da abinda tayi. Cikin kuka Shalele tace waye yayi kisan kan ne? Ta karasa maganar tare da bude idanuwanta ta kurasu akan mutanen dake gabanta. Kece kikayi, wani dan sanda ya fada da sauri Shaleleta matsa kusa dashi sosai saida taja kanta baya sannan ta kuma masa kanta harsai da yaji juwa, cikin bacin rai ta sake cewa waye yace nayi kisan kaine? Wani daban yace kece kikayi, murmushi Shalele tayi tare da jinjina kanta tace zo nan kusa dani ka fadamin ta karasa maganar tana mai daure fuskarta tare da masa wani irin kallo. To wallahi ban kashe kowa ba, ban taba kisa ba nasan duk sharrine da tsabar makirci da kuma munafirci irin na abokan gab ……… Ke saurara mana mu nan ba shari’a mukeyi ba kuma ko zamuyi shari’a ki bari dangin wanda kika kashe din suzo, wani ne yayi magana dan katse mata numfashi ba tare daya bari tayi magana ba, ku shigar da ita ciki karku kwance sakar ku barta da ita. A dakin da akace kada a sakata a dakin aka sakata aka rufe tanaji tana gani suka tafi, banda kuka babu abinda Shalele keyi lallai idan harta fita daga wurin nan babu abinda zai hana ta kashe Mubarak a duniya, saita kashe sa saita kashe ubansa wallahi saidai itama a kasheta a duniya dan duk babu bakin munafikin da yayi munafircin nan saishi. Daga bayanta taji an kece da dariya harda tafawa, da sauri ta juya dan ganin ko waye, wata “yar tsohuwa ce ta gani ta tsufa tuguf bata da hakora jikinta duk yayi tamoji irin na tsufa ta barbaje gashin kanta kamar mahaukaciya sai dariya takeyi tana nuna Shalele. Cikin tsoro Shalele ta goge hawayen idonta tare da kara bin matar da kallo sosai, wace ce ke? Shalele ta tambayeta, kara kecewa tayi da dariya tare da cewa wallahi bani na kashe shi ba, hahahahhhhhhhhhh ta sake barkewa da dariya, tsoro ya kama Shalele sosai ta fara kwarara ihu dan ganin matarta taso ta nufo inda take tsaye. Yo waye yake take Shalele? Wayyo Allahna …………. kiyi hakuri don Allah na bari karki kasheni, saida matar tazo kusa da Shalele sannan tace bani abinci inci tayi maganar cikin hauka. 
Cikin rawar baki Shalele tace wallahi banda komai, kuka matar ta farayi tana maganganu wanda Shalele bata san abinda take cewa ba, cikin tsoro Shalele ta koma gefe ta rakube jikinta sai kyarma yakeyi dan tsoron matar nan takeji sosai. Ita kuma bayan ta gama surutunta taci gaba da kuka wanda dama shine sana’arta. 
Cikin tsananin bacin rai Bashir ya juyo tare da cewa waye yake zaune da itane? Bayan nace kada a hada ta zama da kowa, ranka ya dade wata mai laifi ce aka rufe, kai …………. saurara baya yuwuwa akwai munafirci a cikin zaman nan maza maza a fitar da ita daga wurin nan saboda ba daki daya bane a gidan yari. Kallon wani yaronsa yayi tare cewa kai maza kira min Mubarak duk abinda yakeyi yazo yanzun nan ina neman sa, babu bata lokaci ya fadawa Mubarak, Mubarak yace a fada ma Babanshi gaskiya bazai samu damar zuwa ba. Ranka ya dade yace kayi hakuri bazai samu damar zuwa ba, ansar wayar Bashir yayi da niyar yayi magana amma Mubarak ya kashe wayarsa. Cikin bacin rai Bashir yace sake cewa kirawo minshi, duk kiran da akayi Mubarak bai dauki waya ba, ran Bashir yayi matukar baci sosai fada yakeyi ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. 
Mai gida kuwa bindiga ya dauko ya saita mai fada masa maganar da niyar watse masa kai Mama tace ya saurara, haba Mama dukiyarmu za”ayi mana sakaci da ita ne? Gara na fara aikashi kiyama yaje can ya saurari zuwanmu, Hakuri Mama ta bawa Mai gida badan ransa yaso ba ya hakura dan motsi kadan yayi Mama sai tace zata koma gidan Bashir wannan dalilin yasa ya hakura. 
Shalele kuwa a tsugunne sai kallon matar nan takeyi cikin tausayi. Tanajin tausayin matar nan fiye da yanda takejin tausayin kanta, dan haka ta sakawa ranta salama, 
Bayan sati daya da taflya da Shalele,,,, Mubarak ya shirya dan zuwa wurinta, saidai baisan yanda zasu kare ba, tunda shi kadai yasan dalilinsa nayin haka amma ita ba lallai bane ta yadda da abinda zai fada mata ba. Tafiyar sirri ce yayi daga shi sai Mai nasara suka tafi, kuma gaba daya wayoyinsa a kashe suke baima tafi dasu ba a gida ya barsu. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE