HARSASHEN SO CHAPTER 19

HARSASHEN SO
CHAPTER 19
Da sauri Shalele ta juyo da kallonta zuwa wurin kofa dan jin magana kamar ta Mai gida, 
mikewa tayi tsaye da sauri tare da kallon kanta sannan ta sake kai kallonta wurin mutumin. Bude idanuwa tayi sosai tare da kurawa mutumin ido sosai, kallonsa takeyi ko kyabta ido batayi wannan ba Mai gida bane waye shi kuma? 
Tsohuwar da suke daki daya da ita taga ta tashi cikin hauka kamar yanda takeyi ta fara maganganu cikin rashin hankali. 
Da ido kawai Shalele tabi su da kallo amma tafi kallon wannan mutumin dan gayu dashi hutu ya gama lullube sa kana kallonsa kasan jikon naira ne ko ba’a fada ba kasan akwai hatimin nasara a wurin sa, kuma da gani dai kamarwani babba ne a cikin hukumar “yan 
sanda. Bude kofar dakin akayi jami”an tsaro suka shigo ciki a hankali suka kama wannan matar cikin girmamawa, da sauri Shalele ta mike tsaye amma ta kasa tafiya saboda wannan sarkar da’aka daureta da ita, dago hannuwanta tayi ta kallesu wanda har sunyi kunburi saboda tsabar dauri. Kuka ta farayi tare dayin magana cikin kuka, tace Babana don girman Allah karka tafi ka barni a wurin nan ka tafi dani don girman Allah Babu wanda ya saurari Shalele dan ana fitar da matar aka sake garkame dakin Shalele 
tanaji tana gani suka tafi da “yar tsohuwar nan aka barta a dakin ita daya. ita amma ko motsi sarkar batayi ba, kuka takeyi sosai tare da bubbuga kanta a jikin bango tana duko kanta daidai zuciyarta ji takeyi kamar ta ciro zuciyarta ta yada kasa, a zuciyarta tace wallahi idan dai Allah ya hadata da Mubarak saita kwakwule masa idanuwa. Tsohon da Shalele ta kira da Babanta kuwa, maganar Shalele ta tsaya masa a rai, Babana don girman Allah karka tafi ka barni a wurin nan ka tafi dani don Allah! Wace ce ita? Me tayi aka kawota wurin nan ita kuma?. Ita kuwa Shalele bayan ta gama haukarta ta hakura ta zauna dan bata da mafita wanda ta wuce tayi hakuri ta jira zuwa ranar da za’a kasheta. Tana cikin wannan tunanin kuma taji an bude kofa, Bakin ciki ma ya hanata juyowa kwata kwata tana durkushe sai kuka mara sauti da takeyi zuciyarta tayi mata kunci gaba daya ta rasa mi yake mata dadi a rayuwarta. Maganar Mubarak taji yana cewa ku kunceta, a lokacin zuciyarta harta kawo mata a makoshi. Ko motsin kirki batayi ba har aka kunce ta, mikewa tsaye tayi da sauri tare da juyowa kanta a duke yake ta fara tattara hannun rigarta wato tana nannade shi. Rai a murtuke ta dago kanta idonta ya sauka a idon Mubarak, saida taja baya kadan sannan tace na tsanake a rayuwata ban kaunarka, tabe baki yayi tare da nunawa mutanen dake wurin cewa su fita, Babu wani bata lokaci kowa ya kama gabansa, saida yadan taba kansa da dan yatsansa daya alamar yana nazari, yawwwa, kika ce mene ne ma? 
Cikin bacin rai Shalele ta sake maimaita abinda ta fada sannan ta kara da cewa idan har ka haifu a wurin babanka, idan harda jini mamarka ta haifeka bada manja ba, to yau ina so kasa a harbeni yanzun nan shine zansan kai babban dan iska ne. 
Wannan abu yayi ma Mubarak ciwo sosai, yace ke nine dan iska? Cikin rashin tsoro tace akwai wani bayan kai dama? dakiki banza wawa marar tunani saida na tsinewa zuciyata da tun farko taso ka itama tasan tayi hauka data so kidahumi irinka, a lokacin data gane waye kai saida tayi sumar wucin gadi sannan ta farfado, idan harkai gwarzon maza ne cikakken namiji daya raka cikin miliyoyin maza kamar yanda babanku yace mu koma kauye can tushen kiyayya anan zan nuna maka Shalele jarwuyace. Da mamaki Mubarak yabita da kallo, saida ta gama sannan yace ni kike zagi? Naji na zageka shigowar Mai nasara danyin magana da Mubarak yaji ana maganar zagi, kamar ansashi yace ke kin samu tabin hankaline”yar labai kike ma rashin kunya? 
Anji anyi masa aini a wurina banza n …….. kafin ta rufe bakinta tuni Mai nasara yakai ma bakinta kusha da kasan bindiga, dan ita batasan matsayin Mubarak ba kuma batasan wayeshi ba, itadai kawai taga dan uwanta ne shi yasa take ganinsa kamar a banza yake. 
Cikin bacin rai Mubarak ya kashe Mai nasara da mari harsai daya fadi kasa, da sauri ya tashi saida ya girmama mishi sannan yayi waje ba tare da yayi abinda ya kawoshi ba, da sauri Shalele ta daga hannunta da niyar marin Mubarak amma sai hannunta ya kama kyarma. Jinjina kai Mubarak yayi tare da cewa to bisimillah waye ya hanaki ne? Yawwa kina maganar kin tsaneni ne ko? To jira kiji idan kin sani ki kara sani idan ma baki sani ba yanzun zan fada miki, duk a duniyar nan babu mutumin dana tsana kamarki, idanuwa Shalele ta zaro sosai, Mubarak yace kwarai kuwa. Banza kazama dake, sake zaro idanuwa tayi tana kallonsa yaci gaba da cewa da nayi niyar taimakonki amma yanzun na fasa, gaba daya jijiyon kan Shalele saida suka tashi fitar lumfashinta ya koma kamar wanda take gangara zuwa lahira. Kauyen da kike takama a koma ai ba gidan ubanki bane gidan babana ne, nine dakaina 
na roka alfarma babana yabar babanki yakeyin zama a gidan ada akwai mutunci yanzun kam babu sai ya tashi a gidan tunda shima bana ubansa bane. Wani irin kukan kura Shalele tayi takai wa idon Mubarak caka da akaifunta tana tace ubana kake zagi? Wurgar da ita yayi daga jikinsa tare dakai mata wani irin gigitaccen harbi, gyara rigarsa yayi saida ya sake tattaka ta sannan yace ke so nawa kika zagi babana a gaban idonsa saboda rashin da’a da tarbiya wanda babanki bai koya miki girmama na gaba dake ba, a gaban idonki babanki yayi min rashin mutunci amma ai ban masa rashin kunya ba saboda ni babana ya nunamin sanin darajar na gaba dani, kuma ai nasan suna abunsu amma ban taba shiga ba, inda naso a yinin ranar nan saina mayar da babanki almajiri banza wawiya sakara jaka ma irinki daga yau idan kika sake nuna kin sanni sainabi takanki da mota na WUCe. 
Da sauri Shalele ta sake tashi takai ma wuyan Mubarak Shaka, dakel ya banbare hannunta dagajikinsa yaci gaba da dukanta babu ji babu gani, ihunta yasa sauran jami”an dake waje suka shigo da gudu, rike Mubarak sukeyi amma baya rikuwa yayi dameji da fuskar Shalele bama ka gane ta ina jinin yake futowa, duk wurin an kasa samun mai iya rikesa saida ya gaji dan kansa sannan yace kije ki tambayi ubanki a cikin shida babana waye bashi da gaskiya? Ina kokarin ganin na gyara kin kwabe komai mtswwww ……… yana 
fadin haka ya fice a wurin da sauri kowa yabi bayansa. Aka bar Shalele da jinya. Kukanta ma baya fitowa sai wani kuka kasa kasa takeyi kamar mage ta kware, ta dauka Mubarak irin mazan da take duka ne ta zauna lafiya bata san shinejar wuyar ba, yau kam taci gidansu harta rasa bakin magana ma. Mubarak kuwa rai a bace ya fita tare da cewa a maido case din su Hafsa nan zata gane ina da rana idan banda shi zata tsaya a gaban alkali tayi masa bayani, ku canja komai a gaban idonta tace anyi kisan kai sannan kuma mutum ukku ake so sheda hauka ko yarinta babu maganarsu ace tana da karanci shekaru, duk yana tafiya yakeyin wannan bayani 
glass dinsa ya saka a daidai lokacin da zai shiga mota. Saida kowa ya sake girmamawa sannan ya shige motar aka rufe masa Mai nasara yaja su ka tafi …….. 
Shalele kuwa ta shiga tashin hankali dan ita duk abinda tayi a tunaninta bazai bata rai ba, ashe abun yakai haka? Yau hadda cewa wai gidansu ba gidan ubanta bane kuma ba babanta mai gida ne ya siya ba, goge hawaye tayi tare dayin ajiyar zuciya wai idan yaga dama a yinin nan zai mayar da babanta almajiri. 
Kuka sosai Shalele takeyi, ta tsinewa ‘so“ a rayuwarta, ta tsani kalmar ‘SO’ kamar yanda Maryam tace, yau da zata ga Maryam data kara taimaka mata, kaji dodewar basira kuma, banda yarinta duk asirin da sukayi babu wanda yaci amma yanzun har wani cewa takeyi ta taimaka mata, 
Mubarak kuwa rai a bace ya isa gida, ya kuma fadawa duk masu gadin gidansa idan suka 
sake ganin mai kama da Shalele suyi ta kutubolbol da ita inji shi …….. 
Bayan kwana biyu labari kuwa ya isa a kunne Bashirda Mai gida labarin an tafi da 
matar da suke riko a matsayin dukiyarsu. Hankali ya tashi tsakanin abonkan gabar guda biyu, kowa gani yakeyi abokin gabarsa yaje ya dauketa ya gudu da ita dan yaci kudin shi 
 wannan dalili yasa tashin hankali ya tashi sosai a tsakanin gidaje biyun. Fitina sosai akeyi dan idan dan wani gida yaga dan wani gida to saiya sassarashi sannan ya dorasa a saman doki a mayarda mutum gidansu, tashin hankali sukeyi sosai a kauyen nan babu ji babu gani banda wannan fitinar kuma shi Bashir yace da bala”i sai Mai gida ya tashi a gidan nan da yake zaune saboda gidansa ne shine ya siya da kudinsa. Idan hankalin Mai gida yayi dubu ya tashi kuma shi baya da wani gidan, ya rasa ina zaisa kansa kuma idan takamarsa yakai kara to idanma yaje su Mubarak zai iske dan girmansa yakai duk inda mutum baya tunani yana da matsayi sosai sannan yana da kudi na tashin hankali wanda shi kansa baisan iya adadin abinda yake dashi ba a duniya. Yana da tausayi idan yana san abu. Amma duk duniya abinda ya tsana shine haihuwa ya tsani ya haihu a rayuwarsa dan bayahude ne na karshen zamani. 
Mama tace ma Mai gida kada ya tashi amma yace Mama ki barshi tunda yace wannan ma gidan sane zan tashi nabar masa ya hada duka ya cinye, yafi so kamar yanda muka zauna kotu a shakarun baya mu kara zama dani dashi dan yaga dansa ya zama wata tsiya a duniya. A ranar ba”a kwana ba mai gida ya buga waya wa Alhaji Abas ya fada masa duk abinda yake faruwa ba komai yace masa ya zauna a gidan sa dake nan bayan gidan da zai tashi, a ranar mai gida ya tattara komai nasa ya koma gidan Alhaji Abbas, Asma”u da Mama duk sune sukayi tayin duk wani dan gyare gyare a gidan. Shalele ta samu labari zasu shiga kotu zata bada shedar kisan kan da taga anyi wa bawan Allah da baiji bai gani ba sannan kuma ance zatazo da shedu mutum ukku, ta shiga damuwa sosai tayi kuka har hawayenta suka kare. 
Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE