HARSASHEN SO CHAPTER 20
HARSASHEN SO
CHAPTER 20
Saida tasha kukanta hartayi gyatsar wahala sannan ta danjinjina kanta tare dayin dan gajeren murmushi. Kome ta tuno ne har yasa ta tayi murmushi Ohol.
Tashi tayi daga wurin zamanta ta canja wani wuri danjin ruwan saman da akeyi yana feso mata, a hankali ta zauna tare da dunkule jikinta duka kamar bushi ta hango maciji. Sauke wahalalliyar ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanuwanta a hankali murmushi dauke a saman kyakkyawar fuskarta, babu abinda take gani a cikin zuciyarta sai hoton Mubarak.
Cikin nishadi ta kara sadda kanta kasa ta kaisa saman guyawunta ta kwantar da kanta a gefen haggu har yanzun murmushi takeyi kuma hotonsa bai goge ba tana ganinsa sosai kamar a gabanta yake tsaye da gaskiya. Shigowa akayi cikin dakin hakan baisa ta fasa tunaninta ba kuma bata bude ido dan ganin waye ba, jin karar tasa ya tabbatar mata da abincinta ne aka kawo, daga inda yake tsaye gyargyara mata abinci tare da fita ya kulle wurin.
_Kauyen da kike takama a koma ai ba gidan ubanki bane gidan babana ne, nine dakaina na roka alfarma babana yabar babanki yakeyin zama a gidan ada akwai mutinci yanzun kam babu sai ya tashi a gidan tunda shima bana ubansa bane._
Da sauri ta bude idonta dan tuno wannan maganar da tayi a ranta, a hankali ta mayar dasu ta sake rumtsewa da karfi kamar an watsawa idon tiyagas, hawaye ne suka tsiraro daga cikin idonta bacin ran dake cin zuciyarta ma ya hana ta goge hawayen. A bayyane tace Allah ka dafamin ka kunyata dan makiyin babana, ka kubutar dani daga duk wani sharri da makircinsu ka wanke minshi daga zuciyata ka mantar min dashi a cikin raina, Allah ka kawomin dauki a rayuwata kaba mahaifina hakuri ubangiji ka bashi wurin zama ya tashi a wannan jakin gidab, Allah ka bani karfin da zan rama dukan da makiyina yayimin. Saida ta goge hawaye sannan taci gaba da cewa ya Allah nima kasa na zama soja ka bani kudi na sayi bindiga na gama da bayan Mubarak in matardashi kamar yanda mamana
tabar duniyar nan. Hankalin Mai gida kwance yake sosai dan babu abinda yake damunsa sai bakin cikin rashin diyarsa a kusa dashi wanda a yanzu baya da labarinta kwata kwata, wurin bokansa ma kwana biyu baije ba dan baya da “yan kudin da zai bashi, yanzun dai zama ne yakeyi na rufin asiri dan komai ba kamar daba. Kuma duka yaransa suna tare dashi yace duk kowa yai tafiyarsa neman na kansa amma sunce suda mai gida amana ne dan su basa bakin kaza duk bakin da yaci ya gode.
A bangaren Shalele kuwa tana cikin damuwa dan gobene ranar da zata shiga kotu dan bada shedar kisan da tace anyi a gaban idonta. Idan hankalinta yakai cinnaka kwanciya a saman doron kasa to fa a daren yau ya tashi yafi jirgin sama tashi ……… Ta shiga damuwa ta rasa ta ina zata fara, amma ta yanke shawarar kawai ta fadi gaskiya koda za’a kasheta in yaso duk abinda zai faru kawai ya faru ayita ta kare. Wannan dare Shalele bacci fita yayi daga idonta saidai ta kulla wancan ta warware amma
har safiya ta waye bata samu mafita ba.
08:00am motar gidan yari ta dauki Shalele dan zuwa kotun da zata bayar da shaida. Hannunta da kafafuwanta a daure suke da sarkoki banda hawaye babu abinda yake diga daga cikin idon Shalele kanta a sadde yana kallon kasa idanuwanta a rufe ta cije lebonta
na kasa tana girgiza kanta a hankali ji takeyi kamar ta hadiye zuciya ta mutu.
Harsuka isa kotun Shalele kuka takeyi, tun a wajen kotun taron dinbin mutane ne carko carko sai “yan kananan maganganun dake tashi, wuri ne daya tara dumbin mutane daban daban sannan kuma mutane sun bulbulo daga wurare da dama. Shalele tana fitowa daga cikin mota idonta ya sauka a kan Hafsat itama an dabaibayota iya dabaibayuwa, saida gaban Shalele yayi dakan luguden fura fura, dan Hafsat taci uwarta sosai itama dai kamannunta sun canja zuwa wata siffar daban. Kisan rai ba banza ba, Harsuka shiga cikin kotun gaban Shalele bai daina faduwa ba, cikin kauyanci take bin kotun da kallo tunda take a rayuwarta bata taba zuwa irin wannan wuri ba, kotun katuwa ce sosai ga dunbin mutane kowa ya samu wuri ya zauna mutane iri iri dai take ganinsu wannan abu shine yasa ma Shalelejin dimuwa, tunda ita dai kullum tana kauye a dukunkune bata fitowa babu inda ta sani daga gidan Mubarak sai asibiti, sai gidan da tayi haya, sai kuma gidan Alhaji Abas da dan yawon bin malamansu da sukayi da maryam.
Gaba daya cikin kotun yayi sit bakajin ko wani motsin kirki kowa ya kama kansa, Shalele sai kallon inda aka ajiyeta takeyi tana kuma hango Hafsat sai mutane data gani sunyi kisan wanda duk da a duhu ne hakika ta shaida su amma su miyasa suka koma cikin “yan kallo
wannan tambayar itace tayi ma kanta. Tana wannan tunanin ne taji dan surutu kasa kasa ya fara tashi dan haka ta dawo da hankalinta a cikin jikinta. Mai da kallonta tayi inda Hafsat take dan sun fara wancan tsohon case din na kisan mijinta wanda bai shafi Shalele ba tana daijin ikon Allah.
Bayan “yan korafe korafe da Alkali ya saurara ya daga wannan shari”a zuwa watan gaba, sabon case aka shiga iyayen saurayin Asiya wanda aka kashe a gaban idon Shalele wanda shi kuma aka lakafa mishi shine wanda ya kashe Asiya. Shima karanto karar sukayi daga farko har zuwa lokacin da “yan sanda suka sakeshi da belinsa da Hafsat ta anso, daga nan abokinsa ya dora bayani vidion da abokin nasa ya tura masa a waya, kotu ta bukaci ganin vidion,
Wayarsa ya bada dan tabbatarwa da kotu, neman vidio akayi a wayarsa amma babu an duba iya dubawa amma babu, alkali ya tambayesa ko yana da wata sheda bayan wannan wanda ya bayar?
Cikin sacewar guyawu yace Eh ranka ya dade, mene shedar taka ne? Alkali ya tambayesa, sheda ta daya ce, gata can ya nuna Shalele. Da sauri ta zaro idanuwanta tare da kallonsa ita tunda take a duniya ma bata taba ganinsa ba, inma banda Abak yake so ta mutu wai duka ma miye ya hada alakarta da koto don girman Allah? Ita Hafsat auren dole akayi mata ta kashe mijinta kuma kowa ya sani shine dalilinta na guduwa daga garinsu taje abuja. Sai maganar kisan Asiya shima Abak yayi bincike yasan itace tasa aka kashe ta, kuma sun samu labari saurayinta yana da masaniya akan komai bayan “yan sanda sunka kamashi ita Hafsat taje ta taho dashi da sunan beli shima tasa aka
sheke shi, haba ga gaskiya an sani amma sai an wani tsaya ana munafirci? Maganar Hafsat taji tana cewa ya mai shari‘ ai waccan kurma ce bataji kwata kwata. Cikin yarinta Shalele tace inji waye yace banaji? Ba duk naji abinda kuke cewa ba, gaskiya ke Hafsat kiji tsoron Allah wallahi naji ki lokacin da kikace ya yadda shine ya kasheta da yace baya yadda kika ce akashe banza ina kallon kisar aka toshe masa baki da zani kuma kika Sa aka wani ratayeshi a sama sai kace mataccen rago.
Kallon Shalele alkali yayi tare da tambayarta sunanta, saida ta dan cuno baki sannan tace suna na Ummu Suleim amma a garinmu Shalele ake cemin, shekarunki nawa inji alkali ya tambayeta, Shalele tace ni wallahi bansan ko shekarata nawa ba. Saida alkali ya karewa Shalele kallo sosai sannan yace shin kin gani a lokacin da ita Hafsat take kashe wannan mutumin ne? A gaban idonki akayi? Shiru Shalele tayi ta kasa magana, ita kuwa Hafsa mamaki ne ya lullube mata zuciya kallon Shalele kawai takeyi
cikin mamaki kurmar mutum tana magana. Nazari sosai Shalele tayi sannan tace Eh gaskiya na gani amma ba ita bace ta kashe shi itace dai ta saka akayi kisan. Alkali yace ke da waye kika gani kuma a ina kike a lokacin da sukeyin kisan ne? Labari ta bada tahowarta daga gidan hafsa harzuwanta gidan da aka ajiye mutumin kisan sa fitar ta da kuma komawarta gida amma duka bata sanyo zance Abak ba ko daya dan ita zataci ubansa da kanta wannan hukunci bana alkali bane.
Alkali yace shin kina da sheda ne? Wanda zai tabbatarwa da kotu abinda kike fada gaskiya ne? Ajiyar zuciya Shalele tayi tare da cewa Eh, Alkali yace waye shedar taki, Shalele tace sheduna dukansu suna wurin nan, kallon Hafsat tayi tare da cewa ga daya can ke Hafsat tsakaninki da Allah ki fadi gaskiya ba kece kika sa wancan mutumin da wancan suka kashe bawan Allah nan ba? Kiji tsoron Allah ki fadawa mutane suji don Allah a kyaleni haka
nan na tafi gida…. Kowa kallon Shalele yake saboda duka abun nata na yarinta takeyi.
Alkali yace ke Umma saurara waye yace miki haka ake bawa kotu shedu ne? Shalele tayi shiru alkali yaci gaba da cewa idan har babu sheda hukunci zai kamaki, idanuwa Shalele ta zaro tare da cewa Eye? Kenan kasheni za’ayi su kuma abarsu su tafi? Kallonta alkali yayi sosai tare da gyara zaman glashin idonsa. Sannan yace kwarai kuwa idan kina da wata shedar ina saurarenki.
Ci gaba tayi da kuka tare da cewa to a fara daure mutanen can kada su gudu, sannan kuma nayi alkawari zan kawo shedata a zama na gaba. “yan rubuce rubuce alkali yayi tare da fadar kwanakin watan sake zama. Shalele tanaji tana gani aka tattarata aka mayar da ita gidan yari, banda kuka da tsinuwa babu abinda takejawa Abak wanda shi yama manta da lamarinta baya ma nigeria yayi tafiyarsa huddodin gabansa. Hafsa kuwa yau ji takeyi da a wuri daya suke da Shalele wallahi dasai ta kasheta har abadan duniya, suma dangin mijinta data kashe dasu ka wani kafe kai da fata sai anyi mata hukunci daidai da abinda tayiwa dan uwansu ji takeyi suma ta kashesu ta samu ta kubuce ta huta amma bata da yanda zatayi kisan kai tayi kuma tasa akayi dole itama sai an kasheta, gashi shi kwartonta da yasa mai gadin gidansa yayi ma Asiya fyade sannan kuma
ya kasheta da hannunsa, amma shine shi ba’a kamo sa ba.
Kuka Hafsat keyi sosai tasan babu makawa sai taje lahira, sai yanzun nadama tazo mata bata san rai yana da amfani ba saida taga zata rabu da nata. Kuka takeyi sosai tare da tuno ranardata kashe mijinta. Da shareriyar wuka ta kashe shi, ihun da yakeyi karta kasheshi tayi hakuri ta barshi baisa ta daina ba duk gurnani na fitar rai besa Hafsa taji tausayinsa ba, haka tayi taci gaba da caccaka masa wuka saida ransa ya fita sannan ta samu natsuwa, juyowar da zatayi dan
hutawa tayi ido biyu da mai gadi wanda mai aikinta ta kirawo sa dan ganin abinda ta gani.
Ganin an ganta kuma tasan asirinta zai tonu yasa ta nufosu da wuka da gudu suka arce, wannan gudun da sukayi shine ya bawa Hafsat damar gudu itama daga gidan, wannan
shine dalilinta na zuwa Abuja, anan taga Abak kuma ta kallafa masa rai tana sansa fiye da
tunanin mai karatu. Ita kuma Asiya tasan Hafsat garinsu daya, ita dai Asiya barikinta ta kawo ta ita kuwa Hafsa kisa tayi ta gudo.
Kuka sosai Hafsat takeyi ji takeyi ina ma baya zata dawo data gyara data goge kisan da tayiwa mijinta mai santa da kaunarta, gashi duniya bata tsinana mata komai ba itama zata
iskoshi. Haka tayi ta kuka tare dajin bakin ciki tayi tirrr da halin zuciya mara kyau,
A bangaren Shalele kuwa ta kulla ta warware ta rasa a ina zata samu mafita, bata da wata sheda fa kuma bata san inda zata samo wannan sheda ba, haka ta hakura ta yadda da
mafitar da zuciyarta ta bata wanda ita kadai tasan abinda zuciyar tata ta yanke mata.
Zama na kunci da bakin ciki Shalele taci gaba dayi a gidan yari harzuwa lokacin da zasu koma kotu. Wannan dare yafi dagawa Shalele hankali a cikin ko wane dare da tayi a duniya, ta kulle kanta ta hanyar cewa tana da sheda gashi ranar bayar da sheda yazo amma bata da wata kwakkwarar sheda. Haka tayi tajuyayi har garin Allah ya waye.
Yauma a motar gidan yari aka tafi da ita kamar dai na farkon yauma haka take, a lokacin da suka shiga kotu tuni kowa ya hallara hardai alkali shima bai dade da zuwa ba. Kotu tayi shiru sosai da gani yau abun mai zafine, bayan “yan rubuce rubuce da alkali yayi ya dago kansa ya kalli Shalele cewa,
Ina shedar taki? Wani lauya ne yace ya mai girma mai shari’a yana tambayarki cewa mene ne shedar taki? Ihun fitar ran mutumin nan Shalele ta tunu lokaci guda hawaye sukaci gaba da ambali daga cikin idonta, alkali ya sake cewa mene ne shedar taki? Cikin kuka Shalele tace nice nan, shedar kai tsaye. Alkali yace shin kin gani kinga lokacin da mutane biyun can suke kashe Ibrahim? Cikin kuka Shalele tace ba mutane biyu bane ya mai shari’a mutane hudu ne, cikon na hudun ba kowa bane nice. Gaba daya kotu ta yamutse da maganganu, yayin da wanda sukayi kisan suka fara cewa Shalele ke banza kin samu tabin hankali ne? So kike a kiramu mahaukata?
To kema mahaukaciya ce,
Alkali yace a saurara a saurara, bayan kowa yayi shiru Shalele taci gaba da cewa mu mutane hudu muka azabtar zashi bayan azabtuwar da yayi da kansa ya bukaci mu kasheshi saboda azabar tayi yawa. A lokacin daya fadi haka mu dukanmu a cikinmu nan
kowa yaji dadi saboda ya fadi hakan da bakinsa.
Ni nacewa Hafsa kar mu kashesa amma su sauran sukace mu kashe sa idan ba haka ba zai iya tona mana asiri. Alkali yace idan har hadda ke aka kashe sa me yasa kuma kika daga cikinsu ke kika kawo kara? Shalele tace kudi na bukata su bani tunda ni banda ni akayi kisan nace zan rufa musu asiri a lokacin sunyi alkawari zasu bani, bayan wani lokaci kuma na sake yi musu magana su bani suka hanani wannan dalilin yasa naga gara kawai na tona mana asiri domin mun aikata babban kuskure ga Ibrahim, Cikin kuka Shalele tace ina rokon wannan kotu mai alfar data yanke hukunci akan
mutane hudun nan, domin mun aikata babban kuskure munyi abinda Allah baya so, hada hannayenta tayi duka biyun taci gaba da cewa muna neman alfar ga wannan kotu mai adalici data yanke hukunci kisa akanmu kamar yanda muka kashe Ibrahim baiji bai gani ba inaganin idan har akayi haka kisan kai da ta’addanci zai ragu a kasa ta nigeria ina san nigeria, nigeria kasace mai adalci, duk maiyin sha’awar kisan kai idan yaga hukunci da aka yanke mana zaiji tsoron yi saboda kowa yasan yanda rai yake da dadi a rayuwa.
Bayan “yan rubuce rubuce da Alkali yayi yace a dokar kasarmu a game da kisan kai, wannan kotu mai alfarma da adalci tare da kare hakkin bil’adama wa’annan mutane hudun basu da da’a sannan kuma basu cancanci ci gaba da rayuwa ba, kotu ta yanke musu hukuncin kisa ……………… ta hanyar rataya a cikin sa’o’e 24.
Murmushi Shalele tayi dan ita wannan rayuwar itace tafi dadi a gareta, tana rayuwa ammajinta takeyi a matsayin matacciya, so kuwa idan harya shiga baya fita har abadan duniya wannan shi ake kira da san maso wani ……… yau kam da har zata iya cire ‘HARSASHEN SON’ da yayi tsalle ya soki zuciyarta da zata iya ciresa, hakika dasai ta ciresa
kafin tabar duniya.
Tana wannan tunnanin ne taji an rufa mata da duka ta ko ina, murmushi tayi a lokacin data tabbatarda masu dukan nata wato wanda suka aikata kisan kaine, dan ita Hafsat tuni duniya ta suma, bayan an kwaci Shalele daga hannunsu aka tattara su domin tafiya dasu inda za’a ratayesu ……………
Hmm