HARSASHEN SO CHAPTER 21
HARSASHEN SO
CHAPTER 21
A Flrgice Hafsat ta farfado cikin tashin hankali ta kalli Shalele wanda ita ko,a jikinta abun bai dauketa ya nanikata da kasa ba.
Ajiyar zuciya Hafsat ta sauke tare da cewa karku kashe wannan baiwar Allah wallahi babu abinda tayi na rantse da girman Allah duk abinda ta fada karya ne mu koma zan fadi gaskiya. Babu wanda ya saurari Hafsat ita dama Shalele bata san kowa ya kulata ta kagara taji an turbudeta a cikin kasa. Tuni labari ya bazu, duk wanda yake da dalilin sani yaji labari za’ayi kisan wa’dannan mutane hudu.
Mai nasara ma labari yakai masa domin yayi waya da mai kula da fulawowin gidan Abak tunda kanin matarsa ne aka kashe, ya buga ne yayi masa ya hanya da kuma jin labari ina shari’a ta tsaya. Mutumin ya fada masa komai da kuma wankan tsarkin da Shalele tayi ta dulmiya kanta ciki,
Ya kara da cewa an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya a cikin awanni 24 haka alkali ya fada. Cikin tashin hankali Mai nasara ya kashe wayarsa tare da fara kiran wayar Mubarak dan ya fada masa za’a kashe Shalele amma ya kirasa yafi so babu adadi amma Mubarak bai dauka ba.
Hafsat kuwa Allah yasa mata jin tausayin Shalele akwai rashin adalci wannan zalinci ne cutane sosai, dan haka ta sake rike kafafuwan dan sanda gasu da fuskokinsu na rashin
tausayi cikin kuka tace don darajar ubangiji ku fitar da yarinyar nan wallahi wallahi babu ruwanta.
Mazan biyu da suka kashe Ibrahim sukace kam bala”in nan wallahi bamu yadda kam kenan saimu a kashemu? Ai tuni fada ya kaure duk da hannayensu dukansu suna daure saida suka rika yin harbi da kafafuwansu hanyar tsira da ransu kawai suke nema. Ganin haka yasa driver yin kwana dan dawo dasu kotu tunda basuyi nisa da wurin sosai ba,
amma su makasan suna ta kokarin ansar mukullin su bude hanya su gudu. A haka dai suka iso kotun drivern da kansa ya fito ya shiga cikin kotun ya dade sosai sannan ya Fito dashi da wasu mutanen daban, bude mota akayi aka cirosu dukansu aka koma dasu ciki.
Sake sabon zama akayi bincike sosai alkali yayi da gudamar bayanin da Hafsat tayi kuma ya gamsu da hakan kuma ya gane babu sa hannun Shalele a cikin kisan nan, kotu ta dauraye Shalele a gaban idonta aka sake tafiya dasu, Hafsat sai kuka takeyi. Saida aka tafl dasu sannan Shalele ta sauke ajiyar zuciya, gage hawayen idonta tayi tare da juyawa ta fara tafiya don Alkali ya bata damar tafiya. Tafiya takeyi k0 ganin gabanta batayi sai zance zuci takeyi da tunani iri iri ta fita daga cikin kotun, kai tsaye abun hawa tahau ta nufl tasha babu ko sisi a hannunta, Bayan mai napep ya kaita tasha ta samu motar zuwa abuja, a wurin mai mota ta ansa kudi ta bawa mai napep sannan ta shiga mota, Tunda ta shiga mota kuka takeyi wanda ita kanta bata san dalilin yinsa ba, jigum take her motar ta cika suka kama hanyar zuwa Abuja. Bayan an fara ansar kudin mota wani bawan Allah yaga Shalele bata biya kudi ba, kuma ita ta fadawa mai mota cewa bata da kudi sai sun sauka a Abuja zata basu amma dan iskancin yaron mota sai cewa yakeyi kawo kudln motarki.
Dole wannan bawan Allah ya biyawa Shalele kudin mota, haka suka zugi hanya harzuwa
garin Abuja Shalele ko tari batayi ba sai hawaye dake zuba daga idonta har suka isa Abuja. Suna sauka Shalele bata tsaya wata wata ba ta dire daga mota ta nemi motar zuwa garinsu. shima nan babu kudi, haka ta hau mota a bashi ta wuce garinsu. Saida suka sauka sannan ta bawa mai motar hakuri cewa insha Allah zata bashi kudinshi idan zata koma gari wani satin. Da haka suka rabu ta kama hanyar gidansu. Hankali a tashe ta isa gida dan bata san abinda zata lsko ba, amma ga mamakinta gida wayam babu kowa sai ku kan dawakai da takeji sai maganar mutane kasa kasa wanda baza ta iya tantance muryoyinsu ba.
Da sauri ta fita daga gidan cikin tashin hankali da tsoro kardai Mai glda ya mutu? Tambayar da tayiwa kanta kenan, tana fitowa ta dan dudduba amma babu mutum ko daya wanda zata tambaya, dan haka cikin gidan ta sake komawa a daidai lokacin Bashir yana saukowa daga saman bene dashi da wani mutum suna magana amma batajin abinda suke cewa. Meya kawoki cikin gidana ne iye? Tambayar da yayi mata kenan, kallonsa Shalele tayi cikin tsananin bacin rai sannan tace kai da Allah rufewa mutane baki waye ya baka ikon shigowa cikin gidan ubanda ya haifeni? Da sauri ya sauko tare da dunkule hannunsa yakai ma bakin shalele duka sannan yace ki gyara kalamanki akaina, murmushi Shalele tayi da gefen bakinta tare da goge bakin nata sannan tace kaci albarkacin danka, wanda na raga maka domin shi amma banda shi a yau dasai na kware maka fatar jikinka na barbada mata gishiri.
Cikin fushi sosai Shalele ‘taci gaba da cewa ada bana nan amma yanzu na dawo wallahi ko kasa da sama zata hade wannan gidan babu meshi sai Mai gida, idan har kana san gida irin wannan saika sake tara kudi idan kana da rabo ka gina mai kama dashi marar zuciya ………. idan har na tsani abu a rayuwata na tsanesa idan har nace zanyi saina aikata, daga yau na sake ganin burbushin zuri’arka a gidannan to lallai kogin jini zai fara gudana a cikin kauyen nan. Tana fadin haka ta juya a zuciye ta fita daga cikin gidan, a kofar gida ta samu daya daga cikin yaran mai gida zai wuce tace masa kai zo nan, da sauri ya dawo dan ya dauki muryar Shalele kallonsa tayi cikin damuwa tace ina ne gidan da muka koma? Cikin girmamawa yace karamin mai gida yana ta bayan can.
Tou kaje kacewa Mai gida na dawo dan haka duk mai nemana ina nan kaje maza sannan kuma ka tahomin da abinci yunwa nakeji. Tana fadin haka ta juya ta koma cikin gidan, Bashir yana ganinta yace ke duk iskancin da kikeji dashi a daren nan zansa a sauke miki shi.
K0 inda yake Shalele bata kalla ba ta wuce ciki, Da sauri ta haura sama kai tsaye dakinta ta wuce a cikin dakin nata anan aka daure dawakai sunkai goma, bata tsaya bata lokaci ba ta kwance su tare da daukar wani icce tayi ta dukansu da gudu sukayo waje suna haniniya. Bayan ta korosu ta fito ta samu tsintsiya zata koma cikin dakin taji Bashir yana cewa a kirawo masa Sulaiman wani dan iskan
yaronsa ne shine kadai dama bayajin tsoron Shalele a lokacin tana jarumarta ba yanzu
data koma mace ba.
Mai gida kuwa yanajin labari Shalele tana gidan Bashir daga shi har Mama ba’a baro kowa ba, duka zugar “yan daban sa saida suka biyosa, a Iokacin Shalele har ta fara wanke dakinta. Zuwansu mai gida yayi daidai da shigowar Sulaiman shima a zuciye yazo,
hayaniyarsu ce tasa Shalele fitowa daga cikin dakin tazo ta tsaya suna kasa tana sama,
Daga saman bene Shalele ta fara magana cewa Mai gida da farko ina baka hakuri kayi hakuri kuma ka gafarceni akan abunda nayi maka nayi alkawari haka bazata sake faru ba in Allah ya yadda, sannan kuma na daura damarar ganin bayan duk wanda baka san ganin nunfashin sa a cikin duniya. ldan takamar mutum iya sharri ni nice sharri da kaina, wallahi idan har kaga na fita a gidan nan saika turo min karamin dan iskan danka a gaban idonka zaka ga yanda zanyi gunduwa gunduwa da dashi kamar yanda ake daddatsa kifi haka zanyi kaca kaca dashi a gaban idonka.
Kar kayi tunanin k0 ina sansa shi yasa daka dakeni ban rama ba, nuna maka nayi nima ubana ya bani tarbiyya sannan kuma ya nuna min girmama na gaba dani, a da ina san danka wanda nake fatan ya zama abokin rayuwa a gareni, to yanzun na daina ko sansa zai kasheni saidai a binne ni da raina, Balaga tako daya idan waccan dan iska yayi a cikin gidan nan ka cire min kansa inji ni, Sulaiman take nufl, sannan taci gaba da cewa shi kuma Baba Bashir ku fitar min dashi daga cikin gidan nan cikin girmamawa da martabawa dan ya gane akwai banbancin tarbiyya ku bacemin da shi yanzun …………. nan ………. wutar gaba yanzun nan Shalele ta hurata kiyayyar ta dawo hannuna na cire mahaifina idan shima yaga dama ya fita ya barni da dansa idan kuma zaku shigo dukanku Shalele ruwan wankeku ce wutar dafaku mutuwarku ni Shalele saina mayarda yankin Makiyana makabarta wannan shine burin mai gida kuma mafarkinsa, mutuwarku ta dawo kowa kalli gabansa Shalele ta dawo da zafinta ……….
Bashir yace tirrr da kika kirani da suna babanki badan karna bar abun kunya a bayana ba yau dasai nayi miki wulakanci na karshe. Dariya Shalele tayi sannan tace nikam banajin komai kuma bana hange ko tunanin abinda gaba zatayi har abadan duniya bana fatar Allah
yasa mu zauna lafiya gaba ce da kiyayya muyi ta nunawa juna daga nan har a busaaa
Mai gida zaiyi magana Shalele tace karka wani damu babana karkace komai ka barni dasu Shalele kadai ta ishesu,jinjina kai Bashir yayi tare dajuyawa danshi a duniya duk abinda zaiyi yana hangawa kafin yaje ya dawo, mai tunani kenan. Amma daya biye zuciyarsa da saiya babballa Shalele kuma da mai gidane yayi maganar zai girba masa rashin mutunci saboda shi abokin haihuwarsa ne, amma ita Shalele har gobe tana zama ne a matsayin diya a wurinsa bawai tsoronta yakeji ba, dan idan har zai iya kuncewa yayi danbe da Abak to lallai zai iya nannade kafar wando ya daki Shalele saida ya daketa dan hukunci amma badai sunan fada ba. Tunda har ta zabi kiyayyar “ya”ya su shigo zai barta da Mubarak zataji idan shi laushi ne dashi.
Mama tace Shalele bana hanaki yiwa Yayan mahaifinki rashin kunya ba? Tabe baki Shalele tayi sannan tace babu ruwanki mama shi dansa ba rashin mutunci yayimin ba? Nan banda Allah yasa ina da sauran shan ruwa a gaba da tuni na zama marigayiya Shalele na yadda duk wanda yace baya sanka har abadan duniya kana nan zaman makiyinsa ban gane hakan ba saida naje birni ……………
Ku shigo ciki Shalele ta dawo sabuwar rayuwa ta fara idan har mutum yaci gaba da dorawa lallai Shalele bazata gaji da saukewa ba. Gaba daya kowa ya koma dakinsa.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan, dama shi Baba Bashir inji Shalele, ranar daya koma gida baiyi bacci ba, yana cikin damuwa bai samu kwanciyar hankali ba sai yau da bakinsa ya hadu dana Mubarak ya fada masa iyakar rashin mutunci da Shalele tayi masa komai bai
boye masa ba, harda Baba Bashir da ‘yace masa.
Ummm haka Mubarak ya fada, sannan yace ita Shalinin tace maka zatayi min gunduwa gunduwa a gaban idonka? Baba Bashir yace Eh,jinjina kai Mubarak yayi tare da cewa to
yayi saina zo din. Yana fadin haka ya kashe wayarsa. Iyar bacin rai Mubarak yaji bakin ciki baisan ma iyakar rainin da yarinyar nan tayi masa ba, wai wannan “yar ca kulkular yarinyar wanda idan yayi zuciya yana iya hadiyeta wai itace zatace zatayi masa gunduwa gunduwa, dan gajeran tsski yayi tare da cewa zaki gane kuranki idan ina wasa dake ne. Ba laifi gidansu Shalele suna zaman lafiya yanzu, dama Mai gida ne yake firgita gidan, amma yanzun kam hankalinsu a kwance tunda Shalele tace abar komai a hannunta, kullum burin Mai gida gari ya waye yaji ko Shalele zatace zata kashe Baba Bashir amma shiru yakeji. Zuwa wannan lokaci kuwa Shalele har yanzun tana tunanin Mubarak dan duk abinda kake so da gaskiya yana nan zaune daram a ranka duk abinda zai maka idan dai kana san mutum to fa lallai baka ganin laifinsa.
lta dai har kullum addu’arta Allah yasa ta kara ganin Mubarak ko so dayane a rayuwarta. Koda kuwa zai mata kallon banza tana so kuma zataji dadi, Mai gida kuwa ganin Shalele ta dan samu natsuwa yasa ya sake mata take fita duk inda ranta yake so amma kullum idan zata fita sai Mai gida yace kartayi ta wurin makiyansu. Tanajin saukin kadaici saboda akwai Asma’u amma har yanzun addu’arta daya Allah yasa su hadu da Maryam a sake sabon asiri Mubarak yasota kamar ya haukace itama ta rama wulakancin da yayi mata,
Da gudu Shalele ta fito daga cikin dakinta tana dariya, Asma’u ta biyo bayanta itama da gudu tana cewa wallahi ki tsaya ki bani abuna, dariya Shalele takeyi sosai da gani tayi mugunta, ta gaban Mai gida ta wuce da gudu ta fita daga cikin gidan, itama Asma’u da gudu ta fita kamar zatayi kuka tana magiya Shalele ta bata abunta bata san wulakanci. Gudu Shalele takeyi sosai Asma”u nabin bayanta tana cewa don Allah ta bata, dutsi Asma”u ta dauka tana cewa wallahi jefar miki agara zanyi idan baki tsaya ba, itama Shalele dukawa tayi ta dauki katon dutsinta tace kina jifana nima saina rama. Aiko Asma”u saida ta wurwura sannan ta jefi Shalele kuma ta sameta tana jifarta ta juya da gudu, Shalele tace wai da gaske kikeyi? Wallahi saina rama, jifa tayo sosai da sauri Asma”u ta kauce dutsin ya wuce bai sauka ko ina ba sai saman gaban glass din motar
Mubarak gaba daya glass din saida ya tarwatse. Saida gabanta ya fadi dan tasan sai yace a biyashi, idan hankalinta yayi dubu ya tashi. Tsareta yayi da kallo cikin bacin rai, dan bude baki tayi cikin tsoro da sauri ta sauke idonta
kasa, bayan wani lokaci kuma ta dago ta kalli wurin haryanzun ita yake kallo.
A hankali tajuya ta dan fara tafiya, a hankali shima ya fara binta da mota, karajuyowa tayi taga har yanzun yana biyota, da sauri ta sake juyawa taci gaba da tafiya da dan sauri sauri salda tayi tafi mai dan nisa sannan tajuyo, haryanzun binta yakeyi da mota a hankali, kara juyawa tayi taga har yanzun ita yake bi, ganin ya kusa cimmata yasa ta yada abinda ke hannunta na Asma’u data kwato ta kwalkwala da gudu ………………….. Shima take motar yayi yabi ta da gudun tsiya …….. Cikin tsoro Shalele ta juyo taga ita Mubarak yakebi kuka ta farayi tare da kara kallon gabanta taci gaba da gudu, abinda yasa ta gudu kuwa dan tasan bata iya dukan Mubarak kuma idan ya kamata jikinta zai bata labari, har yanzun ita yake bi bai tsaya ba, ta shiga lungun da baya fita, dole tayi hakuri ta tsaya tare da dukewa kasa ta rufe kanta cikin guyawunta ta dafe kanta da duka hannayenta biyu.. .. Tana jiran isowarsa.
Hmm