HARSASHEN SO CHAPTER 22
HARSASHEN SO
CHAPTER 22
Da gudun tashin hankali ya nufu inda Shalele take da mota, burinsa kawai yabi ta kanta ya
Shalele kuwa jin kukan mota yana tun karota yasa ta dago kama dan ganin ya abun yake? Cikin tashin hankali Shalele ta zaro idanuwa tare da tashi daga wurin cikin sauri.
Tana mikewa motar Mubarak tana dukan daidai inda ta tashi garam ………. , ajiyar zuciya Shalele ta sauke tare da kallon kanta sannan ta kalli wurin, wato da bata tashi a wurin ba, burin Mubarak ya kasheta kenan?
Cikin tsananin bacin rai ta bar inda yake a lokacin harya fara rubas dan dawowa ya banketa, cikin bacin rai Shalele tace kai dakikin wane yanki ne? Sakaran banza kidahumi ko an fada maka ran mutum ran ragon layyane? Da zaka kasheshi anjima ka siyo wani? Tana tsaye tana magana ya sake yo kanta babu wasa, a wannan karon yadan gogi jikinta kadan, cikin fushi Shalele ta duka ta dauki manyan duwatsu taci gaba dajifar motar duk inda wani gllashi yake saida Shalele u bareshi tassss, ci gaba ‘tayi da jifar babu ji babu gani, da gudu Asma’u tazo wurin ta riketa.
Kuka Shalele takeyi sosai tare da kokarin kwace kanta daga jikin Asma”u tana cewa saina kasheshi wallahi ban yadda saina rama yaji min ciwo wallahi ni ba jaka bace, hakuri Asma”u take bata tana jawota dan Mubarak ya fito daga cikin motar amma Shalele cewa take yoni jaka ce? Yoni dutsi ce? A shigo har yankin mahaifia acini da yaki wallahi bazan yadda ba saima naji wanda ya bashi izinin shigowa yanki na.
Yana isowa wurin Shalele ta kwace daga jikin Asma”u takai masa harbi, rike kafarta yayi saida ya wurwurata sannan ya jefar da “ita a gefe daya, da sauri ta tashi tare dayo gudamuwa da dutse a hannunta saida ta saita daidai sai‘in idonsa dan tafijin haushin idon tana kokarin tsiyaye idon ya rike hannunta tare da murdewa ya faffalla mata, Mari Tagal tagal tayi baya Asma”u ta lallabeta kafon takai kasa, hararar Mubarak tayi daga inda take sannan tace dakiki mai fada da mace, kuma Allah ya isa ban yafe maka ba ta karasa maganar tana sakin kuka, Mubarak yace kin fasa ramawa ne? Ke ki kiyayeni na rantse da Allah duk ranar dana rikeki a hannuna wallahi sai kin tsinewa kanki dalilin da yasa kika sanni. Cikin kuka Shalele tace kaima idan na kamaka saika tsinewa kanka albarka dalilin da yasa kasan Shalele,juyawa tayi taci gaba da tafiya tana gunguni wanda babu wanda yasan abinda take cewa sai ita daya.
Asma”u ma bin bayanta tayn itama tana kuka dan taya aminiya Shalele kukan bakin ciki, gadai dama kuma ga damuwa, gata ga Abak bata ci ubansa ba kuma batayi masa kallan kaunar da tace zatayi masa ba idan ta gan shi koda kuwa shi yayi meta kallon banza zataji dadi ba
Tsayuwa yayi a wurin shi daya ransa sai tafasa yakeyi tambayar kansa ya farayi miya ma hana ya kashe banzar yarinyar can ya huta? Dan tunda yake duniya baiga wanda ya raina sa ba kamar Shalele tunda yake a duniya daga yarintarsa har girman sa babu hannun wanda ya taba hawa a saman jikinsa da sunan duka …….. waishi waccan jakar yarinyarta halba, jinjina kansa yayi tare da cewa wallahi aurenki ya zamar min dole da kanki zakici shinkafar bera ki kashe kanki idan dai Abak ne ya isheki riga da zani.
Dole waya yayi aka kawo masa wata motar, saida aka kawo masa sannan yaje gidan Babanshi suka gaisa yajuya dan komawa gidansa…
Shalele kuwa da gudu ta isa gida, babu ko sallama ta shiga, cikin kuka ta wuce dakinta
duk wata takarda data Iika mai dauke da zanen hoton Abak ta yageta tare da yayyagawa ta zubar a kasa ta tattaka,
Sai data gama sannan ta koma gefen gado ta zauna tare da dafe kanta ta fashe da wani irin sabon kuka mai kama zuciya, mai tada hankali, a haka Asma”u ta shiga ta sameta. Tana tausayawa Shalele sosai dan tasan har abadan duniya bata iya rabuwa da san Mubarak dan so a hankali yake shiga amma fitarsa karayar duniya ne idanma ba’ayi hankali ba ya tafi da lumfashi gaba daya.
Zama tayi a kusa da ita tana bata hakuri tare da nuna mata ai Mubarak baiji dadin abinda yayi mata ba, bayan ta tafi ma yana ta kiranta ya bata hakuri amma tayi tafiyarta, dan haka ya turota yace ta bawa Shalele hakuri.
Cikin kuka Shalele Itafa zuciya an halicce tada soyayyar mai kyautata mata ne. sannan babu abinda ta tsana irin mai bata damuwa, cutuka iri iri ne amma bana tunanin akwai mai zafi irin cutar so, kuka biyu yasa nayi a rayuwata bazan bari na ukku ya Cika ba, idan ba saina haramta masa shigowa kauyen nan ba niba Shalelen Babana bace. Hakuri Asma”u taci gaba da bata amma Shalele taki hakura, fita tayi ta barbaza mutane cewa duk wanda yaga Mubarak yana shigowa cikin kauyen nan yazo gidansu ya fada mata, haka tayi ta fadawa mutane saida ta gaji sannan ta dawo gida.
Kwance yake saman makeken gadonsa, kansa yana kallon sama, hannuwansa kuma ya tallabe keyarsa dasu, kafarsa daya saman daya, kallo daya zakayi masa kasan yana cikin fushi, abinda ya faru dashi da Shalele kawai ya tsaya masa a rai, wai kamarshi da girmansa da mutuncinsa kamar wannan yarinya zata harba? Bayan harbi kuma harda maganganu, wai kamarshi Mubarak Abak, ShaleIe tayi masa haka, fara tuno abinda tace masa yayi.
Kai dakikin wane yanki ne? Sakaran banza kidahumi k0 an fada maka ran mutum ran ragon layyane? Da zaka kasheshi anjima ka siyo wani?_
Da sauri ya rumtse idanuwansa tare da rike kansa sosai saida hawaye ya gangaro daga cikin idonsa a lokacin daya kallon harbin da Shalele tayi masa.
Da sauri Mubarak ya tashi zaune duk da sanyin A C dake dakinsa saida zufa ta sassafo daga jlkinsa, da sauri ya sake rumtse idonsa cikin bacin rai yace wallahi, …………………….. banji alkawarin daya daukarwa ransa ba.
Asakace Khadijata shigo cikin dakin tana kuka harta iso gaban gadon zata hau, Mubarak ya daka mata tsawa tare da cewa tashi ki fita ki bani wuri …………. ya karasa maganaryana nuna mata hanyar fita, Da sauri ta sauko kafarta data fara dorawa saman gadon Cikin tsoro ta kalli idon Mubarak fuskarsa babu wasa gaba daya hasken idosa ya goge zuwa launin ja, tsoro ya kama Khadija sosai dan tunda ta auri Abak bai taba mata haka ba, iyakar iskanci tana masa yana hadiyewa amma bai taba bata rai ba, yau kuma batayi masa ba amma yana mata ihu haka a saman kai me nayi masa,? .
Cikin fargaba ta fara tafiya, dan tasan Allah yayiwa Abak tausayin mace sosai a rayuwarsa, yace duk mai tadawa mace hankali baida tunani dan ita mace tana da rauni mace abar tattali ce amma yau da kansa yake daka mata tsawa! Me tayi masa da zafi haka? Addu”arta daya ma karya saketa wannan shine damuwana. Gaba daya zukanta abokan nan gabar biyu kowa wuta yakesha amma banda Mubarak, domin dai ita Shalele kullum a wahalce take rayuwa tsananin san Mubarak kullum kara tsananta yakeyi a cikin bargon ranta, kuma iyakar addu”a yi takeyi Allah ya babbake mata tambarin son Mubarak daga ranta amma kam wutar soyayyarsa kara huruwa takeyi a cikin ranta kamar tana cewa Allah ya kara mata san nasa. Amma duk da haka tana nan tana
jiran zuwansa kyauyensu dan tayi rantsuwa saita haramtawa Abak shigowa garinsu tunda bashi da hankali zata nuna masa ita, itace mahaukaci ga yarinta ga kuma danyen kai,
Shiru shru tanajilan zuwansa amma har anyi sati daya babu labarin Abak, dan yanzun ya daina shigowa garin saida daddare sosai ya shigo yayi“ abinda zaiyi ya fice, danshi yanzun yana tunanin ta inda zaiciwa Shalele mutumci ne, dan zuciyarsa da gangar jikinsa suna da ciwon bakin cikin abinda Shalele tayi masa kuma saiya fanshe abinda tayi masa,
Burin auretan a ransa akwai haka, yayi alkawari zai aureta ya mayar da ita “yar karamar bazawara saiya kacaccala mata rayuwa sannan ya bata saki 3 cikin wulakanci bayan wahalhalu azabartarwa tare kuma da dukan da zata rika sha a kowa ce safiya,
Kullum Idan ya zauna a gaban Babanshi yana so yayi maganar zai auri Shalele amma ya rasa ta ina zai fara. dan kullum yaje harya gama zamansa babanshi baida aiki sai maganar Mansur, ita kuwa Shalele cewa yakeyi ita yarinya ce dan yayi jikarjika da Shalele duk abinda zatayi baya ganin iskanci ne kullum Baba Bashir cewa yake ita yarinya ce,
Labari kuwa ya kawo kunnen Shalele cewa yanzun Abak da daddare yake shigowa kauyensu sannan baya zuwa sai bayan kwana biyu, wani lokaci ma har kwana ukku yanayi sannan yake shigowa. Shalele taji dadi sosai data samu wannan labari kuma zata fara tagawa ta gani. . Mai gida zaune a gaban bokansa kamar mai neman gafara yana kora masa sharhi akan lamarin diyarsa da kuma dan babban makiyinsa na duniya, bayan boka ya kece da dariya ya kalli Mai gida tare da cewa ka sawa ranka salama domin dai har yanzun shi Mubarak baya san Shalele, maganar aure kuwa ai tuni na fada maka babu aure tsakaninsu hara shafe duniyar nan.
Mai gida yace to ita fa tana sansa haryanzun? Bayan “yan al’adunsa da yayi ya kalli Mai gida tare da cewa gaskiya tana sansa har yanzun, Mai gida yace to ya zanyi na cire san da take masa ne? Nidai Allah ya sani bana san wannan soyayyara rayuwata kullum idan na tuno sai naji kamar na hadiye zuciya na sheke zuwa lahira, Boka yace karka damu zanyi wani aiki akai idan da rabo sai a dace. Godiya Mai gida yayi sannan ya tafi dan komawa gida.
lta kuwa Shalele tun bayan sallah isha’i tafita tacan gefen gari, wato ta hanyar da Mubarak yake shigowa, amma haryanzun shiru takeji babu dalilin mota bare ma tasa rai k0 shidin ne. Haka ta gaji da jira ta hakura ta koma gida.
Zama a wurin nan ya zamewa Shalele ibada duk daren duniya tana nan tanajiran shigowarsa amma kullum saidai ta gaji da zaman jira ta koma gida, wannan abu yana bala”in kona mata ranta, dan haka yaudai ta daskare k0 gari zai waye tana nan tana zaman jiransa saita gansa sannan zata koma gida.
Wurin misalin 10:37pm ya shigo clkin garin, tunda Shalele ta hango hasken mota ta fito
daga inda ta boye tazo ta raba tsakiyar hanya ta rike kugu ram tana jiran isowarsa.
Dogon haske yayo wanda tun kafin ya karaso ya gane wacece. dan gajeran murmushi yayi tare da ajiye wani kudiri a zuciyarsa, mugunta iri iri a zuciyarsa harya iso inda Shalele take tsaye da katon dutsinta a hannunta sai karajinjina sa takeyi. Tsayawa yayi ba tare daya fito daga cikin motar ba, ita kuma Shalele zagayawa tayi daidai inda yake zaune ta bude motar tare da cewa fito, babu gardama ya fito tare da rufe murfin motarsa,jingina yayijikin motartare da kurawa Shalele ido. Gyara tsayuwa tayi sannan tace a da na daina sanka amma yanzun kuma dai ina sanka, kaga wannan dutsin? Ta nuna masa tare da tambayarsa, ba tare daya bata amsa ba taci gaba da cewa, idan har kace baka so na haka zan kara farfashe maka gilashin mota kamar dai na kwanakin baya. Tambaya kana so na ko A ,a? Murmushi Mubarak yayi sannan yace waike ana soyayya da karfin tsiya ne? Ko an fada miki kowa yaro ne kamar ke? Kanki rawa yake har yanzu ina tunanin ma baki san miye so ba, dan gyaran murya Shalele tayi sannan tace to dan masanin sirrin so, ban sani ba amma tunda dai anyi sa’a kai kasan miye so ai sai kayi kokarin koyawa zuciyarka dan ina ganin a cikin mu din nan ita kadaice jakarzuciya da bata san abinda ake kira da so ba.
Zuciyata cejakar zuciya? Kwarai ma kuwa shima bakin dake sa’insa da mace ai ina ganin shima bai iya magana ba, dan idan har mutum ya fada maka kyakkyawa ko baka mayar masa da duka mai dadi ba yi kokari ka fada masa mai sanyi, idan har mutum ya fada maka mai zafi to yi kokarin sanyaya kalamanka dan saka farin ciki a cikin zuciyarsa. Ni duk bama wannan ba ni babu wani ruwana da jakar zuciya ko rashin iya kalami, kasan duk abinda kake so kana sansa baka bari, amma ni kawai yau saika fadamin cewa kana so na idan kuwa ba haka ba jikinka ya baka labari. Zuciyarsa ciwo take masa shidai haushin Shalele yakeji haka nan dai batayi masa ba, ga rashin kunya ga jahilci ga rainin hankali uwa uba kauyanci. Kallon rainin wayau yayi mata sannan yace ki bari zanyi shawara, matsowa tayi kusa dashi tana cewa wallahi babu wani shawara ni kawai ka fadamin. Ta karasa maganar cikin sakata. ‘
Mubarak yace to waijira? ldan ina sanki miye ne? Cikin sigar tausayi tace ka aureni don ……. All ….. ah. Mubarak yace shine kawai kike so? Shalele tace Ey ni ko baka sona ma kawai ka aureni,jinjina kai Mubarak yayi sannan yace to wai ke kinma san miye aure? Shalele tace babu damuwa tunda dai kai ka sani a hankali zaka ganardani, Hmmmm Mubarak yayi tare da cewa zan aureki haka yayi ko? Shalele tace Ey to amma yaushe? Mubarak yace yaushe kike sone? Shalele tace ita dai da sauri da sauri take so,
Mubarakyace to babu damuwa jeki, cikin farin ciki taja baya ya shiga motarsa harya tafi tana wurin tana daga masa hannun harsai daya bi hanyar da zata sadashi da gidansu ta daina hangoshi sannan ta juya zuciyarta cike da farin Clki ta nufi gidansu.
Tunda yayi parking ya kasa fitowa daga cikin motar tunani babu iyaka wanda yakeyi ya kulla wancan ya kwance wancan, daya zuciyarsa ta bashi cewa kawai ya yadda ya auri Shalele yayi amfani da damarsa ya azabtar da ita ya wulakanta ta saiya kaskantar da rayuwana wanda ita kanta saita kyamaci rayuwarta. ‘Dan gajeran tsaki yayi tare da fita daga cikin mota ya shiga ciki, bai wani dade ba ya fito dan komawa gida. Bayan wata daya, abubuwa da dama sun faru, maganar gaba da kiyayya kuwa tsakanin iyayensu kullum sai abinda yayi gaba, asiri kuwa boka yana aikinsa sosai ganin ya cire soyayyar Mubarak daga zuciyar Shalele amma a banza, ita kuwa Shalele yanzun ta gane cewa asiri shirka ne halaka ce dan haka ta tattara duk lamarurranta ta mikawa Allah. sallah bata wuce ta tsayuwar dare kullum dare har safiya ibada take tare da addu”ar Allah yasa Abak ya aureta, A bangaren Mubarak shidai bawai so zaisa ya auri Shalele ba, A, a, kawai yana so ta gane ruwa ba sa’ar kwando bane, dan haka yau ya daukarwa ransa k0 mahaifinsa zai tsine masa saiya fada masa kudirinsa akan Shalele,
Shirinsa yayi tsafya kama hanya dan zuwa wurin babansa, bayan yaje ya shiga cikin gidan da sallamarsa kamaryanda ya saba, kai tsaye dakin mahaifinsa ya nufa, yana zaune a saman kujera yajirge daya saman daya, a gabansa Mubarak ya gurfana sukayi irin zaman sarki da fadawansa.
Bayan gaisuwa Abak ya gyara zamansa, tare da kwantar da kansa gefe daya ya fara cewa, Baba don Allah kayi hakuri ka gafarceni wata alfarma daya nake nema a wurinka, cikin kulawa Baba Bashir yace inajinka dana, Saida ya sake kwantar da murya sosai sannan yace Baba na kasance ina cikin wata damuwa, ina cikin tashin hankali, inaji amma kunnuwa na basu da amfani, idanuwana a bude suke amma dani da makaho babu banbanci, ina ci ina sha amma abincin baya aiki a cikin jikina, hakika na fada tashin hankali da fargabar rayuwa, wanda idan harzanyi hukunci banga amfanin rayuwata ba kashe kaina kawai zanyi domin mutuwa itace rayuwar da tafi dacewa dani. Cikin damuwa Baba Bashir yace mene ne wannan? Wannan wane irin tashin hankaline ya tunkaromin jarumin dana? Ban taba ji ba kuma bana fatan naji da nasan haka da tuni nayi gaggawar rage rayuwata tun kafin wannan bakar ranartazo min, Mubarak fadamin abinda ya dameka ko zan samu sauki a cikin zuciyata, Cikin ladabi Mubarak yace Makiyanka, wato uba da “ya. hakika nina kasance ina san diyar ‘MAKIYINKA’ wann …………….
Da sauri Baba Bashir ya tashi tsaye tare da dagawa Abak hannu alamar ya dakata, jikinsa har rawa yakeyi saboda tsabar kwarewa da fitina.
Karya kakeyi, ka zama dan asara da nasan kai zan haifa a duniya dana kashe kaina tun kafun na auri uwarka ta haifo min kai har diyar makiyina tayi sha’awarka. nima ban yafewa kaina ba dana haifl abinda ya burgejinin ‘MAKIYI NA’ na baka mai amfani na gina maka rayuwarka a kyakkyawan turba najiyardakai farin ciki, tunda uwarka ta dauki cikinka nakejin dadin za’a haifo min magaji wanda zai gama min da makiyina ka shafemin tarihinsa a doron duniya ka mayar min da gidansa ‘MAKABARTA‘ na gatanta ka na baka ilimin addini dana zamani, na kashe dukiyiyana wurin ganin na gina maka Ingattaciyar tayuwa yau ka girma ka zama mutum nine zaka watsawa kasa a ido ka rasa wanda zaka so a duniya sai diyar makiyi na?
Hakika uwarka tayiwa kanta sassauci data mutu da yau sai nayi gunduwa gunduwa da ita a gabanka tsinanniya data haifa min kai, goge hawayen idon sa yayi sannan yaci gaba cewa tirrrrr ashe dama zaka juya min baya? Ashe duk kurarin da kakeyi na banza ne ka
rasa wanda zaka so a duniya Sai diyar maKlyl na!
Ashe duk kurarin da kakeyi na banza ne cewa zaka sakani farin Ciki ka kashe min makiyi na ashe kaima makiyi ne nake tare dashi ban sani ba? Ya karasa magana cikin fitina tare da sara wuka a kasa cikin masifa, sannan yaci gaba da cewa wallahi da dai naji kunya gara lahira tayi bako dan dana haifa a cikina kai yau kaine da kanka kake fadamin kana san jinin abibda nafi tsana a duniya, kai ina tattama ma kai dana ne? Dan duk duniya dan dana haifa kiyayyar makiyina a cikin jinin sa take ……………
Dan gajeran murmushi Mubarak yayi tare da sadda kansa kasa, jinjina kansa yayi tare da tunanin wannan wace irin maSIfaffiyar gaba ce? Wannan wane irin fitina ne haka? Ashe ko babu ranar da wannan zuminci zai gyaru? Miye ya hada wannan gaba wanda kowa burinsa yaga bayan dan uwansa Ciki daya kai Allah ya kyauta to. Ahankali Mubarak ya dago kansa ya kalli mahanfinsa hawaye na kwaranyowa daga cikin idonsa, lallal Shalele ta dibo ruwan dafa kanta, ita kuma imdan nata mahaifin yaya zasu kare da ita? Shi Mubarak kukan warwarewar zuminci yake yi amma shi Baba Bashiri a tunaninsa Mubarak yana kuka ne saboda san da yakeyi wa Shalele ne,
Mikewa yayi ba tare da yayiwa Baba Bashir magana ba ya fita daga dakin. duk kiran da yakewa Abak bai amsa ba kuma bai dawo ba, hankalin Baba Bashir kuwa idan yayi dubu ya tashi dan duk duniya idan akwai bakin ciki mai tada masa hankali shine fushin Mubarak, shi kuwa Mubarak bai darje k0 ina ba sai kofar gidansu Shalele. Dan yace gara ayi ta ta kare kawai. ’
Yanayin parking gidan ya shiga kai tsaye idan ta tafasa ma ta kone …….. . ……
Hmm