HARSASHEN SO CHAPTER 24

HARSASHEN SO
CHAPTER 24
Duk wanda ya kalli Shalele yasan tana tsundume a cikin danyen farin ciki, Mai gida kuwa ransa a hade kamar wanda aka fadawa sakon mutuwa, Duk mutum mai hankali yasan Mai gida yana cikin tashin hankali da damuwa a ransa, idan kace masa ya hidima Allah yasa alkairi, amsar da zai baka itace na gode. A kofar gida kuwa taron daurin aure ya taru sosai mutane ne daga wurare da dama wanda suka samu halattar wannan aure da aka kira masa rana. Baba bashir kuwa yana cikin farin ciki dajin dadi a ransa, duk inda Mai gida ya wuce idon Baba b, akansa, yasan bayasan auren nan yana cikin damuwa da tashin hankali wannan dalili yasa Baba bashir shiga farin ciki sosai wanda a zahiri zaka dauka saboda bikin yake murna, a ransa kuwa kwata kwata ba haka bane ba. 
Mubarak kuwa ya daure a cikin wata kafirarriyar shadda talkami hula agogo masu tsada da burgewa, wanda tsaya fada muku adadin kudinsu kauyancinci ne, yayi kyau matuka ya burge duk wanda kedajini ajikinsa, abu na masu kudi ai kuma kunsan amfaninsu kawai a cisu masu karatu ku hasko kyakkyawa ga hutu ga gayu uwa uba ga naira ga mulki, akwai aji ga iya daukar wanka, gashi dai a gefe yana bin iyayensa da kallo. Lokacin daurin aure ya cika ciff kamaryanda shi Baba b, ya rubuta a rubuce, gaba daya mutanen kyauyen nan sun halla suma dan ganewa idonsu wannan aure na “ya “yan abokan gaba guda biyu, 
Fara gabatar da daurin aure akayi kamar yanda kowa yasan anayi a musulince, gaba daya wurin yayi shiru tsitt kakeji kamar babu kowa a cikin garin, babban malamin da zai daura auren Mubarak da Shalele ne ya kalli Baba b, tare da cewa nawa ne aka saka a 
matsayin sadakin ne? Kafin yayi magana tuni Mai gida yayi tsigil yace, nine nan ni zan fada maka nawa za’a saka a matsayin sadakin “yata
Abinda na saka a matsayin sadakin auren “ya ta, ‘UMMU SULEIM’ shine, naira miliyan biyar da fili mai girman Eka dari biyu sai motar hawa kirar ‘KIA RIO’ wanda adadin kudinta sunkai kimanin naira miliyan shidda, 
Gaba daya wurin surutu ya fara tashi kowa mamaki ya kamashi, wannan wace irin rayuwa ce? Shi kuma dalilin Mai gida nayin haka saboda suce sun fasa auren ne, 
Kallon Mai gida Baba bashir yayi tare da cewa Mansur aurar da “yar ka zakayi ne ko kuma siyar da ita zakayi ne? Mai gida yace, sadakin dole ne yayi daidai da matsayin ahalin Mansur, Mai gida yaci gaba da cewa lallai wannan adadin shine za’a rubuta a matsayin sadaki ka gane? 
Baba bashir yace wane sadaki ne yake sama da kasancewar “yar ka zata kasance abokiyar rayuwa ga dan Bashir Abak? Mai gida yace kayi gaskiya Bashir tufkar rayuwar “yata nakeyiwa hanci saboda gobenta kuma ta cancanci hakan kaima kasani, dole ne ku bata cancantar da kuma matsayinta, 
Cikin damuwa Sulaiman yace malam Mansur ana kulla zumunci ne da igiyoyin soyayya, Mai gida yace imma zumuncin ya kullu koya wargaje wannan adadin bazan sauya ba. Ya karasa maganar cikin daga murya sannan yaci gaba da cewa idan kun amince da haka to, 
idan kuma ba haka ba to ku tattara ya naku ya naku ku kara gaba 
Mubarak dake kallonsu yayi kyakkyawan murmushi da gefen bakinsa, tare da bin mahaifinsa da ido danjin abinda zaici gaba da cewa kuma. 
Baba bashiryace Mansur walkiya zata iya walwalowa a sama sannan ta koma hadari zai iya juya akala, amma hukuncin Bashir Abak baya warwaruwa idan harkaga na tattara ya nawa yanawa na juya to lallai mun juya da “yarkane, domin farin cikin dana zan rubanya 
wannan adadin so miliyan a rubuta, 
Malamin yace na rubuta a rubuce cewa zaka bayar da naira miliyan biyar a matsayin sadaki sai kuma fili mai girman Eka dari biyu da motar hawa kirar kia no wanda adadin kudinta sunkai kimanin naira miliyan shidda? Baba Bashir yace shakka babu ka rubuta da biro mara gogewa ta yadda koda Mansur yazo gogewa bazai gogu ba, maza a daura auren yanzun yanzun nan. 
Jinjina kai Mubarak yayi tare da bin “yan uwan guda biyu wanda gaba dayansu suna da damuwa kowa yanajin kamar ya cakawa dan uwansa wuka, a zuciyarsu kuma babu wanda yasan abinda kowa yake sakawa Ana gama gabatar da daurin aure Baba bashir yace a shirya daukar amarya, idan hankalin Mai gida yayi dubu ya tashi, banda zufa babu abinda yake kwaranyowa daga cikin jikinsa, cikin tashin hankali ya nufi cikin gida. 
Fuskar Shalele dauke da farin ciki yau ta zama amarya kuma wanda take tsananin so shine ya kasance abokin rayuwa a gareta, cikin damuwa da kidiwa Mai gida yaje inda take yaja hannunta, yana kokarin hawa sama da ita, yaji maganar Baba Bashir yana cewa ina kuma zaka tafi da matar dana? Bana san makiyi yanayin shishigi a cikin zuri”ata sake mata hannu. Sakin hannun Shalele Mai gida yayi hawaye na digowa daga cikin idonsa, Baba bashir yaci gaba da cewa bana bukatar “yan kai amarya haka kuma bana bukatar duk wani abu daya fito daga cikin gidan makiyina,juyawa yayi ya kalli wata tare da kiran sunan Sulaiman, cikin girmamawa Sulaiman yazo gaban Baba bashir tare da mika masa wata leda dake hannunsa. 
Ansar ledar Baba bashir yayi tare da yafito matar da hannunsa wadda itama tana cikin tawagarsa, ledar hannunsa ya bata tare da cewa ki bawa Amarya ta saka kayan nan, a kaita tayi bankwana da Mama sannan ki kawota a nan gabana. Zuwa tayi taja hannun Shalele saida ta fara kaita wurin Mama, Mama tana zaune a saman kujera Shalele tana durkushe a gabanta kanta na kallon kasa hawaye na digowa 
daga cikin idonta, tayi shiru ta kasa cewa komai, Cikin sanyi Mama tace Ummu Suleim ina miki murna da kasancewarki mata ga dan uwanki, ina tayaki murna tare da addu”a Allah ya baku zaman lafiya da zuri”a masu albarka, ki kasance mai hakuri da kauda kai ga duk wani abu wanda bai shafeki ba, karki tafi da dabi”un mahifinki domin ba dabi”un kirki bane, gaba tsakaninki
Dasu ta kare yayan mahaifinki ne dukansu nice na haifesu Mubarak dan uwanki ne yayanki ne, yanda kikeyi ma mahaifinki biyayya to shima Bashir kici gaba da masa biyayya tashi kije Allah ya bada hakurin zama. Matar ta kamo Shalele tare da kaita dakinta, dakin Shalelen, ta canja kaya wanda Baba bashirya bada a bata ta saka,Mai gida yanaji yana gani aka tafi da “yarsa wanda Baba Bashir ya hana abarsu suyi bankwana, a mota aka dauki Shalele dan kaita gidan Baba 
bashir. Gidan yayi shiru babu kowa a cikinsa daga Mai gida sai Asma’u sai Mama sai kuma zugar “yan dabansa, gaba daya Mai gida yaji gidan yayi masa dan tsukakke, a ransa kuwa tunanin da baisan abin cewa ba yakeyi, a gefen zuciyarsa kuwa tunanin “yanda auren Shalele da Mubarak zai kasance yakeyi haryanzun yana zaune a kan hujjar boka wannan aure baya yuwuwa, 
Shalele zaune a tsakiyar gado sai raba idanuwa takeyi kamar tsohuwar barauniya, babu kowa a cikin dakin sai ita kadai, a hankali ta yaye lullubin dake saman kanta ta fara bin dakin da aka ajiyeta a ciki da kallo. 
Ba laifi dai dakin yayi amma ba wani can sosai ba, ita kuwa bata dakin takeyi ba ta hanyar da Mubarak zai bullo kawai takejira ta gani. Murmushi tayi tare da gyara zamanta ta kara gyara lullubi kada ango yazo ya sameta a hargitse. “ Shiru shiru har aka kira magrib babu labarin ango, isha’i Shalele ta zuba ido taga ango babu shi babu labarinsa, bata wani damu ba tana tunani ko yana fama da jama”a ne, dan haka ta sauko dan fitowa tayi alwallah tunda babu wanda yace ta fito tayi sallah, kuma babu toilet a cikin dakin komai dai a wulakance, 
Cikin natsuwa ta fito tsakar gidan, Baba Bashir shima da tashi zugar “yan tashar sun zagayeshi, ita bata san hanyar toilet ba kuma bata san ta ina zata bi ta wuce ba, bude mata ido “yan daban sukayi dan haka ta kasa magana ta juya ta koma cikin dakinta. 
Tsaye tayi saboda fitsari ya daure mata mara sosai ta rasa ina zata saka kanta, gaba daya tsoro ya kamata hankalinta ya tashi, dan haka ta sake fitowa tsakar gidan, tana dan matse jikinta na irin dai wanda wani abu yake damunsa, Kallo Baba bashir ya bita dashi mai nuni daki shiga taitayinki, cikin rawar murya tace Baba sallah zanyi, daka mata tsawa yayi tare da cewa makiyi baya gicce gicce a gabana idan kika sake fitowa a wurin nan saina karya miki wuya maza koma kije kiyi bacci ……… ya karasa maganar cikin hargowa, da sauri Shalele ta juya ta koma cikin daki. 
Ta cikin labule take lekensa, magana yakeyi amma bata iya jiyo abinda yake cewa, tadai ga duk yaransa daya bayan daya sun tafi daga wurin, kila suma cewa yayi suje su kwanta, Shi kadai ya rage a tsakar gida, a ransa kuwa bakin cikin tafiyar Mubarak yakeyi, amma yanajiran dawowarsa dan ya daukarwa ransa duk ranar daya kwana daki daya da Shalele yasan dole sai wani abu ya shiga tsakaninsu lallai washe garin ranar saiya sa Mubarak ya warware igiyoyin auren Shalele kaf da suka rataya akansa, 
Kudi Mansur ya nema lallai za‘a rubanya masa so adadin abinda aka rubuta, zaiga idan har kudi yana sayen mutunci diya da martabarta, lallai sai Mubarak ya keta mutunci Shalele, wani sabon bakin ciki ya taso masa da wata irin sabuwar kiyayya dan ya tuna a wurin daurin aure, waishi za‘a sakawa sadakin dansa haka saboda a wulakanta sa a tozartashi a bainar idon jama’a, Mikewa yayi cikin bacin rai ya nufi dakinsa, yana shiga Shalele ta fito da saurinta cikin gigicewa tana neman toilet iyakar nemanta bata gani ba, daga dan baya ta zagaya tayi fitsarinta tayo alwalla ta koma dakinta cikin sauri ba tare da Allah yasa wani ya ganta ba. 
Mubarak zaune a saman kujera kallo daya zakayi masa ka gane nazarin duniya yakeyi, girgiza kansa yayi cikin damuwa lallai bai kyautawa Shalele ba, ba’a rayuwar duniya haka, ita rayuwa duk mai sanka yafi karfin ka wulakanta sa tozarci da cin zarafi wannan wulakanci ne yayi mata kuma hakan bai kamata ba, Ajiyar zuciya ya sauke tare da daga idonsa a hankali ya kalli agogo, tunda yake a rayuwa bai taba samun labarin amaryar da aka kawo ba a ranar aurenta ango yayi tafiyarsaba sai shi, a bayyane yace Allah ya baki hakuri. 
Mikewa yayi ya nufi dakinsa, saboda shi daya ne, Khadija ta kulkula yaji tayi tafiyarta gidansu wai idan haryana san zama da ita saida ya saki Shalele ya fada mata yanda yasa sadaki ya aurota haka ya saka ya auro Shalele, yanda yake santa haka yake san Shalele, wannan dalilin yasa tayi yaji ta tafi gidansu. Shi kam Mubarak yace sauka lafiya danshi bazai wani je biko ba dan da ba’a aure itama da baza’a auro ta ba. Dan rage kayan jikinsa ya farayi bayan ya shiga dakinsa, hankalinsa da tunaninsa damuwa sosai yakeji rashin Shalele a kusa dashi da tana tare dashi yau daya fada mata yana santa, tausayinta yaji har a ransa ta bashi tausayi. A bayyane yace insha Allah zan 
zame miki gata saina saka farin Ciki a zuciyarki Allah ya bani ikon kyautata miki “yar uwata. 
Saida ya watsa ruwa sannan ya kwanta dan hutawa, bai dade da kwanciya ba dan bacci ya figeshi wayarsa kuwa sai kuka takeyi. A hankali ya mika hannunsa ya jawota, dakel ya bude idonsa dan yaga mai kiransa, dan gajeran murmushi yayi ganin Khadija ce sannan ya kashe wayar baki daya dan a gajiye yake. Fiki fiki take sai ciccira idanuwa takeyi ta wayi gari a sabon wuri, zaune take saman abun sallah ta zabga takugumi tana tunanin gidansu, Allah sarki Mai gida da Mama, suna can ko ya sukeji na rashinta a kusa dasu? Ko Mama zata zo ganina? Dan taga yanda na tashi? Maganar Baba Bashirtaji yana cewa ina yarinyar nan ne? Da sauri ta tashi ta fita tana cewa gani, har kasa ta durkusa sannan tace barka da kwana irin gaisuwar da take ma Mai gida, Amsawa yayi tare da mika mata waya yace Mubarak zaiyi magana dake, hannu biyu tasa ta ansa shi kuma ya juya ita kuma ta koma cikin dakinta, a gafen gado ta zauna tare da kara 
wayar a kunnenta cikin ladabi tace Yaya ina kwana. 
Cikin gajiyayyar murya yace lafiya qalau ya kike? Lafiya lau, shiru na wani lokaci ya ratsa danshi dama haka yakeyin wayarsa ko a magana idan kayi masa magana yana dan daukar lokaci Kafin ya baka amsa ba. Komai dai nasa na natsuwa yakeyi, Sorry jiya na tafl kiyi hakuri, saida tayi murmushi sannan tace to babu komai yaushe zaka zo to? Zanzo insha Allah, Shalele tace to ka fadaman mana, saida yayi nazari sannan yace yaushe kike so inzo to? Shalele tace ko yaushe, Mubarak yace to zanzo kinji ko, ki kwantar da hankali ki rika cin abinci sosai zanzo in taho dake wurina ai zaki zauna k0? Shalele tace Ey mana, Mubarak yace to yayi sai nazo insha Allah. Shalele tace Allah ya yadda sannan ta kashe wayar. Mikewa tayi ta fita dan mayar wa Baba Bashir wayarsa, katon palonshi ta shiga da sallama Baba Bashir yana zaune a saman kujera kafarsa daya a saman daya. dakel ya ansa sallamar kamar zaici fushi a gabanshi ta durkusa dan duk haka takeyi wa Mai gida, cikin ladabi ta mika masa wayar, yace ajiye nan. A gefensa ta ajiye wayar ta tashi ta fita Baba Bashir yabi bayanta da harara. 
Tana fita ya dauki wayarsa, audio ya shiga danjin abinda Mubarak yacewa Shalele, dubawa yayi sannan ya kunna ya saurari firarsu, kwafa yayi tare da cewa kazo ka tafi da 
itan ina nan inajiranka. ‘ 
A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, satin Shalele biyu a gidan Baba Bashir babu wanda yazo daga gidansu kuma dai tana zaman lafiya, babu abinda ta nema ta rasa hankalinta kwance ba abinda yake damuwanta. Amma shi kuma Baba Bashir yana nan yana jiran zuwan Mubarak dan yayi alkawali sai ya dandanawa Mansur bakin ciki a zuciyarsa, za’a bata kudin ta tafi dasu zatayi lalatacciyar 
rayuwa dan Mubarak zai gama da ita ne. A bangaren Mubarak kuwa yana cikin damuwa neman hanyar da zai dauko Shalele kawai yake nema amma ya kasa dan yayi karya cewa baya kasa shi burinsa kawai ya dauko Shalele sai ya tafi da ita amma abun ya gagara. Ganin bai samu mafita ba yasa ya kira Sulaiman, Sulaiman yace kada ya damu insha Allah duk ranar da Baba bashir baya nan zai fitar masa da Shalele daga gidan. Godiya Mubarak yayi tare da cewa yana saurarensa, 
Shi kuwa Sulaiman yasa ido sosai akan duk wata shiga da fitar Baba Bashir yana so kawai ya samu tazara ya fadawa Mubarak, Bayan Kwana biyu Sulaiman ya kira Mubarak a waya cewa yau cikin daren nan ya shigo Baba Bashir zai fita da daddare, Mubarak ya tambayesa ina zaije ne? Sulaiman yace wallahi bai sani ba amma dai yaji yana cewa zai fita, Mubarak yace zaibar gari ne? Sulaiman yace A, a, yana dai cikin kauyen, Mubarak yace to babu damuwa zaizo insha Allah. Cikin farin ciki Mubarak ya fara shirin tafia, a gaggauce yayi wanka yana fitowa ya dan fara shirinsa, sudai dama gayu bawai wani shafe shafe sukeyi ba tunda su komai nasu ya tafi yanda suke so, kana nan kaya ya saka tare da tultula turare, kamshin turaren mai daukar hankali da narkar da zuciyar duk wanda yaji kamshin.
Wayarsa kadai ya dauka ya fita.
Hmm mai zai faru muje zuwa 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE