HARSASHEN SO CHAPTER 26

HARSASHEN SO
CHAPTER 26
Banda ajiyar zuciya babu abinda Shalele takeyi, tunani ta farayi a zuciyarta. So da yawa kakanso abu ya zamar maka babbar matsala a rayuwarka, hakika idan dai har haka ne har abadan duniya babu abinda zai 
mayar da ita gidan Mubarak, 
Tunani iri iri dauke a zuciyarta harsuka isa, Mai gida bai wani ji dar ba haka kuma baiji tashin hankali ko damuwa ba, domin tun kafin zuwan Shalele 
Baba bashir ya aiko da takardar sakin Shalele. 
Bayan Mai nasara ya ajiyeta yayi tafiyarsa gidan Baba bashir aiki ne aka 
saka sa kuma yayi ya wuce wurin. 
Shalele kuwa cikin rashin damuwa ta wuce dakinta, tayi kwanciyarta a saman gadonta bata dade da shiga ba Mama ta shigo, jajen abinda ya faru 
tayi mata tare da addu”ar Allah ya canja mata alkairi a rayuwarta. 
Mubarak kuwa tattara dan abunda zai bukata yayi yabar gidan, saboda tafiya zaiyi shine dalilinsa na dawo da Shalele wurinsa su tafi tare, to hakan data 
faru baisa ya fasa ba ya tattara ya nasa yana sa ya bace abunsa daga nigeria. 
Baba Bashir kuwa ya jira yaji ko Mai gida ko Mama wani zaice wani abu amma shiru, dan hausawa sunce idan kare yana haushi bai samu an tayasa 
ba shima shiru yakeyi, “ 
Duk ranar nan Mubarak da tunanin Shalele ya rayu a zuciyarsa, abinda ya faru a darenjiya tsakaninsu ya tattare ya kafe masa kokan zuciya. Duk lokacin daya tuno babban network inda suka hau shida Shalele a daren jiya 
saiya runtse idanuwansa da sauri. A daren yau kuwa kwata kwata bacci yayi masa wuya daga cikin 
idanuwansa, ya rasa abinyi haka kuma ya rasa mafita. 
Wayarsa ya dauka ya kira kakansu domin Mubarak kadai yake da halaka dashi shima dakel ya ganosa ba tare da sanin iyayensa ba, sai kuma Shalele data gansa so daya a rayuwarta wanda bata san ko waye ba kuma tun daga 
ranar ta manta da Iabarinsa. 
Duk abinda ya faru ya fada masa, aurensa da Shalele komai da komai bai boye ba ya fada masa, jinjina kai yayi bayan ya gama saurare sannan yacewa 
Mubarak idan ya dawo ya sanar dashi domin shima kansa  baisan inda shike ba dashi da Mai gida. 
Haka dai kwanaki sukaci gaba da tafiya, abubuwa sun faru sosai a ciki harda gama iddar Shalele kamar yanda suke lissafi a cewar an saketa danshi Mubarak bai wani san da zancen saki ba, Baba Bashirya rubuta ya bada, 
Har yanzun Mubarak bai dawo ba, amma ita Khadija ta bishi inda ya tafi, kuma da taje bai wani dago maganar tayi yaji ba kawai basar wa yayi aka 
dora rayuwar aure daga inda aka tsaya. 
Ita kuwa Shalele tana zamanta a gidansu cikin kwanciyar hankali, tana tunanin Mubarak amma ba wani can da yawa ba shidai yafita tunaninta sosai, ita kuma yanzun zuciyarta ta rabu biyu da nazari dan Mai gida yace 
aure zatayi da dan babban amininsa wato Alhaji Abas. 
Yau gidansu Shalele ya dauki kamshi yaji gyara ta ko ina, ran Mai gida 
kuwa fes yana cikin farin ciki jin dadi da annashuwa, Faysal zaizo zawarci. ltama Shalele tasha gayu ta daurayu sosai duk da “yar kauyece bata da 
irin wannan kauyanci sannan kuma tana da “yar gogewarta daidai burgewa. 
Asma”u kuwa babu wanda ya kaitajin dadi da farin ciki Shalele zata zama “yar gidansu. Shalele kuwa gayenta banda kamshi babu abinda ke fita daga jikinta. 
Jin tsayuwar mota yasa Asma”u fitowa da gudun tsiya dan ko ba’a fada ba 
tasan Yaya Faysal ne, cikin farin ciki ta taresa tare da masa sannu da zuwa. 
‘Dan murmushi yayi tare da wucewa zuwa ciki bai bata amsa ba, Mai gida da kansa yakewa Faysal sannu da zuwa tare da masa jagora har zuwa cikin babban palonsa. 
Bayan gaisuwa mai gida yasa aka gabatar da abin tabawa  sannan suka bashi wuri dan yadanyi wa cikinsa chargy, 
Bayan ya kammala ne Mai gida ya gatarwa da Shalele Faysal da kansa ya rakata har palonsa yana cikin farin ciki, itama dai Shalelen tanayi amma dai 
ba wani can sosai ba, kusan rabin zancen da Mai gida akayi sa. Mai gida sai azarbabe yakeyi yana ta wuce gona da iri, sannan yacewa Faysal tunda dai yaga Shalele kuma tayi masa itama Shalele Faysal yayi mata dan haka kawai su daura aure a cikin satin nan babu wani abinda za’a nema a rasa. A takaice dai Faysal kwanansa 2 sannan ya koma, daya tashi tafiya kuwa ya wanke kowa na gidan nan da kudin masu sa ciwon tunani dan shima yana da 
rufin asirinsa amma Mubarak yayi masa zarra iyakar zarra. 
Alhaji Abas kuwa yayi farin ciki sosai aminci yakai aminci tunda har ga auratayya zata shiga tsakanin “ya “yansu. 
Komai dai yayi musu zamzam a bangarori guda biyu, dan haka sunka 
tsayar da auren Shalele sati biyu masu zuwa, 
Hidimar biki akeyi sosai Mai gida shiri yakeyi yanda ya kamata, labarin 
auren Shalele kuwa ya fallasa a cikin kauyensu, duk mai dalilin sani ya sani, 
Baba Bashir kuwa ya tashi hankali danjin Shalele zatayi aure wato saboda iskanci shi za‘ayiwa aure da auren dansa? Dole ya hakura saboda baya da mafita. 
Biki ya rage saura kwana 2 dan haka shi Faysal ya dawo nan gidansu Shalele 
anata hidimar arziki yanda ya kamata. Sai an daura aure su tafi da amarya. 
Baba Bashir ganin abun na gaskiya ne, yasa shi ya kira Mubarak da kansa ya sanar masa cewa Shalele zatayi aure danshi Baba Bashir bai fadawa 
Mubarak cewa yayi saki ba. 
Hankalin Mubarak idan yayi dubu ya tashi, suna gama waya da Baba Bashirya kira Kaka ya sanar dashi duk iskanci dake faruwa. Sannan kuma ya kara da cewa duk abinda akeyi lallai gobe zai shigo. Fatan alkairi Kaka yayi 
masa tare da masa addu”ar Allah yasa yazo lafiya. 
Tun a daren Mubarak ya fara shirye shiryen tahowa, ita kuwa Khadija tace 
bata tashi tafiya ba kawai yaje zata taho daga baya. 
A gidan Mai gida kuwa kowa yana cikin farin ciki, itama Mama haka 
Asma”u kuwa tafi kowa zakewa, uwa uba Mai gida. 
Kudi sosai Mai gida ya kashe wurin ganin ya fitar da Shalele kunya, duk abinda akeyiwa diyar gata babu abinda Mai gida baiyiwa Shalele ba. ‘ 
An gurza IV an raba birni da karkara, amma Mai gida bai aika da IV a gidan Baba bashir ba wannan abu kuwa ya kara hayakashi matuka, bala”i da masifa kadai ne yake kwalkwalar zuciyarsa. 
Mubarak kuwa a filin jirgin kano ya sauka. wanda tun kafin saukarsa ya sanar dasu Mai nasara su samesa a can, Mubarak yana sauka bai tsaya wani bata lokaci ba suka shiga motoci suka kama hanyar katsina, 
Haka sukayi ta wuta a hanya har suka isa katsina lafiya lumi, a katsina suka kwana dukansu a tankamemen gidan Kakansu, gari na waye wa kuwa suka kamo hanyar zuwa Abuja, da Mubarak da Kaka da wannan matar da suka zauna daki daya da Shalele a gidan yari …… Taron . Daurin aure ya taru sosai a kofar gidan Mai gida, duk fuskar wanda 
ka kalla yana cikin farin ciki, mutane daga wurare da dama sun hallara, 
Shalele tana cikin farin ciki sosai itama cikin jin dadi da kwanciyar hankali 
take komai nata, haka Mama itama tanajin dadinta. 
Mubarak kuwa suna shigowa kauyensu kai tsaye gidan Baba Bashir su ka wuce, iyakar tashin hankali hankalinsa ya tashi ganin mahaifinsa tare da 
binsa da kallo sannan kuma ya mayar da kallonsa wurin Mubarak. Cikin damuwa ya mayar da dubansa wurin mahaifinsa yana kokarin yin magana Kaka ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannun. Kallon Mubarak 
yayi tare da cewa ku wuce muje gidan Mansur din. 
Haka suka rantafo sukayo gidan Mai gida tashin hankali shima ba”a magana a idanuwansa, Kaka bai tsaya waje ba ya shiga ciki, dole tasa Mai 
gida yabar wurin daurin aure tare da tashi da sauri yabi bayan mahaifinsa. 
Itama Mama kanta ta shiga tashin hankali sosai ganin mijinta data tattara ta barosa ba tare daya warware igiyoyin aurensa akanta ba, Shalele kuwa ko inda Mubarak yake bata kalla ba kuma ta ganshi tasansa amma saita basarta 
manta da lamarin sa, 
Kallon Kaka tayi sosai tare da shiga nazarin ina ta taba ganin wannan hutaccen tsoho? Lallai ta ganesa kuma ta tuna a ina ta sansa, bin “yar tsohuwar tayi da kallo sosai itama ta ganeta amma abin tambaya meya kawosu nan su dukansu? 
Kaka baiyi magana da kowa ba a cikinsu sai da Mubarak yayi yace Mubarak bani wurin zama, Mubarak ne yayi masa jagora har zuwa babban palon Mai gida. ‘ Tsakanin Mai gida da Baba Bashir kuwa dukansu kamar zuciyoyinsa zasu fito waje saboda tsantsagwaron tashin hankali da kuma shiga tashin hankali sunajira suji abinda Kaka zai fada. 
A kofargida kuwa “yan taron daurin aure sunka fara magana, dan kowa yanajira a daura dan duk wanda yake wurin ya kagara a daura ya kama gabansa. Cike da izza Kaka ya fara magana dukan “ya “yan sa suna gurfane a 
gabansu tattare da dumbin nadama a cikin zukantasa, Mubarak shima yana gefe Shalele kuwa tana durkushe kusa da Mai gida, amma ita Mama bata 
shigo cikin palon ba sannan kuma batayiwa Kaka ko sannu da zuwa ba. Kaka yace Mansur mutanen daka tara waje me zaka basu ne? Kai tsaye yace zan basu auren Ummu Suleim ne, Kaka yace dama ana aure a cikin aure ne? Mai gida yace hakika baba matsawar aure ya warware tsakanin ma”aurata guda biyu. Miye dalilinka na fadar hakan ne? Mai gida yace dalili yana wurinta, itace aka saka sannan kuma itace ta sake zabar mijin da takeso ta sake zama dashi a matsayin abokin rayuwa a gareta karo na biyu. 
Kallon Shalele Kaka yayi sannan yace ke kece Shalelen? ltama ba tare data kallesa ba tace Eh, jinjina kai Kaka yayi cikin natsuwa tare da karewa Shalele kallo dan shima yadan tuno ya taba ganinta a rayuwarsa amma ya rasa a ina. Saida ya gama nazari sosai sannan yace tunda kike a rayuwarki kin taba ganin mace ta auri miji biyu? Shalele tace sosai ma kuwa mace tana auren namiji fiye da biyu ma a rayuwarta, wannan dalilin nema yasa Allah yayi duniya da girma idan kaji matsi anan saika kara gaba ko za’a dace. 
‘Dan takaitaccen murmushi Kaka yayi tare da bin Shalele da kallo har zuwa wani lokaci, kallon Mai gida yayi sannan yace hausawa sunce idan har ka rabu da mutum ka tambayesa yayi arziki karka tanbayesa ya sake hali, bakin 
halinka yana nan kafiyarka da rashi da’a naka. ‘ 
Shiru Mai gida yayi baice komai ba, fada Kaka ya farayi tare da tambayar ba’asin da yasa za”a daurawa Shalele aure yau, komai mai gida ya fada 
karara babu munafirci. 
Nan dai hayaniya ta fara tashi domin Baba bashir yace shi karya ake masa komai ma baisan anyi ba, Mai gida yace karya ne, Baba bashiryace ni zan maka karya ne? Dan, ya daddana zagi, hayaniya sosai kamar za‘a biga,juna Kaka yace su saurara, bayan kowa yayi shiru ne Kaka yace wa Mubarak ya dauki matarsa su tafi, Mai gida yace idan ba Shalele ta gama auren Mubarak ba dan kanbabban bura’uba yake. Dan duk duniya idan akwai abinda ya tsana a rayuwarsa wallahi bai wuce 
wannan dakikin yaron ba da kuma ubansa, kallon Mubarak Kaka yayi tare da cewa dauki matarka ku tafi, Shalele tace maimaita aji aisai dakiki, tuni na rufe littafin Mubarak.Kallonta Mubarak yayi amma baiyi magana ba, yadai kafeta da kyawawan idanuwansa masu tattare da burgewa da kuma daukar hankalin duk wanda aka kalla dasu. Jin shirun tayi yawa yasa Alhaji Abas shigowa dan yaji lafiya, yana lakafe a bakin kofa yaji anan wannan cakarniya, dan haka bai tsaya komai ba ko shawara da wani dan ransa ya baci gani yakeyi kamar da sanin Mai gida cewa Shalele tana da aure yace dansa yazo ya auri Shalele, ko Asma”u bai bari ba a 
gida ya tattara nasa da nashi yayi gaba cikin dauka  zafi. 
Murmushi Kaka yayi sannan yasa aka kira Mama, bayan tazo itama ta samu wuri ta zauna, itama wannan matar da suka zauna gidan yari da Shalele tana wurin, Baba Bashir Mai gida Mubarak da kuma Shalele, Kaka yace ku saurara 
kuji abinda baku sani ba, kai Mubarak ke Umma Suleim daku nake. Kunsan abinda ya faru shekaru da dama da suka wuce? Ku saurara kuji 
sannan ku fada min waye bashi da gaskiya a cikin iyayenku? ………… Mai gida ya kalli Baba bashir cikin sauri, shima Baba bashir Mai gida yake kallo, Mubarak kuwa tasowa yayi ya dawo kusa da Shalele, da sauri ta tashi daga wurin ta koma kusa da Mama, gaba daya palon yayi shiru bakajin motsin komai sai shu …… dinnan mai ziyarta kunnuwa idan shiru ‘yayi yawa, 
gyaran Murya Kaka yayi sannan ya fara bayani kamar haka. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE