HARSASHEN SO CHAPTER 3
HARSASHEN SO
CHAPTER 3
Mai gida yabi bayan shalale da kallo yana mai jin farin ciki, ji yakeyi kamar ya jawo gaba ta dawo yanzun, dariya mai gida yayi sosai harda daga kafa sama sannan yace Allah ya maido ruwa cikin kwari “yan gari su gane kuren su! Murmushin karfin hali mama tayi sannan ta kalli mansur tace Allah yayi ma kwarya makama abar rungumarta, kallon mama mai gida yayi yace me kike nufi da haka kuma?
Shiru mama tayi ba tare da tace komai ba, tashi tayi tabar wurin, wata irin flrgitacciyar dariya mansur yayi sannan ya kalli balaga yace kaji wata magana wai Allah yayi ma kwarya maka abar rungumarta, Ina fada maka mama fa tana bayan dan iskan nan, cikin girmamawa balaga yace mai gida kabar komai a hannu na, a yau cikin saflyar nan ka bukaci kan Basir saina ciro maka shi! Cikin nuna nau”in azabobi yake nunawa cewa idan na datso kan dan iska tun a can zan fara kwallo da kansa harsai nazo kofar gidan nan, cikin tsumi yace ka yarda? Mikewa mai gida yayi tare da dafa kafadar balaga yace barmin komai a hannun Shalele ganin bayan Bashir wulakanta tattalin arzikinsa halakar da yaransa da yake takama dasu kaca kaca da danshi daya daya haifa wannan duk aikin Shalele ne, Shalele zai gama dasu dukansu sannan Bashir yazo ya dafa kasan kafafuwana kuka zaiyi dan neman tuba ya roka alfarma a daina karan batta haka nan, ni kuma in taka masa kansa da kafafuwana in mummurza in diddirza in tattaka sannan nahau saman doki na kashe dan iska kamar yanda ya kashe min dana guda daya da nake so nake kauna a duniya, Ya karasa maganar hawaye yana zirarowa daga cikin kwarin idonsa, da karfl ya fada cewa na tsanake duk duniya bani da babban makiyi wanda na tsana yanda nake san ganin mutuwarka bana kaunar ganin mutuwar mazinata haka nan, Wani irin tari mai gida ya farayi tare da dafe daidai saitin zuciyarsa dan ya tuno abunda ya dade bai tuno ba, amma saboda masifa fada yakeyi yana cewa ko an zaro raina yazo daidai makoshi saina fara zare ran Bashir sannan zan mutu!
Shalele dake tsaye daga saman bene yana hango mahaifinsa yaji wata irin faduwar gaba tare da sake tariyo maganganu mai gida, a hankali yayi magana a bayyane cewa wato kisan kai shine ya hada tsohuwar gaba kenan? Tambayarda yayi ma kansa wanda ya rasa mai bashi ansa,kenan dan haka juyawa yayi ya koma ciki, balaga da sauran makarraban mai gida suka kamashi dan zuwa sama,
Koda suka zo daidai saitin hoton Bashir saida mai gida ya harbeshi sosai har saida hoton ya tsage, sannan su balaga suka jashi cikin girmamawa suna bashi hakuri har dakinsa, Magani suka bawa mai gida yasha, sannan suka kwantar dashi, har sun juya zasu fita mai gida yayi magana suka dawo, nuni yayi musu da wani jibgegen littafi, daukowa sukayi suka mikashi wa mai gida yayi dan rubutu saman littafin sannan suka mayar dashi a inda yake suka fita daga dakin, Shalele tsaye a dan nesa da mama ba tare daya kalleta ba yace, mama na rokeki daki bude min wannan dunkulallaliyar gabar naji yanda take? Kullum labari yana shan banban kuma kullum da sabuwar maganar da take fitowa miye gaskiyar lamari? Kallonsa mama tayi sannan tace babu ruwana kaje ka tambayi mahaifinka, cike da bacin rai shalele ya juya ya nufi dakin mai gida,
A dan nesa dashi ya tsaya sosai sannan yadan sadda kansa kadan alamar girmamawa, jinjina kai mai gida yayi alamar ya anshi gaisuwar, cikin “yar karamar murya irinta mata yace mai gida tambaya zanyi, Da hannu mai gida ya nuna masa alamarya bashi dama, godiya shalele yayi sannan yace mai gida wai meye gaskiyar abinda ya hada gabarku ya cusa kiyayyar juna a cikin zukantanku kaida Bashir? Kallon zanci ubanka mai gida yayiwa shalale tare da mikewa tsaye cike da masifa yayo kan shalele, wata irin shakara yayiwa shalele sannan ya kuma masa kai da bango ya dagoshi ya kara gwara masa saidai ya tabbatar kwakwalwar sa tadauki zafi sannan yace me kace? Cikin jarumta yayi dan gajeren murmushi yana mai kallon cikin idanuwan mahaifinsa, cikin ladabi ya hada hannayensa biyu tare da cewa Allah ya baka hakuri, Cikin fada mai gida yace daga yau idan ka sakemin maganar mai kama da sunan makiyina saina kasheka, danni a gidan nan ko sunan Bishiya ba’a fada saboda tsanar da nayi ma babban makiyi na, idan kuwa ba haka ba kaima zaka shiga cikin jaddawalin matacce na fada maka, Godiya nakeyi mai gida zan kiyaye insha Allah, yana fadin haka ya fita daga dakin zuciyarsa banda kuna babu abinda takeyi, tafiya yakeyi baya ko ganin gabansa, dan tunda yazo duniya baisan so ba cikin kiyayya yazo duniya a cikin ta ya rayu kuma a ita ya ginu babu so kuma babu tausayi ko tausayawa a cikin zuciyarsa, danshi shalele ya dauki kansa wani sakaho mara zuciya, maganar mai gida ta kara dawo masa a cikin kwanyarsa,
Shalele zai gama dasu dukansu sannan Bashir yazo ya dafa kasan kafafuwana kuka zaiyi dan neman tuba ya roka alfarma a daina karan batta haka nan, ni kuma in taka masa kansa da kafafuwana in mummurza in diddirza in tattaka sanan nahau saman doki na kashe dan iska kamar yanda ya kashe min dana guda daya da nake so nake kauna a duniya,_Ajiyar zuciya shalele yayi a bayyane yace idan har haka zai saka farin ciki a zuciyar mai gida sai Bashir ya kwanta a kasan kafarsa, sai mai gida yahau doki yayi sukuwa saman ganganr jikin Bashir insha Allah! ‘ Dan gajeran tsaki yayi a daidai lokacin daya iso bakin kofar dakinsa, yana shiga ya kulle kofar da makulli sannan ya cire dukan kayanjikinsa dan sun masa nauyi sosai, Gashin kansa ya nade yayi gammo dashi, kallon kyawawan idanuwansa yayi a cikin madubi tare dakai hannunsa saitin dan ziririn hancinsa ya shafawa, ajiyar zuciya yayi tare da cewa idan Allah yaki addu”ar bire sai ya mutu a gonar arne, Zuwan Bashir a kafafuwan mai gida bashine farin ciki ba, mutuwar dansa kadai shafe labarin sa a duniyar masu lumfashi shine kadai abinda zaisa Bashir mutuwar tsaye, ma”ana zai mutu babu idanuwa yawan kuka zaisa idanuwansa su makance wannan shine hukunci mai sauki, amma waye dan nasa?
Mai viseline ya dan lakuta ya shafawa lallausar lebonsa dan lasar lebonsa yayi na kasa tare dayin kallo mai dauke da darissa da dama, mu zuba ………. Ya fada tare da kankance dukan idanuwansa,
Wata irin haddiyar motar ce kirar ‘_Rolls Royce: wanda kudinta zasu kai darajar kimanin naira miliyan dari da ishirin, sojoji ne a gaban motar Hilux ukku sannan motar sai kuma wasu Hilux din a baya wato sun saka wannan motar a tsaki dan ba motar kariya da kuma wanda aka dauko a cikin motar, suma Hilux din dauke suke da sojoji da mobayil masu tada hankali duk bindigogin hannunsu an daura musu jan kyalle wanda wannan alamace ta an basu damar halbi, ‘ A barke suke tafiya cike da izza tare da nunawa duniya su sune nigeria, motar ko mashin kuwa idan ya gansu da gudu yake saukewa gefen titi dan tsira tare da kaucewa rayukansu fadawa cikin musiba, kana ganinsu kasan gwamnati ce da kanta take tafiya saman kwalta,Bakajin karar komai sai kukan tayoyin motocin da suke kartar kwaltar, tafiya sukeyi har barin wuta sukeyi saboda mulki, kallo daya zakayi musu sai gabanka ya fadi, idan kuma mai karyayyan zuciyane zaice Allah kayi mana arziki ka bamu duniya da lahira, amma ai imani zaice ubangiji ka bamu arziki na halal mai albarka da amfani! Gudu suke falfalawa na fitar hankalin mai kallo har suka isa inda zasu tsaya, wani irin banbareran gida sukayi ma tsinke wanda tunda akaji wannan kukan na motar hukuma aka yaye musu get din gidan, Da gudu motocin suka rika shiga, tun kafin motocin su tsaya wasu sojoji suka fara dirowa da dan gudu gudunsu suka nufi wurin motar dauke da wani kafet red mai kyaun gaske, daidai inda motar tayi parking suka shimflda kafet din sannan suka fara kokarin bude
motar, A hankali ya fara ziro kafarsa daya, kallo daya zakayi ma kafar ka gane mai kafar hutu ya gama kama masajiki, kafar har wani hurhurun kyau takeyi yatsun kafarsa ma kansu abin kallo ne, saboda bawai takalman gayu bane a kafarsa mu a wurinmu ba haka zamu kallesu ba amma ga wanda yasan takalmi yasan takalmi ne mai tsadar gaske a kafarsa kuma ba rufaffe bane Cike da izza ya fito daga cikin motar duk sojan dake wurin saida ya kame kam sunan wata waka, suka sara dan bashi girma, k0 inda suke bai kalla ba ya wuce ta saman kafet din ya ke tafiya,
Kai Allah yayi halitta dan gayu ne ajin farko kisan boko, wayayye ne na layin farko, yana da kyau mai burgewa yana da aji mai jan hankalin duk wata mace mai jini ajikinta, idanuwanshi sun bude lallausar gashin kansa ya saddo ya gangaro gefen kunnensa wanda ake kira da saje,
Tafiyarsa ma kanta abun burgewa ce, kallo daya zaka masa kasan dan dizgine baya daukar sakarci yana da wulakanci sosai idanuwansa idan ya tsareka dasu sai kayi zufa saboda tsoro, uhumm ‘MUBARAK BASHIR ABAK’ kenan da daya tal a wurin bashir babban makiyin mai gida ………. ,
Wani irin tari mai gida yakeyi wanda yayi sanadiyar fitowar duk wani mai numfashi dake cikin gidan nan, shalele ne a gaba cikin damararsa wanda dai ya saba a kullum, A sikwane ya gurfana a gaban mai gida ya durkusa saman guyawunsa tare da tallafo kan mai gida cikin kuka yace me gida miye? A hankali mai gida ya karkato kansa ya kalli shalele hannunsa ya riko cikin nasa sannan yace shalele dokina, cike da damuwa shalele yace wane dokin? Nayin wanjo mai gida ya fada, shalele yasan irin kaunar dake tsakanin dokin
nan da mahaifinsa, gogewa mai gida hawayen idonsa yayi sannan yace meya sameshi ne? Saida mai gida ya gwara kansa kasa sosai sannan yace magauta, magauta sun kashemin dokina, da sauri shalele ya runtse idanuwansa tare da kauda kansa gefe daya yana mai jin kuna sosai a ransa, dan yanda mai gida yake kaunar dokin nan bai san rayuwarsa haka, a ran shalele yace biyu kenan, daya banji ba, ban gani ba, amma wannan anyi ina da rayuwa kuma ina numfashi bana barin bashi, Da sauri ya saki mai gida ya mike tsaye, cikin damuwa sosai ya nufi wani lafiyayen doki ya daka tsalle ya haye, babu ko wuka a hannunsa bare ma a saka ran ya dauki wani abu wanda zai bawa kansa kariya, ‘ Mai gida dake kwance cikin wahala yace shalele cikin murya irinta wanda yake cikin damuwa da tashin hankali, karkaje kai daya ka tsaya karka tafI akwai baki a gidansa azzaliman gwamnati sunzo bindigu ne sosai a hannunsu, karka tafl ……….. kar kaje inaji a jikina wani masifa zai tunkaro mu jiki zayajigata zuciyoyi zasuyi dokon wahala karkaje, saboda duk wanda aka taba nasa bazai yadda ba ….. ,,,, shalele a daidai lokacin da mai gida ya mike cikin karfin hali da jarumta, Lalibar hanya mai gida ya farayi dan duhu sosai ya bayyana a garin bakajin kukan komai sai cidar hadari dake tashi mai kidima duk wanda yaji ta, sai an dauki wani lokaci mai tsawo zaka ga walkiya ta haska tartar irin dai walkiyar nan mai sa tashin hankali, cikin kuka mai tada hankali mai gida yace shalele ………. , Cikin tashin hankali su balaga suka kamashi dan maidashi ciki, amma kokarin kwacewa yakeyi, su kuma abinda yasa basu bi shalele ba sun san namijin duniya ne, ba bindugu bane hannunsu ko wuta ce suka rike shalele zaiji dasu, Shalele kuwa gudu yakeyi sosai a saman doki zuciyarsa kamar zata fashe saboda bakin ciki,ji yakeyi yana iya tamke Bashir da duk wanda yayi makwabtaka dashi, saidai ya fada wannan rami ya fita ya fada kwari ya flce dokin sai murgudewa yakeyi saboda tafiya ba ta hankali akeyi dashi ba,
A gidan Bashir kuwa tunda yaransa suka fada cewa an kashe dokin da mai gida yafi kauna a duniya suka shirya cikin kayan fada dan Bashir ya dauki alkawari yau ko waye yazo saiya cire masa kansa, ana cikin wannan shirin ne Mubarak ya iso danyi ma mahaifinsa bankwana zaiyi tafiya zuwa london, Ya samu ana wannan magana, shima ransa idan yayi dubu ya baci dan duk duniya bai hada babanshi da kowa ba, kuma shi baima cika shigowa wurin nan ba sai anyi sa”a saboda mahaifinsa baya so, amma yau yana ganin Mubarak ya fara fada masa damuwarsa cikin tashin hankali, ran Mubarak kuwa ya baci sosai amma saiya bawa mahaifinsa hakuri, shi kuma yace masa yayi sauri yabar garin nan kafinma mutane su ankara da zuwanshi dan dan Mansur yana neman hotonsa dan ya kasheshi, ‘
Kyakyawan murmushi mubarak yayi sannan yace Mubarak ba ganin yaro bane kwantar da hankalinka Babana, a daidai lokacin da sukaji haniniyar doki a kofar gida, maganar shalele sukaji yana cewa kibiyar ajali sulke baya tsareta sai ta wuce sa, ranar tsafi bunsuru ke kudi tunda idan tururu ta tashi lalacewa sai tayi gash’l, yau dakai da duk wani wanda yake cikin gidan nan sunanku gawa, Bashiryace kaji dan iskan yaron can yazo dan firit dashi sai masifa, murmushi Mubarak yayi da gefen bakinsa sannan yace Baba, ya karasa maganar yana mai ‘tabe bakinsa, don Allah ka daina wannan rayuwar ka futa harkar kazaman mutanen nan don Allah ni banga ma amfanin zaman garin nan ba,
Bashir yace wallahi ban taf‘lya ko ina harsai na tafi da mahaifiyata tunda bashi daya ta haifa ba kiri kiri ansan gaskiya amma ake boyewa, cikin sanyi Mubarak yace to kayi hakuri zanyi maganin abun, wani laflyayyen soja ya kalla sannan yace dauko min yaron, Bashir yace karka daukoshi barshi ni kadai na ishi dan iska, Mubarak yace Baba barshi dani, sake kallon sojan yayi sannan yace idan ka daukoshi kulleminshi mu tafl dashi zan koya masa hankali, ……….
Hmm