HARSASHEN SO CHAPTER 31
HARSASHEN SO
CHAPTER 31
Shiga yayi ya ajiye wayoyinsa, rage kayan jikinsa yayi ya shiga toilet dan watsa ruwa,
lta kuwa Shalele wuri ta samu tayi zamanta, Kamal ta kira domin ya tara mata tulin miss calls bata dauka wayar ba.
Tana nan palo zaune tana waya da Kamal, bayani tayi masa akan Mubarak ta fada masa mijinta ne, amma tayiwa Babanta alkawari bazata kara zama da Mubarak ba yau kuma rabon ayi suka hadu ya taho da ita.
Kamal yace tou nidai Allah ya kyauta, idan Momy ta kira ya zance mata ne? Shalele tace
ai zan dawo, kuma tunda bata nan ai bata san bana nan ba.
Kamal yace tou yayi sai Allah ya kaimu, Shalele tace nagode saida safe, Kamal yace yau babu labari Shalele, murmushi tayi tare da kashe wayarta bata bashi amsa ba.
Gyara zamanta tayi saman kujera ta jingina bayanta da hannun kujerar ta dora kafafuwanta sama, ta harde ta zubawa kofar dakin da Mubarak ya shiga ido,
Mubarak kuwa yana fitowa wanka yaga babu Shalele a daki da sauri ya fito dan a tunaninsa ta shigo, zaune ya ganta ta zuramai zara zaran idanuwanta kamar hauka sabon kamu haka take kallonsa.
Saida yayi gajeren tsaki sannan yace waike miyasa kike da taurin kai ne wai Eye?
Cikin tsiwa Shalele tace kazo ka mayar dani inda ka dauko ni, ta karasa maganar tana murguda baki.
Allah ya sawake, haka Mubarak ya fada tare da komawa daki yayi kwanciyarsa, saboda bacci da gajiya yakeji sosai baida lokacin da zai tsaya wani surutu ko mayar da magana. Yana komawa ciki kwanciyarsa yayi. Bai dade da kwanciya ba bacci mai dadi yayi gaba dashi domin duk wayoyinsa ya kashe su dan ya samu wadatacce bacci. Shalele kuwa jin Mubarak shiru bai sake fitowa ba yasa taji bacin rai, don ita a tunaninta zai tsaya ne yayi ta rarrashinta amma sai taji sabanin haka.
A zuciye ta kwanta saman kujerar ta takure tana gunguni, mita tayi, tayi har bacci ya dauketa.
Da asuba kuwa koda ya tashi don tafiya masallaci bai tashi Shalele ba, kukan motarsa ne ya farkar da ita shima zai tafi masallaci, abinda yasa kuwa ya fita a mota tsakanin gidansa da masallaci da akwai nisa shi yasa bai tafi a kafa ba ya tafi a mota.
Yana tafiya ta tashi ta shiga dakin da taga Mubarak ya shiga jiya da daddare, alwallah tayi domin gabatar da sallah asuba.
Tanayin sallah ta fito ta dawo mazauninta najiya, tana nan zaune har Mubarak ya dawo daga masallaci, ko inda take bai kalla ba ya wuce ciki,
Komawa tayi ta kwanta dan kara bacci, bata dade da kwanciya ba Mubarak ya fito ya fice,
Da sauri Shalele ta tashi tabi bayansa da sauri, yana kokarin rufe mota ta rike murfin da sauri tace ina zakaje ne? Kallonta yayi sannan yace tafiya ……… Shalele tace zakaje ina
kenan? Kauda kansa yayi tare da cewa zanje neman abinci ne. Shalele tace babu abinci ne a gidan? ‘Dan tabe bakinsa yayi sannan yace aike za‘a tambaya, ga fara ki gani mutane suna jirana.
Shalele tace wallahi bazan gafara ba, kallonta yayi sosai amma baiyi magana ba, Shalele tace tou kace wani abu mana,
Murmushi yayi tare da cewa zakije ne? Shalele tace bazan je ba, amma don Allah ka mayar dani inda ka daukoni,
Mubarak yace to shikenan naji zan mayardake koma bara in dawo yanzun in Allah ya yadda bazan dade ba.
Kallonsa Shalele tayi sosai sannan tace kayi alkawari? Jinjina kai Mubarak yayi tare da saukewa Shalele gajiyayyen kallo sannan yace nayi alkawari ya karasa maganaryana murmushi.
Sakin murfin motar tayi tare da cewa Allah yasa ka dawo laf’lya, amin Mubarak ya fada tare da rufe motar ya fara tafiya, tana tsaye a wurin harya bace daga inda take iya hangosa.
Cikin damuwa ta koma ciki, tana shiga wayarta fara ringing, Mai gida ne yake kiranta, cike da zumudi ta dauka tare da zama saman kujera.
Mai gida barka da safiya, ta fada tana maiyin murmushi kamar tana gabansa, laflya qalau Shalele ya kike? Lafiya qalau, Mai gida yace insha Allah ina nan zuwa gobewa gobe zanzo na ganki, ‘
Shalele tace Allah ya yadda yasa kazo lafiya, Mai gida ya ansa da amin, ina Kamal? Ya tambayeta, Shalele tace yanzun nan ya fita bada dadewa ba,
Mai gida yace a gaishe shi idan ya dawo, Shalele tace zaiji, “yar fira sukayi daga baya kuwa sukayi sallama kowa ya ajiye wayarsa.
lta kadai ta yini a gida, abinci kuma kawo mata akayi daga kalacin safe har na rana, tana nan jigum tana jiran tsammani, amma har akayi isha”i babu labarin Mubarak. Idan hankalin Shalele yayi dubu da guda guda ya tashi kuma gashi bata da number Mubarak ta shiga damuwa sosai, abincin dare ma da aka kawo mata ko kallonsa batayi ba saboda fargaba.
Zagaye zagaye tayi tayi bata palo bata dakin bacci, har 12:30am Mubarak bai dawo ba,
kuka Shalele ta farayi da fargabar yanda gobenta zata kasance mata idan Mai gida yazo basu hadu ba.
Mubarak kuwa yana cikin garin jos abubuwa ne sukai masa yawa, amma hankalinsa yana wurin Shalele shima baiyi tunanin zaikai yanzun bai koma gida ba.
Tana nan zaune tana kuka har bacci ya dauketa dan da bacci yayi shawara da ita hakika da bazai ziyarci idanuwanta ba a wannan daren ba, Shi kuwa Mubarak sai 02:07am ya shigo gida, da sauri ya shiga ciki yayi wanka, sannan ya fito palo, kusa da Shalele yaje ya zaune ya kura mata idanuwa yana kallon kyakyawar fuskarta.
Bacci takeyi cikin natsuwa da kwanciyar hankali amma lokaci lokaci tanayin shashshekar kuka,
‘Daukarta Mubarak yayi gaba dayanta ya rabota daga saman kujerar. A hankali ta bude idonta tana mai sauke ajiyar zuciya,
Swry haka Mubarak ya fada a lokacin da Shalele ta saka idanuwanta a nasa. Cikin kuka tace shine kayi tafiyarka ko? Mubarak yace yi hakuri ba gani na dawo ba, ya karasa maganar yana murmushi a daidai lokacin da suka isa daki, saman gado ya kwantar da ita.
Kallonsa Shalele tayi sosai sannan tace ka dade da dawowa ne? Yace Ey mana yana kokarin cire jallabiyar jikinsa, Shalele tace wanka kayi yanzu? Umm ya fada a takaice, Shalele tace nima sai nayi, tou kawai ya fada a daidai lokacin da yake hawa saman gado.
Sauka tayi daga saman gadon da sauri itama ta nufi toilet, ta dan dade sosai sannan ta fito, a can gefe tayi tsaye tana goge jikinta, saida ta gama goge jikinta Mubarak ya nuna mata lader daya shigo dashi yana cewa akwai kaya a ciki ki duba zaki samu na bacci.
Matsawa tayi ‘ta bude, dubawa tayi ta dauki riga da wando masu laushi ta saka, sannan ta haye saman gado kusa da Mubarak danyin bacci. ‘
Barge Mubarak yaja tare da cewa yawwa mu huta gajiya. Murmushi Shalele tayi tare da kara kwanciya sosai a kusa dashi.
Sha’anin miji da mata sai Allah, abin duk da zai faru a daren nan ya riga da ya gama faruwa, komai dai ya faru a cikin wannan daren, domin dai su dukansu babu wanda yayi bacci har aka fara kiraye kirayen sallah asuba,
Mubarak ya fara shiga toilet dan tsarkake kansa, bayan ya fito ya zurajallabi, makullin motarsa ya dauka ya nufi masallaci,
Itama wanka tayi tazo tayi sallah asuba,, a inda ta gama sallah anan tayi kwanciyarta.
Shima yana dawowa daga masallaci dauke Shalele yayi daga kasa ya mayar da ita saman gado, ya lullubesu sukaci gaba da bacci,
Wurin 10:49am wayar Shalele ta fara ihu, amma bata farka ba, Mubarak ne ya farka tare da dauko wayar daga inda Shalele ta ajiye shi, dubawa yayi dan ganin mai kiranta.
“MAI GIDA‘ wannan shine sunan da Mubarakya gani, kuma ya gane cewa Baba Mansur ne, dan haka ya dauki wayartare da karawa a kunnensa amma baiyi magana ba.
Mai gida yace Shalele, Mubarak yayi shiru, Mai gida yace hello, Mubarak ya sakeyin shiru, Mai gida yace wai bakyaji na ne? Da sauri Mubarak ya fara tashin Shalele tare da saka wayar a h»free, ya nuna mata Baba ne bayan ta tashi.
Cikin muryar bacci Shalele tace Mai gida ya hanya? Alhamdulillah nifa inajos tun jiya kin fada miki nayi, naso kawai saidai ki ganni amma na kasa gane gidan, wallahi na manta
sunan anguwar ma.
Shalele tace kana ta ina ne yanzu? Mai gida ya fada mata inda yake, Shalele tace tou ina zuwa, Mai gida yace kinsan wurin ne? Tace Ey zamuzo da Mub ……. dade mata baki Mubarak yayi tare da kashe wayar. Yace meye haka? Sauran kuma azo ayita tashin hankali nan ma? Shalele tace aje ayi wallahi tare dakai zamuje, a daidai lokacin da wayar Mai gida ta sake shigowa. ‘Dauka Shalele tayi tare da cewa Mai gida ka jira a wurin zamu zo dani da Mubarakyanz ………
Kashe wayarsa Mai gida yayi cikin bacin rai, Shalele kiran wayar tayi amma sai Mai gida yayi rejected tare da kashe wayar duka gaba dayanta, Mubarak yace kinga irin abinda nake fada miki k0? Sauka Shalele tayi daga saman gadon da sauri ba tare da ta bawa Mubarak
amsa ba. Ganin tana saka kaya yasashi sauka daga saman gadon yana cewa ina zakije ne? Shalele tace zanje wurin Mai gida, Mubarak yace bara mu tafi tare, yana fadin haka ya nufi toilet, wanka ya farayi kuma dalilinsa nayin haka dan ya bata lokaci yasan lokacin da zasuje k0 kurar Mai gida bazasu gani ba.
Koda ya fitoma, shiririta yayi tayi, Shalele tana azalzalarsa amma sai yace wai idan ana masa magana yana shiri rudewa yakeyi, zama tayi tanajiransa ya gama amma sai dawo da aiki baya yakeyi.
Azuciye ta mike tsaye tare da cewa da Allah ka barshi ai da Babanka ne baza ka masa haka ba, tana fadin haka tayi waje da saurinta,
Tsaki yayi tare da saka kayansa ya fito da sauri, a lokacin Shalele harta fita daga gidan
Tuni tayi nisa sosai sai tafiya takeyi kamar zata tashi sama, gabanta Mubarak yasha da mota tare da fitowa yana cewa haba Shalele miye haka? Bata kalleshi ba taci gaba da tafiya.
Rikota yayi tare da cewa bakijin ina magana ne? Fizge hannunta tayi taci gaba da tafia bizim bizim, cikin bacin rai Mubarak ya sake fizgota, da hargowa yace idan ina miki magana kina tafiya ranki zai baci. Tsayuwa tayi ba tare data kallesa ba, zoki shiga mota mu tafi, tsaki tayi ta wucesa taje ta shiga cikin motartana gunguni,
Shima shiga yayi yaja suka tafi suna tafiya tana kara kiran wayar Mai gida amma bata shiga, har suka isa inda Mai gida ya fada yana nan basu sameshi ba.
Shalele bataji dadi ba, sosai hankalinta ya tashi amma sai Mubarak yace ta manta dashi, cikin daren nan suma zasu bar gari, kuka Shalele tasha sosai kamar idonta zai fita.
Sosai Mubarak yake rarrashin Shalele amma ko saurarensa sai kuka takeyi, idan hankalinsa yayi dubu ya tashi, sai hakuri yake bawa Shalele amma sam taki ta sauraresa kuka takeyi tana karawa,
Har suka dawo gida Shalele kuka takeyi tuni kanta ya fara ciwo saboda kuka, dakel Mubarak ya lallaba Shalele tayi bacci,
Palo ya dawo ya zauna sai kallon agogo yakeyi dan shima su Mai nasara yakejira suzo, suma SU WUCE,
Jigun din ya isheshi dan kukan da Shalele tayi yasa duk yaji babu dadi, dan haka ya kira Mai nasara dan yaji lafiya har yanzun basu iso ba.
Hakuri Mai nasara ya bawa Mubarak tare da fada masa suna zuwa nan da 30minutes insha Allah.
Tashi yayi bayan ya gama wayar yaje yayi wanka, saida ya fito sannan ya tashi Shalele dan itama tayi wanka, da kuka ta tashi saboda ta kwanta tanayin sa,
Cikin kuka ta nufi toilet har tayo wanka ta futo kuka takeyi, a lokacin harsu Mai nasara sun iso, mai da powder ta shafa sai kwalli bata shafa wani jan baki ba kawai tadan murzawa lips inta viseline, kayanta ta saka ta koma gefen gado ta kwanta sai bacci,
Su Mai nasara suna da yawa sosai, su da yawa suka zo, abinci aka kawo musu, Mubarak
yace suci suyi sallah yana da meeting kafin su gama ya dawo insha Allah. Tafiya yayi su kuma sukaci gaba da hidimarsu.
Mai gida kuwa salati yayi ya sanar da ubangijinsa, taya akayi kuma Shalele ta sake haduwa da Mubarak? Wannan wace irinjarabace da masifa ne haka? Jikinsa a sanyaye ya shiga motarsa yaja, tare da addu”ar ubangiji ya tarwatsa wannan lamari,
Shidai kam Allah ya sani har a ransa bawai Mubarak ne baya so ba, shidai kawai aurensa da Shalele ne ya tsana a rayuwarsa, kuma hargobe yana addu”a Allah ya rabasu rabuwa mai muni wanda kada wanda ya kara sha’awar zama da wani a cikinsu har abadan duniya.
Mubarak kuwa saida ya gama abinda yakeyi ya dawo, a lokacin su Mai nasara sun gama
duk abinda sukeyi suna zuwanjiran Abak. Yana dawowa ciki ya shigo dan tashin Shalele, bayan ta tashi ya tambayeta tayi sallah?
Tace A, a, yace maza kiyi tafiya zamuyi,
Alwallah tayo tazo tayi sallah, shi kuma dan abinda yasan yazo dasu ya tattara amma banda kayan sakawa.
Bayan ya gama tattara komai ya koma palo yana jiran fitowar Shalini. Ita kuma tana gama sallah tayi addu’a ta fice daga dakin.
Tunda Mubarak ya hango ta taho ya mike yayi hanyar fita, domin duk kowa ya fita shi kadai ya rage yana jiran fitowarta ne shima su fece.
Bayansa tabi suka fita, gaba dayansu suka fada mota suka ibi hanya dan dawowa gida. Babu abinda suka tsaya yi kuma basu tsayawa wasa ba har suka iso gida lafiya.
Sabon gida suka sauka, wanda Mubarakya kashe miliyoyin kudi wurin gina sa, gida ne
na gani na fada sahu daya a lissafin manyan gidajen da suka amsa sunan su a cikin duniya,
lyakar haduwa gida ya hadu, kuma an bishi an baza ama”aikata sosai maza da mata, katon gidane sosai wanda zai iya hadiye kimanin duban nan mutane, bayan girma kuma an
tsara sa an kuma kawatar dashi daidai da zamani.
Bayan motocin sun gama parking Mubarak ya fita Shalele tana biye bayansa cikin natsuwa har suka isa ciki,
Nan fa kallo ya koma sama a wurin Shalele tayi ta raba idanuwa kamar tayiwa mai gari sata, samun wuri tayi ta zauna cike da kauyancin tana kallon irin kudaden da aka kashe wurin ganin an gina gida mai daukar hankali haka.
Hawaye taji ya gangaro mata daga cikin kwarin idanuwanta, me mutane suka dauki duniya? Wannan gida haka da’aka tsara aka ginasa kamar baza’a mutu ba? lta dai addu”a tayi ubangiji yasa mu cika da imani Allah ya bamu kyakyawan masauki yasa mu dace da
aljannar firdausi dan albarka annabin rahma, ameen.
lta dai a ranar duk a tsorace tayi bacci banda ma ta yadda da Mubarak zuciyarta tayi amanna dashi wallahi da bazata yadda ta zauna a gidan nan ba.
Tana kwance a jikinsa tana bacci cikin fargaba da tsoro dan zuciyarta tana ta sake sake tou itama zuciyarta sai rawa takeyi ta kasa tsayawa wuri daya.
03:02am Mubarak ya farka danyin sallah, a hankali ya sauke Shalele daga samanjikinsa yaje yayi alwallah ya fara ibadarsa, saida yayi sallahn asuba sannan yayi wanka ya shirya.
Tashin Shalele yayi dan tayi sallah itama, saida ta fito daga toilet Mubarak yace mata toni
zan tafi, cikin ko Oho tace Allah ya tsare, Mubarak yace amin, ita dai bata tambayesa ina zaije ba kuma shima bai fada mata ba.
Wayarta ya dauka ya saka mata numbersa sannan ya kirata wayarsa, wayarta ta shiga
cikin wayarsa yaga numberta, yayi save abinda ya rubuta shine, Shalini. lta kuma a wayarta ya rubuta mata Mubarak.
Kudi masu yawa ya ajiye mata danyin hidimar gida, sannan ya sakeyi mata bankwana, rumgumeta yayi sosai a jikinsa yace bance kije ko ina ba kinji? Tace tom, Mubarak yace duk abinda kikeso ga number na nan a wayarki ki fadamin kinji ko? Tace tom, shiru na wani lokaci sannan Mubarak yace ‘INA SAN KI’ ‘
Ina sanki da yawa da yawa…. ..kuma ko Baba Mansur yayi miki waya karki fada masa inda kike kinji na fada miki k0? Jinjina kai tayi cikin gamsuwa, saketa yayi daga jikinsa tare da daga mata hannu ya fice daga dakin.
Caf abinda Shalele ta fada kenan bayan fitar Mubarak, azumi sattin din da tayi alkawari tsakaninta ubangijinta cewa duk ranar da Abak ya fada cewa yana santa dazatayi. Tou yau ya fada cewa yana santa kuma lallai idan tana numfashi gobene zata fara azumin da yaddar ubangiji.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, Shalele tanayin azuminta kamar yadda tayi alkawari amma ita kam ta kasa ganewa jikinta, kullum dai a wahalce take yini ga wani masifar kwadayi wanda ta dangantashi da yunwar azumi ce,
Harta kare azuminta Mubarak bai dawo ba, amma sunayin waya kowa yanajin kaunar kowa a cikin babban birnin zuciyarsa.
Kuma lokaci lokaci yana hadasu suyi waya da Khadija, tun Khadija tana yin waya a ciccije harta hakura ta saki ranta koba Mubarak takan kira Shalele da wayarta suyi fira.
Watan Mubarak biyarcas amma har yanxun bai dawo ba, suna waya da Shalele ta fada masa cewa bata da lafiya, Mubarak yace meya sameta ne? Tace ita dai cikinta yana mata wani iri kuma ta kasa gane ko miye.
lta dai bata taba ganin mace mai ciki ba, sannan kuma bata san yanda ake gane mai ciki ba, bata da Mama sannan kuma bata da wasu kawaye wanda zasu rika irin wannan labarai dasu.
Wannan dalili yasa ta fadawa Mubarak cikinta yana mata wani iri, shidai bai kawo
komai ba a ransa dan haka yace zata samu sauki.
Bayan lokacin da sukayi waya da Mubarak da sati biyu ya dawo dashi da Khadija uwar gida sarautar mata, a lokacin cikin Shalele wata biyar da satika,
Iyakartashin hankali Mubarak ya shiga damuwa ganin Shalele da ciki, kai amma wannan yarinya ta raina masa hankali, dan ubanta tasan tana da ciki shine bata fada masa ba, idan ya zauna da mace mai ciki Allah ya tsine masa albarka.
Aishi dan kwanan da yayi da ita so daya tal ajos baiyi tunanin zatayi iki ciki ba, amma shine taje tayi kwance ta tsotsi ciki,
Bacin rai sosai Mubarak ya nunawa Shalele, kuma idan tayi masa magana baya amsawa, kuma ma cikinta yayi wani rundumeme wallahi dan yasan bazai zubu ba wallahi dasai yakaita an fitar dashi.
Ita kuwa Khadija fitina takeyi sosai ta hana gidan zaman lafiya kwata kwata, gaba daya ta birkicewa Mubarak ya rasa ta ina zai baibayota, ita kukanta Mubarak ya zalince ta kullum
idan zai kwanta da ita saiya cuceta yayi amfani da maganin hana daukar ciki. Amma da yake Shalele “yar uwarsa ce ita ya yadda tayi ciki.
Bata san Shalele tana fuskantar fushin Mubarak ba, har Shalele ta yanke shawar guduwa daga gidansa, wata zuciyar tace idan kin gudu kije ina? Shalele bata da mafita dole ta hakura ta zauna amma batajin dadin zaman kwata kwata.
Shi kuwa Mubarak tattara yanashi ya nashi yayi tafiyarsa dashi da Khadija, kuma naira daya bai bawa Shalele ba, kai Shalele tana shan wuta sosai.
Da wahala ta ishi Shalele ta kirawo Mai gida kuma tayi sa”a ya dauka, ta fada masa halin da take ciki, sosai ya tausayawa Shalele kuma baiji dadin abinda Mubarak yayiwa “yar saba, don haka Mai gida ya kirawo Mama ya fada mata halin da ake ciki, itama taji abun wani bakon al‘amari wai Mubarak baya san aihuwa dan yace idan dai Shalele tana san zama dashi wallahi saidai taje a markade cikin jikinta idan kuma ba haka ba shi babu wani ruwansa da lamarinta,
Mama da kanta ta fadawa Baba Bashir iskancin da Mubarak yakeyi, ya kirasa yayi masa magana amma sai yace shifa kada a wani dameshi rayuwarsa ba rayuwar wani bane, tunda yace baisan a haihu bafa ya zama da macen da tayi ciki kuma baya zama da macen da ta taba
Haihuwa,
Mubarak ya kara da cewa kuma idan ana damunsa akan maganar Shalele lallai zai warware aurenta akansa kada a mayardashi karamin yaro mana mtwsss, Baba Bashiryace ka saketa dan uwarka, ka dade baka saketa ba, na rantse da girman Allah duk ranar da ka saki yarinyar nan saina tsine maka albarka.
Yana fadin haka ya kashe wayarsa, Baba Bashir da kansa yazo gidan Shalele ya bata hakuri tare da kwantar mata da hankali, kudi masu yawan gaske ya bata sannan ya bata numbersa yace duk abinda take so tayi masa magana.
Godiya Shalele tayi sosai Cikin ladabi da girmamawa, Baba bashir da kansa ya samowa Shalele mai aiki babbar mace mai hankali da natsuwa dan Mubarak duk ya kori ma”aikatan dake gidan yace abar Shalele sai ta gane bata da wayau.
Mai gida kuwa dariya kawai yakeyi duk da baiji dadi abinda Mubarak yayi wa Shalele ba yana addu”a Allah yasa Shalele ta aihu lafiya Mubarak zai gane shi karamin dan iska ne.
Cikin Shalele wata bakwai Mubarak ya dawo kuma ya kori mai aikin da Baba b ya kawowa Shalele shi kuma ya hura wutar azabtar da Shalele.
Kuma yayi juyin duniya suje asibiti a saka mata ruwan nakuda ta haihu yasan idan ta haihu dan zaizo a mace tunda bai isa aihuwa ba, amma sam Shalele ta birkice idanuwa cewa bazata je ba tace wallahi saida ya saketa, wannan abu ya kara kartarzuciyar Mubarak dan haka yaci gaba da balbalawa Shalele azaba babuji ba gani, “
Itama kuma taci damara sukaci gaba da gasa juna tunda taga abun nasa bamai karewa bane, ta shafawa idonta kwallin rashin mutunci, idan ya fada mata ciwo itama saita fada masa mutuwa.
Yace kuma ta bar masa gidansa tace wallahi babu inda zataje saidai shi idan ya gaji da ganinta yabar gidan, amma itakam zama daram daram yanzun ma ta farajin dadin zama a gidan.
Fitina sukeyi sosai fa,jin tashin hankalin yayi yawa yasa Mama tazo dan tafiya da Shalele amma Shalele tace wallahi babu inda zataje tana nan daram, Mubarak kuwa bin Shalele yayi da kallo sai tsinana baki takeyi tana masa rashin kunya wanda idan yayi zuciya ufff daya zai mata saita mutu a wurin,
Mama kuwa ganin Shalele bata taflya yasa ta hakura tayi tafiyarta, kuma ta fadawa gwaggo ta kwantar da hankalinta babu wani abu insha Allah.
Mama tana tafiya Shalele tabar palon Mubarak yabi bayanta da harara tare da cewa sakarar banza kina danya kike wani kokarin tsufar da kanki, zakici ubanki idan kikaje labour room zakiji idan dadi ne aihuwar.
Momy kuwa taji Iabarin Shalele tana da ciki kuma taji dadi sosai, dan haka tajibgo mata kayan jarirai masu kyau da tsada da taje dubai, dan babu sisin Mubarak yace wallahi dan
da za’a aifa ya dade bai tafl tsirara ba sisin sa wallahi bazai iya bayarwa a siyawa abinda Shalele zata aifa ba.
Itama bata wani damu ba, da yayi magana sai tace taji ba komai ciki daine bazata zubar
ba, gida kuma bata bari mutum ko yana tsafi da bakarjaba.
Koda cikinta ya shiga wata tara, Mama ta sake dawowa dan tafiya da ita, amma Shalele tace wallahi fa babu inda zanje Mama kuma wani daina wahalar da kanku, saidai ku tafl da
Mubarak amma badai ni ba.
Mubarak dake zaune a gefe yace kedai ce ya kamata ki tafi tunda nan ba gidanki bane, Shalele tace tou fadamin mai gidan bayan ni? Mubarak yace gidana ne, kuma nine na kawoki dan haka a tafi da tsiyan tsiya a barmin gida.
Dariya Shalele tayi tare da kallon Mubarak tace tunda kake duniya ka tabajin ance gidan namiji? Ai saidai ace gidan mace, yanzun kamar kai ba’a cewa gidan Mubarak saidai kaji ance gidan Shalele ko ace gidan Khadija, gina gidan kawai kayi amma gida babu maishi sai Shalele, karamin namiji dakai kawai mai wa mace gori.
Murmushi Mubarak yayi amma bai sake magana ba, nan Mama ta yini harta tafi Mubarak bai fita ba yana nan zaune ya tsaresu dan kar fada baiji ba.
Bayan sati daya Momy tazo wurin Shalele farin ciki a wurin Shalele ba’a magana, Momy ita da Kamal suka zo amma shi Kamal din bai zoba yana gidansu Mama ya sauka a dakin Gwaggo. A daddafe suka gaisa da Momy domin Shalele tanaji wani bakon yanayi a tattare da ita, Momy ta lura da hakan amma saita dan basar sukaci gaba da firansu.